Da walakin...

PAGE 7

by @sadiyaabdulrazak954

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* ***** *Serious buyers pls* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅

"Suwaiba me yake faruwa?" Alhajin ya tambaya yana kallon Hajara da take hawaye riƙe da takarda.

Hajara ta ce"Amma Alhaji na faɗa maka ina kan neman magani, me yasa za ka yi mini haka, wannan hukuncin ya yi tsauri, har saki uku? Larura ce fa, kana da ƴaƴa mata, idan Allah Ya jarabce su da irin wannan mijin ya yanke irin hukuncin nan ya za ka ji?"

A hasale Suwaiba ta ce"Mugun fatanki ya ƙare a kanki da ahalinki! Ke ma alhakin mutanen da kika cuta ne yake bibiyarki, ƴaƴana ba su zalunci kowa ba, saboda haka alkhairi za su tarar a gidan aurensu!".

Alhaji ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Suwaiba wane ne ya ba ki izinin ɗakko takardar nan ki ba ta?"

Tana juya ido ta ce"To Alhaji me za ka jira? Ko kana nufin za ka cigaba da zama da wacce take bin mazan waje da aurenta? Za ka zauna da wacce ba ta fatan haɗa shimfiɗa da kai?"

Kalmar bin maza ta daki zuciyar Hajara, sosai ta shiga sabon tashin hankali, jikinta ya hau rawa ta kasa furta ko kalma ɗaya.

Alhaji ya ce"Hajara tun farko me yasa kika aure ni kin san ba kya so na? Me na rage ki da shi da kika zaɓi kula wasu mazan da aurena a kanki? Me yasa ba ki ce na sawwaƙe miki ba?"

Da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce"Allah shi ne shaidata, ban san komai ba akan waɗan nan maganganun da kuke jifana da shi" Ta kalli Suwaiba ta ce"Na san wannan duk makircinki ne, kar ki manta Allah Yana kallon kowa da komai, zai tsayar da mu ranar shaida, kuma abin da kika yi mini in sha Allah sai an yi wa ƴaƴanki!".

Alhaji ya ce"Ke Hajara! Idan kika sake ambatar ƴaƴana kika nema musu masifa wallahi kotu ce za ta raba mu!".

Ta zauna a bakin gadon tana hawaye cikin rashin sanin abun yi, ya kalli Suwaiba ya ce"Ki fice".

Ta fita tana jin ranta fess, ya kalli Hajara ya ce"Ba ki amsa mini tambayoyina na?"

Cike da takaici ta ce"Ba ni da lokacin nan, don ba su da wani amfani, tun da ka riga ka yanke hukunci, idan kun cuce ni kai da matarka Allah Ya bi mini haƙƙina!".

Daga haka ta tashi ta buɗr sif, ta fara fito da kaya, Alhaji ya fice jikinsa ya yi sanyi, duk da ba ya nadamar sakinta, tun da yana da hujjar yin hakan. Yana fita ta tsaya da fito da kayan, ta ɗauki waya ta kira yayanta, a taƙaice suka gaisa ta ce"Yaya Sani Alhaji fa ya sake ni yau..."

"Ya sake ki!?" Ya katse ta da tambayar a razane.

Tana kuka ta ce"E".

Ya ce"Yau ga baƙin labari! Yanzu Hajara ba za ki yi wa kanki faɗa ki rungumi maraucinki ba? Yaushe aka yi auren? To ki rufa mana asiri yanzu dai ki zauna ki yi idda a ɗakinki, ko Allah zai sa ya mayar da ke kafin ki gama".

Ta ce"Saki uku ne, bai halatta na yi zaman idda a gidansa ba".

Yaya ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! To wai ma wane mugun abun kika yi masa da har ya yi miki saki uku!?"

Ta ce"Wallahi ban yi masa komai ba, makircin kishiyata ne kawai".

Ya ce"To ai shikenan, tun da haka kika zaɓa, sai ki tattara ki zo ki ci gaba da zama cikin yara, kina hana matana sakewa, ga nauyi ya ƙaru a kaina, kai wannan ai masifa ce!". Ya katse kiran, sai ta bi wayar da kallo tana sake sakin sabon kuka, da a ce saki ɗaya ne ko biyu, tsaf za ta je ta duƙa ta ba Alhaji haƙuri saboda ya mayar da ita, tana ji a jikinta gara zaman gidan na shi duk rintsi, a kan zaman gidan yayanta, wanda sam ba ya son jikinsa ya raɓi arziƙinsa, ga ƴaƴan shi ƙananun yara wanda da ace Allah Ya ba ta haihuwa da tuni tana da waɗanda suka fi su, amma sun yi mata raini kyakkyawa, uwargidansa kuwa kamar za ta cinna mata wuta saboda ƙiyayya, ko tsakar gida ta fito suka haɗa sai ta bi ta da harara, kuma ta girme ta da shekaru, har gara amaryar ba ta raina ta ba, sai dai ita ma kadaran-kadahan, haka rayuwar take.

Tsaf ta gama haɗa kayan sakawarta, ta je ta tattara na kitchen, duk ta dawo da su ɗaki, sai isha'i ta gama, sai ta yanke ta bari sai gobe ta tafi, saboda haka ta yi kwanciyarta, bacci kaɗan ta yi, saboda tunanin yadda gobenta za ta kasance. Washegari da sassafe ta kira Yaya Sani ta ce masa ya za a yi da kwasar kayan? Sai ya yi tsaki kawai ya kashe wayar, ƙarshe sababbin kulolinta ta saka a hijjabi ta kai kasuwa ta siyar, ta taho da masu kwasar kayan, ƙarfe ɗaya mota ta tsaya a ƙofar gidan Yaya Sani, aka juye kaya, ta sa yaran unguwa sun fara shiga da su, Hau'wa uwargidan Yaya ya fito da yaran, ta tare ƙofar gida ta ce"Hajara da izinin wa ake shigo mini da tarkace gidana?"

Ba yau Hajara ta saba jin haka daga bakinta ba, don ta sha kiran gidan nan da nata, a cewarta na ƴaƴanta ne, saboda haka ba ta wani damu ba ta ce"Hauwa! Kin manta matsayina a wurin mai gidan nan ne, da har za ki tare mini ƙofa?"

Hauwa ta ce"Sanin matsayin naki ne ya sa na tsaya magana da ke ai, shi Sanin ne ya ce akwai wajen ajiye shirginki a nan?"

Cike da baƙinciki Hajara ta fito da waya, ta kira Yaya, yana ɗagawa ta ce"Yaya kai ne ka hana ni shigar da kayana gidanka?"

"Wasu kaya kuma?" Ya tambaya yana haɗe gira.

Ta ce"Kayan ɗakina mana, ga ni a ƙofar gida, Hauwa ta hana na shiga da su, yanzu kuma idan muka yi hayaniya sai ka ga laifina..."

A zabure ya katse ta da faɗin"Ke don Allah ya isa! Wace irin hayaniya ana zaune ƙalau? Ki tarar da mace a ɗakin mijinta ki ce za ki yi mata hayaniya? To da wane ya ce miki akwai wurin ajiyar kayan ɗakinki a gidan nan? Ke makauniya ce? A zaure za ki bar su ko a tsakar gida?"

"Shikenan!" Abin da ta ce kenan ta kashe wayar, tana kokowar mayar da ƙwallarta, Hauwa ta juya ta koma gidan har da rufo ƙofa.

A dole ta sa yara su jire mata kayan, ta bazama neman dillalai, kafin magriba ta samu ta siyar da kayan a araha, na kitchen ɗin kuma ta shiga da su, da niyyar su ma siyarwar za ta yi. Tamkar ita ce ta nemi sakin nan, haka Yaya Sani ya rufe ido ya dinga surfa mata masifa da gori kala-kala, a gaban matansa da ƴaƴansa, haka dai ta yi shiru tana share hawaye. Baccin ƙunci ta yi, tana ta tunanin mafita, ta ƙulla ta kunce, ta fara tunanin komawa ƙauyensu ta zauna a can, sai dai ta san tana zuwa za a nema mata mijin aure, ita kuma ba ta jin za ta iya rayuwar ƙauye, saboda haka take ganin gara ta jure, indai Allah Ya sa ta gama idda zamanta a gidan na taƙaitaccen lokaci ne in sha Allah.

Washegari yadda aka yankawa yara biredi haka aka bata, kafin ta tashi daga bacci ma shayinta dake ɗan kofi a buɗe har ya yi sanyi salam, takaici ya sa ta ƙi sha, ta leƙa ta aiki yaro ya siyo mata abun karyawa, wunin ɗaki ta yi a ranar, da daddare da Yaya Sani ya dawo, ya kira ta suka zauna a tsakar gida, ya sanyaya murya sosai, ya ce"Hajara tun da har aurenki ya mutu, na san zaman gidan nan ya kama ki, tun da ba ki da wanda ya fi ni, to ni kuma kin ga yanayin kasuwar tawa sai godiyar Allah, wallahi samuna ya yi baya, ɗan abin da nake samu bai taka kara ba ballantana ya karya, ga mata biyu da ƴaƴa, shi yasa nake ganin zamanki a gidan tamkar ƙarin nauyi ne a gare ni, amma ba kyararki nake yi ba da kika ga ina ta faɗa, wani abun ya kamata ki duba kafin ki aikata, kin yi girma da zaman gida...".

Ta katse shi da faɗin"Wallahi duk na sani Yaya, kuma ba ka fi ni son na gan ni a ɗakina ba, amma babu yadda zan yi da ƙaddara".

Ya ce"Hakane, da ƙaddarar ma.To yanzu dai ki yi haƙuri da maganar da za ki ji daga bakina, a gaskiya Hajara ina ganin idan kina ajiye kayan abincinki kina yin girkinki sai ya fi mana kwanciyar hankali bakiɗaya, kin ga kin yi girman da kin wuce a dinga sammiki abinci, wani abun ka girme shi fa, amma ya kika gani?"

Ta sauke numfashi ta ce"Hakane, sai dai kuma wane ne zai dinga kawo mini kayan abincin?"

Ya ce"A wannan wace irin magana ce? Ke nufinki zama kika zo yi ki miƙe ƙafa komai na yi miki? A'a sana'a za ki kama, ki dinga buƙatunki hankali kwance".

Ta ce"To shikenan zan duba abin da zan yi".

Ya ce"Yanzu ai kina cikin idda bai dace ki yi ta gagari a titi ba, amma ba na ga kin siyar da kayan ɗakinki ba?" Ta gyaɗa masa kai alamar e.

Ya ce"To shawarar da zan ba ki, ki haɗo kuɗin ki ba ni, na saka a kasuwa na dinga juyawa duk wata sai na dinga ba ki ribarki, duk sanda kika tashi yin wani auren sai na ba ki uwar kuɗin ko?"

Ta ce"E hakan ya yi na gode". Ta shiga ɗaki ta ɗakko dubu ɗari uku ta ba shi, ya ce sai an fara zai ga abin da za ta dinga samu duk wata.

LITTAFIN DA WALAKIN... NA KUƊI NE, A KAN NAIRA 500 KACAL, ZA KI IYA BIYAN KUƊIN KARATUNKI TUN YANZU, AKWAI RAGI GA WANDA YA SAYI LITTAFAINA GUDA BIYU. 8028966015 Sadiya Abdulrazak Opay bank ki tura shaida ta nan ***

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.)

WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE ALHAKIN SO MATACCEN BURI MUKULLIN NADAMA DUKA ZA KU SAME SU COMPLETE ***