Da walakin...

PAGE 2

by @sadiyaabdulrazak954

Sai la'asar ta fito sakamakon yunwa da ta addabe ta, ta nufi kitchen don ta nemi abin da za ta ci, sai ta same shi a rufe da mukulli, ta juyo ta kalli Suwaiba da ke falo tana kallo ta ce"Shi ma abinci an haramta mini ne?"

Suwaiba ta ce"Ba a isa a haramta miki ɗin ba ne? Ni umarnin mai gida na bi, ya ce kar a bar ki ki taɓa komai na gidan nan, don kar ki goga mana wannan azababben warin na jikinki".

Ba ta ce komai ba, ta koma ɗakinta, sai ta ɗauki doyar da ta soya masa da safe, ta shiga ɗaki ta ci, ta sha ruwa. Babu jimawa ta ji shigowarsa gidan, dama ba ta saka ran zai ƙaraso ɗakinta ba, duk da yau ranar kwananta ce, ta idar da sallar magriba sai ga kiran shi a waya, ta ɗauka suka yi shiru na ɗan lokaci, ita ta katse shirun da cewa"Alhaji ka aure ni ne don ka wulaƙanta ni?"

Ya girgiza kai kamar tana kallonsa, ya ce"A'a ko kaɗan! Na aure ki ne don ina sonki, ina son zaman aure da ke, amma wannan ƙazantar taki ce take damuna, ban tsammaci haka daga gare ki ba".

Ta share hawayen da ya zubo mata, ta ce"Wallahi Alhaji ba ƙazanta ba ce, larura ce, zan warke in sha Allah!".

"Larura!?" Ya tambaya da mamaki.

Ta ce"E, amma don Allah ka ba ni lokaci, zan nemi magani kuma na san zan dace, komai zai wuce".

Ya ce"To Allah Ya sa, zan turo miki kuɗi sai ki fara maganin, wallahi ni ma ba a son raina nake ƙyamarki ba, to ba ni da yadda zan yi ne".

Ta ce"Yanzu ya zan yi da kayan kitchen ɗina da ka sa a fitar da su?"

Ya ce"Ki yi haƙuri, ni da na yanke kawai ki koma wancen ɓangaren na gefe ki zauna a can, tun akwai ɗaki da ban ɗaki, ki kwashi kayanki masu muhimmanci ki kai, ki rufe ɗakinki, ko a waje ai za ki yi girki ba zai a kitchen ba ko?"

Ta yi shiru zuciyarta babu daɗi, kafin ta ce"To na gode".

Shi ma jikinsa a sanyaye ya ce"Allah Ya ba ki lafiya, yanzu zan je na buɗe miki zan bar mukullin a jiki". Ya katse kiran, ta tashi ta je ta gan shi a buɗe, ta share tass ɗakuna ne ƙananu biyu da ɗan filin tsakar gida, sai banɗaki a ciki, tsaye ta yi bayan ta koma ɗakinta, tana tunanin abubuwan da za ta kai can ɗin, ta sani ba za ta iya ɗaukar katifarta ita kaɗai ba, amma ba ta jin za ta samu mai kama mata a cikin gidan nan, saboda haka ta ɗauki barguna ta kai ta shimfiɗa, ta dawo ta dawo ta kwashi kayan sakawarta akwati ɗaya, sannan ta kwashi masu muhimmanci a kayan kitchen ɗin, ta kai duk da ajiye, gas ne babu, tun da dama wanda take amfani da shi a gidan ta tarar da shi, dayake babba ne kowa da shi yake yi, ta kira shi ta faɗa masa, da daddare ta fito alwala don sallar isha'i ta ga ƙaramin gas a tsakar gida, ta ɗauka ta shigar da shi ɗayan ɗakin da ta zuba kayan kitchen a ciki.

Washegari da safe bayan ya fita aiki ya kira ta a waya sun gaisa, ya ce zai turo mata kuɗin yanzu sai ta je ta nemi maganin, ta yi masa godiya, suna ajiye waya ya turo mata kuɗin da mamaki ta kalli alert ɗin, jikinta ya yi sanyi da ta tabbatar da dubu biyar take gani ba dubu hamsin ba, a saninta da shi mutum ne mai kyauta, wanda take yi masa kallon bai san ciwon kuɗinsa ba ma, ya kashe kuɗi sosai wurin neman aurenta, tun da aka yi auren wata kyauta ba ta shiga tsakaninsu ba, ba ta damu ba tun da wata ɗaya kenan da auren, sai yau da ya ba ta dubu biyar a matsayin kuɗin neman maganin da ba ta san tsawon lokacin da za ta yi kafin ta warke ba, kamar ta yi masa ƙorafi, sai kuma ta fasa, don ba ta so ya yi mata kallon mai rainuwa.

Jiki a mace ta yi wanka ta shirya, bayan ta ci abinci ta kama hanyar gidan yayanta, wanda ke da matsayin mahaifinta a yanzu, ba ta same shi a gida ba, sai matan nashi, ta shiga sashen amaryar wacce suka fi sakewa, a nan ta wuni sai magriba yayan nata ya dawo, suka gaisa ta kwashe matsalarta tass ta labarta masa, "Yanzu dubu biyar ce za ta yi mini magani?" Ta ƙarasa kamar za ta yi kuka.

Sani ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Allah dai Ya kyauta, ni dai ba kuɗi ne da ni ba gaskiya, irin wannan tun da matsalar a gidan shi ta same ki, ai shi ne yake da alhakin ɗaukar nauyinki duka".

Sarai ta san yayan nata a kan zancen fitar da kuɗi, don haka ta ce"Yaya ban ce kai za ka yi ba dama, kawai na faɗa maka matsalata ne don ka yi mini jagora wurin neman magani, jikina yana ba ni sihiri ne aka yi mini, idan ka san wani malami sai ka samo min maganin karya sihiri na gwada na gani, wallahi ba na so aurena ya mutu".

Ya ce"Dama me ya kawo zancen mutuwar aure? Wannan ma ba ta taso ba in sha Allah! Ki kawo kuɗin na je gobe na ji yadda za a yi".

Bayan ta miƙa masa ya duba, ya ce"Ya na ga dubu huɗu?"

Ta ce"Na hau adaidaita sahu ɗari huɗu, idan zan koma ma haka zan biya".

Ya ce"To ina sadakinki? Ina ɗan kuɗi da kike tarawa kafin auren?"

Ta ce"Haba Yaya, ka sani fa komai ni na yi wa kaina, wallahi ba ni da ko sisi a yanzu".

Ya ce"To, zan je na gani, ki gai da gida".

Ta tashi ta tafi tana fatan samun maganin matsalarta.

Washegari Yaya Sani ya je wurin wani malamin zaure a ƙasan layinsu, ya yi masa bayani, tare da faɗa masa kuma ba ta kuɗi dubu biyu ne da ita, don a jiyan ya zari dubu biyu ya sayi biredin da suka karya da shi, malamin ya ce dole a ƙaro kuɗi, dubu biyu sharar fage ce a abubuwan da za a siya, amma yanzu zai yi rubutu ya wanke a kai mata ta fara, haka aka yi ya wanke rubutu ya ba shi.

Yaya ya kira ta ya faɗa mata yadda aka yi, ya ce ta aiko a karɓar mata rubutun, sannan ya tambaye ta yadda za a yi da sauran kuɗin maganin, ta ce"Yaya wallahi ban san yadda zan yi ba, amma zan tambaye shi na ga nawa zai ƙara min, sai na turo maka a yi komai". Akwai wani matashi da yake yin aike da wanki a gidan, shi ta kira ta sa ya karɓo mata rubutun, yana kawo mata ta yi bisimillah ta shanye, tana fatan waraka.

Da daddare da Alhaji ya dawo ta so ta je ta same shi su yi magana, tunawa da yadda yake ƙyamarta ya sa ta fasa, ta kira shi a waya, ta yi masa bayanin da Yayanta ya yi mata, Alhaji ya ce"Wannan wace irin magana ce haka nake ji? Shirka za a fara yi a cikin gidana? Me ya kawo zancen sihiri? Kin je kina ƙazanta ko kuma wani ciwon ya ruɓar da ke za ki ce sihiri aka yi miki? Wane ne yake baƙinciki da aurenki da zai yi miki sihirin?"

"Ka yi haƙuri don Allah..." Ba ta kai ƙarshe ba ya katse ta da faɗin"Kar ma ki sake na sake jin zancen sihiri, matsalar da bai fi ki sayi sabulun dubu biyu ba ki gyara jikinki shi ne za ki fara biye-biyen malamai? To wallahi ba a gidana ba, yanzu zan turo miki dubu biyu gobe ki je asibiti a duba ki sosai, idan magani suka rubuta miki ki kawo min na siyo miki, wannan shi ne magana".

Bai ma jira cewarta ba ya katse kiran, babu jimawa ya turo mata dubu biyun, ta yi shiru riƙe da wayar tana tunanin ta inda za ta fara fahimtar da shi matsalarta ba ta asibiti ba ce, ba ta son ja da shi, don haka ta yanke za ta je ɗin, ƙila idan aka tabbatar da babu matsala zai yarda da ita, ya zauna su fahimci juna.

***