HASASHEN SOYAYYA

Hs 20

by @legendspen

_Page 20_


A cikin kwanaki ƙalilan Habiba ta fita a hayyacinta, ta rame ta canja gaba ɗaya, kuma hakan bai dakatar da mahafinta kan ƙudirinsa na aurar da ita ga mutumin da ba ta san shi ba.

Ranar da makwannu biyu suka cika, ranar aka ɗaura auren Habiba da Ahmad mutumin da ba ta san shi ba, ba ta san ko sunan sa ba sai ranar, Habiba ta gigice bayan ɗaurin auren, amma ganin an ɗaura auren ya sa ta haƙura ta fawwalawa Allah komai, tasan hakan ya zaɓa ma ta, ta koma tausayin Yunusa da halin da yake ciki, ta dai na tausayin kan ta gaba ɗaya. 

Yunusa kam yana lisaafe da kwanakin auren Habiba, domin ranar ɗaurin auren har ƙofar gidansu yazo domin tabbatarwa da kan sa, ya matuƙar kaɗuwa shima, ya koma tausayin Habiba da halin da zata shiga, ya bar tausayin kansa.

Bayan dawowarsa gida ne ya ga babu amfanin zaman shi cikin garin Yobe, hakan yasa ya tarkata ya bar garin Yobe zuwa Kano, ya sha matukar wahala a kano kafin ya mance da tunanin Habiba, ya fuskanci sabuwar rayuwa da sabon sauyi.

Habiba kam sai da ta ƙara sati guda a gidansu kafin a kai ta na ta gidan, sakamakon doguwar jinya sa ta yi, Ahmad mijinta mutum ne mai zurfin tunani da hakuri, yasan Habiba ba ta son shi shima kuma hakan, domin umarnin mahaifinsa ya bi, hakan ya sa ya yi amfani da iliminsa da tunaninsa ya dinga bin Habiba sannu a hankali yana hakuri da halayenta, har zuwa wasu shekaru da ta yarda ta karɓe shi a matsayin mijinta, ta man ta da Yunusa. 

Haka shima ya ɗauke shekaru da son ta a ran sa, domin har san da ya haɗu da matarsa ya aura bayan ya samu abin hannu ya dawo Yobe state, ko da ya dawo tunanin Habiba ya sake dawo wa sabo cikin rayuwarsa, da ƙyar ya dinga yaƙi da zuciyarsa a kan ta.

Wanan shine labarin Mahaifin Senate da Mahaifiyar Bhatool. 

Ci gaba.

"To Amma Justice aina kasamu wanan tabbacin?."

"A binciken da na yi a kan lamarin auren mana."

"Amma Justice idan haka ne ai bai kamata na hana auren Senate da 'yar wajen ta ba, ina ganin kamar Allah ne ya tsara kasancewar su tare." 

"Yanzu zaka iya zuba ido ɗan ka ya auri 'yar Habiba."

"Justice kenan, mai Habiba ta yi mun a rayuwa ban da alheri, sanan shi kan shi mijin Habiban ai ba shi da laifi."

"To ai mijin ma ya rasu, shekaru da dama." 

"Allah ya yi masa rahama, amma akan wanan dalilin bazan hana auren su ba." Daga haka Dad ya shige ciki ya bar justice. Ɗakin Mom ya shiga, tana zaune gefen gado tana faman tunanin halin da ɗan ta zai shiga idan ya rasa auren Bhatool. Da sallama Dad ya shigo, amsawa ta yi ba tare da ta ɗaga ido takalleshi ba, zama ya yi gefenta sanan ya ce. "Fushi kike da ni?." Girgiza kai ta yi kawai. "Justice ya zo mun yi magana da shi, kuma ya faɗamun dalilansa." 

"Tom yanzu me ka yanke?."

"Na yanke shawarar nema masa aurenta, domin dalilin da ya ba ni ba wanda zai hana aure ba ne." Da murmushi a fuskar mom ta juyo sanan ta ce. "To ko kai fa, amma da ka ɗaga hankalina ka ɗaga na ɗana." 

"To yanzu sai ku sauke shi ko, domin gobe sa safe ma zan tura aje gidansu yarinyar, kuma har da ni za a je."

"Alhamdulillah ya rabbi." 




~~~~~Bhatool....

Ƙarar da wayarta ke yi ne ya tashi daga baccin da ta koma bayan ta yi sallar asuba, hannu ta kai ta ɗauke tana jan tsaki, ba tare da ta kula da mai kiran ba. "Hello." Ta faɗa murya cike da magagin bacci. "Bhatool." A zabure ta miƙe jin muryar Dr Hisham. "Na'am." Ta faɗa a tsorace. "Bhatool aure zaki yi?." 

"Innullahi wa'ina illahir raji'un." Ta furta a zuciyarta, a fili kuma sai ƙara cewa ta yi. "Waye?." 

"Dr Haisam ne."

"Ina kwana?." 

"Bhatool tambayar ki nake fa."

"Ni ba auren da zan yi, bikin Suhaima fa a ke yi." 

"Nasan ai bikin Suhaiman ake yi, amma ke ma ai aure zaki yi ko?."  Shiru ta yi ba ta iya cewa komai ba, sai zallan mamakin yadda a ka yi yasan da maganar. "Toh Bhatool, ki je ki yi auren kin ji, zaki ga ni a idonki." Daga haka ya kashe wayar, shiru Bhatool ta yi "wanan wace irin masifa ce, waye yasan ma zan yi aure?." Ta tambaye kan ta, amma sanin babu mai ba ta amsa ya sa ta yi shiru, ƙofar ɗakin aka buga sanan a ka ce. "Wai yau ba zaki fito ba?." 

"Gani nan Yaya." Ta faɗa tana mikewa, a falo ta sami Yaya Karima da mijinta suna zaune, ƙarasawa ta yi inda suke sanan ta ce. "Ina kwana?." 

"Lafiya kalau Bhatool, kin ta shi lafiya?."

"A'a Yaya da matsala Babba." 

"Wace irin matsala kuma, ke fa mahaukaciya ce." yaya Karima ta faɗa. "Ba irin wanan matsalal ba ce, kuma ni bake nake wa magana ba, Yaya Ka na ji?." 

"Ina jinki Bhatool."

"Akwai wani malami a makarantar mu Dr Haisam, ya ce yana sona, kuma ɗan iska ne kowa ya san shi a makaranta, ranan ya yi mun baraxana na zo na faɗawa Yaya Karima, yau kuma ya ƙara kirana yanzu wai aure zan yi ko?." 

"Ai ina ya samu labarin zaki yi aure to?."

"Nima Yaya bansani ba wallahi." 

"Yanzu da safe nan mahaifin senate ya kira ni, bayan na je ya sanar da ni yana so zai ce ya samu su kawu yau shi da yan uwan sa, a sanya lokacin aurenku na yi tunanin ke ma bakisan maganar ba?."

"Yanzu dai nasan magnar da kafaɗamun." Bhatool ta faɗa sabida ita gaba ɗaya ta tsorata da lamarin Dr. "To amma shi ina ya sa ni?." Yaya Karima ta sake tambayarta. "Wallahi bansani ba Yaya." 

"Ba ni lambarsa kawai." Miƙa masa wayar ta yi yaɗauki lambar. "Ki ta shi ki je ki yi breakfast." Yaya Karima ta faɗa ma ta. "Tom." Ta faɗa tana miƙewa zuwa dinning, gaba ɗaya jikin ta ya mutu. 


~~~~~~Hausari.....


Gaba ɗaya yan uwan Mahafinsu Bhatool ne zaune a ɗakin Goggo Larai, cike har da Furai da Habi wayanda suka kawo gulmar, wacce suma ƙarya suka shirgo abun su. 

"Ku maimaita abinds ku ka faɗa." Isiyaku ya faɗa, wanda shine mahaifin Habi kuma yayan wanda suke son bawa Bhatool Saddiƙu, Furai ce ta fara magana. "Daman mun sami labarin cewa Bhatool tana shirin barim gari ne, ita da Yayarta da mijin yayarta, sanan Abdul za su tafi ƙasar waje shi da mahaifiyarsa da yarinyar da yake son aura har da iyayenta." 

"Kutumar b***a u**a." Ɗan ladi ya mako wata ƙatuwar ashariya, sanan ya ɗora da cewa. "Lallai yaranan 'yan iska ne, mun sun mayar da mu banzaye kenan ko me, Shi Abdul ɗin har ya yi kuɗin da zai tafi ƙasar waje da iyayen yarinyar da zai aura, mu gamu anan shashashai." 

"Ai yaron da manyan yan kasuwa yake mu'amala dole ya yi kuɗi, amma sabida baƙat zuciya irin ta uwarsa ba zata ba shi umarnin xuwa nan cikin dangin ubansa ya nemi aure ba shine ta tura shi duniya." Isiyaku ya faɗa rai a ɓace. 

"To ni yanzu so  nake mu yi musu dirar wuri, a yau ɗinan a ɗaura auren Bhatool da Saddiƙu, sanan shima Abdul a ɗaura masa aure da Sajida yar wajen ka Ɗan ladi, shikenan a raba komai." 

"Tabbas Larai kin yi basira kin yi tunani, kuma kin cika babba." Auwala ya faɗa wanda shine ɗan autan su. "Yanzu yaushe zamu samesu?." Isiyaku ya faɗa. "Ai yanzunan zamu je, ayi komai da a kan lokaci. Zasu san girman dangin uba."