Chapter ONE
by @gadanya
Kukan da take ne ya hana taji tsayuwarsa akusa da ita, sai daya yi salama kusan sau uku sannan ta xago da kai. Mutumin da suka samu savani a cikin jirgine wanda ya kira kansa da Hafiz, ta xago tana kallon sa. Ya xaga kai irin yana tambayarta me ya same ta take kuka, kamar bazata yi masa magana ba amma da ta tuna kusan mintinta talatin ba wanda ya kulata, sai shi da ya tausaya mata.
Sai da ya qarace mata “kukan me kike, ina ‘yar uwar taki tayi na ganki ke xaya” tana shasshekar kuka tace “an shiga da ita can xakin tana nuna masa da hannun ta”. Yar jakar dake rateye a kafaxarsa ya sauke a kusa da ita. Ya nufi wajen mutumin dake duba computer xin da ake screening na mahajjata.
Tana ji yana masa magana da larabci, bayan sun gama magana ya dawo wajenta yace, “garin qaqa ta saka wani abu a jikin ta har ta bari suke zargin ta”.
Tana kallonsa kamar ba zata yi magana ba cikin sanyin murya “ni ma ban san ta saka wani abu ajikin ta ba sai bayan an turata xakin ne qawarta ke gaya min goro ta voye a jikinta, cikin mamaki ya kalleta “ ina ita qawarata ta ke?” ta na nuna masa hanya fita “ta wuce tun xazu ta waccan kofar, ita kuma sun shiga da ita can xakin, “ yace ki daina kuka ba abinda za ayi mata checking xin ta za suyi su qwace abinda ta voye su fito da ita.”
Ba a fi yan mintuna ba Najwa ta fito daga xakin idanun ta sun yi zuru zuru, ta nufo inda ta hangi Najma ita da Hafiz. Tana zuwa ta rungume Najma tana “ki yafe min Yaya Najma ba zan kuma ba tsautsayine da sharrin zuciya, “ tana ta kuka.
Hafiz ya kalle ta ya kauda kai sannna yace“mu wuce ko? Dare na qarayi”. Ko da suka fito motacin da zasu xauke su suna jiransu, sukayi sallam suka wuce kowa ya nufi masaukinsa.
Koda aka kaisu masaukinsu Najma ta kalli Najwa tace, “amma baki yi min adalci ba mai yasa baki gaya min ga abinda zaki yi ba ni da na bar nawa a jaka me ya same shi. Haka kawai zaki biyewa wata, gashi ita ta wuce ta barki da jangwan ko wannan tashin hankalin aka barki da shi ya isheki banda nawa da ya tashi. Banda Allah ya kawo Hafiz da bansan me zai faruba naje banxaki kamin in dawo akace an shiga da ke wannan xakin.”
Najwa kallon ta take yi kawai dan bata san abinda za tace ma ta ba dan ta san bata da gaskiya. Amma abin na damun zuciyarta dan ba a tava yi mata irin wulakancin checking xin da aka yi mata yau ba dan sai da ta sa ta cire komai na jikin ta.
“Kiyi hakuri Yaya Najma kamar yarda nace miki tsautsayine bazan qara ba nima banji daxin abinda akayi min ba”.
Ko daNajma ta kwanta sai tunanin mutumin nan da ya kira kan sa da Hafiz ashe mutumin arziki ne ba kamar yarda da zuciyarta tayi mata zargin mara mutunci ne ba.
Farkon haxuwar su rashin mutunci tayi masa sanda suka shigo cikin jirgi kusa da taga tayi booking amma sai ganin wani tayi ya tsare wajen dan haka tayi masa magana ya nuna kamar ma bai san tana yi ba.Dan haka taje ta kira ma’aikatan jirgin sukayi masa magana, “bai ga mai tada shi ba ai cewa akayi kowa ya samu waje ya zauna kawai” abin da ya fito daga bakinsa ke nan.
Dole tana zunburar baki ta zauna a kujerar kusa da shi tana ta mita haka kawai ya tsare mata waje bai san yarda ta yi qoqarin ayi mata booking window sit ba amma ya bata mata budget dan ba abinda ke burgeta taga jirgi na keta hazo to yau dai yai mata buqulu.
Bayan jirgi ya daidaita an yi xan nisa ta tafiya sai yayi ma ta sallama zai wuce ya shiga toilet bayan ya dawo sai yace, “ta shige ciki xin shi zai zauna a mazauninta.”
Abin kamar bai bata haushi dan bata zaci yana jin hausa ba yarda taga kamanninsa, dan daga ganin sa kaga balarabe dogo ne bashi da qiba can, yana da dan saje kaxan ba mai yawa ba hancin sa na da tsawo kamar na larabawan idanun nasa ma daidai misali shirt ce da blue jeans a jikin sa gashin sama irin na larabawa, kyakkyawane na ajin farko, amma daga baya sai taji xan kunyar maganganun da ta faxa tace, “ba komai ka shige na hakura, yace, “a’a ki shiga wajen tagar dan na lura tunda ki ka shigo fushi kike baki saki fuskar ki ba”.
Bayan ya zauna yace, “sunana Hafiz ke fa menene sunan ki?” ta na kallonsa bakinta ya dan motsa da ba a kusa da ita ya ke ba, da ba zaiji ba, “Najma”.Shima kalon na ta yake, “ba dai fushi kike da ni ba ayi hakuri ayi min afuwa na bata ran gimbiya”.
Kallon shi take kurum dan ta qasa magana fushin fuskarta ya warware sai murmushi take yi kawai, a hankali ta saki su ka cigaba da hira kamar su san juna baa yau ne haxuwarsu ta farko ba.
Ita Najwa bacci ne ya dauketa har sai da suka isa Madina sannan ta farka da yake mazauninta a bayansu take ita da wata mata wacce har suka yi sabo kan su sauka. Lokacin suka shirya wannan kitimirmira ta boye goro a jikin su.
Maganar Najwa ce ta jawo hankalinta ta dawo daga dogon tunanin da take, “Yaya Najma kiyi haquri nace miki ba zan kuma ba wannan ma tsautsayine”.
Ta dafa kanta “kada ki damu Najwa komai ya wuce, mushirya mu tafi masallaci lokaci na qara kurewa.”
Kwanan su biyu da zuwa madina bayan sallar asuba sun shiga Rauda sai suka vacewa juna dan haka Najma tana tsaye a kofar shiga ta gate (7) saboda nan su kayi za su riqa jiran xaya daga cikin su idan sun vacewa juna a masallaci.
Kamar daga sama taji an kira sunanta Najma tayi saurin juyawa bata san sanda murmushi ya kuvuce mata ba dan itama tana son ta qara ganin sa dan tayi masa godiyar da bata samu tayi masa a wancan likacin ba har suka rabu dan ba karamin alkhairin yayi mu su. Ya qaraso, “Alhamdulillah, Allah ya qara haxamu ina ta addu’a sai yau Allah ya qaddara, “tana murmushi “an dai samu akasi ina jiran Najwa” yace, “har yau kin ki yarda da qaddara ke haxamu ba wai akasi ba.”
Najwa ce ta katse musu taqaddamar da suke ta kalli Hafiz, “barka da asuba Yaya” ya amsa cikin sakin fuska dan yaji daxin karanta sunansa da tayi, “kina lafiya ya kwanan Yayarmu” tana dan murmushi tana kallon Yayarta take amsa ma sa “lafiya lau.”Suka jera suna tafiya da ya ke hotel xin su kusa da Harami ne a qafa suka qarasa.
Sun dan tsaya a bakin hotel xin ne Najwa ta wuce ciki. Yana kallonta ya na murmushi baki bani lambar ku ta qasar nan ba dan ni yau zan wuce Makka tana kallonsa cikin mamaki yace “daina kallona kamar mai tuhumata kinsan banda ina tunanin zan qara ganinki da tun jiya ina Makka na so tafiya amma zuciyata taqi yarda ina ganin Allah zai qara haxa mu sai gashi bai fi saura awoyi na tafi ba Allah ya qaddara sake haxuwarmu. Ina gani da akwai abinda Allah yake shirin haxawa a tsakaninmu ya bita da kallo irin ta faxi nata ra’ayin amma miskilar sai cewa tayi an dai samu akasi ne amma ba wata qaddara da ke shin faruwa. Yace yanzu dai mu bar maganar ku sai jibi za ku zo Makka ke nan tace haka ne ya kaleta sai yaushe ke nan tace sai an kuma samun wani akasi xin yace wata qaddarar dai.Duk suka kwashe da dariya, yayi mata sallama ya wuce tare da karbar number wayarta.
Bayan Hafiz sun isa Makka ya gama xawafi yayi safa da marwa ya sauke umrah sai yayi tunanin kiran Najma ya bata tabbacin har ya sauke umra amma wayar taqi shiga cewar ba daidai ba ce dole ya haqura gashi bai bata tasa ba bare ya sa ran zata kira shi. Ya so ya wuce Riyadh kashe gari amma rashin ji daga wajen Najma ya hakura da tafiya ko Allah zai qara ara masa ranar ya gansu abin da ya hana masa tafiya ke nan.
Kwanan su Najma huxu a madina suka xauko umrah sai Makka, har ta shiga yar damuwa da rashin jin Hafiz amma bata yiwa Najwa magana ba amma ta fahimceta sai ta nuna kamar bata san tanayi ba. Bayan an kaisu masaukinsu sai suka nufi harami dan sauke umrah, sun jira har akayi sallar asuba sannan suka wuce masaukinsu su.
Najma na tsaye a bakin Darul Tauhid tana cikin damuwa saboda rashin ji daga gurin Hafiz yau kusan kwanan su uku da zuwa Makka zuciyarta cunkushe amma fuskarta bata nuna sosai ba, tunani take ina ma ta juya ta ganshi yana mata murmushin nan nasa. Kamar daga sama taji an ce “Najma gani a kusa daina tunani na” da sauri ta juya cikin firgici na rashin tsammani. Bata tava tsammanin zata ganshi a wannan lokacin ita kanta bata san sanda ta sauke ajiyar zuciya ba tare da murmushin farin ciki.
Ya kalle ta ko baki faxa ba na san kin yi farin ciki da ganina. Ta dan sha kunu waya faxa maka yace, “fuskar kice dan san da na ganki fuskarki ta xan nuna damuwa amma kina ganina sai naga damuwar kamar an wanke ta. Allah na roqa kuma ya amsamin yanzu zan koma in qara gode masa dan na sha wuya, Najma ina ki ka shiga kullum cikin neman ku nake bamu haxuba sai yau.