30
by @gureenjoh
Ammar ya yi ta mishi magana amma ya ƙi amsawa don Sam ba ya son maganar ta ma, wani fanni na zuciyarshi na tambayar Meyasa take shiga rayuwarsa haka? Meyasa duk inda zai juya sai ya ganta? Zai iya rantsuwa duka rayuwarsa bayan danginsa babu wata mace da ta taɓa crossing rayuwarsa kaman yadda yarinyar take yi daga haɗuwa sau ɗaya wani kaddara ne yake cigaba da haɗa su haka? Ya tsinci kanshi da adu'ar ko alkhairi ne ko sharri ne duk baya so kawai baya son sake haɗuwa da ita ne a rayuwarsa.
Suna isa gida ya sauƙa ya nufi sashensa ba tare da ya cewa Ammar komai ba haka ya gyara parking ya sauƙa shima yayi nasa ɓangaren cikin tunani shima da mamaki.
******
Tun da motar ta tsaya al'ummar rumfar Dagaci duk suka zuba mata ido har motar ta buɗe malam Musa ya sauƙo, ai da sauri suka mimmike kowa na Allah Allah ya ƙaraso su ji lafiyar yaransu barin ma Baffan su Ma'u da kullum sai ya zo yayi zaman wurin ko Allah zai sa Malam Musa ya dawo a idonsa.
Ganinshi a yanzu ya ƙara musu ɗokin son ganin 'ya'yan na su da jin labarin su, Malam Musa ya nufo su a gajiye ya zube ya miƙa gaisuwa ga dagacin kan yace
"Ranka ya dade Al'amarin nan babu haske, adireshin jikin Takardar nan babu shi don unguwar da ke rubuce babu inda ban shiga ba kusurwa kusurwa amma babu haka kowa na tambaya bai taɓa sanin abu haka ba"
Wani irin tension ne ya hau kawunansu aka rasa ma me fara magana sai Salati kuma ya kaure wurin.
Dagaci ya ce
"Ka tabbatar da batun ka Malam Musa?"
"Kwarai da gaske na tabbatar Ranka ya daɗe"
"Toh ina za su je? Ta ya yara za su ɓace haka kaman kudi?"
Wani ya faɗa inda Allah ya taimakesa babu nasa don sai da ya riƙe mahaifin su Ma'u da ya nemi faɗuwa ya zaunar kan ya shiga maganar cikin mamaki.
"Yaranmu babu abin da zai same su in Shaa Allahu, zan shirya yanzu na tafi cikin gari na kai report na abin da ya faru na san za su tsaurara bincike kuma zan yi takarda in aikawa mai martaba ku kwantar da hankalinku"
Ya faɗi hakan ne amma ya san babu mai iya kwantar da hankali cikinsu kuma shima ya rasa natsuwa don tsoro ne ya fara shigarsa akan yaran da aka fita da sunan taimakon.
Mota aka kawo Dagaci ya shiga suka tafi yayinda mahaifin Ma'u ya nufi gida yana ganin hazo hazo, babu mai gane halin da ya shiga sai uban dake tsananin kaunar yaransa da musu mafarkin rayuwa mai kyau da inganci bai san me zai faɗawa innarsu ba idan ya shiga gidan haka ya ƙarasa jiki a sabule tana amsa sallama kuwa ta jefo mishi tambayar da yake tsoron
"Ya dai Malam shi wanda aka turan ya dawo? An samu labarin Yaran nan???".....
*****
"ke Zubaidah wai menene matsalar ki ne? Tun yaushe yanzu rabon da na hura wuta a gidan nan ina ta binki kudin chefene kin min banza ga Malam chan yana fama da ciwon kai yana neman magani ki ba da kudin a amso kin yi shiru"
Idanu Zubaidah ta ɗaga ta zubawa Mamartata dake wannan zance sai ta ji wani irin ɗaci da raɗaɗi na mamaye mata harshe da jiki, zuciyarta na wani irin karyewa dukda taurin ran da take jarumtar arowa kwana da kwanaki ta yafawa kanta.
"Mama ni ce alhakin ciyar da gidan nan ke wuyana? Ko kuma ni ce nake da alhakin samawa Mijinki magani idan bai da lafiya? Ba ni da kudi bani da hanyar samu"
Ta faɗa tana kallon Mamar da ta sake baki
"Me? Me kike cewa? Ke kin ma isa? Toh na rantse da Allah idan ba za ki nemo mana kudi a gidan nan ba sai dai ki bar sa ba za ki zauna ba, uban wa ke hure miki kunne? Nace uban wa ke neman sauƙar da ke turbar da na ɗora ki? Idan baki nemi kudi ba uban wa zai nemo mana?"
"Da turbar kwarai kika ɗora ni sai ki samu zarafin ihu da masifa idan na sauƙa amma me? Don na ce na bar yawon banza saboda ciyar da ku shine kike tada jijiyoyi? Ba zan je ko ina ba idan za mu mutu duka da yunwa sai dai mu mutu"
Mama ta riƙe haɓa
"Eh lallai ne! Lallai ne toh Daaɗin abin ba ke kaɗai na haifa ba Zubaidah. Ke Khadija! Khadija??"
Khadija da ke daga ɗakin tana kukan bakin ciki ta fito
"Ki wuce ki je ki fara naki neman kudin tunda yayarki ta yi ritaya"
"Mama a ina zan nemo?"
Ta zaro mata ido
"Ke ba mace ba ce? Ko ma a ina ne ki fita ki nemo babu ruwana ko me zaki yi ki samu ki yi kawai kudi nake so"
Kuka Khadija ta fashe da shi Mamar ta rarumi icce za ta daketa in bata fita ba sai karab Zubaidah ta riƙe ta.
"Ki koma ciki..."
Tana kai nan ta kalli Maman tana jin tsana, baƙin ciki da wani irin kiyayya na uwar na mamayeta. Ta ya za ta fara amincewa Khalil cewa tana son shi? Ta ya za ta fara Shiga zuri'ar wasu da irin wannan uwar?
"Zan kawo!"
Tana Faɗin haka ta juya ta fice tana jin Mamar na cewa
"Gwara miki don wallahi muddin baki kawo ba wannan da baki so a taɓa sai ta fita ta nemo uban da ya haifeku bai tsaya ya yi wahalar ku ba ni da nayi dole in fanshe!"
*****
Ko da Shehi ya shirya fita taron da yammacin da Imamu da kuma malam Bala ya fita, taro ne na seminar don haka ya dauki lokaci Sossai don anan suka yi magrib ko da suka idar aka cigaba har tara na dare aka tashi.
Tun ana adu'ar tashi Aka kawo mishi shayi kaman yadda aka kawowa kusan duka manyan wurin, saboda yadda yake jin gajiya ya sa ya ɗauka ya shiga kurba a hankali Amma cikin yan mintuna, idanunsa suka fara nauyi, kunnuwansa suka fara daukar amo kamar daga nesa kila gajiyar ce ta haddasa masa hakan ya raya a ransa yana Miƙewa Imamu ya taso ya tattare komai nasa suka fice malam Bala ne ya bude masa kofa ya shiga ya zauna yana miƙe bayansa jikin kujerar, glasses na idonsa ya cire ya ajiye yana shafa fuskarsa a hankali har suka fice daga wurin.
Akwai nisa Sossai kuma hanya ce mai shiru musamman da dare ya fara sun sha kwanar wata titi da gidajen wurin suka zama sabbi kuma uncompleted suka ga wasu sun tare hanyar kaman faɗa suke yi don hayaniya ya ɗan cike wurin ga motoci har biyu Parke a kan titin.
"Ko me ke faruwa?"
Imam ya tambaya yana kallonsu
"Kaman rikici ne suke yi gashi na riga na shigo da sai mu sauya hanya kawai"
Malam Bala ya faɗa yana danna horn.
Shehi ya buɗe idanu yana kallon wurin ya sake lumshewa yana jin suna mishi nauyi, dukda Ac da ke cikin motar zafi ne yake ji Sossai ya cire alkyabbar jikinshi ya ajiye kan ya buɗe kofar
"Shehi da baka fita ba, bari na je!"
Imam ya yi kokarin hanasa amma sai ya ce
"No ka zauna! Zan musu magana ne..."
Yana kai nan ya fice daga motar ya nufesu.
Yana isa wurin kaman jira suka mishi kawanya dama an faɗa musu motar shi duka bullet proof ce, bibbiyu ya fara ganinsu yana jin kafafunsa suna masa nauyi, daga nesa yake jin Imam na kwalla kiran sunansa sai ya ga wasu daga cikin mutanen sun nufi wurin su da gudu, Malam Bala kokarin fitowa yake suka rufu musu da duka daga shi har Imamu.
"Maganin ya riga ya gama taking effect mu gama da shi kawai mu yi gaba"
Ɗaya daga ciki ya faɗa cikin kakkaurar murya.
"Akwai police station kusa dole ce ta sa muka zo nan don sun yi nan ɗin amma muna harbi za su jiyo mu"
Wuƙa babban ya zaro Shehi da ba ya ma ganinsu da kyau yana jiyo maganasu daga sama sama yana jinshi yana shawagi Ya yi yunkurin magana, amma kalmomin suka rikice a bakinsa, babu zato wani irin zafi da bai tantance ba ya ziyarci gefen cikinsa da sauri ya dafe wurin yana fusgo sunan Allah duk da ya zo bakinshi yana ambata.
Hannunshi ɗaya na kan gefen cikinshi da yake jin zafin na ƙara tsananta sai jin wani hannu yayi ya shiga cikin hannunshi na hagu da ke lilo, ko kan ya motsa ya ji an fusgo shi taka kafafunsa ya shiga yi ba tare da ya san inda yake saka su ba sun jima kwarai don ya jiyo ƙarar harbi ya ji haki da magana da muryar da yake jin kaman ya san muryar kokarin faɗuwa yake yana ji muryar na cewa
"Ka daure kar ka tsaya anan mu ƙara gaba"
Amma innaaa ba ya cikin hankalinsa tunaninsa ya riga ya gushe yana ji ta rikesa suka ƙarasa inda ba zai ce ba ta ajiye shi zaune ta tsuguna daidai fuskarshi yana jin sunan Sheikhhh na fita daga muryarta a hankali kuma sai ya shiga buɗe idanu dukda rufuwa da suke da kansu fuskarta ya gani wannan fuskar da ya gama adu'ar kar Allah ya sake haɗa shi da ita ko a mafarki ko a zahiri, wannan fuskar da yake jin duk duniya ya washi gani fiye da komai.
"SUHAN!"
Lips ɗin shi suka furta ba tare da kwakwalwarsa ta sarrafa kalaman ba, a hankali kuma duhu ya mamaye ganinshi gaba daya.
BAYAN AWANNI!
A hankali ya ɗan motsa wani azaba da raɗaɗi da bai taɓa jin irinsa ba na ziyartarsa amma yanayin da ya ke ciki ya sa dole ya buɗe idanunsa, hasken rana ne irin na safiyar nan dake fita tarrr ya shige mishi idanu da ya sa yayi saurin rufe wa saboda zafi da ya ziyarcesa kan ya sake tattare ɗan ƙarfin da ya rage masa ya buɗe idanunsan da suka sauya kwarai.
A kan gefen cikinsa da yake jin azabar ta fi yawa ya sauƙe idanunsa yana tunano abin da ya faru a jiyan, tabbas wani abu aka bashi a cikin shayin da ya sha amma ba zai ce ko abin bugarwa ba ce ko guba amma ya san ya fice a hayyacinshi, kan Wuƙa ne kuma a jikinshi jini ya lalata duka ɓangaren farar jallabiyarsa ta sauya zuwa ja.
Ya runtse idanun a hankali ya sake bude wa kan ya juya kanshi zuwa gefen kafadarsa da yake jin nauyi idanunsa suka sauka kan gashinta da ya wargaje ya rufe mata fuska gabadaya, hannunta na cikin nasa ɗaya kuma kanta na kwance a kan kafaɗarsa dayan hannunta na riƙe da cikinta.
Sai a lokacin ya tuna a jiyan ya ganta kamar almara, ya tuna yadda take rikesa take kuma jansa don tseratar da rayuwarsa, ya tuna yadda take kara masa karfin gwiwar yayi gudu idan suka riskesu ita kaɗai ba za ta iya ba!
Hannu ya sa a kanshi ya cire Ghutra dinshi da har lokacin yana kanshi ya saka mata yana rufe mata gashin, motsin da yayi ya farkar da ita sai idanunsa suka sauka kan jinin da duk ya bata jikinta, idanunsa ya tsayar a kai kan ya kawar ya mayar kan wuƙar jikinshi ya na kokarin taɓawa tayi carab ta kama hannunsa.
"Kana motsa wannan wuƙar ko ka cireta babu abin da zai hanaka mutuwa! A jiyan ma da sun zare da yanzu wani maganar ake ba wannan ba!"
Ta faɗa chan ƙasa yanayinta babu ƙarfi sammm Idanunta suna ta lumshewa, hayaniya suka soma ji kaman mutane sai kuma suka ji ana ta kwalla kiran sunanshi don wuri ne uncompleted buildings na dayawa cikin ɗaya daga ciki suke, ta miƙe da kyar ya sake kallon jikinta amma bakinshi ya kasa furta komai ta riƙe shi ya miƙe suka fito daga nesa suke hangen motoci da hukumomi ana ta cigiyarsa! Sai da suka fito sarari har wasu sun gansu kan ta sake shi ko kan yayi magana ta juya ta bar wurin yayi ƙasa a daidai nan aka janyo hankalin su Ammar
"Ga shi chan! Ga Sheikh chann!!"
Kan ka ce kwabo an rufu mishi aka ɗauke shi Ammar na ta kiran sunanshi amma bai buɗe idanu ba aka sanyashi a ambulance sai asibiti.
Tashin hankali karamin suna ne da za'a ƙira halin da ahalin Familyn suka shiga don a daren da abin ya faru yayi munin da ko ina maganan ya baza Malam Bala yana coma, Imam na kwance asibiti sai kuma ga labarin an kama Abbiey an kuma rufe companynsa don ana zarginsa da safarar miyagun kwayoyi da sunan Company!
Ammar ya rasa inda zai sa kanshi shi da Abba dole Abba ya tsaya wurin hukuma shi kuma Ammar ya bi ayarin masu neman Shehi don Imam ya tabbatar musu mutanen basu kashe shi ba ya gudu sun neme shi sun rasa a kan idanunsa komai ya faru kuma Shehi ba zai iya nisa ba saboda raunin da suka ji masa!
Surgery kai tsaye aka shiga da shi don wukar a ƙasan cikinsa ne, Ammiey kam ta fice hayyacinta Maamah da su Daddah sun yi kuka har sun rasa hawaye a iya jiya rayuwarsu na neman juyewa daga sama zuwa ƙasa!
Neman faɗuwa Ammar ke yi a sadda yake jin wasu kalamai da suka girmi tunaninsa cikin TikTok da mutumin gefensa ke kallo zaune cikin reception na asibitin da Shehi yake, da sauri ya kalli su Maamah tabbas su ma sun ji don Tuni sun miƙe tsaye!
Girgiza kai tayi ta isa ga mutumin ta fusge wayan tana kallo tana girgiza kai Idanunta na tsiyayar da kwalla!
"Tabbas 'yata ta dawo gida amma cikin wani mummunan yanayi, daga taimakon wannan babban Malamin Sheikh Irshad Al-Noor Kasancewar ba ya hayyacinsa ya yi Mata FYADE! Hotunan dake zagayawa ba ƙarya ba ne!"
Bugawa ne ya saura zuciyoyinsu basu yi ba, scrolling hannun Maamah yayi sai ga hoton Irshad ɗin riƙe a jikin Diva jikinta akwai jini kaman yadda nashi yake da jini, basu san daga ina ya fita ko wa ya ɗauka ba amma tabbas a safiyar ne kuma media ta ɗauki dumi dama kiris ake jira nan Scandal ya fara Shehi ya yi wa wata 'yar Daba fyade daga taimako!
Abu ne da hankali ba zai taɓa ɗauka ba amma sanin Imam ya ce musu kaman tun farko Shehi ba ya cikin hankalinsa don tabbas akwai abin da ya shiga kansa a lokacin don har hana shi sauƙa yayi amma yadda yake abu kaman cikin maye ya tsinka musu gaba! Tabbas idan wani abun maye ne aka shayar da shi zai iya aikata hakan ba tare da ko ya sani ba Innalillahi wainna ilaihi raji'un...!!!!!
*Toh jama'a anan muka kawo ƙarshen free pages za mu tafi hutun kwanaki, da yardar Allah bayan kwana goma za mu dawo muku da cigaban wannan labari!
Idan har Shehi ya aikata fyade wa Diva me kuke tunanin zai faru? Zai ma rayu kuwa? Me ya haɗa Abba da Safarar kwayoyi? Zubaidah kuna ganin mahaifiyarta za ta cigaba da cin galabar tarwatsa rayuwarta? Ma'u na hannun NAPTIP Jiddah na hannun J shin waye ne ma J ɗin? Iyayensu za su samesu kuwa ko sun tafi kenan? Kuna tunanin Dagaci da ya kama gomnati ya kama dahir kuwa a taimakon al'umma? Menene Jagaban ke ɓoyewa? Waye ke sace kudin company kuma yake ɗora wa Ammar? Diva za ta shiryu kuwa? Waye yake neman ran Shehi??
Ko anan muka tsaya na san kun fahimci wannan kalma ta ƙarfe ɗaya ba ya amo dole sai ya haɗu da wani ƙarfen ɗan uwansa!
Hmmm akwai fah sauran tafiya a gaba ku dai ku gyara zama kawai ku mu cigaba da tafiya*