PAGE 4
Tana kiran fashe da kuka ta ce"Yaya ya ce wa'adin kwana bakwai ya ba ni, idan ban warke ba a bakin aurena".
Yaya Sani ya ce"Kwana bakwai!? Lafiya a hannun shi take da zai ba da wa'adi, sai ka ce jahili? Larurar ta same ki a gidan shi, ya aure ki lafiya lau ya kasa ɗaukar nauyin maganinki kuma shi ne har da ma ƙa'ide lokacin warkewar taki?Wannan ai wulaƙanci ne".
Ta ce"Ni dai Yaya ba wannan ba don Allah! Kawai a nemo mini maganin don Allah, na samu na warke, don na tsira da aurena".
Ya ce"To Hajara abu da gaggawa haka fa kin san yana buƙatar kuɗi, don haka ya zama dole ki fito da su..."
"Ina na gansu? Yaya walllahi ba ni da su" Ta faɗa tana kuka.
Ya ce"Zan turo a karɓi kayan sai a duba a ga nawa za a samu, lesuka za ki bayar".
Ta ce"Amma Yaya kana ganin babu damuwa na yi ta fitar da suturata ina siyarwa? Gaba da me zan yi ado?"
Ya ce"To ba sai da lafiya za ki yi adon ba? Yanzu idan kin yi adon wanda kika yi don shi yana gudunki ballantana ya yaba ina amfanin suturar? Idan kuwa kika warke zamanku ya daidaita shi mai yi miki sababbi ne".
"Hakane" Ta amsa a sanyaye. A ranar ta haɗa leses ɗinta guda biyar wanda su suka yi mata saura ba ta ɗinka ba, Yaya ya aiko aka karɓa, komai take yi a tafin hannun Suwaiba take, tana ganin duk sanda take fita tana kai abu, amma ba ta gane ko mene ne ba, don haka ta saka mata ido sosai.
Washegari ta aiki yaron gidan ya karɓo mata magani a wurin Yaya, wannan karon ma rubutu ne, haka ta sha tana fatan samun sauƙi. Suwaiba kuwa a waya ta tambayi yaron inda Hajara ta aike shi, ya faɗa mata, sai ta ce za ta ba shi dubu ashirin, duk lokacin da zai karɓo mata maganin nan ya fara zuwa wurinta, za ta ba shi wani, idan ya karɓo natan sai ya zubar a hanya ya kawo mata wanda ta ba shi, ai kuwa nan take ya aminci. Suwaiba ta sa ya samo mata tawada, don ya faɗa mata ruwan rubutu ne, ta sheƙawa tawadar ruwa, kullum sai ta ƙulla a leda, suke yin yadda suka tsara ita da shi.
A ɓangaren Hajara sam ba ta san ana yi ba, ita dai shan ruwan rubutunta take yi da zuciya ɗaya, tana fatan samun sauƙi kafin kwana bakwai ɗin. Lokacin da aka yi kwana biyar duk sai ta shiga damuwa, don ba ta san a halin da take ciki ba, warin nan dai shi kaɗai yake jin shi, saboda haka shi ne zai tabbatar da warkewarta, ga shi yanzu ta wayar ma kamar ya ja baya da ita, idan sun gaisa sai dai idan ita ce ta kira shi, tana so ta sani ta warke ko a'a, saboda haka ta kira shi, bayan sun gaisa ta ce"Alhaji ina ta shan maganin dai"
Ya ce"To Allah Ya sa a dace".
Ta ce"Amma ta ya zan gane na warke ko akasin haka, bayan ka ƙaurace min, kai kaɗai ne kake ji, ka ga kai ne za ka tantance".
Ya ce"Hakane, idan kwanakin da na ba ki sun cika ai zan zo inda kike".
Kamar za ta yi kuka ta ce"Idan kuma aka yi rashin sa'a ban warke ba shikenan fa na zama sakakkiya".
Ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya, shi ma sai bayan furucin ya ji bai kyauta mata ba, yana sonta ya aureta, kuma har yanzun ma yana jin sonta, wannan larurar tata ce kawai ta dagula masa lissafi.
"Alhaji ka yi shiru, kar ka yanke hukunci cikin fushi, alhalin ba ni na ɗorawa kaina larurar ba". Ta faɗa a raunane.
Ya ce"Na janye furucina, Allah Ya ba ki lafiya".
Ta ji daɗi sosai ta ce"Na gode Allah Ya saka da akhairi".
Ya amsa da amin, har suka ɗan taɓa fira.
Bayan kwana goma wata ranar Lahadi, ya kira ta a waya ya ce"Akwai wata Gwaggona da ta zo garin, za ta zo ta ganki, yanzu ya za a yi kenan?"
Ta ce"To ai sai yadda ka ce".
Ya ce"Babu damuwa, ki dai dawo ɗakinki ki zauna don kar a zargi komai, ni kuma Allah Ya ba ni ikon jure zama inuwa ɗaya da ke".
Ta sauke numfashi ta ce "Amin".
Ta koma ɗakinta, ta yi wanka ta yi kwalliya, bayan ta gama girki a ɓangarenta ta ɗakko kulolin ta kawo su kitchen ɗin gidan. Suwaiba tana bin ta da wulaƙantaccen kallo, don Alhajin ya sanar da ita dalilin shigowarta ɗakin.
Wajen sha biyu Gwaggon ta zo, ta gama cin abinci suna zaune ana taɓa fira sai ga Alhaji ya shigo, tun daga nesa gabansa ya fara faɗuwa tunawa da halin da yakan shiga idan warin nan ya buge shi. Sai dai abun mamaki duk takun da ya yi ji yake yana kusanto wannan ƙamshin nata na amarci, mai saka shi cikin shauƙi da son kasancewa da ita, bai gasgata ba har sai da ya zauna dab da ita ya ji tabbas zahiri ne ba mafarki ba, ita ma sosai ta ji daɗin yadda ya daure bai nuna mata ƙyama ba, cikin ranta tana fatan Allah Ya sa ta warke. Fira sosai suka sha da Gwaggon wacce duk su biyun suka ƙagauta ta tafi, don kowa ya amayar da abin da ke cikinsa, bayan ta tafi yana rakata ya dawo, ya tarar da Suwaiba a falo ya washe baki ya ce"Hajiya da alama fa Hajara ta warke, yau dai kam ƙalau na ji".
Suwaiba ta yi murnushi ta ce"Alhamdulillah! Amma kuwa na yi muku murna, to me za ta jira? Ai sai ta tattaro ta dawo ɗakinta, dama kwana biyun da babu motsinta duk babu daɗi, kuma dama Malamin ya faɗa min indai an yi wannan ciwon cikin to alamun waraka ce, to ganin ba ku yarda da ni ba, shiyasa na zuba muku ido".
Alhaji ya ce"Ikon Allah! Kenan tun a ranar ma ta warke? Lallai na yarda a rashin tayi akan bar araha! Mun gode uwar gida ran gida, ta gaban goshin Shamsu".
Hajiya ta yi wata bazawarar dariya tana bin bayan shi da kallo. Sai da ta ga shigewarsa, sannan ta tashi ta shiga kitchen, a zaninta ta fito da wani abu a leda, ta buɗe kulolin Hajara, tuwon shinkafa ne, miyar kuɓewa, ta juye abun a cikin miyar ta saka hannu ta jujjuya, ta rufe ta fice bayan ta wanke hannunta tass, ta ce"Kin gama da kashi na farko saura na biyu, Hajara ba za ki sake doguwar rayuwar farinciki ba a gidan aure, don ba ta cancance ki ba!".
Alhaji yana shiga ɗakin, ta miƙe tsaye, sai suka tsaya suna kallon kallo "Kin warke?" "Na warke?" Suka haɗa baki wajen faɗa.
Sai duk suka yi murmushi, ya ƙarasa ya rungume ta ya ce"Kin warke, Alhamdulillah".
Ta ce"Da gaske yanzu ba ka jin warin?"
Ya ce"Wallahi ƙamshi nake ji, wannan ƙamshin naki mai daɗin shaƙa".
Ta ce"Alhamdulillah!". Sai ta fara hawaye.
Ya goge mata yana cewa"Ai ya wuce, komai ya zama labari, ki kwaso kayanki daga can, ko kuma bari na je na karɓo saƙo na dawo sai na taya ki, don ba na so ki gaji, kin san yau akwai sabon amarci". Duk suka yi dariya.
Yana fita ta kira Yayanta, cike da farinciki ta shaida masa ta warke tass, ya taya ta murna, sannan ta fito ta shiga kitchen ta ɗakko sauran tuwonta ta shiga ɗaki ta ci, tass ta cinye shi, don ta daɗe ba ta cika cikinta irin ranar ba, saboda damuwa tana hana ta cin abinci, yanzu kuwa ji take ranta fess.
Da daddare ta sake tabbatar da warkewarta, don kuwa sosai suka sharɓi romon soyayya da Alhaji yana ta yabonta, musamman da ta tashi kansa da shu'umar humra, shi kuwa yadda ya saki jiki da ita sai ka rantse ba shi ke gudunta da ƙyamarta ba kwanan baya.
Lafiya lau suka gama ranakun kwananta, kwanan Suwaiba ya shiga, ranar da girki ya dawo kan Hajara duk sai shirinta ya wargaje sakamakon jinin da ya yanke mata da daddare, haka dai ta gama ranakun kwananta, wanda a ranar ya ɗauke, har ta yi mamaki don al'adarta kwana biyar take yi, ba ta kawo komai ba, ranar girkinta yana zuwa jinin ya dawo, haka ranar da ta bar kwana ya ɗauke. Ita a halittarta ma ba duk wata take yin al'ada ba, saboda tana da matsala a mahaifarta don haka wannan rikicewar jinin ya sa ta zuwa asibiti, saboda ta fara ganin damuwa a fuskar Alhaji, kuma ba ta son abin da zai ruguza fatincikin da suke ciki. Magani aka rubuta mata take sha, amma a banza man kare, don babu wani abu da ya canza, tun tana yi wa matsalar kallon mai sauƙi har ta fara ɗarsa mata tunani, don Alhaji ya yi ƙorafi, ƙarshe ma sai ya ce indai ta san tana al'ada ta dinga zamanta a ɗakinta, sai da suka yi wata ɗaya a haka babu abin da ya canza, zuwa lokacin ta tabbatar da ta shiga wani sabon ƙalubalen.
*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.)
WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE ALHAKIN SO MATACCEN BURI MUKULLIN NADAMA DUKA ZA KU SAME SU COMPLETE ***