FreeArewaPen original
MATAR GIDA
- 1views
- 50chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I'm a Author Ni marubuciya ce
Sample · MATAR GIDA
MATAR GIDA 001YOTA ID/022P1Safiyar lahadi karfe 11:24am na safe,zaune take cikin kitchen kan wata karamar kugerar ruba hannunta riƙe da wata farar roba cikin robar shinkafa ce ƴar gwamnati,cike da nitsuwa take cire wasu kananun kwari dake cikin shinkafar,ƴarta ƴar shekara ɗaya da wata biyar ce ta shigo kitchen hannunta riƙe da wata karamar kofi cikin hausarta da bai fita da kyau ta ce ''Mumy in ca tea'' murmushi Amirah ta yi tare da ajiye robar shinkafar kan carbin ɗin kitchen,har sannan fuskarta dauke da murmushi ta dauke ƴarta mai suna Fauziyya ta ce ''yunwa ki ke ji?" alama Fauziyya ta yi wa mahaifiyarta alamar eh hakan yasa Amira faɗin ''sorry yanzu zan maki tea ko autar Dady'' nan Amira ta shiga haɗawa Fauziyya tea daidai lokacin da ta zuba ruwan zafi cikin kofi ta dauke tea spoon tana juyawa Fauziyya tea mijinta mai suna Ɗalhat ya shigo kitchen ɗin fuskar nan tamau babu fara'a wata...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.