MATAR GIDA
MATAR GIDA 001
YOTA ID/022
P1
Safiyar lahadi karfe 11:24am na safe,zaune take cikin kitchen kan wata karamar kugerar ruba hannunta riƙe da wata farar roba cikin robar shinkafa ce ƴar gwamnati,cike da nitsuwa take cire wasu kananun kwari dake cikin shinkafar,ƴarta ƴar shekara ɗaya da wata biyar ce ta shigo kitchen hannunta riƙe da wata karamar kofi cikin hausarta da bai fita da kyau ta ce ''Mumy in ca tea'' murmushi Amirah ta yi tare da ajiye robar shinkafar kan carbin ɗin kitchen,har sannan fuskarta dauke da murmushi ta dauke ƴarta mai suna Fauziyya ta ce ''yunwa ki ke ji?" alama Fauziyya ta yi wa mahaifiyarta alamar eh hakan yasa Amira faɗin ''sorry yanzu zan maki tea ko autar Dady'' nan Amira ta shiga haɗawa Fauziyya tea daidai lokacin da ta zuba ruwan zafi cikin kofi ta dauke tea spoon tana juyawa Fauziyya tea mijinta mai suna Ɗalhat ya shigo kitchen ɗin fuskar nan tamau babu fara'a wata farar takarda ya miƙo mata ɗan jimm Amirah ta yi kafin ta sa hannu ta ƙarɓa takardar amma ta ƙasa buɗe saboda fargaba da kuma tsananin tsoron,kafe sa ta yi da idanunta alamar tambaya shima ita yake kallo kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce ''ki je gida na sawwaƙe maki,bazan iya cigaba da zama da ke ba,ƙazantar ki da rashin iya kula miji sun ishe ni ba a kan ki aka fara haihuwa ba,mata da yawa sun haifi ƴaƴa sama da 7 amma basu sake jiki sun sawa kansu lalace da rashin tsafta kamar ki ba''shiru ya yi kamar bazai ce komai ba sai kuma ya ja wani dogon numfashi kafin ya ce ''tun ba yau nake faɗa maki cewar zan iya rabuwa dake kan rashin tsafta amma kin ƙi gyara hali'' nan ma wani shirun ya kuma yi kafin ya ɗan yi ƙasa da murya yana shafa kasimba dake fuskarsa ya ce ''nan da sati uku za'a daura min aure'' yana gama faɗin haka ya fita daga kitchen ɗin
Amirah ta dauki a ƙalla mintina goma tsaye cikin kitchen kamar wacce aka dasa lokaci ɗaya tunaninta ya tsaya cak da gaske yake all this while da yake ce mata zai rabu da ita ya auro wata,me yasa wasu mazan basu da lissafi ne auren ta da Ɗalha shekaru 9 cikin shekarun nan ta haifi ƴaƴa 7 maza huɗu mata uku kusan duk shekara take haihuwa,babu kalar planing ɗinda bata yi ba amma da yaro ya cika watanni takwas zuwa tara sai wani ciki hakan yasa ta hakura daina yin planing ɗin gaba ɗaya, tana iya bakin ƙokarinta waje ganin ta kula da gidan da yara har shima Ɗalha amma gaba ɗaya abubuwa sun ƙi mata saiti tayi ta roƙon Ɗalha ya sama mata ƴar aiki amma yaƙi duk sanda ta yi masa maganar ƴar aiki cewa yake sai da ya ƙaro mata kishiya da zasu riƙa raba kwana hakan zai sa ta sami sauƙin ayyukan cikin wasa yake faɗa mata haka ita ma sai ta biye masa ta ce ta amince ya auro koma wace ita bata da matsala,ƙarancin shekaru da kuma auren wuri da aka yi mata yasa har yanzu ta ƙasa saita gidanta,mahaifiyarta ta rasu tun tana ƴar shekara goma duk ƴan uwanta maza ne su shidda mazaje sai ita kaɗai mace,da su take shawarwarin rayuwarta, bata taɓa kawo zai iya sakinta da gaske ba duba da irin soyayyar da suka yi kafin aure cike da ƙidima zuciyarta ta yi mata nauyi sosai ji take kamar an daura mata dutse a ƙirji,kukan Fauziyya ne ya dawo da ita hayyacin ta hakan yasa ta nufi inda firiji yake ta buɗe firijin tare da daukan ruwar gora ta xubawa Fauziyya ruwan cikin tea yadda zafin tea zai yi mata daidai sha,ta mikawa Fauziyya kofin ta ce ''maza je ki parlour'' babu musu Fauziyya ta karɓi kofin zuwa parlour wasu hawaye masu zafi suka rinƙa zuba daga idanun Amira haka ta daure ta gama dafa abinci saboda yaranta bayan ta gama girkin ne ta zuba masu sun ci ta kuma yi masu wanka babban ɗanta Muhammad Sudais da me bin sa Afef suka yiwa kansu wanka,bayan ta gama masu wanka ne ta zuba kayan wanke su cikin injin wanken kaya ta cewa Sudais da injin ya gama wanke kayan ya kwashe ya baza su ƙara shan iska daman shi ke yi kullum,duk abinda take Ɗalha na zaune cikin parlour yana danna wayarsa kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci chat yake kuma yana jin dadin chat ɗin,Amirah ta haɗa yaranta duka cikin ɗakinta ta yi masu nasiha ta ce za ta yi tafiya saboda haka su kula da ƙansu sosai ta yi masu nasiha,Rayyan ɗan shekara shidda ya fara kuka ya ce ''Mumy ni zan bi ki'' nan ta shiga rarrashinsa da ƙar ta samu ya daina kuka,Allah ya taimaka tuni Fauziyya ta yi barci hakan yasa Amirah daukar jakarta da ta zuba kaya kala huɗu a ciki ta fita zuwa parlour sai a sannan ne Ɗalha ya kalle direction ɗinta ganin tana shirin fita ita kaɗai ba tare da ce masa komai ba yasa ya ce ''wa zai kula da Fauziyya?" ya kare magana fuskarsa babu alamar wasa'' murmushin takaice Amirah ta yi ta ce ''aiy kana nan zaka kula da ita'' cike da ɓacin rai Ɗalha ya tashi zaune daga kwanciyar da ya yi kan kugera 3 siter ya ce ''nono gare ni da zan bata yarinyar da ba ki yaye ta ba'' a takaice Amira ta ce ''na yaye ta ɗazu''daga haka ta fita daga parlour cike mamaki Ɗalha ya bi bayan Amirah da ido baki buɗe
SHUUKRAN