CIN AMANA BOOK ONE JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ZUZU
CIN AMANA BOOK ONE JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ZUZU
CIN AMANA BOOK ONE ***JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ***
Dukkkan yabo da godiya sun tabbata ga allah madaukakin sarki mekowa me komai wanda yabani iko da damar rubuta wannan littafi CIN AMANA allah yasa yanda nafara asa'a nagama asa'a tare da temakon ubangiji
Naware lokaci don miqa godiya ta ga uwata mahaifiyata madubina (hjy zainab Muhammad)dakuma
Bangona majinginata abun adona mahaifina (mahboob ibrahim)
Jinjina gareku manyan yayuna da qannena allah yashiga lamarinku ameen 🙏
CIN AMANA …………1
______________KADUNA_____________
Da sanyin safiyar Litinin, hasken alfijir ya fara ratsa manyan gine-ginen birnin millennium city dake garin Kaduna. Motoci kaɗan ne ke yawo a kan tituna, yayin da iska mai ɗauke da sanyin safiya ke busawa cikin nutsuwa.
A cikin ɗaya daga cikin unguwannin masu hannu da shuni, unguwar millennium city katafaren gida mai bene uku ya tsaya cike da kyan gani. A ƙofar gidan akwai jami'an tsaro, lambun furanni kuwa ya yi kyau kamar an zana shi
A saman benen gidan, cikin wani katafaren ɗaki da aka kawata da kayan alatu, wani kyakkyawan matashi ya buɗe idanunsa tare da qara murzasu ahankali
Muhammad Aruk Tafida kenan.
Aruk matashi ne mai shekaru ashirin da bakwai. Allah Ya azurta shi da kyakkyawar fuska, tsayi mai kyau da kwarjini. Duk wanda ya gan shi a karo na farko zai yi tunanin ba ɗan Nigeria bane. Amma abin da ya fi jan hankalin mutane ba kyawunsa ba ne, halinsa ne.
Ko da yake yana rayuwa cikin yalwar dukiya, bai taɓa raina talaka ba. Yana girmama manya, yana tausaya wa ƙanana, kuma yana yawan taimakon mabukata ba tare da neman yabo ba.
Bathroom yashiga be jimaba yafuto daure da towel closet yashiga bejima ba yafuto shiryawa yayi cikin wata bakar shadda sunyi bala'in karbar jikinsa . Agogon da ke hannunsa da takalmin da ya saka sun ƙara masa kwarjini.tare da qara futo da hasken farar fatarsa Duk da irin arzikin da yake ciki, babu alamun girman kai a fuskarsa.
Da ya sauko falo, ya tarar da Ammi tana zaune tana duba wasu takardun wata gidauniyar taimakon marasa galihu da take gudanarwa.
"Assalamu alaikum, Ammi."
"Wa alaikumus salam, Aruk." Ta ɗago tana murmushi. "Ka yi barci lafiya?"
"Alhamdulillah. Ke fa?"
"Lafiya lau. Zo ka zauna."
Aruk ya zauna kusa da ita.
"Ammi, me kike dubawa ne?"
"Jerin wasu marayu ne da za mu biya musu kuɗin makaranta. Na ce in sake duba komai kafin a tura kuɗin."
Aruk ya ɗan yi shiru, sannan ya ce cikin nutsuwa,
"Idan akwai ƙarin yara da ba su samu ba, ki saka su. Zan ɗauki nauyin karatunsu."
Hajiya Zainab ta kalle shi cike da farin ciki.
"Allah Ya ƙara maka arziki da zuciya mai kyau."
"Amin, Ammi."
A daidai lokacin ne ƙofar falon ta buɗe.
Wani dattijo mai cikar kamala cikin farar shadda ya shigo. Takunsa kaɗai ya isa ya nuna cewa mutum ne mai daraja.
Alhaji Yusuf Tafida, kenan mahaifina Muhammad Aruk.
Aruk ya miƙe tsaye cikin girmamawa.
"Ina kwana, Daddy."
"Lafiya lau, Aruk."
Suka yi musabaha.
Daddy ya zauna, sannan ya ce,
"Na ji daga Mustapha cewa ka kammala yarjejeniyar kamfanin nan jiya."
Aruk ya gyara zamansa.
"Eh Daddy. Alhamdulillah komai ya tafi yadda muka tsara."
Daddy ya yi murmushi.
"Na san za ka iya. Amma ka tuna abu ɗaya..."
Aruk ya mai da hankali.
"Dukiya tana zuwa tana tafiya. Sunan mutum da mutuncinsa su ne ba sa saurin gushewa."
Aruk ya ɗaga kai cikin ladabi.
"Na riƙe maganarka, Daddy."
A lokacin ne cooker ya qaraso cikin girmamawa ya gaishe su tare da fadin hajiya an kammala kamai toh sannu kaji ammi tafada sannan suka mike zuwa dining. Suka ci suna tattauna harkokin kasuwanci da ayyukan gidauniya. Bayan sun gama, Daddy ya ce,
"Ka shirya. Da ƙarfe tara muna da taro da wasu manyan masu zuba jari."
"In sha Allah, Daddy."
Aruk ya nufi harabar gidan. Tsayawa yayi yana kallon , manyan motocin da ke ajiye cikin tsari. Wata farar Mercedes-Benz yabude yashiga.
Kafin ya kunna motar, wayarsa ta sake yin ƙara.
Da ya duba, sai ya ga sunan Jabir.
Aruk ya yi murmushi.
"Yau kuma me Jabir yake nema da wannan safiyar?"
Amsawa yayi ….
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU)
ALQALAMI✍️ YAFI TAKOBI 🤺
CIN AMANA…….2
KADUNA
Aruk ya ɗaga wayar tare da ɗora ta a kunnensa.
"Assalamu alaikum."
Daga can ɓangaren kuwa, wata dariya jabir yasaki
"Wa alaikumus salam, Sir"
Aruk ya yi murmushi.
"Jabir kenan. Da safe-safen nan ka fara zolaya?"
Jabir ya yi dariya.
"Wallahi idan ba na zolayarka ba wa zan zola? Tun jiya nake kiranka ka ƙi ɗagawa."
"Na yi meeting ne har dare."
"Haka nayi tunani nima. Yaushe za ka iso office?"
"Cikin mintuna talatin."
"To, ni da Mustapha mun riga mun iso. Akwai wasu takardu da za mu duba kafin Daddy ya zo."
Aruk ya ce,
"Shi kenan, ka jirani."
Bai gama faɗar haka ba sai Jabir ya sake cewa,
"Amma akwai wani baƙo da ya zo tun da wuri. Ya ce sai ya ganka da kansa."
Aruk ya ɗan yi mamaki.
"Baƙo kuma?"
"Eh. Bai faɗi cikakken dalilin zuwansa ba."
"To, yanzu zan zo."
Ya kashe wayar.
Ya kunna motarsa, yafara tafiya a hankali daga harabar gidan. Jami'an tsaro suka buɗe masa katafaren get din gidanya cilla hancin motarsa zuwa katafaren ,babban titin Abuja.
A hanya idanunsa na kan titi, amma zuciyarsa tana tunanin wanene wannan baƙon.
---
A wani gini mai hawa goma sha biyu da ke tsakiyar Abuja ne kamfanin Tafida Group of Companies yake.
Kamfani ne da ya shahara a fannin gine-gine, sufuri, da kasuwanci. Ma'aikata da baƙi suna ta shiga da fita cikin tsari.
Hone daya getman din ya wangale masa get din company motar Aruk ta tsaya a harabar kamfanin, masu gadi suka yi saurin qarasowa suna gaidashi
"Ina kwana, yallabai."
"Lafiya lau."
Ya amsa cikin fara'a, ba tare da nuna isa ba.
Da ya shiga ciki, ma'aikata da dama suka tsaya suna gaishe shi.
"Ina kwana, Sir."
"Lafiya lau. Ya aiki?"
"Alhamdulillah."
Aruk ya kasance mutum mai son gaishe da kowa. Wannan ne ya sa ma'aikata suke girmama shi ba don dukiyarsa ba, har da halinsa.
Da ya isa hawa na uku, ya tarar da Mustapha tsaye a bakin ƙofa, hannunsa ɗauke da wasu manyan files.
Mustapha ya yi murmushi.
"Ka iso kenan."
Aruk ya rungume shi cikin fara'a.
"Lafiya Mustapha."
"Lafiya ƙalau."
"Kai har yanzu kana riƙe da files din nan?"
Mustapha ya yi dariya.
"Idan ban yi aikina ba wa zai yi?"
Girgiza kai kawai aruk yayi.
Kafin su shiga ofis, Jabir ya fito daga ciki da sauri.
"Yanzu ne ka samu zuwa?"
Aruk ya girgiza kai yana murmushi.
"Ka san Abuja.Akwai cunkoso ."
Jabir ya ce,
"To ka shirya. Baƙon nan yana ciki, kuma ya nace wai sai ya ganka."
Aruk ya ɗan ɗaga gira.
"Mu shiga."
Ya tura ƙofar office a hankali...
Bayan ya shiga, ya tarar da wani dattijo zaune cikin nutsuwa, fuskarsa cike da damuwa kamar wanda ya daɗe yana jiran wannan ganawar.
Aruk ya tsaya cak.
Bai taɓa ganin mutumin ba a rayuwarsa...
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU)
ALQALAMI ✍️ YAFI TAKOBI 🤺
CIN AMANA……..3
KADUNA
Aruk ya ɗan tsaya yana kallon dattijon da ke zaune cikin nutsuwa a kujerar baƙi. Fuskar mutumin ta nuna ya sha wahala a rayuwa, amma yadda yake zaune ya nuna cewa mutum ne mai cike da kamala da mutunci.
Aruk ya yi sallama.
"Assalamu alaikum."
Dattijon ya ɗago kai da murmushi.
"Wa alaikumus salam, ɗana."
Aruk ya ƙarasa ya miƙa hannu.
"Sannu da zuwa."
"Yauwa ɗana."
Bayan sun gaisa, Aruk ya zauna a kujerarsa, yayin da Jabir da Mustapha suka zauna a gefe.
Na ɗan lokaci babu wanda ya yi magana.
Aruk ne ya katse shirun.
Da cewa.
"Baba, an ce kana son ganina."
Dattijon ya gyara zamansa.
"Hakane."
"To, ina sauraronka."
Mutumin ya sauke ajiyar zuciya.
"Sunana Alhaji Bashir."
Aruk ya gyada kai cikin girmamawa.
"Na yi farin cikin haɗuwa da kai."
Alhaji Bashir ya yi murmushi.
"Ni ma haka."
Ya ci gaba da cewa,
"Na daɗe ina bibiyar ayyukan kamfaninku. Na ga yadda kake mu'amala da ma'aikata, da yadda kake taimakon mutane. Wannan ne ya sa na ce sai na zo na ganka da kaina."
Jabir ya kalli Mustapha, Mustapha ma ya kalli Jabir, amma babu wanda ya ce komai.
Aruk ya yi murmushi.
"Alhamdulillah. Duk abin alheri daga Allah yake."
Alhaji Bashir ya jinjina kai.
"Ba kowa ne yake faɗin haka ba idan Allah Ya ba shi dukiya."
Aruk ya ce,
"Mutum bai san gobe ba. Shi ya sa dole ya gode wa Allah."
Dattijon ya yi shiru na wasu daƙiƙu kafin ya buɗe wata baƙar jakar fata da ya zo da ita.
Ya fito da wasu takardu masu yawa ya ɗora a kan tebur.
Jabir ya ɗan matsa gaba.
Mustapha ma ya zura ido.
Aruk ya kalli takardun cikin mamaki.
"Waɗannan kuma?"
Alhaji Bashir ya ce cikin natsuwa,
"Takardun wani babban aikin gini ne da nake son kamfaninku ya gudanar."
Jabir ya yi murmushi.
"Ashe wannan ne ya kawo ka?"
Dattijon ya gyara zamansa.
"Ba wannan kaɗai ba."
Kalmar ta sa ɗakin ya sake yin tsit.
Aruk ya haɗe hannayensa a kan tebur.
"To, me kuma?"
Alhaji Bashir ya ɗan yi shiru, kamar wanda yake neman kalmomin da zai yi amfani da su.
"Duk da ban taɓa haɗuwa da kai ba, akwai wani al'amari da ya sa na ga dole na fara saninka kafin lokaci ya kure."
Aruk ya ɗan daure fuska.
"Wane al'amari ne?"
Dattijon ya yi murmushi kaɗan.
"Zan gaya maka... amma ba yau ba."
Jabir ya buɗe baki cikin mamaki.
"Ba yau ba?"
"Eh. Sai idan lokacin ya yi."
Ya miƙe tsaye, ya tattara jakarsa.
"Na gode da lokacin da ka ba ni."
Aruk ya tashi tare da shi.
"Amma ai..."
Alhaji Bashir ya katse shi.
"Ka yi haƙuri. Za mu sake haɗuwa nan ba da jimawa ba."
Ya juya ya nufi ƙofa.
Aruk ya tsaya yana kallonsa har ya fice.
Da ƙofar ta rufe, Jabir ya yi saurin cewa,
"Wallahi ni ban gane komai ba."
Mustapha ya ɗan yi murmushi.
"Ni ma. Amma na tabbata mutumin nan yana ɓoye wani babban sirri."
Aruk ya zauna a kujerarsa yana kallon ƙofar da dattijon ya fita ta cikinta.
A zuciyarsa tambaya ɗaya ce kawai ke yawo...
Wane irin sirri ne wannan mutum yake son ya bayyana masa?
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU)
ALQALAMI ✍️YAFI TAKOBI 🤺
CIN AMANA…….4
Aruk ya ci gaba da kallon ƙofar da Alhaji Bashir ya bi ya fita. A karo na farko cikin dogon lokaci, ya ji wani abu yana yawo a ransa. Maganganun dattijon sun yi masa nauyi fiye da yadda ya zata.
Mustapha ne ya katse masa tunani.
"Aruk..."
Ya ɗago kai.
"Na'am."
"Me kake tunani?"
Aruk ya sauke numfashi.
"Ban sani ba. Amma akwai wani abu a tattare da mutumin nan. Yadda yake magana ya nuna ba mutumin banza ba ne."
Jabir ya jingina bayansa da kujera yana dariya.
"Ni dai na fara tsoro. Wai ya ce yana da sirri amma ba zai faɗa ba. Kamar a fim."
Mustapha ya kalle shi.
"Kada ka ɗauki komai da wasa. Ka ga yadda yake kallon Aruk? Kamar wanda ya san shi tun shekaru da yawa."
Jabir ya ɗan yi shiru.
"Hakane."
Aruk ya miƙe tsaye ya gyara rigarsa.
"Mu bar wannan maganar yanzu. Daddy yana jiranmu a ɗakin taro."
Suka fito daga ofishin tare.
...
Babban ɗakin taron kamfanin Tafida Group ya cika da manyan jami'an kamfanin. Kowane mutum yana zaune a kujerarsa yana jiran zuwan Alhaji Yusuf Tafida.
Da Aruk ya shiga, kowa ya miƙe yana gaishe shi.
"Ina kwana, Sir."
"Lafiya lau."
Ya amsa da fara'a yana musabaha da wasu daga cikinsu.
Mintuna kaɗan bayan haka ƙofar ta sake buɗewa.
Alhaji Yusuf Tafida—ya shigo cikin takunsa na natsuwa. Kowa ya sake miƙewa.
"Assalamu alaikum."
"Wa alaikumus salam."
Daddy ya zauna, ya buɗe babban file da ke gabansa.
"Bismillah..."
Ya fara duban waɗanda suke cikin ɗakin.
"Na tara ku ne saboda muna gab da fara wani sabon aiki da zai zama mafi girma da kamfaninmu ya taɓa yi."
Nan take hankalin kowa ya koma kansa.
Ya ci gaba.
"Mun samu tayin gina wani sabon rukunin gidaje da cibiyar kasuwanci. Aikin yana da girma sosai, kuma ba zan ɗora wa kowa nauyinsa ba sai Muhammad Aruk."
Wasu daga cikin jami'an suka yi murmushi.
Wasu kuma suka kalli Aruk cikin mamaki.
Daddy ya ci gaba.
"Na san akwai waɗanda za su yi tunanin saboda ɗana ne. Amma duk wanda ya san yadda yake aiki zai tabbatar cewa ya cancanci wannan amanar."
Aruk ya sunkuyar da kansa cikin girmamawa.
"Na gode, Daddy."
Daddy ya ɗaga hannu.
"Kar ka gode min. Ka tabbatar ka yi aikin da zai sa sunan Tafida ya ci gaba da kasancewa abin alfahari."
"In sha Allah."
Ana cikin taron ne ƙofar ta buga.
Daya daga cikin masu karɓar baƙi ya shigo.
"Yi haƙuri, Alhaji."
Daddy ya kalle shi.
"Lafiya?"
"Akwai baƙuwa a waje. Ta ce tana son ganinka."
"Wace ce?"
"Ta ce sunanta Husnah."
Aruk ya ɗan ɗaga gira.
Jabir kuma ya saki murmushin da Mustapha ya lura da shi.
Daddy ya ce,
"Ka ce tashigo ."
Wata kyakkyawar budurwa cikin shiga mai tsari ta shigo cikin ɗakin taron. Ta yi sallama cikin ladabi.
Da idanunta suka sauka kan Aruk...
Ta yi murmushi.
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU)
ALQALAMI ✍️YAFI TAKOBI 🤺
CIN AMANA………6
KADUNA
Shigowar budurwar ya sa hankalin duk mutanen da ke ɗakin taro ya koma kanta.
Ta yi tafiya cikin natsuwa, cikin shigar atamfa mai launin ruwan hoda da baƙin mayafi. Ba ta yi kwalliya mai yawa ba, amma yanayin fuskarta ya nuna cewa Allah Ya hore mata kyau da kwarjini.
Ta tsaya a gaban Daddy.
"Assalamu alaikum."
"Wa alaikumus salam." Daddy ya amsa da fara'a. "Sannu da zuwa, Husnah."
"Yauwa Daddy."
Aruk ya ɗan yi mamaki. Ya juya ya kalli Daddy.
"Daddy... kun santa ne?"
Daddy ya yi murmushi.
"Kwarai kuwa."
Jabir ya yi murmushi yana kallon Aruk.
"To oga, ashe kai ne ba ka santa ba."
Mustapha ya ɗan yi dariya.
"Ni ma na san ta, amma ban taɓa haɗa ku ba."
Aruk ya sake kallon Husnah tare da tabe baki .
Ta sunkuyar da kai cikin ladabi.
Daddy ya ce,
"Husnah 'yar marigayi Alhaji Sani ce. Ni da mahaifinta mun yi shekaru muna kasuwanci tare. Bayan rasuwarsa, na ci gaba da kula da wasu daga cikin harkokin kamfaninsu."
Husnah ta gyara mayafinta.
"Na zo ne saboda wasu takardun kamfaninmu. Lauyanmu ya ce ya kamata na kawo su da kaina."
Daddy ya karɓi file ɗin da ta miƙa masa.
"Madalla."
Ya buɗe ya fara dubawa.
Aruk yana kallon yadda take magana shi abun ma haushi yake bashi
Bayan ɗan lokaci Daddy ya rufe file ɗin.
"Komai ya yi kyau. Za mu kammala sauran bayanan nan da kwana biyu."
"Nagode sosai."
Daddy ya yi murmushi.
"Kafin ki tafi..."
Ya juya ya kalli Aruk.
"Ki haɗu da Muhammad Aruk."
Husnah ta ɗago kai.
Dauke kai aruk yayi.
"Barka ."
Barka shima yace mata tare da maida hankalinsa ga daddyi.
" Muhammad Aruk." Dago kai yayi yakalleta.
Aruk ya ɗan yi mamaki.
"Kin san ni?"
Ta yi murmushi kaɗan.
"Wa bai san Muhammad Aruk Tafida ba a KADUNA?"
Jabir ya yi dariya.
"Ka ji ko? Shahararka ta fara yawa."
Aruk ya girgiza kai tare da hararar jabir.
"Jabir kenan."
Mustapha ya ce,
"Mu bar zolaya. Muna cikin aiki."
Duk suka yi dariya.
Amma banda aruk
Daddy ya miƙe tsaye.
"Aruk."
"Na'am Daddy."
"Ki raka Husnah zuwa ƙasa. Bayan haka ka dawo mu ƙarasa taron."
"In sha Allah."
Yafada tare da miqewa.
"Na gode."
“Tafada tana satar kallonsa .
Kai kawai ya gyada mata.
Suka fito daga ɗakin taron suna tafiya a hankali cikin doguwar hanyar da ta haɗa ofisoshin kamfanin.
Na ɗan lokaci babu wanda ya yi magana.
Sai Husnah ta karya shirun.
"Gaskiya na daɗe ina jin sunanka."
Aruk ya yi Jim kafun yace.
"Kamar ya kenan?"
Ta ɗan yi shiru kafin ta ce,
"An ce kai mutum ne mai taimakon jama'a, kuma ba ka cika son a yaɗa abin da kake yi ba."
Aruk ya sauke numfashi.
"Idan mutum zai taimaka, ya kamata ya yi don Allah."
Husnah ta gyada kai cikin gamsuwa.
"Kalaman nan sun tabbatar min cewa abin da ake faɗa gaskiya ne."
Suna isa harabar kamfanin, direban Husnah ya fito ya buɗe mata ƙofar mota.
Ta juya ta kalli Aruk.
"Na gode da rakiyar."
"Ina fatan za mu sake haɗuwa."
Aruk ya kalleta kawai batare da yace komaiba ."
Husnah ta shiga motar, ta yi masa sallama kafin motar ta bar harabar kamfanin.
Aruk ya tsaya yana kallon motar har ta ɓace.
Tsaye yake awani ɓangare na filin ajiye motoci, yana kallon duk abin da ya faru .
Mutumin ya matse hannunsa cikin fushi.
Ya ce a hankali,
"To... ashe an fara."
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU)
ALQALAMI ✍️YAFI TAKOBI 🤺
CIN AMANA……..7 KADUNA
Aruk ya ɗan tsaya yana kallon hanyar da motar Husnah ta bi har ta ɓace daga idanunsa.
Jabir ne ya fito daga cikin ginin kamfanin yana dariya.
"Wallahi ka tsaya kana kallon motar nan kamar wanda aka sace masa wani abu."
Aruk ya juya ya kalle shi.
"Jabir kenan, ba ka da aikin da ya wuce zolaya."
Jabir ya matso kusa da shi.
"To ba haka bane? Kai da ban taɓa ganin ka kana rakiyar baƙuwa ba, yau har ka kai ta mota."
Aruk ya girgiza kai.
"Daddy ne ya ce in raka ta."
"Ai na sani."
Mustapha ya fito yana riƙe da wasu takardu.
"Kun tsaya nan kuna hira, Daddy yana jiranku."
Suka nufi cikin ginin tare.
---
Da suka shiga ofice Daddy, suka tarar yana zaune shi kaɗai. Ya cire gilashinsa ya ajiye a kan tebur.
"Ku zauna."
Duk suka zauna.
Daddy ya haɗe hannayensa.
"Aikin da muke shirin fara ba ƙaramin aiki ba ne. Ina son ku uku ku kasance masu haɗin kai."
Mustapha ya gyara zamansa.
"In sha Allah."
Jabir ya ce,
"Ba za mu ba ku kunya ba."
Daddy ya kalli Aruk.
"Kai kuma?"
Aruk ya ce cikin ladabi,
"Zan yi iya ƙoƙarina, Daddy."
Daddy ya yi murmushi.
"Wannan ne nake so."
Sai ya buɗe wani babban taswirar aikin da aka shimfiɗa a kan tebur.
"Wannan sabon aikin zai gudana a jihohi uku. Abuja, Kaduna..."
Ya ɗan yi shiru.
"...da Kano."
Aruk ya ɗago kai.
"Kano?"
Daddy ya gyada kai.
"Eh. Muna shirin buɗe sabon reshen kamfaninmu a can."
Mustapha ya ce,
"Wannan babban ci gaba ne."
Daddy ya ci gaba.
"Saboda haka dole ne wani ya riƙa zuwa Kano lokaci-lokaci domin kula da aikin."
Jabir ya yi dariya.
"Ni dai kada ku ce ni. Ban saba da tafiya ba."
Mustapha ya girgiza kai.
"Ni kuma idan aiki ya buƙata zan je."
Daddy ya ɗan yi shiru kafin ya kalli Aruk.
"Amma wanda nake so ya jagoranci wannan aikin shi ne kai."
Aruk ya ce,
"Ba damuwa Daddy. Idan hakan ne ya dace, zan je."
Daddy ya yi murmushi cikin gamsuwa.
"Na san za ka iya."
Hmmmmmmmm
---
Da yamma...
Aruk ya dawo gida bayan ya kammala ayyukan ranar.
Lokacin daya shiga falo, ya tarar da Ammi tana zaune tare da wasu mata daga gidauniyar taimako.
Da ta gan shi, ta yi murmushi.
"Aruk, ka dawo kenan?"
"Eh Ammi."
"Zo nan."
Ya ƙarasa ya zauna kusa da ita.
Ta shafa kafaɗarsa cikin ƙauna.
"Yaya aikin yau?"
"Alhamdulillah. Daddy ya ba ni jagorancin wani sabon aiki."
"Allah Ya sa albarka."
"Amin."
Sai ta ce,
"Na ji za ka riƙa zuwa Kano saboda aikin."
Aruk ya yi mamaki.
"Har Daddy ya gaya miki?"
Ta yi dariya.
"Ka manta ni da shi muna magana a kan komai ne?"
Duk suka yi murmushi.
Ammi ta ɗan yi shiru kafin ta ce,
"Aruk."
"Na'am Ammi."
"Duk inda za ka je, ka tuna da tarbiyyar da muka koya maka. Dukiya da suna kada su sa ka manta da mutuncinka."
Aruk ya kama hannunta cikin girmamawa.
"Na yi miki alƙawari, Ammi."
A wannan lokaci kuwa...
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU)
ALQALAMI ✍️YAFI TAKOBI 🤺
CIN AMANA…..8
KADUNA
Washegari tun kafin ƙarfe bakwai na safe, Aruk ya isa kamfanin Tafida Group.
Ba kasafai shugaban kamfani mai matsayinsa yake zuwa ofice kafin yawancin ma'aikata ba. Amma wannan yana ɗaya daga cikin halayensa. Yakan ce,
"Idan shugaban ya gaji da aiki, ta yaya zai sa ma'aikatansa su ƙaunaci aikinsu?"
Da ya fito daga motarsa, jami'an tsaro suka yi saurin miƙewa.
"Ina kwana, Yallabai."
"Lafiya lau. Yaya dare?"
"Alhamdulillah."
Ya yi musu murmushi ya shiga cikin ginin.
Tun daga ƙofar shiga har zuwa hawa na huɗu, duk inda ya wuce sai ma'aikata suna gaishe shi.
Wasu suna kiransa M.D, wasu kuma suna kiransa Sir Aruk.
Amma duk wanda ya gaishe shi, sai ya tsaya ya amsa cikin fara'a.
Da ya isa office dinsa sakatariyarsa miƙe tsaye.
"Assalamu alaikum, Sir."
"Wa alaikumus salam, Aisha. Yaya aiki?"
"Lafiya lau. Akwai wasiƙu guda huɗu da aka kawo, sannan ƙarfe tara akwai meeting."
"Tom."
Ta miƙa masa files din.
"Ga kuma jadawalin tafiyarku na mako mai zuwa."
Aruk ya buɗe fayil ɗin.
Da idanunsa suka sauka kan jadawalin, ya ga an rubuta da manyan haruffa:
ABUJA → KANO
Ya ɗan yi murmushi.
"Ashe Daddy bai canja shawara ba."
Aisha ta ce,
"A'a Sir. Har an fara shirya komai."
"Shi kenan."
Ya ajiye file ɗin a gefe.
---
Mintuna kaɗan bayan haka, Jabir ya shigo ba tare da ya buga ƙofa ba.
"Assalamu alaikum."
Aruk ya ɗago yana dariya.
Meyasa bakayi knock ba"
Jabir ya ja kujera ya zauna.
"Saboda na san idan na buga, za ka ce 'shigo'."
Aruk ya girgiza kai.
"Ka dai ci gaba."
Jabir ya ce,
"Na ji za ka tafi Kano."
"Eh."
"To ni ma zan rakaka."
Aruk ya ɗaga gira.
"Wa ya ce?"
"Ni na ce."
Duk suka yi dariya.
Aruk ya ce,
"Aikin fa za mu je yi, ba yawon buɗe ido ba."
Jabir ya ɗora ƙafarsa kan ɗaya.
"Ni ma aiki zan yi."
"Kai?"
"Eh mana."
"Wane aiki?"
"Naka."
Aruk ya yi murmushi .
A daidai lokacin ne Mustapha ya shigo ɗauke da computer.
"Na san idan na zo zan tarar da ku kuna hayaniya."
Jabir ya nuna shi .
"Mutumin da ko murmushi seyaga dama
Mustapha ya ce,
"Idan ba a yi aiki ba, wa zai biya albashi?"
Aruk ya yi dariya.
"Ku zauna duka."
Suka zauna.
Aruk ya buɗe taswirar aikin Kano.
"Ga yadda za mu gudanar da aikin."
Na kusan awa guda suna tattaunawa, suna tsara komai dalla-dalla.
a wajen ƙofar office din ..
Kuwa
Akwai wani mutum a tsaye .
Ya ɗan buɗe ƙofar kaɗan.
Yana sauraren duk abin da suke faɗa.
Da ya tabbatar da abin da yake so, ya rufe ƙofar a hankali.
Ya zaro wayarsa.
Ya kira wani.
Da aka ɗaga wayar sai ya ce cikin murya ƙasa-ƙasa,
"Sun tabbatar."
Daga can aka tambaye shi,
"Wane lokaci zai tafi?"
Mutumin ya amsa,
"Tomorrow"
Sai aka ce,
"Yawwa.... ku tabbata komai ya tafi yadda muka tsara."
Wayar ta katse.
Mutumin ya yi murmushi mai cike da mugunta.
Lokacinka yakusa Muhammad Aruk Tafida…..
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU) ALQALAMI ✍️YAFI TAKOBI 🤺 CIN AMANA……..9 ABUJA
Aruk, Jabir da Mustapha ba su san cewa akwai wanda ya saurari tattaunawarsu ba.
Har suka gama duba taswirar aikin Kano, babu wanda ya yi zaton wani yana saurarensu daga bayan ƙofa.
Mustapha ya rufe computer
"Alhamdulillah, na gama gyara dukkan bayanan aikin."
Aruk ya karɓi takardun ya duba su ɗaya bayan ɗaya.
"Kana da ƙwarewa sosai, Mustapha."
Mustapha ya yi murmushi.
"Kai ne ka koya mana kula da daki-daki."
Jabir ya kwanta jikin kujera.
"Ku dai ku ci gaba da yabon juna, ni dai yunwa nake ji."
Aruk ya kalle shi.
"Yunwa kuma? Ba ka karya ba ne kafin ka zo?"
"Na karya mana, amma ai ni Jabir ne."
Mustapha ya girgiza kai yana dariya.
"Wallahi ba na jin akwai abin da zai taɓa kosar da cikinka."
Jabir ya ɗaga hannu.
"Ni Allah Ya halicce ni da son abinci."
Aruk ya yi murmushi.
"To mu je restaurant ɗin company n."
"Yanzu ka yi magana."
---
Suka sauko zuwa babban ɗakin cin abinci na kamfanin.
Da zarar ma'aikata suka ga Aruk ya shigo, wasu suka miƙe suna gaishe shi.
"Ina kwana, Sir."
"Lafiya lau."
Ya amsa babu yabo babu fallasa..
Ba ya son a ware masa teburi na musamman. Duk lokacin da ya samu dama, yakan zauna tare da ma'aikatansa yana hira da su.
Hakan ne ya sa kusan kowa ke ƙaunarsa.
Suka zauna.
Ana kawo musu abinci, Jabir ya ce,
"Aruk."
"Na'am."
"Ban taɓa tambayarka ba."
"Me?"
"Me ya sa har yanzu ba ka yi aure ba?"
Mustapha ya ɗan yi murmushi ba tare da ya ce komai ba.
Aruk ya ɗauki kofin ruwa ya sha kaɗan kafin ya ce,
"Lokacin Allah nake jira."
Jabir ya yi dariya.
"Lokacin Allah ko lokacin da za ka samu wadda ta dace?"
Aruk ya girgiza kai.
"Duk abu ɗaya ne."
Mustapha ya ce cikin natsuwa,
"Gaskiya ne. Aure ba wasa ba ne."
Jabir ya ce,
"Ni dai ina ganin 'yan mata da yawa suna bibiyar Aruk."
Aruk ya katse shi.
"Ka bar wannan maganar."
"Me ya sa?"
"Saboda ba ita ce ta kawo mu nan ba."
Jabir ya yi shiru.
Zaune take tana kallonsu tana sakin murmushi daka kalleta zakasan tana cikin shauqi
Aruk take kallo tun lokacin da ya shigo.
Ba ta ma ko ɗauke idanunta daga kansa ba.
Husnah.
Ta zo kamfanin ne domin ta sake kawo wasu takardu.
Amma da ta ga Aruk yana dariya tare da abokansa, sai ta zauna a nesa tana kallonsa cikin nutsuwa.
A zuciyarta ta ce,
"Lallai abin da Daddy Tafida ya faɗa gaskiya ne. Muhammad Aruk mutum ne mai sauƙin kai."
Ba tare da ta sani ba, wata ma'aikaciyar kamfanin ta lura da yadda take kallon Aruk.
Ta yi murmushi a ranta.
"(Da alama akwai abin da zai faru nan gaba...")
---
A wannan lokacin kuwa...
A katafaren gidan Tafida.
Ammi tana zaune a falo tana shan shayi.
Wayarta ta yi ƙara.
Da ta ɗaga, sai murmushi ya bayyana a fuskarta.
"Assalamu alaikum."
Daga can aka amsa.
"Wa alaikumus salam, Hajiya Zainab."
"Ashe kece?"
"Eh."
"Ya gida?"
"Lafiya lau."
Suka ɗan yi hira.
Can sai matar ta ce,
Ina yarona kuwa.
Wai aruk yana company
Gobe ma yake shirin shigowa kanon
Matar tace ."
Tom Allah yatemaka
Amma me zezo yi
Ammi ta gyara zamanta.
"Eh, akwai wani babban aikin kamfani."
"Allah Ya kiyaye hanya."
"Amin."
Da aka kashe wayar, murmushin Ammi ya ɗan gushe.
Ta kalli hoton Aruk da ke rataye a jikin bango.
A hankali ta ce,
"Allah Ka kiyaye min ɗana daga sharrin mutane."
(Hmmmm nikam nace ammi Ba ki san cewa addu'ar ki ta zo daidai lokacin da wasu mutane suke shirin kitsa wani mugun makirci ba...ameen dai )
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU) ALQALAMI ✍️YAFI TAKOBI 🤺 CIN AMANA…….10
KADUNA
Bayan sun gama cin abinci, Aruk, Jabir da Mustapha suka koma ofis.
Lokacin da suka shiga, Aruk ya cire agogon hannunsa ya ajiye a kan tebur, sannan ya zauna yana duba wasu takardu da ake buƙatar ya sanya wa hannu.
Mustapha ya buɗe computer.
"Aruk."
"Na'am."
"Waɗannan takardun na company Kaduna sun rage."
"Ka kawo su."
Mustapha ya miƙa masa file ɗin.
Aruk ya fara dubawa a hankali. Ba ya son sanya hannu a kan takarda ba tare da ya karanta ta dalla-dalla ba.
Jabir kuwa ya zauna yana jujjuya biro a hannunsa.
Ya kalli Aruk.
"Wallahi ina mamakin haƙurinka."
Aruk bai ɗago ba.
"Da me?"
"Ni da na ga takardu masu yawa haka, tuni kaina ya fara ciwo."
Mustapha ya yi dariya.
"Shi ya sa kai ba shugaban company ba ne."
Jabir ya harare shi.
"Kai ma ka samu bakin magana."
Dukkansu suka yi dariya.
Sai wayar cikin ofice ta yi ƙara.
Aruk ya ɗaga.
"Hello."
Daga can sakatariyarsa Aisha ta ce,
"Sir, akwai wata ma'aikaciya a reception. Ta ce tana son ganinka."
"Wace ce?"
"Ta ce sunanta Khadija. Ta ce daga sashen lissafi take."
"To ki ce ta shigo."
"Okay, Sir."
Mintuna kaɗan bayan haka aka buga ƙofa.
"Shigo."
Ƙofar ta buɗe.
Wata budurwa cikin shigar ma'aikata ta shigo. Ta yi sallama cikin ladabi.
"Assalamu alaikum."
"Wa alaikumus salam."
Ta miƙa wani file.
"Sir, an ce na kawo wannan domin ku duba kafin a tura shi banki."
Aruk ya karɓa.
"Nagode."
Ya buɗe file ɗin.
Da ya fara dubawa, sai fuskarsa ta sauya.
Ya sake duban wata takarda.
Sai wata.
Sai ya ɗago ya kalli Khadija.
"Waye ya shirya waɗannan takardun?"
Ta ɗan ruɗe.
"Sir... ni dai an ba ni ne kawai na kawo."
Aruk ya matsa kujera gaba.
"Ki kira shugaban sashen lissafi yanzu."
"To Sir."
Ta fita da sauri.
Jabir ya kalli Aruk.
"Lafiya?"
Aruk ya nuna masa takardar.
"Duba wannan."
Jabir ya karɓa.
Bayan ya karanta, sai ya ce,
"Subhanallah..."
Mustapha ya karɓi wata takardar.
Ya haɗe gira.
"Wannan adadin kuɗin bai dace da wanda ke cikin tsarinmu ba."
Aruk ya gyada kai.
"Hakane."
Mustapha ya ce,
"Wato akwai wanda ya canja bayanan kuɗin?"
Aruk ya ce cikin natsuwa,
"Ko dai kuskure ne..."
Ya ɗan yi shiru.
"...ko kuma wani yana ƙoƙarin yin zamba."
Office ya yi tsit.
Babu wanda ya ƙara cewa komai.
Bayan kusan minti biyar, shugaban sashen lissafi ya shigo da sauri.
Gumi ya fara keto masa.
"Assalamu alaikum, Sir."
"Wa alaikumus salam."
Aruk ya nuna masa kujerar da ke gabansa.
"Zauna."
Mutumin ya zauna, amma ana iya ganin tsoro a fuskarsa.
Aruk ya ɗaga file ɗin.
"Ka san wannan?"
"Eh Sir."
"Ka duba shi sosai kafin ka kawo?"
"Eh... na duba."
Aruk ya zaro wata takarda daga cikin file ɗin.
"To ka gaya min, me ya sa adadin kuɗin da ke nan ya bambanta da wanda ke cikin tsarin kamfanin?"
Mutumin ya yi shiru.
Jabir ya kalle shi.
Mustapha ya ci gaba da nazarin fuskarsa.
Aruk ya sake maimaita tambayar .
"Ina tambayar ka..."
Mutumin ya haɗiye yawu.
"Sir..."
Ya kasa ƙarasa maganar.
A lokacin ne wayar Aruk ta yi ƙara.
Ya duba.
Daddy Calling...
Ya ɗaga wayar.
"Na'am Daddy."
Muryar Daddy ta fito cike da damuwa.
"Aruk, ka zo office dinsyanzu."
"Lafiya Daddy?"
"Ka zo kawai."
Kafin Aruk ya sake magana...
Daddy ya kashe wayar.
Aruk ya kalli Jabir da Mustapha.
Fuskarsa cike da damuwa.
Ba tare da ɓata lokaci ba ya miƙe tsaye, ya nufi office din Daddy...
TOH JAMA'A WANNAN SHI'AKE KIRA DA RUDANI
SHIN WAYE YAKE BIBIYAR ARUK ?
ME ZE FARU DA ARUK NAN GABA?
SHIN INA KUDADEN SUKA SHIGA?
ME DADDY YAGANI?
DUKA KUBIYONI ACIKIN WANNAN LITTAFIN NA CIN AMANA
WANDA NI JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM
WACCE AKAFI SANI DA (ZUZU)
TARUBUTA
Karku manta da like and follow
*** Ko https://www.arewapen.com/chapter?id=6a744c4ce594357692ccaa8f
Don samun cigabansa
Masu sha awar tuntubata akan wani littafi ***