Da walakin...

PAGE 3

by @sadiyaabdulrazak954

Da daddare ya kira ta a waya ya tambaye ta yadda aka yi a asibitin, ta ce sai gobe za ta je, babu jimawa ya turo mata saƙo, ya ce ga asibitin da za ta je ya yi magana da wata likita, idan ta je ta kira lambarta. Da safe ta shirya ta tafi, likitan ta karɓeta a mutunce ta duba ta tare da tambayoyi, sam ba ta ga wata matsala ba, don haka ta tambaye ta"Bayan kun kwanta ne yake jin warin?"

Hajara ta ce"A'a ko ɗakin da yake fa na shiga ya ce wari yake ji, don Allah ke yanzu kin ji?"

Likita ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Sam ban ji ba, gaskiya ina tunanin matsalarki ba ta nan ba ce, ya kamata ki nemi na islamic ki gwada".

Hajara ta ce"Hakan na yi ƙoƙarin fahimtar da shi, amma ya kasa ganewa, don Allah ki yi masa bayanin da zai gamsu". Suka rabu a kan za ta faɗa masa, ta yi mata godiya sosai. Da azhar Yaya Sani ya kira ta yana tambayar cikon kuɗin, ta faɗa masa ba ta da su, ya rufe ta da faɗa kamar zai daketa ta cikin wayar "To shikenan kar ki samo su, ki zauna da larurar har zuwa lokacin da mijin zai gaji ya sake ki, amma ki sani wannan karon ba za ki yi zaman zawarci a gidana ba, don kina hana matana sakewa!". Ya kashe wayar.

Ta yi shiru tana tunanin mafita, kafin ta kira shi, ya ɗaga ta ce"To Yaya idan za ka sayi wasu daga cikin kayan lefena sai na siyar na samu kuɗin".

Ya ce"To dama mene ne amfanin kadara idan ba ta sama maka lafiya ba? Ki aiko a kawo min, ko na aiko a karɓa?"

Ta ce"E ka aiko ɗin zai fi". Suka ajiye waya. Ta duba cikin kayanta, ta ɗakko leshi ɗaya atamfa ɗaya, wanda take kyautata zatom masu tsada ne, da aka kai sai Yaya ya ce dubu goma sha biyu aka siya, haka ta amince ba don ta yarda ba. Da daddare ta kira Alhaji a waya suka gaisa, ta ce"Na je asibiti..."

Ya ce"Ai ta yi mini bayanin komai, to gaskiya abun ya ba ni mamaki, mun tattauna matslar da Suwaiba, take faɗa mini yawanci mata masu aljanu ne suke irin haka, aljanu kuma masu haɗari, don sukan iya kashe mijinta matar ma, tun da ni kaɗai nake jin warin".

Wani abu ya zo ya tsaya a ƙirjin Hajara saboda baƙinciki, ta ce"Amma Alhaji na ga wannan matsalar mu biyu ta shafa, akan me za ka sako wata a ciki? Wannan ai cin fuska ne".

A fusace ya ce"Kamar ya cin fuska!? Matar tawa ce wata? Na ga dai ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, kuma sanin Suwaiba ba ta baƙinciki da auren nan shiyasa na je mata da matsalar, ga shi kuma an yi sa'a ta san mafitar, tun da ta ce akwai ƙawarta da irin haka ta faru da ita, ƙarshe ta yi magani ta warke".

Ya cigaba da cewa"Yanzu dai ta ce gobe za ta je wurin mai maganin a ji, idan ta kama ku je tarema sai ku je, don haka yanzu ki je ki yi mata godiya, za ta yi miki ƙarin bayani".

Hajara ta haɗiyi yawun takaici ta ce"Amma Alhaji da ba ta wahalar da kanta ba, ni zan yi wa kaina magani, akwai wani malami da yaya ya fara karɓo min a wurinsa".

Alhaji ya ce"To daga yau na soke shi, wannan ɗin da shi na yarda, saboda haka shi za a yi, idan kuma ba kya so ki faɗa min, sai na san matakin ɗauka".

"Shikenan, a karɓo ɗin" Ta faɗa tana ajiye wayar.

Washegari da safe ya kira ta a waya ya ce ta zo falo.Ta tashi ta tafi, ta tarar da Suwaiba tana zaune cikin shirin fita, ta tsaya suna kallon kallo kafin ta ce"Ga ni".

Suwaiba ta ce"Ina fatan zuwa yanzu kin lura gidana ramin kura ne? Kin fara tsara yadda rayuwar sabon zawarcinki za ta kasance kuwa?"

Hajara ta ce"Ai kuwa wanna kirarin bai dace da gidanki ba, don kuwa da ta tabbata ramin kura ne da ban shigo ba".

Suwaiba ta ce"Ina sane na ba ki damar shigowa gidana, saboda dalilina, ina da ƙudurin saka ki a baƙinciki madawwami, Hajara in sha Allah rayuwarki ba za ta yi kyakkyawar ƙarshe ba, domin kuwa sai kin girbe gonar sharrin da kika shuka tun a duniya!".

Hajara ta ce"Ban nufi kowa da sharri ba, don haka alkhairi zan girbe, kuma zaman gidan nan yanzu na fara shi, babu ranar ƙarewa, dole ni ki amsa sunan kishiyar Hajara" Ta faɗa duk da tana jin shakkarta.

Ta juya za ta tafi, Suwaiba ta fincikota, tana riƙe da rigarta ƙam ta ce"Dole za ki bar gidan nan, amma ba yanzu ba, sai wa'adin da na ɗaukar miki ya cika, sai na shayar da ke maɗaci!". Ta hankaɗe ta har ta kusa faɗuwa, ta juya ta shige ɗakinta.

Hajara ta fita ta koma ɓangarenta zuciyarta tana azalzalarta sosai. Tana zama Alhaji ya kira ta, ta ɗauka, ya ce"Kin je ta yi miki tambayoyin?"

Ta amsa da "Na je".

Ya ce"To shikenan Allah Ya sa a dace". Suka ajiyr waya.

Wajen azhar ta ji dawowar Suwaibar, da magriba da Alhaji ya dawo sai ga ƴar Hajara an aiko ta da ƙullin baƙin ruwa a leda, wanda ya yi mata kama da rubutu, ta karɓa ta kalle shi ta yi ƙwafa ta ajiye, da Alhaji ya kira ya ce"An kawo miki maganin kin sha kuwa?"

Ta amsa da "E"

Ya ce"To ma sha Allah! Ta ce nan da sati ɗaya ne za ki warke indai kina sha kullum, don Allah kar ki yi wasa da shi, wannan ƙullin dubu ashirin kenan".

Ta ce"To na gode".

Tun da aka siyar da kayan nan ta ji Yaya Sani shiru, bai aiko mata maganin ba, da aka kwana uku ta tambaye shi sai ya ce malamin ne ya yi tafiya sai ya dawo za a kawo mata, a ranar ne kuma Alhaji da Suwaiba suka shigo har ɓangarenta, suna shiga ɗakin Alhaji ya toshe hanci yana kallon Suwaiba, ita kuma ta ce"Hajara anya kuwa kina shan maganin nan? Malam ya tabbatar mini cikin kwana uku kashi hamsin zai ragu".

Hajara ta ƙi cewa komai saboda takaici.

Alhaji ya ce"Haba Hajara ke fa ba yarinya ba ce, da sai an saka ki a gaba za ki sha magani, ni wallahi na aurowa kaina ƙaddara".

Suwaiba ta ce"Haba Alhaji ka daina cewa haka, ƙarin aure ai alkhairi ne, kuma daga yau ni zan dinga ba ta don na rabbatar tana sha ɗin".

Ta ƙasara kusa da Hajarar ta ba ta ƙullin maganin, ta ce"Ki daure ki sha kin ji?" Ta karɓa tana bin ta da kallo kamar sakarya, sai ta kalli Alhaji da yake yi mata mugun kallo, ta janyo kofin kusa da ita, ta juyo ta kafa kai ta shanye, ta ajiye kofin hawaye ya zubo mata, suna ficewa ta fashe da kuka.

Da ƙyar ta tashi ta yi sallar isha'i saboda cikinta da yake ciwo, tsakar dare kuma abun ya yi tsanani, ta dinga murƙuƙusu ita kaɗai, tana jin kamar za ta mutu. Da ƙyar ta lalubo wayarta ta kira lambar Alhaji, bugu biyu ta ji an ɗauka, sai dai muryar Suwaiba ta ji, ta ce"Matsiyaciya dama na san za ki kira ai!". Ta kashe wayar, tana tabbatar da sai yau ne ta fara shan maganin.

Sai dab da asuba ciwon ya lafa mata, har ta ɗan samu bacci. Da safe ta kira Alhaji ta sanar mata maganin jiya ya saka ta ciwon ciki, kuma ta kira wayarsa don ta sanar masa Suwaiba ta ɗaga, babu jimawa ya sake kiranta ya ce ya yi magana da ita, ta faɗa masa dama haka maganin yake sai mutum ya ji ciwon ciki, ya ɗora da faɗin"Kenan na sauran kwanakin duk ba ki sha ba, sai jiya da aka saka ki a gaba?"

Ta ce"Duka na sha, jiyan ne dai ya yi min haka. Amma Alhaji gaskiya ka yi haƙuri, ba zai yiwu na sake shan wannan maganin ba, ni zan nema da kaina, zai iya haifar mini da wata matsalar..."

Sai ya katse ta da masifa ya ce"Me kike nufi? Kina nufin na yi asarar kuɗina? Dubu ɗari da arba'in fa na bayar, saboda ba ki san zafin nema ba ko?"

"Ba haka ba ne" Ta faɗa kamar za ta yi kuka.

Ya ce"To a gaskiya na gaji, na jingine matsalarki a gefe, ba za ta sake karɓo miki ba, amma na ba ki sati ɗaya ki warke, indai ba ki warke ba har tsawon kwana bakwai to ki tafi gida na sawaƙe miki".

Ƙirjinta ya doka da ƙarfi, tana shirin yin magana, ya katse kiran, ta ji kamar ta ɗora hannu a ka ta fasa ihu, wannan wane irin irin ɗanyen hukunci ne? Ta ya zai ƙayyade mata lokacin samun lafiyar larurar da ba ita ce ta ɗorawa kanta ba? Kuma har ya maƙala igiyar aurenta da ita?

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ta furta, tana nemo lambar yayanta a wayarta.

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.)

WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE ALHAKIN SO MATACCEN BURI MUKULLIN NADAMA DUKA ZA KU SAME SU COMPLETE ***