PAGE 10
*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* ***** *Serious buyers pls* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅
Ya kai awa ɗaya yana buga ƙofar, ba ta buɗe ba, ƙarshe sai ya fara zaginta yana cewa"Ke don kaza-kazanki saboda tsabar raini ni za ki rufewa ƙofa? To don me aka yi auren? Bari gari ya waye yayan ya zo na ji don me aka yi mini auren, wannan ai jahilci ne ba ƙarami ba!".
Har ya gaji ya bari, ba ta buɗe ba, tana zaune tana ta kukan baƙinciki, ba ta taɓa zaton faɗawa tarkon irin wannan ƙaddarar ba, yadda ta ga rana haka ta ga dare, kuma tana jin shi, shi ma bai yi baccin ba, sai sintiri yake yi a tsakar gidan, da asuba tana son fitowa ta yi sallah tana jin tsoro, ana idar da sallah ta kira Yaya Sani a waya, ta yi sa'a kuwa ya ɗauka a kiran farko, ko sallama ba ta yi ba ta ce"Yaya Sani wa ka aura mini?"
Da mamaki ya ce"Ban gane wa na aura miki ba! Sau nawa yaron yana zuwa wajenki kafin auren? Ko wani kika ga ya zo gidan ba shi ba?"
Ta ce"Ina nufin wane ne shi? Amma mahaukaci ne ko?"
Ya ce"Kamar yaya?"
Ta ce"Wallahi Yaya mahaukaci ne, hauka yake yi tuburan, don Allah ka zo ka fitar da ni daga gidan nan!".
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ya faɗa yana jin dirar tashin hankali a kansa. Abokinsa ya faɗa masa dama Sa'id ba shi da lafiya sosai, wani lokacin za a same shi a nutse, wani lokacin kuma yana abu na rashin nutsuwa, kuma ya ce jifa ne aka yi masa, amma ana yi masa magani, zai warke. To amma shi bai taɓa tunanin ya yi tsamarin da har kowa zai fahimta ba, idan ta tabbata mahaukacin gaske ne ya kenan? Ya san dole Hajara rabuwa za ta nema, wanda hakan ba zai yi wa Aminu daɗi ba, don ya faɗa masa ba shi da burin da ya wuce ya ga ɗan'uwansa ya kintsu, kuma aure yana ɗaya daga cikin abin da zai sa ya gyaru, har yake ce masa shi fa zai ma iya biyan kuɗi kawai saboda a samo masa matar da za ta iya zama da Sa'id, ta yi haƙuri da halinsa, to shi ne fa da ya ji zancen kuɗi nan take ya kwashe labarin Hajara ya ba shi, kuma ya tabbatar masa da tabbas Hajara za ta iya wannan jihadin, saboda tana da haƙuri sosai, sannan tana buƙatar yin aure da gaggawa, ya ce masa muddin zai biya shi to zai san duk yadda zai yi don ta amince ta aure shi.
Yaya Sani ya sauke gwauron numfashi tunawa da yarjejeniyar su da Aminu, sanda yake cewa"Sani na san halinka fa, kana iya yin komai a kan kuɗi, indai ka yaudare ni za ka sha mamaki, zan ba ka dubu hamsin indai yarinyar nan ta amince da auren Sa'id".
"An yanka ta tashi!" Cewar Yayan, don kuwa ya karɓe dubu hamsin tun kafin auren, shi kuwa yanzu da ya fitar da kuɗin nan ya mayar wallahi gara a yi masa shegen duka raga-raga, gara ya san magani ya yi da kuɗin, da dai a ce yana ji yana gani ya ƙirga ya mayar masa, saboda haka dole Hajara ta yi haƙuri ta rungumi ƙaddara.
Bai ma san ta kashe wayar ba, sai da ta ƙara kira, firgigit ya dawo daga tunaninsa, ya ɗaga wayar, ta ce"Yaya ko sallah na kasa fitowa na yi, wallahi tsoro nake yi kar ya yi mini wani mugun abun".
A sanyaye ya ce"A'a Hajara, ba a munanawa miji zato, tabbas Sa'id yana da wannan matsalar, jifa ne maƙiya suka yi masa, amma ana kan magani, zai warke in sha Allah!".
Ta ce"Kenan Yaya kana nufin na cigaba da zama da shi a haukan!?"
Ya ce"To Hajara ya za ki yi, ko na ce ya za mu yi? Ƙaddara ce kowa da kalar tasa, ni wallahi idan kika gujewa auren nan ni kika cuta, ni ne a ruwa, don zan shiga wata ƙwarya-ƙwaryar masifa..."
Da sauri ta katse shi da faɗin"Yaya ban gane ba! Ta ya mutuwar aurena zai cuce ka? Idan ma masifa ce ai ni ce zan shiga ba kai ba".
Ya ce"Ba za ki gane ba Hajara, ni ɗan harƙalla ne, yanzu dai anjima zan zo gidan naki, mu ga yadda abun yake". Daga haka suka ajiye waya.
Sai ƙarfe bakwai ta yi shahada ta fito a hankali, ta yi alwala a gurguje ta koma ɗaki don sallah ta tuna babu hijjab ko mayafi a falon, saɗaf-saɗaf ta leƙa ɗakin gadon, ta hango shi shame-shame a gado yana ta bacci har da munshari, har lokacin kuma babu kaya a jikinsa, da wata muguwar sanɗa ta shiga ta ɗakko mayafinta, da janyo ledar sauran kazarta ta fice tana sauke ajiyar zuciya, ta koma falo ta mai da sakata, bayan ta yi sallah ta ƙarasa kazarta ta sha ruwa, sai kuma ta fara hawaye.
Haka ta yi ta zaune tana tufka da warewa, sai ƙarfe goma sannan ta ji ana buga gidan, ta kasa fita ta buɗe, sai da Yaya ya kira ta ya ce ta zo ta buɗe, sannan ta fita ta buɗe, su biyu ta gan su, ko ba a faɗa ba ta san yayan Sa'id ɗin ne, don ta ga kamanninsu sosai, ta gaishe su, sannan suka shigo cikin gidan.
Da damuwa sosai a fuskar Aminu ya ce"Bai yi miki komai ba dai ko? Yana ina?"
Ta ce"Yana ciki".
"Ki taso shi to". Cewar Yaya Sani.
Da sauri ta ce"Wallahi ba zan iya ba, sai dai ku ku shiga".
Aminu ya wuce ɗakin, sun ɗan jima kafin su fito a tare da Sa'id ɗin, a wannan karon da kaya a jikinsa, kuma fuskarsa babu yabo babu fallasa. Suka shiga falon gabaɗaya, suka zauna shiru na ɗan lokaci kafin Aminu ya ce"Sa'id ya muka yi da kai a kan auren nan? Wane alƙawari ka yi mini jiya?"
Da muryar bacci Sa'id ɗin ya ce"Wallahi kuskure aka samu, amma in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba".
"Ka ba ta haƙuri" Aminun ya yi masa umarni.
Ya kalle ta ya ce"Ki yi haƙuri".
Aminu ya ce"To me ka ba ta, ta ci da safen nan?" Ya girgiza kai alamar babu komai.
Ya ce"Ka fita ka samo mata wani abun ta ci". Ya tashi ya fita.
Sannan Aminu ya kalli Hajara ya ce"Don Allah ki yi haƙuri ƙanwata, wannan larurar tashi ce ta raba shi da mata biyun da ya aura, a da Sa'id nutsattsen mutum ne, mai hankali da kamala, ga mai da kai sosai a kan kasuwanci, yana neman halak ɗinsa har yanzu da yake a haka, kwatsam ya faɗa shaye-shaye, wallahi babu wanda ya san dalilinsa, ashe ƙwayoyi yake sha mugaye, har da giya, wanda har suka taɓa ƙwaƙwalwarsa, matarsa ta farkon ita ce uwar ƴaƴansa uku, tana son shi, kuma ta yi iya ƙoƙarinta a kan shi, ƙarshe iyayenta suka ce dole sai ta rabu da shi, rabuwarsu sai ta ƙara ta'azzara abun, shaye-shayen ya yi tsanani, ni na shige gaba aka aura masa wata, satinta ɗaya ta ƙi zama, ƙarshe kotu ta kai mu aka raba auren".
Ya sauke numfashi sannan ya cigaba"Hajara Sa'id shi da kansa yana ƙin wannan rayuwar, kawai rashin wacce za ta saita shi a hanya ne, namiji fa idan ba shi da uwa a raye, ba shi da matar aure to sai a hankali, wani lokacin sai ya zauna ya yi ta kuka yana cewa ya zai yi ya daina wannan rayuwar? Ni kin ga ina da mata har biyu, ba zai yiwu na ce zan zauna na dinga kula da shi ba, amma idan yana da aure matarsa za ta dinga sanin shige da ficensa, kuma za ki iya jan hankalinsa wurin hana shi yawon daren ma a hankali abun zai ragu in sha Allah!".
Hajara tana share hawaye ta ce"Amma idan kun duba zamana da shi akwai haɗari, idan ya yi mini wani abun fa? Ga shi mu kaɗai a gida, jiya fa kamar zai ɓalla ƙofar nan, ya dinga zagina, ga katifarsa sai wari take yi ya ɗauka ya ɗora ta a kan gadona".
Ya ce"Abun babu daɗi, amma ki jure, za ki iya gyara shi in sha Allah!".
Ta ce"Gaskiya ba zan iya ba, ina son rayuwata, ina ga rabuwarmu sai ta fi alkhairi, har giya fa!".
A fusace Yaya Sani ya ce"Ke Hajara wannan ai wulaƙanci ne! Ta ya mutum ya kwantar da murya yana ta ba ki baki, kina neman aibata masa ɗan'uwa? Ke ba musulma ba ce ba ki san ƙaddara ba? Idan kin rabu da shi kin san inda za ki faɗa kuma? Ke kenan haka za ki ƙare rayuwarki da garari a gari da sunan aure? Wannan fa aure na uku ne!".
Aminu ya ce"A'a Sani ka bi ta a hankali, dole za ta ji tsoro dama".
Ya kalli Hajara ya ce"Ƙanwata, Sa'id idan yana cikin hayyacinsa wallahi mutum ne mai sauƙin hali, kin ga yadda nake ba shi umarni a gabanki? Ke ma haka zai bi umarninki, ina tabbatar miki muddin kika ja shi a jiki, tsaf za ki hana shi fitar daren ma bakiɗaya, don Allah ki daure, ki taimaki rayuwar shi, ƴaƴan shi suna gidana wurin matata, idan kina so ko guda ɗaya sai a kawo miki ku zauna, kya rage jin tsoron".
"Ko dai ba ki amince da zaman nan ba?" Ya tambaye ta jin ba ta ce komai ba.
Yaya Sani ya yi farat ya ce"Ta amince mana!".
Aminu ya ce"A'a Sani, ba kai ne mai zama ba".
Hajara ta share hawaye duk ta firgice, ta ce"Shikenan zan gwada na gani, a kawo yaran duka mu zauna".
Aminu ya ce"Allah Ya saka miki da alkhairi, kuma tun da har kina da zuciyar taimako Allah zai tallafa miki, in sha Allah za ki iya. Duk wani abu da ya yi miki zan ba ki lambata kawai ki kira ni, idan akwai abin da kuke buƙata bai siya ba, ki sanar min zan kawo miki, zan dinga zuwa ina duba ku, don Allah ki yi mini wannan alfarmar ki zauna da Sa'id".
Ta ce"Allah Ya ba ni iko!".
Sai da ya dawo sannan suka yi mata sallama suka fita. Ta zauna shiru kafin Sa'id ya shigo ɗakin, ta lura jikinsa a sanyaye yake, ya miƙa mata leda, ta karɓa hannunta yana rawa, don wani mugun tsoron shi take yi, ta fita ta je kitchen ta ɗakko kofuna da faranti, ta zuba shayi da indomi ta miƙa masa, ita kuma ta ajiye nata a gefe, ya ɗauka ya fara sha, sai da ya gama sannan ya ce"Ki karya mana" Kamar mai jiran umarni ta fara ci, sai da ta cinye tass, ta sunkuyar da kai.
A sanyaye ya ce"Hajara!".
Ta ce"Na'am" Hawaye ya zubo mana.
Ya ce"Dole aka yi miki kika aure ni ko?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.
Ya ce"Ki yi haƙuri don Allah, na san ba za ki so ni ba, saboda ni ba mutumin kirki ba ne, amma ina iya kokarina ganin na canza halina, in sha Allah za mu zauna lafiya".
Ta ce"Allah Ya sa".
Suka yi shiru na dan lokaci kafin ya fita, tana ji ya yi wanka ya zo ya ce mata yana zuwa, kai kawai ta gyada masa, ya fice daga gidan, ya dan jima sannan ya dawo, kayan abinci ya kawo masu yawa, sannan ya dauki gas ya ce ya zubo, ya ce mata ya tafi kasuwa, har azhar tana zaune shiru jikinta duka ya mutu, tana tsoron zaman auren nan, amma ta saka a ranta za ta gwada, idan ta ga ya fi karfinta kuma dole Yaya ya shafa mata lafiya, da ta yi rayuwa cikin hadari gara ta koma kauye da zama ki tsoho ne ta aura. Sai da ta yi sallah ta shiga kitchen, komai na bukata ya siyo har kayan miya, ta yi girki ta ci ta shiga dakin gadon ta dage katifar tashi, ta jinginata da jikin bango, ta gyara dakin.
Bayan magriba ya dawo, ta kawo masa abinci, yau ta lura yana cikin hayyacinsa, yana ta janta da fira tana nokewa, karshen ta bar shi a falo ta je ta kwanta, sai wajan karfe tara ya shigo dakin duk tana lura da shi bai yi sallar isha'i ba, ya cire kayansa tsaf kamar jiya ya kwanta, ya matso kusa da ita, a darare ta yarda ta ba shi hakkinsa, ko da ta fita wanka ta dade a tsakar gida tana kuka, kafin ta koma dakin, ta tarar har ya yi bacci haka tsirara, sai ta shimfida sallaya ta dauki fulo ta kwanta a kasa, washegari da ta yi sallar asuba zaune ta yi tana ta tunanin ta inda za ta fara gyara shi, sanda ya tashi gari ya yi haske sosai, haka ba kaya ya fita bandaki, da ya dawo ba ta ga alamar ya yi wankan tsarki ba, ya saka jallabiya ya tada sallah, kamar ta yi masa magana, sai dai tana fargaba, bayan sun karya ya fice.
Yau da daddare shiru bai dawo kamar jiya ba, har ta gaji ta yi bacci, sai sha biyu da rabi ya dawo yana ta buga gidan, ya tashi ta je ta bude, tana budewa ta ji yiff! Ya fado, ashe manne yake a jikin kofar, ta ja da baya da sauri tana furta"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
Sau uku yana faduwa kafin ya samu ya tashi tsaye, yau kam tana da tabbacin a buge yake sosai, ta rufe gidan, ta tsaye tana kallon ikon Allah, sai dafa bango yake yi yana kiran sunanta.
A tsorace ta zo za ta shige dakin, ba ta Ankara ba ta ga ya yi tsalle ya rikota, yana cewa"Kama ni mana Hajara".
Firgici ya sa ta kwalla kara, da iya karfinta ta hankade shi, kan shi ya bugu da bango sannan ya zube a kasa, ganin bai sake yunkurin tashi ba, sai ta haska shi da wayarta, tana yana ta fari da ido, wani ihun ta kwala sakamakon ganin jini a kansa, nan jikinta ya hau karkarwa, ta cika da tsoro, tana sake haska shi ta ga ya ma daina motsin, da sauri ta nemo lambar yayan shi, ta kira bai daga ba, sai ta kira ta Yaya Sani, ta yi sa'ar samun shi, yana dagawa ta fashe da kuka ta ce"Yaya ka zo gidana, ina ga fa na kashe Sa'id".
Ya tashi a zabure yana salati, ya zura riga ya fice.
A NAN ZA A DAKATA A FREE PAGE, MAI SO SAI YA BIYO NI, INA KYAUTATA ZATON BA ZA KU YI NADAMAR KARANTA LABARIN NAN BA, AKWAI DARUSA DA DAMA A GABA, BA KU SAN WACE CE HAJARA BA, DA KUMA DALILIN RABUWARSU DA MIJINTA NA FARKO, AKWAI ABUBUWA DA DAMA CIKIN RAYUWARTA TA BAYA DA ZA KU JI, DA WACCE ZA TA FUSKANTA A NAN GABA.
DA 500 DINKI ZA KI SHA KARATU
8028966015 Sadiya Abdulrazak opay bank *** *** [9/20, 9:44 AM] Sadiya Abdulrazak: *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* ***** *Serious buyers pls* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅