HASASHEN SOYAYYA

Hs 21

by @legendspen

_Page 21_ 




~~~~~~Nyan'ya



Umma ce zaune kan kujera yar tsugunno ta figar zogale, daga gefen ta kuma Abdul ne tsaye jikin rijiya yana ɗebo ma ta ruwa cikin rijiyar. Kwankwasa ƙofar gidan na su aka fara yi da ƙarfi babu nutsuwa. "Waye anan?." Abdul ya faɗa, bai ƙarasa magana ba Goggo Larai ta shigo cikin gidan babu ko sallama, tsayawa ta yi sanan ta ce. "Ku shigo mana." Ba ta rufe baki ba Su Isiyaku da Ɗan-ladi suka shigo, har da saddiƙu da wasu yan cikin gidan. Da mamaki dai Umma da Abdul suke kallonsu, domin basa iya tuna lokaci na ƙarshe da su ka zo gidan gaba ɗayansu haka, zai iya kasancewa tun lokacin mutuwar mahafinsu.


Ta shi Umma ta yi ta shiga ɗakko musu tabarma tana faɗin. "Sannunku da zuwa." 


"Yawwa." Goggo Larai ta faɗa, sauran kam shiru su ka yi na su ce ko ƙala ba. "Ga waje ku zauna." 


"Bazama ya kawo mu ba, ina sauran yaran?." isiyaku ya faɗa. "Wane yara?." Abdul ya yi tambayar ganin zasu nemi rainawa mahaifiyarsu hankali. "Sauran yayun na ka." 


"Au ba sa nan." Ya faɗa yana ci gaba da jan ruwan sa, domin yasan ba alheri ba ne ya kawo su. "To anemo su." 


"Yaya Isiyaku Lafiya dai?." Umma ta tambaya. "Wai ba mu isa mu nemi ganin su ba ne?." Goggo larai ta faɗa tana wani hare-hare. "Basa nan ne, Bhatool suna biki ta je gidan biki, ita kuma Karima ta na gidan mijinta."


"To duka ayi musu waya su zo muna son ganin su." 


"Abdul kira mun Karima." Waya ya shiga dannawa, bayan ya kira Yaya karima ne ya bawa Umma wayar, Bhatool ce ta ɗaga wayar tana faɗin. "Ƙanina ya ake ciki ne?." 


"Bhatool."Ummah ta faɗa. "Na'am Ummana ina kwana?."


"Lafiy ƙalau Bhatool, ina Kariman?." 


"Suna ciki ita da Yayan."


"Kai ma ta wayar."


"Lafiya dai Ummah?."


"Kai ma ta Bhatool." Ummah ta faɗa a dakile. "Yaya zo ki karɓi waya." Bhatool ta faɗa, tana zuwa ƙofar ɗakin na ta, fitowa ta yi tana faɗin. "Me yasa baki da hankali ne dan Allah?." Cuno baki ta yi gaba sanan ta ce. "Ni dai amshi." 


"Hello, au wai Ummah ce?." Yaya karima ta faɗa a lokaci guda. "Ni ce Karima mijinki na nan?." 


"Eyh yana nan Ummah."


"To ina so dake da shi da Bhatool duk kuzo gida yanzu."


"Iyayen Senate ɗin sun zo ne?."


"Waye Senate? , ni dai na ce ku zo yanzu."


"Mu bamu gayyaci mijinta bah." Yaya Karima ta jiyo muryar Goggo Larai ta faɗa, kashe wayar Umma ta yi ba ta so su Yaya Karima su ji mutanen dake gidan. "Goggo Larai?." Yaya Karima ta faɗa a ran ta. "Su wane Goggon?." Bhatool ta tambayeta. "Haka Umma ta ce mu zo gida dukan mu yanzu, kuma na ji Goggo Larai ta na magana wai ba su gayyaci mijina ba." 


"Mene ya kawo su gidanmu haka?."


"Wallahi Bhatool nima bansaniba, je ki shirya dai." Yaya Karima ta faɗa tare da shigewa ciki.



"Wai wane mutumi ne take kira haka?." Ɗan-ladi ya tambayi Isyaku. "Nima bangane wanda take nufi ba." 


"Lauya mijin yarta ta fari." Goggo Larai ta faɗa. "A'a mene na gayyato mana shi kuma, to kar ya kuskura yazo." 


"Dole yazo mana, domin a yanzu shine wakili a kan ta da sauran 'yan-uwata, domin wayanda ya kamata su zama wakilan na su sun watsar da su." 


"A'ah, kar ki kuskura ki gaya mana magana fa." Goggo Larai ta faɗa. "Muma kar ku kuskura ku faɗawa Mahafiyar mu magana." Abduk ya faɗa, domin wani mugun haushin su ne ya dirgar masa a zuciya. "Kai ka kiyaye fa." Saddiƙu ya faɗa cikin muryarshi ta marasa jin magana. "Rufe bakin ka Abdul." 


"Wallahi Umma babu wanda ya isa ya zo cikin gidanan ya ce zai gaya miki magana, idan da sun yi sum ci banza yanzu basu isa ba, yanzu 'ya'yanki sun ta sa, sun yi girman da zasu tsaya miki a ko ina, wallahil azim duk wanda ya ce zai ɗaga miki hankali sai na haɗa shi da shari'ah." 


"Eyh, Lallai yaro ka fara riƙe kuɗi." Ɗan-ladi ya faɗa yana kallon yadda Abdul yake magana. "Kabarshi kawai." Goggo Larai ta faɗa. 



Ba'afi mintinu ashirin ba su Bhatool suka shigo gidan, Bhatool na sanye cikin doguwar rigar atamfa, ta yafa ƙaramin mayafi fuskarta a haɗe kamar wacce aka aikuwa da saƙon mutuwa haka ta shigo gidan, tsayawa ta yi ƙiƙam tana ƙare musu kallo. "Lafiya?." Ta faɗa cike da mamaki. "Bhatool masoyiyah." Saddiƙu ya faɗa, yana washe ma ta baki. Da wani mugun kallo tabi shi, sanan ta ce. "Waye wanan kuma?." Dan ota harga Allah ba ta gane shi ba. "Mijinki, wanda zai aure ki."  Goggo Larai ta faɗa, tsaki ta ja sanan ra shige ciki kusa da Ummah dai-dai lokacin da Yaya Karima suka shigo, gaishe su su ka yi sanan su ka ƙarasa wajen Ummah, ba su kai ga zama ba Goggo Larai ta ce. "Ba ma son bare ya zauna a nan." 


"Duk maganar da zakuyi anan, to a gabansa za ayi domin shine yake kamar jagora a garesu, shi ke tsaya musu a kan komai da komai, Allah ne gatan 'ya'yana, shine gatan su." 


"Mu mu yi maganar da zamuyi da abunda zamu yi mu huce." Isiyaku ya faɗa. "To daman mun zo ne mu gaya muku cewa zamu ɗaura auren Bhatool da Saddiƙu, Abdul da Sajida, kuma mun zo ne mu daura auren a yau."


"Dake a garin mahaukata ake ko?." Abdul ya faɗa yana wani hararasu, Bhatool kam miƙewa tsaye ta yi sanan ta ce. "Ni kam wanan rashin hankalin ba a gaba na ba." daga haka ta yi cikin ɗaki. "Bari na fara kiran jami'an tsaro daman Umma nema nake kawai su shigi hannu, wallahi sai sun yi aman kuɗin da suka ci na gadon mahaifinmu." Abdul ya faɗa yana zaro wayarsa, wani ƙululu cikin su Goggo Larai ya ba da. "Ah kaga kai me yasa baka da hankali ne?." Ɗan-ladi ya faɗa. "Bar shi dai ya kira su, tun da jahili ne." In ji Isiyaku. "Abdul kar ka kuskura ka kira wani." Umma ta faɗa daga inda take, wayar ya mayar cikin aljihunsa sanan ya ce. "Ku ta shi ku fice mana daga gida, kar ku kuskura na sake ganin ƙafar wani cikin gidanan, dan wallahi sai na ɗauki mummanan mataki a kan sa." 


"Ai ba mu yi lalacewar da zaka yi mana haka ba, to ba zamu fita ba." Isiyaku ya faɗa. "Abdul ka rufe baki kar na sake jikin bakin ka anan." Ɗakin da Bhatool ta shiga nan shima ya shiga. "Ni Umma a ganina wanan abu ne mai sauƙi, a matsayina na babban lauya kuma mai kare su Bhatool, ki bar su su yi duk abinda su ka ce zasu yi, ai shari'a na nan." 


"Kai ɗan ɗorin ɗo sa no, rufemun baki mara kunya." Goggo Larai ta faɗa tana maka mai harara. "Yoo ban da rashin ta ido har mu ne zai faɗawa shari'a, muna matsayim sirikan sa." Ɗan-Ladi ya faɗa, dama su uku ne suke ta magana sauran duk sun yi shiru. "Ai da an nuna masa darajar mu dai bazai mana haka ba, har yau ina baƙin cikin Ahamdu da ya aura wanam figaggiyar mitsiyaciyar." Goggo Larai ta faɗa. "To Shima ba Umarnin Baba ya bi ba, amma nasan har ya mutu baya farin ciki da aurenta." 


"Kum ga bayin Allah ya isheku haka, tun da bakwason harkar arziƙi bari ayi ta tsiya." Yaya Karima ta faɗa tana miƙewa. "Abdul fito ka kira mutanen kawai, gwanda mu dan gana ga kotu." Sallama su ka ji a ƙofar gidan duk kan su su kalli ƙofa. Abdul da ya fito yanzu ne ya nufi ƙofar, ya bar su Goggo Larai ciki na ƙululu. 


Manyan mutanen da ya gani ne ya sa shi tsugunnawa ya gaida su, ciki har da Alhaji Habu Naira wanda suke kasuwanci sosai da sosai. Alhaji Habun ne ya ce. "Abdul nan ne gidan ku kenan?."


"Eyh yallaɓai nan ne."


"Toh Ma sha Allah, Abdul muna son masauki domin magana mai muhimmanci ce ta kawo mu." 


"Tom yallaɓai." Abdul ya faɗa tare da komawa ciki, daga farkom gidan ya tsaya ya kira Barrister, tasowa Bartister ya yi zuwa inda Abdul ɗin ya ke sanan ya ce." Su waye?." 


"Wasu manyan mutane ne, ciki har da Alhaji Habu naira ɗan kasuwarmu, sun ci magana ce mai muhimmaci suna son waje kuma ga shi wayanan tijararrun suna ciki." 


"Wallahi kam Abdul, yanzu za su iya musu hauka."