ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

29

by @gureenjoh

"Na san duk kun san da cewa allurar pentazocine ba'a yi ta don bugarwa ba, allura ce mai ƙarfi ta rage raɗaɗin ciwo sannan dole ana amfani da ita ne bisa umurnin likita kuma a asibiti, don rage raɗaɗi da zafin ciwo mai tsanani misali bayan tiyata ko wasu manyan raunuka, saboda tana iya haifar da jaraba da sauran matsaloli ya sa bai kamata a yi amfani da ita gaba-gaɗi ba tare da umurnin likita ba. Wannan patient da kuka kawo yana cikin abin da yake fuskanta na daga cikin manyan hatsarinta."


Duk sun sani duk sun san Pablo is addicted to penta, irin addiction da zai iya yin hauka idan ya ɗauki awwani masu tsawo bai yi ba haka kuma duk inda zai samu jijiya yi yake idan zai yi a wuri ɗaya sau goma muddin jijiyar bai ɓace ba a wurin zai cigaba amma basu taɓa sanin illarta ta kai haka ba.


"Likita zai iya warkewa ko? Jijiyon da ka ce sun ɓace har suna haifar da ruɓewar tsokokinsa duk za su dawo daidai?"

Diva ta tambaya muryarta na bayyana damuwarta don tabbas hankalinta ya tashi.


Likitan ya dubeta yace 

"Abu na farko da za'a fara shine dakatar da shi daga wannan allurar saboda lalacewar bata yi tsanani har chan ba za mu ɗora shi kan wasu magunguna da zai murmure a hankali bayan watanni amma muddin bai daina ba zai zama ya ƙarasa lalata jijiyoyin nashi na har abada"


Hankalinsu ya ɗan kwanta har ma Diva ta sa a ranta dole ya daina ko da zai koma wani abin buguwar ba damuwa ba ne tunda duk suna yi din sai dai kowa da abin da ya fi so ne amma dole ya bar penta.


Sun bar Pascal ne asibitin suka koma gida ko da ta yi wa Jagaban bayanin yadda abubuwan suka faru tayi mamakin rashin ganin kololuwar damuwa a tattare da shi har kaman ta yi shiru sai ta ce 


"Baba"

Ya kalleta 

"Ina so bayan an sallami Pablo daga asibiti ko da ya zo neman penta kar ka sayar masa"


"Meyasa?"

Yadda yayi tambayar sai da ya sakata ɗan tsayar da Idanunta kansa

"yanzu fa na gama maka bayani Baba idan bai daina ba komai zai iya faruwa da shi gaba, tsokokinsa ruɓewa za su yi Baba"


"Sohana ba zan miki ƙarya ba muddin ya kawo kudinsa yana so sayar masa zan yi, ni sana'ata ce hanyar samun kudina kenan"


Mamaki tsantsa ya bayyana a fuskar Diva.

"Na zaci da ni da su Pablo duk ka daukemu ɗaya ne, idan ni ce na zama addicted to penta har yana neman rayuwata za ka cigaba da ba ni?"


"Sohana sana'ata ce ba damuwa ko rashin damuwa ba, muddin shi ya kawo kudi yana so zan sayar masa abin da ya fi muhimmanci kudina ne"


Wani irin abu da bata taɓa ji kan Baban ba ke taso mata, a hankali hawaye suka cika Idanunta amma bata bari sun yi tasiri ba ta haɗiye ta miƙe kawai ta fice daga gidan gabadaya ya bita da kallo a fili yayi dariya 


"Hmmm Sohana har yanzu ke yarinyar ce, har yanzu da sauranki a sanin Underground world"


Ɗakin Shaly ta ya da zango kawai ta kwanta tana runtse Idanunta, a hankali ta shiga tunanin ya matsayin tarin waenda babanta ya jefa cikin duniyar kwaya? Meyasa bayan ta san yadda rayuwarsu ke tafiya ba kan daidai ba ne amma ba za ta iya daina wa ba? Ta ya za ta fara hana Pablo allurar penta alhali itama ta riga ta zama addicted to Ice? Har ranta ta fara jin ƙiyayyar yadda mahaifinta ke tafiyar da rayuwar matasa amma ba za ta iya wani abu ba sai ma ta bashi gudummawa ta wani ɓangaren.


Maganan Shaly da Zee ne ya ɗan dawo da ita daga tunanin da ya fara addabarta sun riga sun san halin ta za ta iya gama zamanta ma a dakin idan bata yi ra'ayi ba ba zata musu magana ba, hakanan dama yanayinta ba mai wasa da dariya ba ce bare su fahimci abu na damun ranta.


"Zee ni kam baki fahimci Zubash kwanan nan tana cikin damuwa ba?"


Zee ta ce

"Ai tun tafiyar Diva na fahimci ta rage walwala kuma fa yanzu ko yawan zuwa hotels hotels din nan bata yi, na kula har kudin abin da za ta sha bata da shi shiyasa jiya ta sha codein da bata cika so ba"


Diva ta buɗe Idanunta tana kallonsu 


"Shaly menene matsalarta?"


"Wallahi bamu sani ba amma zan bincika Diva"


Numfashi ta ɗan sauƙe ta koma ta kwanta shiru, sai tayi tsaki kawai ta miƙe tana kiran Skipo.


"Raina a wuya yake ina so a yau ba gobe ba ka binciko min bullet din nan in sauƙe masa zafin kan nan"


Yace 

"An gama Diva"


Ficewa tayi daga gidan gabadaya ta koma gida zuwa ɗakinta haka ta haɗa ice ta shiga sha ko zai rage mata abubuwan da suka fara tarar mata a kai.


Kaman yadda ta umurta a yammacin Skipo ya sanar mata ai yana wani restaurant gashi nan shi da Obafiya sun tsare shi, ficewa tayi daga gidan bata nemi su Shaly ba ma ta ɗauki mota ta nufi restaurant da ya ce mata suna nan ɗin.


*****


Shehi ne ke driving Ammar na daga gefenshi yau ya shiga BUK yayi lectures Kasancewar ya kwana biyu ba ya gari abubuwan sun ɗan taru a son shi ne ma gobe ya wuce Katsina ya dawo a goben saboda yana so ya fara batun gyaran Gidan sheikh Nasser da tsara yadda zai sauƙa har ya tafi, daga BUK company ya je kai tsaye inda ake shigo musu da kuma fitar da kaya ya nufa ya ɗan yi magana da wani a sirrance kan ya bar wurin ya nufi office na Ammar a chan ya zauna har Ammar ya gama abin da yake suka fito a tare.


"Bari na bika kawai mu wuce gida motan nan zan kira mechanic ya ɗauka a nan birkinta ta sake ina zuwa da safe kadan ya saura ban yi hatsari ba"


Dalilin da ya sa ya bishi kenan, a natse yake tukin har ya nufi hanyar gida ma duka sai wani da zai bashi saƙo ya ƙirashi akan komai ya kamallah ga takardun hannunsa.


"Kana ina?"

"Ina dab Majlis restaurant"

"mu haɗu  a chan kawai"

Ya faɗa yana juya kan motar, dukda gajiyar da yake ji yana son kawo karshen abubuwan da yake bincikowan nan, wanda tabbas idan bai gano ba cikin kankanin lokaci komai zai iya faruwa da companyn bayan ɓacewar makudan kudade.


Kai tsaye chan suka nufa sanye yake da Ox blood jallabiya da jubba da ya zama mahadar jallabiyar don kalar su ɗaya sai dai akwai adon ruwan gold daga jikin riga mai kama da alkyabbar, Ghutra da ya sa a kansa ma mai surkin Ox blood din ne da baƙi sai baƙin Agal da baƙin takalmi.


A natse yayi parking motar suka sauka suka shiga ciki, bayan sun zauna waiter din ya zo sai Ammar ya umurceshi da ya kawo musu coffee, matashin mai sanye da kananun kaya ya zo ya zauna suka gaisa kan ya ɗauki brown envelope din ya ba Shehi, ya karɓa tare da furta

"Jazakallahu khairann"


Matashin yayi murmushi cikin girmamawa ya tashi zai fice Shehi na mishi tayin ma ya tsaya ko coffee da suka yi order ne ya sha ya ce a'a kan ya wuce.


An kawo musu coffee din suna sha Ammar na tambayar shi ko ya kira Na'ima ɗin yace ya ƙira bata yi picking ba kuma ba ya tunanin zai ma sake kiran, Ammar yayi murmushi kawai daidai lokacin suka shiga jin hayaniya...


Duk hankulansu suka mayar kai idanunsa basu sauƙa ko ina ba sai kanta tana sanye da wando dogo baƙi da wani blouse kalar maroon haka jersey vail din kanta ma kalar maroon ne, dab da su suke don za su iya cewa table nasu ne yake kusa da inda suke ɗin, ƙafanta ɗaya na kan kujerar gefen kato kuma jibgegen mutumin da suka zagaye su uku wanda daga kallo ɗaya ma za ka masa ka san cewa ba bahaushe ba ne ga mamakinsu hannu ta ɗaga ta tsinka masa mari.


Sai ga muryarta cikin kaushi da ƙarfi tama cewa 

"Kai ne akuyar da ya tsallakemin danga? Kai ne dattin da ka rasa inda zaka yi da ruwa ya kwaso ka sai hanyana? Me ka ƙira kanka ma?..."


Jikinshi na rawa yace 

"Babu! Babu komai..."


Kallon Obafiya tayi sai ya kai mishi naushi yana chakumo kwalarsa 

"Me kake kiran kanka?"


"Boss...boss da ya kori Diva"


Skip ya sake kai masa naushi a baki

"Kana kara ambatar sunanta sai na zubar maka da hakwara, Shugaba har wasu daga cikin yaran da ba'a taɓa mana su a layi ya taɓa da ikirarin ya riga ya ɓatar da ke yanzu mu ma duk karkashin sa muke"


Wuƙa ta zaro 

"Bari na kasheka in kashe banza... Za ka san ka shiga hurumina"


Waiters da kuma securities din wurin ne suka zube suka rokonta kar ta zubar musu da jinin kowa a wurin tayi hak'uri don duk sun san labarin sun kuma sun san bata ɗauruwa.


Lip ta cije ta saukar da kafarta daga kan kujerar tana juya Idanunta a wurin don bata son yawan magiya, idanunta basu sauƙa ko ina ba sai kanshi da shima yake kallonta mamakin fuskarshi ya koma takaici don har ranshi ganinta hakan yana jin daci da takaicin ta amsa sunan diyar musulmi a irin wannan ɓata.


Miƙewa yayi kawai ya sa hannu aljihu ya zaro kudin da bai san nawa ba ya ajiye kan table ɗin ya kalli Ammar

"Mu je"


Miƙewa Ammar yayi suka nufi fita, baya baya ta ɗan yi ta zauna kan table da suka tashi ta kalli Obafiya 

"Ku kyaleshi for now! Ku tabbatar duk inda kuka sake ganinshi a birnin Kano ya baƙunci lahira umurni ne"


Baya suka matsa ya fice da gudu, tana Miƙewa ta taka abu, ido ta kai wurin sai ta duka ta ɗauka wallet ce ta maza, buɗe wa tayi Idanunta suka sauka kan ID cards da kuma Atms, sunanshi ta fara gani kan hoton shi na passports, ta kalli kofar da basu jima da fita ba sai ta miƙe ta nufi kofar don har ranta tana son jin ko police sun kira shi batun yarinyar chan? Ko iyayenta sun same ta? Don da tausayinta take kwana.


Dab motar su ta hange su da sauri ta ƙarasa tama furta 

"Excuse me!"


Babu wanda ya juyo a cikinsu Karon farko da bakinta ya furta 

"Sheikhhh!"


Babu zato ba tsammani ta ga ya juyo cikin kaushin murya da tsawa yace 

"Whatt??"


Har Ammar sai da ya waigo yana kallonshi don Shehi ba gwanin ɗaga murya haka ba ne, sai ya fahimci ranshi a ɓace irin ɓacin da yana wuya a gani a tattare da shi.


Yadda ya juyo a zabure kuma idanunsa na kallon nata ya sa ta ji ta tsaya chakk ta kasa motsi Karon farko da wani murya ya girgiza zuciyarta don tsawar ya sauƙa har cikin zuciyarta ga idanun da ya tsare ta da su lokaci ɗaya abin ya zo mata bazata.


Tattaro jarumtarta tayi ta hade fuska ta watsa masa harara 

"Da ma abin kirki ai bai karɓi kare ba... Idan da ban nemi na taimake ka ba ba za ka min ihu a kai ba.."


Wallet ɗin ta miƙa masa dukda wata zuciyar na cewa ta jefar in ya so ya je ya ɗauka amma bata yi hakan ba sai da ta miƙa mishi.

"Idan ba za ka karɓa ba wallahi cilli zan yi da shi ko ma me a ciki sai dai ya salwanta"

 a ranta tana ƙirge don tana kirga uku bai sa hannu ya karɓa ba sai ta yi cilli da shi wallahi dab ta gama uku tana kokarin wullar da shi ya sa hannu sai ta kalleshi suka haɗa idanu ta sakar masa kan ta juya ta bar wurin a fusace laifinta ne da har ta taimake shi ma zai tsaya yana mata tsawa a kai ta yi tsaki ya fi cikin kwando kan su isa gida.


Kanshi ya ɗan dafe yana jan tsiririn tsaki kan ya wullawa Ammar key ɗin yana nufar seat na mai zaman banza don ba zai iya tukin ba kuma.


"Shehi me ke faruwa ne?"


Tambayar ya zo mishi ne a daidai sadda yake tambayar kansa me nashi ma na jin haushi don ya ganta cikin yanayin da halinta ne kuma dabi'arta? Menene bai san tana yin ba shaye shaye ne ko dabanci? Ko ko ganinta cikin shiga da ta saɓawa shari'a da ma tsarin musulunci? 

Me ya sa zai ji haushin da ya kamata a ce uban da ya haifeta shi ya kamata ya ji mata? 


Gobe in Shaa Allah free pages za su ƙare!