SAUTIN KARSHE

Chapter 20

by @amanarcool323

SAUTIN ƘARSHE

BY AMANARCOOL

YOTA/021

Under Yota's Amazing Pens 

Book 1 

Page 20


Ilham wani baƙon al'amari ta ji yana ziyartarta, gabaɗaya rikicewa ta yi, ta fara ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ta kasa, tana jin yadda Sudais yake yi mata abubuwan da ko a mafarki ba ta yi tunanin zai yi mata ba, ganin babu sarki sai Allah ya sa dole ta haƙura ta daina mutsu-mutsun da take yi. Zabura ta yi da ƙarfi ta rirriƙe shi a lokacin da ta ji wani azababben zafi yana ratsata, fashe masa ta yi da kuka tana girgiza kanta. Hannuwanta ta sa ta fara ture shi amma ko gizau bai yi ba, haƙura ta yi ta ci gaba da kukanta. Sudais bai bar ta ba sai da ya tabbatar da ya mayar da ita cikakkiyar mace sannan ya sarara mata, mirginawa gefe ya yi yana sauke numfashi. A hankali ya sauka daga kan gadon ya buɗe ƙofar ɗakin ya fita, Ilham tana jin fitarsa ta sake fashewa da kuka, ta daɗe kwance a gurin tana kuka sannan ta tashi da ƙyar ta shiga toilet ta tsarkake jikinta ta fito, canza wata rigar bacci ta yi, sannan ta kwanta tare da jawo bargo ta rufe jikinta. Nan take wani zazzafan zazzaɓi ya rufe ta.

Sudais kuwa yana fita ɗakinsa ya je, shi ma toilet ya shiga ya yi wanka sannan ya dawo ya zauna bakin gado yana tunani abin da ya shiga tsakaninsa da Ilham, wata irin kunya ya ji ta kama shi. Ya ji takaicin kansa da ya kasa sarrafa kansa har zai da ya je ya zubar da class ɗinsa a gurin waccan yarinyar, tsaki ya yi ya ce "Duk da haka ba zan ba ta fuskar da za ta raina ni ba". Murmushi ya yi ya shafa sajensa ya ce "Kodayake raini na nawa kuma, tunda har na iya je mata da wannan gagarumin abin." Ya yi maganar yana kallon kansa ta cikin madubi, lokaci ɗaya fuskarsa ta sauya, ya runtse idanunsa da ƙarfi sakamakon tuna wani babban al'amari da ya faru da shi. A fili ya ce "Ya Allah! Duk da shauƙi da farin cikin da na ji yau na kasancewata tare da Ilham bai kai...." Sai kuma ya yi shiru ya kasa ƙarasa maganar, ya buɗe idanunsa, ya furzar da wani iska mai zafi. Kwanciya ya yi yana jin wani irin raɗaɗi a zuciyarsa. Tabbas bai taɓa ganin tozarci ba kamar wanda ya gani a rayuwarsa. 

....

Misali ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare, Ma'u na zaune ta kasa bacci, ta tsurawa guri ɗaya ido ko ƙiftawa ba ta yi, haka kawai take jin wani irin zafi a zuciyarta da ta kasa tantance kona me ye, ba ta yi aune ba ta ji hawaye na bin fuskarta, numfashi Abida ta fara ji yana tashi sama-sama. Da sauri ta haske ta da fitila, nan taga jikinta na girgiza. Tashi ta yi cikin azama ta isa inda take tana faɗin "Subhanallah! Abida ba dai jikin ba ne?" Cikin bacci Inna ta ji murya Ma'u, "Ke Ma'u lafiya kike surutu a cikin daren nan?" "Inna jikin Abida ne ya tashi." Da sauri Inna ta miƙe tsaye tana faɗin "Innalillahi yanzu kuma?" Ta yi maganar tana isa inda Abidar ke kwance, yanayin yadda jikinta ke jijjiga ba ƙaramin tsoro suka ji ba, da sauri Inna ta fita ta je ta ta so da Aliyu. Ko da ya shigo ɗakin yaga halin da take ciki shi ma ba ƙaramin tsoro ya ji ba, tsayuwa ya yi a kanta yana binta da kallo. Inna ta ce "Haba Gadanga ba tsayuwa za ka yi ba, ka fita ka nemo abin hawa mu mayar da yarinyar nan asibiti." Aliyu ya ce "To shikenan Inna, wallahi jikina ne ya yi sanyi gabaɗaya, bari in je gidan maƙocinmu Habu in yi masa magana sai ya zo ya kai mu asibiti." Daga haka ya fita, yana fita Ma'u ta ce "Inna don Allah kar a mayar da ita asibitin nan"

"Wace asibitin?" 

Ma'u ta ce "Wadda aka kai ta farko, don Allah a canza mata asibiti."

"Soboda me kika ce haka?" Inna ta tambaya tana kallonta. Ta ce "Ni dai Inna ba na son mu koma can ne, haka kawai na ji na tsani asibitin ban san dalili ba."

Cikin hasala Inna ta ce "Rufe mini baki, ke dai Ma'u kin shiga uku wallahi. Allah ya yi miki sauƙin wannan halin. Yanzu duk alkhairin da mutanen nan suka yi mana ba ki gani ba? To wallahi a can za a mayar da ita." 

Ma'u ta ce "Ni dai wallahi Inna..." "Ba za ki yi mini shiru ba ne?" Inna ta katse ta, Aliyu ne ya shigo da sallama, ya ce "Inna ɗakko ta mu tafi." Ma'u ta dube shi ta ce "Don Allah Yaya kar a koma da ita asibitin nan ta farko, a mayar da ita ta gwamnati mana." Aliyu ya ce "Eh, ai da ma ta gwamnatin za mu je" Inna ta yi sauri ta ce "Ba za a je ta gwamnatin ba, dole inda aka yi mata aiki a farko nan za mu koma." Yanayin yadda ta yi maganar babu alamar wasa a fuskarta ya sa Aliyu bai ce mata komai ba, ya ɗakko Abida da kansa ya fita da ita, Inna ta ɗaukar musu abin da za su buƙata suka fita, rufe gidan suka yi, kai tsaye suka nufi asibitin da a ka yi wa Abida aiki a farko. 

.....

Cikin ikon Allah ko da Ilham ta tashi sallar asuba zazzaɓin ya sauka, sai dai jikinta gabaɗaya ya yi mata tsami, ta ɗingisa ta shiga toilet ta yo alwala ta fito, bayan ta idar da sallah ba ta kwanta ba. Duk da yadda take jin jikinta haka ta daure ta gyara ɗakinta da falo, ta saka turare, nan take gidan ya ɗauki ƙamshi, sai da ta gyara ko ina sannan ta koma ɗakinta ta kwanta. Ko da Sudais ya dawo daga masallaci ya yi mamakin ganin falon a tsaftace duk da dai da ma can bai da wani datti, amma alamu sun nuna an sake gyara shi tunda ga ƙamshin turare nan yana tashi. Kallon ƙofar ɗakinta ya yi, ya yi murmushi ya shige bedroom ɗinsa. Ko da Zahra ta zo kawo musu breakfast ta yi ta knoking ba a buɗe ba, gajiya ta yi ta koma da abincin, sai wajen ƙarfe tara da rabi Ilham ta farka daga baccin da take yi sakamakon yunwar da ta ji ta adda ba mata, tashi ta yi ta saka doguwar rigar abaya da mayafinta ta fito. Sanin da ta yi babu abinci a kitchen, kuma yadda take jinta ba za ta iya wani dogon motsin da za ta dafa wani abin ba, ya sa ta nufi gurin Mammy ba tare da ta tsaya sanar da Sudais ba. Suna zaune a falo suka ga Ilham na saukowa a hankali take tafiya, kallo ɗaya Mammy ta yi mata ta fahimci halin da take ciki, murmushin jin daɗi ta yi a zuciyarta ta ce "Alhamdulillah." Ilham ta gaishe da Mammy, Zahra ta dube ta ta ce "Sannu Anty, shi ne na ie kai muka abinci sai knoking nake yi kuka yi mini banza." 

Ilham ta yi murmushi ta ce "Yi haƙuri ƙanwata, wallahi ban ji ba ne, ko da kika je ina bacci da yake ba na jin daɗi." 
Zahra ta ce "Subhanallah sannu Anty, Allah ya sauwwaƙe". Mammy na murmushi ta ce "Zahra tashi ki ɗakko mata breakfast ki jawo mata nan ta ci, idan ta gama sai mu tafi asibiti a duba lafiyarta." Tashi Zahra ta yi ta je ta haɗo mata abin karin ta kawo mata nan, Ilham na zaune tana karyawa sai ga Sudais ya fito, gaishe da Mammy ya yi ya nemi guri ya zauna, Zahra ta gaishe ya amsa yana basarwa. Mammy ta ce "A kawo maka breakfast ɗin ne?" Girgiza kai ya yi ya ce "A'a Mammy bar shi, idan na je office zan karya a can." Yana nan zaune Ilham ta gama cin abincin, Mammy ta ce "Bari in shirya sai mu tafi asibitin ko." Da sauri Sudais ya kalli Ilham, sannan ya mayar da kallonsa ga Mammy ya ce "Asibiti kuma, waye ba lafiya?" 

Mammy ta ce "Ilham zan kai a duba ta"

Ya ce "Ce miki ta yi ba ta da lafiya?"

Mammy ta ce "A'a, alamun hakan dai na gani a tattare da ita." Sudais na jin haka ya sunkuyar da kansa ya kasa magana, wata irin kunya Mammy ya ji, ko ba ta faɗa ba ya san ta fahimci abin da yake faruwa. Cikin jin kunya ya ce "Mammy ina ga ba sai kin je ba, bari in kai ta da kaina." Ya yi maganar yana kallon Ilham ya ce "Tashi mu tafi." Tashi ta yi, Mammy ta ce "Shikenan ka hutar da ni." Bai tsaya ba ya fita, Ilham ta bi bayansa. Mammy kuwa dariya ta yi ta ce "Allah ya kyauta."

Suna tafiya a hanya babu zato ta ji ya ce "Wato sanar da Mammy kika yi ko? Illar auren yara kenan. Ke ba za ki iya rufe wannan sirrin ba ne har sai kin bari wasu sun sani?" Ilham ta marairaice murya ta ce "Ban gaya mata komai ba, ita ce ta ce za ta kai ni asibiti."

Ya ce "Yi mini shiru, ai ko ba ki faɗa ba, kin yi abin da zai sa ta gane ne." Shiru ta yi ba ta ce masa ƙala ba, Sudais ya shiga mita har suka isa wata pravit hospital, aka duba Ilham babu wata matsala, zafi ne kawai take ji kasancewar wannan ne na farko, kuma sannan ta ɗan ji matsi a hannun mijin nata, magunguna suka ba ta, sannan ya mayar da ita gida. Ba tare da ya shiga ciki ba ya ajiye ta a ƙofar gidan ya wuce gurin aikinsa.

.....

Tun jiya da suka zo da ita aka shiga cikin wani ɗaki da ita har yanzu ba a ce musu komai ba, hankalinsu ya tashi sosai, gabaɗayan su sun yi zuru-zuru barin ma Aliyu, yana dauriya ne kawai saboda jarumta irin ta namiji, wata nurse ce ta zo za ta wuce da sauri Inna ta ce "Don Allah ƴata ki taimaka mana." Zuhura ta tsaya tana kallonta ta ce "To Mama wane taimakon?" Inna ta ce "Yarinya ce muka zo da ita tun jiya cikin dare aka shiga da ita waccan ɗakin har yanzu ba a ce mana komai ba." Ajiyar zuciyai Zuhura ta sauke, ta kalli Ma'u da ta yi kicin-kicin da fuska ta ce "Ita ce wadda aka shigo da ita wuraren ƙarfe ɗaya na dare?" Da sauri Inna ta ce "Eh ita ce"

"Ok ina zuwa" shi ne abin da Zuhura ta ce ta nufi wani office. Da sallama ta shiga, ta tarar da Dr ɗin zaune yana duba wasu takardu, fuskarta babu walwala ta ce "Barka da wannan lokacin Sir" ya ɗago da kansa ya kalle ta ya ce "Yawwa barka, lafiya dai Zuhura naga ganki cikin wannan yanayin?" Ƙara ɗaure fuskarta ta yi ta ce "Sir da ma na zo ne akan batun yarinyar nan da aka zo da ita jiya da daddare, iyayenta duk sun damu suna son su ji halin da take ciki, sun ce tun jiya ba a ce musu komai ba." Cire gilas ɗin fuskarsa ya yi, ya ce "Abida Aliyu?" 

Zuhura ta ce "Eh Sir, ina tunanin ita ce." 

Dr ya ce "Subhanallah! Da ma ba a sanar da su ba? Ai Allah ya yi mata rasuwa ɗazu da misalin ƙarfe takwas na safe, ya aka yi ba a gaya musu har yanzu?" Ya yi maganar yana kallon agogon hannunsa ya ga ƙarfe goma da minti goma. Zuba masa ido ta yi tana kallonsa, ganin irin kallon da Zuhura ke yi masa sai da gabansa ya faɗi. Ya ce "Zuhura lafiya kike bina da wannan kallon?" Cikin damuwa ta ce "Sir ba a kyautawa bayin Allahn nan ba. Yanzu ni taya zan je in sanar da su cewar yarinyar nan ta rasu? Wallahi ba zan iya ba." Ba tare da nuna damuwar komai ba ya ce "Muje ni in sanar da su" daga haka ya bar office ɗin, bin bayansa ta yi jiki a sanyaye. Wajen su Inna ya je, ya dube su ya ce "Mama don Allah ku yi haƙuri, na rashin sanar da ku da ba a yi da wuri ba. Mun tsaya kammala cike-ciken da ya kamata ne, ina mai baƙin cikin sanar da ku Allah ya yi wa yarinyar nan rasuwa ɗazu". Runtse ido Aliyu ya yi, wanda zuwansa kenan wajen saboda ya fita waje yin wani uzurin. "Inna lillahi wa inna ilaihim raji'un" shi ne abin da Inna take ta nanatawa, lokaci ɗaya hawaye suka wanke mata fuska. Ma'u kuwa kasa ƙwaƙwaran motsi ta yi, ta kafi Dr nan da ido, Zuhura kuwa sunkuyar da kai ta yi ƙasa tana jin wani irin ɗaci a zuciyarta, tunanin abin da ta gani jiya ta yi, cikin zuciyarta ta ce "An cutar da ku sai dai Allah ya saka muku."

Dr na ƙoƙarin wucewa ne Aliyu ya ce "Za a iya bamu gawarta yanzu mu tafi gida da ita?" Dr ya ce "Eh za ku iya tafiya da ita gida biyo ni muje." Jiki a sanyaye ya bi bayansa, babu ɓata lokaci aka basu gawar Abida suka tafi gida da ita. 



Sai kuma Monday idan Allah ya nufa, amma idan naga ruwan comment da yawa zan iya ba ku gobe da jibi.

Amanarcool
***