Chapter 12
by @barista
BIYU A ƊAYA
(Don't judge a book by its cover)
Page 12
Sayyada barrister
***
YOTA 13
TEAM FIVE INK LEGENDS
Yamma lis Dr Waahab ya tashi daga bacci, ya faɗa toilet ya sake watsa ruwa, haka yake ko ya yi wanka da zaran ya yi bacci ya farka yake sake yin wanka, yana da tsafta sosai tsam baya son datti. Ya ɗauro alwala ya fito ya gabatar da sallah la'asar duk da ya maka sannan ya janyo wayar sa ganin missed calls yasa ya buɗe yaga ƴan'uwan sa ne, Daddy, ya Sa'eed, Mamie da Abbie da sauran kannensa, Abbie ya fara kira, bugu biyu ya ɗauka yana cewa
"Likita kun sauka lafiya?"
"Abbie lafiya kalau tun tuni muka iso bacci ne ya ɗauke ni"
"Ai dole likita kun gaji ai, to madallah tun da kun isa lafiya"
"Alhamdulillah Abbie ya mutan gida?"
"Kowa yana lafiya, Hajjiya ma yau aka tafi da ita Abuja"
"Allah sarki Allah ya bata lafiya, Sa'eed yana Abuja tare da su ko?"
"A'a da Qaseem suka tafi, Sa'eed bai samu excuse ba a wajen aiki"
"Ayya sha'anin aiki sai hakuri, Daddy ma ya kira ni, bari na kira yanzu"
"Ai gashi nan kusa ba sai ka kira shi ba, zan miƙa masa wayar"
Kafin ya yi magana yaji sauƙar muryar Daddy yana cewa
"Ai ni na jima da sanin an min kwacen ɗa"
Murmushi Dr Waahab Waseem KIRAWA ya yi sosai yana sosa keyarsa kamar Daddy yana ganinsa ya ce
"Daddy barka da hutawa"
"Yawwa Waahab, ya Ghana kun isa lafiya"
"Alhamdulillah gamu a Ghana"
"To ma sha Allah tun da komai lafiya, ubangiji ya yi jagora"
"Amin, na gode Daddy"
Sun ɗan taɓa hira sannan ya kashe ya kira Mamie, suka gaisa sannan ya kira Sa'eed suka gaisa, haka ya dinga bin duk wanda ya yi masa missed calls yana kiran su ....
Nocking Kofar ɗakin ya ji ya ta shi ya buɗe, ma'aikaciyar hotel ɗin ne tsaye ɗauke da ƙaramin plate da aka haɗa coffee, ta miƙa masa kamar ba zai jarɓa ba ya karɓa tare da cewa
"Thanks"
Kwarjininsa yasa ta kasa magana ta yi saurin barin wajen, ya ajiye ko ta kansa bai sake bi ba, ya sake jin nocking ya buɗe, Dr Faisal ne ya koma ciki shima ya shigo tare da cewa
"Ai zuwa na yi na duba ko kana raye"
Murmushi sosai Dr Waahab ya yi har fararen hakwaransa suka bayyana, ya zauna sosai bakin bed ya ce
"To ina raye ban mutu ba"
Shima Dr Faisal ya yi dariya ya ce
"Kana ƙaunar bacci sosai"
"In na samu chance ba, in ban samu ba sai na wuni na kwana ido biyu"
"To ai haka lamarin gauro yake"
"Oh! Gori ko?"
"So nake ka fusata ka yi aure"
"To ina matar ma"
"Za a samo ta ko anan muka samu masallaci za mu nufa a ɗaura kawai"
"A'a raba ni da matan nan, a cen Nigeria zan nema kuma na aura"
"To Allah ya yi zaɓi mafi alkhairi"
"Amin Dr Faisal, me labari neh"
"Yanzu Oga yake cewa an shirya bana wajen cin abincin dare anjima duk za mu fita mu je wajen"
"To kenan ba a nan hotel ɗin bane?"
"Eh haka ya ce"
"To hakan ma ya fi, don ni bana son ma'aikatan hotel su kawo min abinci ko abin sha"
"Ai ko za ka gamu dasu kala kala in dai a hotel ka ke"
"Dakatar dasu zan yi"
"Aboki me yasa baka son masu aiki, is there something behind?"
"There's friend, there's a lot of secret behind"
"Umm na fahimta amma ka sani, ba duk aka taru aka zama ɗaya ba"
"Yeah friend amma in kare ya cije ka sau ɗaya, ba za ka sake bari ya sake cizon ka ba"
"Haka ne, naga coffee kai ka haɗa?"
"A'a ma'aikaciyar hotel ce ta kawo min"
"You see friend, ba za ka gujewa hakan ba"
Sun jima suna hira, kiran sallar magriba ne yasa suka ɗaura alwala a toilet sannan suka fito suka tadda sauran likitoci suka sun fito yin sallah, tare suka fito neman masallaci ba wahala suka samu, sai da suka isar da ishai sannan suka dawo hotel daga nan suka shirya tafiya wajen cin abinci...
************************************
ALAJA SPECIAL RESTAURANT
Zuwa wannan lokacin komai ya yi ready jiran isowar baƙin ake yi, sun kunna deep light na bangaren dining area, hakan ya sake ƙarawa wajen kyau, an hana kowa shigowa. Haka ma farfajiyar restaurant ɗin an gyara shi sosai ga fararen ƙwayayyakin wuta da suka haskaka wajen, tamkar a turai ake haka wajen ya koma.
Dr Waahab suka iso restaurant ɗin kallon sign board ɗin ya yi yaga an rubuta ALAJA SPECIAL RESTAURANT, ya maimaita sunan kusan sau uku, a ransa har suka shigo ciki, a farfajiyar restaurant ɗin motar tayi parking suka fito sai mamakin gurin suke yi har suka shigo reception a ka yi musu jagoranci zuwa ciki, dining area ya matuƙar burge su suka zauna, nan su Bilqees suka fara serving nasu, Dr Waahab bai ɗago ba har aka kammala kawo musu duk abin da already shi aka ce su shirya musu. Bilqees tana bin dukkanin table ɗin tana ajiye musu ruwan roba suna yi mata godiya har mamaki ta ke yi, tun da ta fara aiki a restaurant ɗin nan ba a taɓa yin customers sun gode mu su ba sai wannan karon, ko daga ina suke.
Ta iso table dake gaban wani da taga ana girmama shi, sai dai tun da ya shigo ta fahimci bai yi magana ba kamar yadda sauran su ke yi, suna nishaɗi suna hira. Ta ajiye masa bottle water, tana ƙoƙarin barin wajen ta ji muryar sa kamar me raɗa ta yi magana ba tare da ya ɗago ba ya ce
"Ina buƙatar shayin gargajiya, in akwai"
Shiru ta yi tana kallon table na shi sai a lokacin ta fahimci bai ma fara cin komai ba yadda aka ajiye haka yake ko cukali bai taɓa ba...
Jin shiru ba a amsa ba yasa ya ɗaga da idanunsa masu kaifi da ƙwarjini ya kalleta dasu nan ta nutsu tare da cewa
"To Yallaɓai"
Ta yi sauri ta bar wajen, ya sauke numfashi ya maida hankalinsa kan wayar sa....
Bilqees ɗakin Alaja ta shiga, bayan ta yi nocking ta bata izinin shigowa, ta turo ƙofar ta shigo ta ɗan rage tsawon ta saboda ganin Alaja a zaune, cikin girmamawa ta ce
"Maa ana buƙatar shayin gargajiya yanzu"
"Waye?"
Cewar Alaja, Bilqees ta rasa waye za ta ce, saboda suna da yawa babu yadda za ta yi wa Alaja bayanin shi...
"Ke bana son shashanci, kin yi magana ina tambayar ki kuma kin yi shiru"
"Uhm ɗaya daga cikin ɓakin da suka shigo ne"
"To ki hanzarta ki dafa masa, kamar yanda ya buƙata"
"Ok Maa"
Tana shirin ficewa daga ciki, Alaja ta ce
"Duk abin da suke buƙata a basu ba sai an zo an tambaye ni ba"
"Ok Maa"
Ta fice kai tsaye ta shige kitchen cikin sauri ta ɗaura shayin gargajiya, ta yi masa haɗi na musamman, citta, kananfari, girfa, lemon grass, na'ana , habba, hulɓa, green tea da red tea da sugar ta haɗa su waje guda ta dafa su, sai da komai ya haɗe ya dahu sannan ta zuba a madaidaicin tea flask tare da madaidaitan cups ta ta jere a kan madaidaicin plate sannan ta fito tabar cikin kitchen ɗin...
Laraba da Jummai da suke zaune suka zuba mata ido tun shigowar har ta kammala suna taɓe baki ƴar iya ta shigo za ayi iyayi...
"Na taɓa ki da alkhairi"
Cewa Jummai wa Laraba.
"To ina jinki boom"
"Au sunan da ki ka bani, to ke kuma gurnet"
"Na gode, me ki ke shirin ɗanawa yarinyar nan? Tafa ishe ni"
"Kwantar da hankalin ki, wani idea ne ya faɗo min, amma sai gobe zan faɗa miki sai mu tsara plan namu"
"Ok Allah ya kai mu, amma don Allah ki hanzarta bana son ganinta kwata kwata"
"Kwantar da hankalin ki, saura kiris"
Suna ta hira sakaninsu sauran ma'aikatan suna jin su babu wanda ya soma baki, ai ko suna magana yanzu sai su haɗa musu sharri a wajen Alaja ta kora su....
Bilqees ta shigo dining area kai tsaye ta wuce table na mutumin da ya ce yana son shayin gargajiya, tana isowa ta ajiye masa, sai a lokacin ya fara cin abincin saɓanin wasu har sun kammala, ta soma buɗe tea flask zata zuba masa amma ya ɗaga mata hannu alamar ta bari zai yi da kansa, shiru bai ce ya gode ba, ta taɓe baki a ranta ta ce ko shi ba irin su bane baya godiya, uhm wannan cloud face na shi ma ai ba zai bari ya yi godiya ba, ta juya zata tafi ta ce muryar
"Thanks"
Ta juyo taga ko kallon inda ta ke bayyi ba hankalin sa yana kan zuba tea ɗin, ta juya zuwa in da wani ya yi mata magana, sai taga da mace yake zaune, ta iso tare da cewa
"Me kuke buƙata?"
"Wannan matata ce, amarya ta"
Ta taɓe baki to ita me ya shafeta da wannan maganar, amma a bayyane ta ce
"Ok Yallaɓai me ta ke so?
"Dr Faisal sunana ba Yallaɓai ba"
"Ok sorry, Dr Faisal"
"Yawwa tana da ulcer bata cin abu me yaji a sabo mata komoniya mara yaji"
"Dr Faisal ban gane sunan abin ba"
Ya juyowa Amaryar ta shi ya ce
"Beb ya ake kiran sunan abin bayan wanda muke kira?"
"My laban ( my milk) ban sani ba, mu da haka muke kiran shi"
"Yo in ba abun ku ba, ina zata sani nan ƙasar ku ne, ai bayani za ku yi mata ta gane"
Cewar Ismail, Dr Faisal ya juyo ya kalle shi tare da cewa
"To malam me bayani an gode"
Ita dai Bilqees sai bin su da idanu take yi, Dr Faisal ya ce
"Da kayan ciki ake yin shi, babu romo sosai za ki ga ya kame jikin shi, ba kamar pepper soup ba"
"Oh! Na gane babu shi sai pepper soup mu ke da"
"To samo mata mara yaji"
"To"
Ta faɗa ta juyo zuwa kitchen, babu jimawa ta fito dashi worming tayi ta kawo, nan ya yi godiya yana baiwa Beb, haka ita da sauran suka yi ta bi inda me buƙatar abu ya faɗa a kawo masa, mamaki ɓakin nan su ka yi, akan karamcin ma'aikatan wannan restaurant ɗin....
Bilqees ta iso ɗakin ALAJA ta taddata zaune, jiki a sanyaye ta ce
"Maa zan koma gida dare ya yi"
"Eh mu ɗin kuma ba mutane bane anan za mu kwana"
Cewar Alaja cikin ɓacin rai, Bilqees ta sudda kai ƙasa cikin sanyin murya ta ce
"A'a Maa, ba haka nake nufi ba, ina tunanin Mamata a gida ne"
"To babu inda za ki je har sai mun tashi ba ki ɗaya mu tafi gida tare"
"Uhm"
Kawai ta faɗa ta fito dining area a lokacin sun kammala cin abincin su, suna hira ban da wannan mutumin da ta kawowa shayi, tun da suka shigo bata ga ya yi magana ba har wannan lokacin, tana tsaye ko za a buƙaci wani abu sai taga Dr Faisal ya mik'e ya iso ya yi masa magana, sai taga ya yi murmushi tare da jinjina kai, ya mik'e duk suka mik'e suka fito, kai tsaye suka wuce cikin motar su suka fice.
ALAJA ta fito tana karewa wajen kallo, ganin komai ya tafi kan tsari, sun shigo lafiya kuma sun fita ba ɓacin rai yasa ta sauke numfashi tare da cewa, a tattare komai sannan kowacce ta tafi ta sallame ta.
Cikin mintina kaɗan an tsaftace ko'ina sannan suka fito aka rufe restaurant ɗin suka dawo gida.
A bakin ɗan madaidaicin verender Bilqees ta tadda Mamanta zaune, ta iso tare da cewa
"Mama...
Kan ta ƙarasa Mamanta ta ce
"Me yasa ki ka yi dare?"
"Baƙin aka yi shiyasa Alaja ta ce mu zauna sai sun tafi"
"Maman Bilqees, mun dawo woo, yau aiki ya yi yawa mu ka zauna sai yanzu muka dawo"
"Bilqees, ki shiga ciki zan yi magana da Alaja"
"To Mama"
Ta shiga cikin, Alaja ta wuce side nata, Maman Bilqees ta bi bayanta, suna shiga Maman Bilqees ta ce
"Amma ai kin ji na ce zan yi magana dake"
Juyowa Alaja ta yi tana karewa Maman Bilqees kallo, tana kalau kuwa yau ita ta ke yi wa magana kai tsaye da fushi.
"Maman Bilqees umurnin tsayuwa ki ke bani ko neman na tsaya ki ke?"
"Duk wanda ki kayi daidai ne, tsayuwa sunanta tsayawa"
"Heheheeee Maman Bilqees, me yasa ki ke jin tsoro? Na ce me yasa ki ke jin tsoro?"
"Ba tsoro nake ji ba, so nake komai ya tafi daidai"
"Ya isa haka, enough Maman Bilqees, kina tunanin ban san me nake yi bane? Ko kuma ni ma shashasha ce kamar ki. To ki sani an zo in da za ki kai ni bango, in kuma ki ka ce za ki ja dani sai na nuna wa Bilqees matsayina a wajenta, na kuma saka Almakashi na datse alakar dake sakaninku"
"A'a Maman Bilqees, kada ki yi haka"
"Ashe kina da hankali, to ki sani don na riƙe Bilqees har wannan lokacin a restaurant hakan ba zai sauya alkawarin da na yi ba, don haka ki fice min"
"Zan tafi amma ki sani, zamanta a wajena ya fi dacewa akan a wajen ki, sannan a yarjejeniyar da mu ka yi babu aikin dare, da safe sai kuma yamma ta dawo gida"
"A lokacin tana karatu ne, amma yanzu ta gama, dole mu yi aiki tare, Bilqees tana da baiwar da Allah kaɗai ya sani, kuma zuwanta RESTAURANT nawa komai ya sauya, kada ki ga ina yi mata wasu abubuwan ki ɗauka bana sonta, a'a ina sonta, kada ki ce ke kin fini sonta"
"Uhm na san abin da yasa ki ke yi mana haka, saboda yarjejeniyar dake sakanin mu ne, amma zan yi ƙoƙarin na kawo ƙarshen komai"
"Maman Bilqees kina bani dariya, ki yi kada ki fasa, ni ma zan yi nawa, sannan burin da nake son cikawa ya kusa cika kuma ban da wasu satika komai zai sauya"
"Bilqees ba za ta taɓa zama a ƙarƙashin ki ba da yardar Allah"
Maman Bilqees tana gama faɗin haka tafi, ta dawo ɗaki ta tadda babu Bilqees, ta sauke numfashi ganin shigowar ta, tare da cewa
"Daga ina ki ke?"
"Toilet"
"Kin ci abinci?"
"Eh"
Ta faɗa, Maman Bilqees ta ce
"To ki kwanta ki huta gajiya"
Ta sauya kayanta jiki a sanyaye, ta dawo ta kwanta, a hankali ta furta
"Yarjejeniya"
Baccin gajiya ya ɗauke ta.......
*********************************
International hotel
Kwance yake kan bed ya lumshe idanunsa, duk da ba bacci yake yi ba. Tun da suka baro Alaja restaurant ya dawo yake jin kasalar da yake tare da ita ta wassake amma ya fi tunanin shayin da ya sha ne ya sauke nasa duk wata kasala da yake tare da ita, gashi ya hana shi bacci, ya buɗe idanunsa ya kurawa sling idanu kamar me nazari, sai dai baya iya tuna komai.
Ya mik'e ya sauƙo daga kan bed, ya zura jallabiyansa akan gajeren wondo da yake jikinsa da vest ya fito tare da rufe side nasa, ya fito har wajen hotel ɗin yana tattaki har bakin titin yana kallon mutane suna harkokinsu hankali kwance yana ta mamaki kusan 11:00 pm fah...
Ya dawo ya zauna kan wasu dakali da ya gani a wajen, ya kurawa titi idanu yana ci gaba da kallo, har 12:00am gani an fara watsewa yasa ya dawo cikin hotel ɗin, ya shigo side nasa ya cire jallabiyansa ya kwanta sai a lokacin bacci ya yi awun gaba da shi...
______________________________
Sannun mu fa da gajiyar zuwa Ghana, na san fan's na BIYU A ƊAYA ba su bar ni na taho ni kaɗai ba, tare mu ka taho.😎
Ya muka ji da girkin ALAJA SPECIAL RESTAURANT da fatan ya yi muku daɗi 😅
To a gwada dafa shayin gargajiya da Bilqees ta dafawa babban baƙon mu, yana ƙara lafiya sosai a jikin ɗan Adam, musamman manya waɗanda shekarun su ya ja, kada su saka red tea su yi amfani da green tea ma ya wadatar.🥰
Ko dai mu ci gaba da tafiya, wannan labarin na musamman ne, ba za ku yi nadamar karanta labarin ba.
Comments and share fisabilillah