Da walakin...

PAGE 5

by @sadiyaabdulrazak954

*

Zaune take a ɗakin shi, shi yana kwance a gado ita tana gefen gadon, fuskarsa kicin-kicin kamar bai taɓa dariya ba, saboda a yanzu an kai matsayin da ko kallon Hajara ya yi sai ya ji ɓacin rai sosai da tsanarta.

Da muryar kuka ta ce"Alhaji yanzu haka rayuwar aurenmu za ta cigaba da kasancewa? Shikenan don larura ta same ni sai ka juya mini baya? Ka fa san ba ni na ɗorawa kaina ba, na fi ka shiga damuwa".

A fusace ya ce"Don Allah tashi ki fice mini daga ɗaki! Kai ni dai na yi asarar kuɗina wallahi, ko sadakina ban gama mora ba, ashe kura aka rufe min da fatar akuya, kin san kuwa ko kotu na kai ki Hajara sai an bi mini haƙƙina? Kin san ke ba lafiyayyiya ba ce kina da larura kala-kala kika bari na aure ki ba tare da kin yi mini bayani ba! Kin cutar da ni!".

Ta share hawaye ta ce"Wallahi Alhaji komai a gidan nan ya same ni, ni lafiyayyiya ce, kuma irin wannan a hankali ake bin komai, ban ji daɗin furucinka ba na cewa na cucuce ka, Allah ne fa ya ɗora min, kuma zan nemi magani zan warke".

Ya ce"Wannan ke ya shafa, ki warke ko ki dawwama a haka zaɓinki ne, ni dai duk lokacin da na waiwayo ki to fa tabbas komai zai iya faruwa, don ba zai yiwu a ce ko wata biyu ba mu rufa da aure ba, kina ta tsiro da cuttutuka kala-kala, ba zan lamunta ba sam wallahi".

Ta ce"Zan nemi magani, amma sai dai na Hausa tun da na asibitin ya ƙi, sai dai ina buƙatar kuɗin..."

Ba ta ƙarasa ba ya ce"Tashi ki fita don Allah! Wallahi sisi ba zan sake ba ki da sunan neman magani ba, ba a banza nake samun kuɗin ba!".

Ta tashi a sanyaye ta koma ɗakinta, zama ta yi ta fara kuka a hankali har ya yi tsanani sosai, ta yi mai isarta sannan ta ɗauki waya ta kira wata ƙawarta, don neman mafita, kaf suturunta ta siyarwa da Yayanta wajen neman magani, yanzu saura ɗinkakku kawai, kuma maganin ya ƙi aiki, shiyasa take so ta canza wani maganin ko za ta dace kafin sauran kuɗaɗen hannunta su salwanta ta rasa tudun dafawa.

Ringin ɗaya biyu Fatima ta ɗauki waya, suka gaisa suka taɓa fira tana tsokanarta da amarya, amarci ya ɓoye ta Hajara ta ce"Hmm Fatima ina amarcin yake? Ni da ake ƙoƙarin raba ni da gidan ma".

Fatima cike da son jin gulma ta gyara zama ta ce"Habawa ƙaryar kunnena da ya ji wannan maganar, dama a duniya akwai ranar da kishiya za ta firgita ki? Ke ce fa Hajara...".

Hajara ta ce"Fatima mu bar wannan maganar don Allah! Ni dai yanzu mafita nake nema". Ta ba ta labarin rayuwarta a gidan tsaf

Fatimata ta ce"Lallai ruwa ya daki babbab bargo! Reshe ya juye da mujiya".

Hajara ta haɗe gira kamar tana kallonta kafin ta ce"Ni ce mujiyar? Wannan wace irin Hausa ce? Idan ci mini mutunci za ki yi ki faɗa min, sai na nemi wata mafitar, gari da yawa maye ba ya cin kansa".

Fatima ta ce"A'a ƙawata, ai tuba abun taya murna ne, duk da dai an ce kowa ya tuba don wuya babu lada".

Hajara ta rintse ido tana jin zafi a zuciyarta, amma ba ta yi yunƙurin kashe wayar ba, don ta tabbata Fatima ba za ta rasa maganin matsalarta ba, mahaifiyarta Malamar islamiyya ce, kuma tana haɗa magungunan karya sihiri masu inganci.

Fatima ta ce"To yanzu ya za a yi? Zan faɗawa Mama sai ta haɗa miki, ke za ki zo ki karɓa ko aiko miki za a yi?"

"A aiko min ɗin dai, ko na aiko wani ya karɓa mini" Ta faɗa da sauri don ba ta son haɗa ido da Maman saboda tana ganin kamar duk Fatima sai ta ba ta labarinta, wanda ta san ko ta ba ta maganin za ta iya Allah wadai da halinta na baya.

Fatima ta ce"Babu damuwa, gobe za ki ji ni".

Hajara ta ce"Kuɗin fa, nawa ne?"

Ta ce"Babu matsala, kayan aikin kawai za a siya ai, Mama ko kyauta za ta siya miki, idan an yi zan kira ki". Ta yi mata godiya suka ajiye waya, tana jin sauƙi a zuciyarta, duk da ra san yanzu famtsamar labarinta cikin gari ba zai zama abun mamaki ba, saboda sarai ta san halin ƙawar tata da son jin sabon labari kamar ƴar jarida, ga surutu a duk inda ta zauna, amma indai za ta samu ta warke ta zauna da mijinta lafiya wannan ba wani abun damuwa ba ne.

Washegari da azhar Fatima ta kira ta ta ce ta aiko a karɓar mata. Hajara da farinciki ta ce"Har an yi?"

Ta ce"An yi, tun jiyan na faɗa mata, ta ce za ta koya miki ki dinga yi da kanki, sai kuma na ga ba lallai kin iya ayoyin ba, shi ne kawai na ce ta dinga yi miki ɗin zai fi ko?"

Hajara ta ce"Babu koma ai duk ɗaya ne, na gode".

Ta ɗauki waya ta kira yaron gidansu Ibrahim ta yi masa kwatancen gidan da zai karɓo mata, ta so a ce da ya dawo ya kira ta a waya ta leƙa ƙofar gida ta karɓa, bai yi haka ba, sai ya shigo falon kai tsaye da leda a hannunsa, tana jin muryarsa suna gaisawa da Suwaiba ta fito, ya miƙa mata, ta karɓa tana miƙa masa ɗari biyar ta ce"Ibrahim ga kuɗin babur".

Ya ce"A haba Anti, ki bar shi wallahi, ai gidan ma babu wani nisa, kuma ma kun wuce haka a wurina, ta ce gobe ma za a karɓo".

Hajara ta ce"Na gode sosai!".

Ya fice, tana shirin shiga ɗaki Suwaiba ta ce"Ki dai gama kame-kamenki, wa'adin da na ɗibar miki yana cika, ko Malamai kike kwaɗawa a kwano kina ci sai kin bar gidan nan".

Hajara ba ta ce komai ba ta shige ɗakinta, ta kira Fatima a waya ta sanar da ita duk yadda za ta yi da shi, ta tashi ta yi tana jin kamar matsalarta ta kusa zama tarihi.

Suwaiba ta shiga ɗakinta, ta ɗauki waya ta kira Ibrahim, ranta a ɓace ta ce"Ibrahim da alama ka gaji da zama a ƙarƙashin mijina ko?"

Cikin rashin fahimta ya ce"Hajiya mene ne ya faru?"

Ta ce"Ban sani ba! Har Hajara ta cigaba da aiken ka ba ka sanar da ni ba, ba don yau na kama ku ba?"

Ya ce"Ai ba ki ce duk sanda ta aike ni sai na faɗa miki ba shiyasa Hajiya, kuma yau ne ma kawai ta fara aiken nawa".

Suwaiba ta ce"To idan ka karɓo na goben ka tsaya a waje, zan aiko Saudat ta kawo maka wani ka musanja ka ba ta nawan ka ba wa Saudat wanda ka karɓo ɗin".

Jikinaa ya ɗan yi san yi ya ce"To".

Ta ce"Wallahi idan wani ya ji maganar nan, ko kuma ka saɓa min sai na san yadda na yi na nesanta ka da Alhaji".

Ya ce"Yi haƙuri Hajiya ba zai faru ba ma in sha Allah!".

Washegari kuwa yana karɓowa suka yi yadda suka tsara, aka bawa Hajara ruwa ƙulle a leda ta yi amfani da shi. Tsawon sati ɗaya ana yin haka, wanda idan da ba a yi haka ba da tuni ta warke, Mama ta yi mamaki da ta ji wai matsakar ƙara ƙaimi ma ta yi, saboda haka ta ce ya kamata ta dinga yi da kanta a gani.

Hajara ta shirya ta je gidan suka tattauna, ta ba ta kayan ta koya mata yadda za ta yi, bayan ta biya mata ayoyin sosai, ta kuma yi mata recordin a wayarta, saboda ta riƙe sosai. Tana komawa gida ta zauna ta yi, kwana uku da farawa ta fara jin salama a zuciyarta, har ƙuncin da take ji duk ta ji yana ta raguwa.

Suwaiba tana lura da duk wani motsinta, saboda haka ta gane kullum da safe sai ta zo ta ɗauki kofi da roba mai faɗi a kitchen ta shige ɗakinta, ta rasa me take yi, don haka yau bayan Hajarar ta shiga ta je a hankali tana leƙenta ta window dake bayan ɗakunan, nan ta ganta zauna da ganyen magarya da ruwa ga Qur'ani a kusa da ita, tana daka ganyen magaryar da wasu ƙananun duwatsu, Suwaiba ta koma da baya tana dafe ƙirji, don ta yi zaton Hajarar haƙura ta yi da neman magani, ashe ita canza taku ta yi, ta dawo ta ci gaba da leƙenta har ta gama komai tass, ta jinjina kai tana haki kamar wacce aka yi mata babban laifi ta ce"Idan kin san wata ba ki san wata ba! Hajara wallahi duk nacinki sai kin bar gidan nan".

Ta koma ɗakinta, ta zauna tana jiran dawowar Alhaji.

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.)

WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE ALHAKIN SO MATACCEN BURI MUKULLIN NADAMA DUKA ZA KU SAME SU COMPLETE ***