MATAR GIDA
MATAR GIDA 002
SHUUKRAN/022
P2
Karfe hudu na la'asar Amirah ce zaune cikin wani ɗakin hotel laptop daure kan cinyarta tana rubuta letter,so take ta tura letter a wajen aiki, annual leave take son dauka,hutun kwanaki talatin na ranakun aiki, bayan ta gama lissafin kwanakin ta ga ya fita mata kusan wata ɗaya sati biyu,bayan ta gama drafting letter ne ta yi editing kafin ta turawa oganta ta e-mail,wayarta dake gefinta ta dauko dalilin kira da ake mata ganin me kiran yasa ta kashe wayar gaba ɗaya Ɗalha ne ke kira,daga lokacin da ta fita daga yanzu ya yi mata miss called kusan sau hamsin dalilin kiran nasa bai wuce Fauziyya ba,bayan ta kashe wayar ne ta fita harabar hotel ɗin cikin fita ta mutumci sanye take ciki wata doguwar riga egyptain abaya ligth blue yadda ta yi rolling farin gyale kafafunta sanye da simple black shoe,fita daga hotel ɗin ta yi gaba ɗaya yadda ta kama hanyar cikin gari,ta tare abin hawa ta faɗa masa sunan pharmercy dake kusa da hotel ɗin,tafiyar mintina goma sha biyar ne daga hotel ɗin zuwa pharmercy,bayan ta sallame ɗan sahu ne ta shiga cikin pharmercy ɗin yadda ta sami ɗaya daga phamarcist ɗin wata babbar mace ce da a ƙalla zata kai shekaru 50 a duniya bayan Amirah ta gaishi matar ne ta cewa matar ta yi yaye ta bata maganin zazzaɓi da kuma wanda zai rage mata zugin nono,ba tare da ɓata lokaci ba matar ta haɗawa Amirah magunguna,ATM card ɗinta ta ciro daga hand bag ta biya ƙudi magunguna kafin ta bar phamarcy ɗin,wani resturant dake can tsallakin titi Amirah ta nufa inda ta siya abinci har take away biyu
Bayan komawarta hotel ta rage kayan jikinta kafin ta samu waje ta zauna kan resting chair dake cikin ɗakin hotel ɗin ta dauki take away ɗaya ta buɗe ta fara cin abinci nan take wani kuka ya taho mata tun barinta gida take kukan zuci sai yanzu ta samu damar buɗe baki ta fara kuka gwanin ban tausayi,tunawa ta yi da ƴaƴanta,abincin da ta girka masu ta sani bazai kai su ci har dare ba,cikin muryar kuka ta ce ''ya Allah ka tsare min ƴaƴana ya Rabbi ka kulan min da su Allah ka bani hakuri da juriya'' tana kaiwa nan kuka ya ci karfin ta saida ta yi mai tsafta kafin daga bisani ta tashi ta shiga bathroom dake ɗakin hotel ɗin wanka ta yi sannan ta dauro alwala a lokacin har an tayar da sallah kasancewar hotel ɗin tana sabuwar unguwa ce so akwai gidajen mutane da kuma masallatai a layin,bata tashin kan dardumar ba saida ta yi sallar isha'ai ta dauki lokaci mai tsawo zaune kan darduma tana jero addu'oi kafin daga bisani ta shafa,da kyar ta samu ta ci abinci rabin take away shima ɗin dan tana son shan magani ne shi yasa,kwanciya ta yi lamo kan king size bed ta takure kanta waje ɗaya tun sanda ta yi aure yau shine rana na farko da zata kwanta ita kaɗai ba tare da ƴaƴanta a gefinta ba,babban abinda yafi damunta shine Fauziyya bata san halin da take ba,so take ta ƙoyawa Ɗalha hankali kullum cikin kushi ta yake bai taɓa yabon ta ba duk wani ƙokarin da take wajen kula da ƴaƴanta baya gani kullum cikin ƙorafi yake,tun sanda ta aure shi bai taɓa yin sati ba tare da ya ce mata zai saketa ba,a ranar ta cika kwanaki takwas a gidansa ya dawo gida ya tarar ta yi barci bata rufe ƙofa ba ya tambaye ta dalilin da yasa bata rufe ƙofa ta ce masa bata san sanda barci ya dauke ta ba,saboda uni ranar ɓaƙi sun yi ta zuwa ganin ɗakin amarya hakan yasa ta gaji bata san sanda barci ya dauke ta ba ,ta daura da ''kasan ban saba ayyuka masu yawa ba,a gidanmu bana aikin komai sai dafa abinci shima kuma ba kullum ba'' ta yi magana cikin wasa,buɗar bakinsa sai cewa ya yi ''tunda ba ki saba aikin karɓar baƙi ba sai ki koma gidanku aiy in baza ki iya ba''tun daga wannan ranar Ɗalha ke mata baraza kullum nuna mata yake shi zai iya rayuwa ba tare da ita ba,ita kuma babu abinda take tsoro kamar rabuwa da Ɗalha da ya fahimci hakan sai ya rinƙa mata barazanar rabuwa da ita ba ƙaramin kuka ta yi cikin wannan daren ba,dalilin zuwanta hotel so take Ɗalha ya ga amfani ta a gidansa shi yasa ta tafi hotel ta kama ɗaki,ba da niyyar iskanci ba,ta kama ɗaki ne dan bata son iyayenta su kira Ɗalha su bashi hakuri kan ya maida ta,da gangan ta bar masa yara har Fauziyya,ta barsu ne dan ya yi reno yaji yadda mata ke ji,Amirah da Ɗalha baƙi ne garin aiki ne ya kawo Ɗalha Lafia asalinsa ɗan Zamfara ne iyayensa da kowa nasa a can duke ita kuma Amirah bafulatana ce ƴan asalin Chad zama ya kawo iyayenta ƙaramar hukumar keffi dake jahar Nasarawa,ta hadu da Ɗalha ne a garin Lafai lokacin ta samu addimision a Fulafai,bayan auren su mahaifinta ya sama mata aiki a state wani babban kamfani a garin Lafia,babu abinda ta nema ta rasa wajen Ɗalha matsalar sa ɗaya rashin iya magana da kuma rashin sanin darajar ɗan adam,mai da sabulun wankanta kaɗai take siya da albashinta sai ƴan abubuwan da ba'a rasa ba haka yasa ta tara ƙuɗaɗe masu yawan gaske cikin asusun bankinta a wannan dare barci ɓarawo ne ya dauke ta
A can wajen Ɗalha kuwa tun azahar Fauziyya ki aikin kuka ya yi rarrashi har ya gode Allah,gashi ta ƙi yarɗa ƴan uwanta su riƙeta ida Dady kawai duk motsin da ya yi sai ta kira sunansa duk inda ya sa ƙafa Fauziyya na manne da shi,da kyar ya samu ta sha tea,bayan ta gama sha tea ta sa wani sabon kuka tana kiran Mumy alamar tana son shan nono,zuwa wannan lokaci Ɗalha ya fara fita hayyacinsa ga kukan Fauziyya ya ƙarwaɗe gida ga hayaniyan da ƴan uwanta ke yi yadda yaran maza su huɗu ke ta bugun ball,matan biyu kuwa sun mayar da hankali kan bebin roba dake gabansu sai faman surutu suke su kaɗai,wani tunani ya faɗowa Ɗalha nan take ya cire wayarsa cikin aljihu ya buga layin ƙanin Amirah Kabir,bayan Kabir ya amsa kiran Ɗalha ya fara jansa da hira suna cikin hira Fauziyya ta sake kuka nan Ɗalha ya shiga rarrashinsa hankalinsa ya rabo biyu hakan yasa Kabir faɗin ''ina mamanta? kaita wajen mamanta mana'' shiru Ɗalha ya yi,a tunaninsa Amirah ta je gidan mahaifinta maganar Kabir yasa shi fahimtar bata gidan mahaifinta to ina ta tafi?" maganar Kabir ne ya katse wa Ɗalha tunani inda ya ce ''hello.. hello kana jina Yayanmu?" Ɗalha ya ce ''ta zaga ne yanzu zata fito''Kabir ya ce ''yauwa Yayanmu pls in ta fito ka ce mata tun ɗazu nake kiran layinta a kashe akwai maganar da nake son yi da ita ne'' cike da tsantsan mamaki Ɗalha ya ce ''ok zan faɗa mata'' tsabar mamaki Ɗalha ya ji gaba ɗaya bazai iya cigaba da magana da Kabir hakan yasa ya ce ''zan kiraka anjima Kabir'' daga hakan suka yi sallama bayan Ɗalha ya kashe waye ya faɗa duniyar tunani mamaki ne ya cika shi bai taɓa kawo Amirah zata iya tafiya ta bar yaranta ba a tunaninsa tare da yaran zata tafi gidansu,amma sai yaga har Fauziyya ta bari me hakan ke nufi? ba yau ya fara yi mata barazana da saki ba,da sai ta yi ta basa hakuri har da kuka,sai yaga ta daina bashi hakuri duk sanda ya ce zai saki ta sai ta ce kana sakina zan tafi da yarana bazan bar ƴaƴana sun sha wahala wajen matarka ba,amma abin mamaki sai gashi yau ya mata saki ɗaya ta tafi ta bar yaran gaba ɗaya yana cikin wannan tunani ne ya ji wani ruwa mai ɗumi ya gangaro masa cikin wando nan ya fara kalle kalle so yake ya gano daga inda ruwa yake ƴarsa Sumayya ƴar shekaru biyu da rabi ta ce ''lah Dady Fauziyya ta yi maka fitsari a jiki'' ta kare magana tana babbaƙa dariya wani irin zabura Ɗalha ya yi ya ce ''what fitsari,a ina?" har sannan Sumayya na dariya ta ce ''wallahi Dady fitsari ta yi maka,in ba'a sa mata pampers ba bamu daukanta har Mumy ma bata daukan ta,kullum sai Mu ta ce mata in zata yi fitsari ta yi magana amma bata ji''wani mugun kallo Ɗalha ke yiwa Fauziyya ta ƙi yarda ta kallesa ta sa kai ƙasa kamar munafuka Ɗalha ya yi magana cikin ɗan fushi ya ce ''wuce ki je toilet'' har sannan kanta ƙasa a hankali ta sauko daga kafarsa ta nufi hanyar ɗakin mahaifiyarta,daidai kofar ɗakin ta sake wani kuka cikin Hausar ta da bai fita da kyau ta ce ''Mumy fiyaye'' wani mugun kallo Ɗalha ya bi bayanta kafin ya kira babban ɗansa ɗan shekara takwas Sudais ya ce ya je ya yiwa Fauziyya tsarki
Karfe uku da wasu ƴan mintina na rana Ɗalha ne tsaye cikin ɗakinsa cikin shirin zuwa zance wajen masoyiyarsa Unisa Sudai ne ya shigo ɗakin cikin uniform ɗin islamiyya,bakinsa dauke da sallama Ɗalha ya amsa masa sallama cike da girmamawa Sudai ya ce ''Dady kaga Haydar yaƙi sa uniform ɗinsa kullum sai ya sa mun yi lattin zuwa islamiyya,kuma bulala ake mana in mun yi latti'' shiru Sudais ya yi yana wasa da gefin rigarsa ya ce Ummu Abiha kuma ta ƙi wankin plate ɗinda muka ci abinci'' wata doguwar numfashi Ɗalha ya sauke kafin ya ce ''ka je ka ce masu in na fito basu gama shire ba sai na zane su'' da to Sudais ya amsa kafin ya fita daga ɗakin ita dai Fauziyya har sannan tana manne da Dadynta, karfe huɗu saura mintina goma Ɗalha ya fito daga ɗakinsa tsayawa ya yi a parlour yaga duk sun ɓata ko ina gaba ɗaya sun hargitsa gidan nan ya fara kwala masu kira duk suka fito amma banda Rayyan har Ɗalhat ya tada mota Rayyan ya fito da gudu hannusa riƙe da rigar islamiyya ɗaya hannu yana riƙe da robar ruwa,daga shi sai gajeren wando wani irin tuƙiƙin bakin ciki ne ya tasowa Ɗalha cike da ɓacin rai ya fita mota ya ce ''me ka ke tuntuni me ya hanaka sa uniform ɗinka?"nan take Rayyan ya fara kuka cikin muryar kuka ya ce ''banga wando islamiyya na ba'' baki buɗe Ɗalha ke kallon sa cikin zuciyarsa ya ce ''haka Amirah ke fama da yaran nan kullum ya ilahi''
SHUUKRAN