Chapter 5
PAGE 5
A hanya ya tsaya ya siyawa Gwaggo tuwo ya tafi da shi gidan, ya miƙa mata ya zauna ya yi shiru, ta ce"Nazifi, ko daga gidan nasu kake?"
Ya ce"Daga can nake".
Ta ce"Ya kuka yi?"
Ya ce"Wallahi ita da babar tata sun ƙi fahimtata, wai zancen ma na sake ta suke yi".
Gwaggo ta ce"La ila ha illallahu! Saki kuma? Duk saboda ni? Ka ga taya ni haɗa kayan nan na bar maka gidanka yau, ba ka ba ta haƙuri ba ka faɗa mata ni ba baƙuwar zafi ba ce?"
Nazifi ya ce"Na faɗa mata za ki tafi tun da haka ta zaɓa, amma duk da haka zancen rabuwa take yi".
Ta ce"To Allah Ya kyauta".
Ganin ta janyo tsohuwar akwatinta ta fara haɗa kaya jikinsa ya yi sanyi kamar an zare masa laka, zuciyarsa kuma ta fara kumbura, sai a yanzu ne ma yake ganin Maryam da uwarta fa sun ci mutuncinsa, ya tuna ƙima sa daraja irin ta uwa, ya tuna goyon ciki, haihuwa har zuwa shayarwa da raino, ga kula da tarbiyya da karatunsa Gwaggo ba ta gajiya ba, anya kuwa idan ya zaɓi ra'ayin wata mace wacce suka haɗu rana tsaka ya wofantar da mahaifiyarsa zai gama da duniya lafiya? Sai ya ji tausayinta ya kama shi, har ya ji gara ya zaɓi rayuwa babu aure a kan ya zama silar ɓacin ranta, ya matsa kusa da ita, ya mayar da kayan ya zuge akwatin ya matsar gefe, sai ya sunkuyar da kai, Gwaggo ta kafe shi da kallo, ya ce"Gwaggo babu inda za ki je fa, ke uwata ce ba a canza uwa, amma ana canza mata, babu macen da za ta raba ni da ke dare ɗaya, zan iya rayuwa babu auren ma gabaɗaya matuƙar ina tare da albarkarki".
Ita ma sai jikinta ya yi sanyi, ta ce"Nazifi ba zai yiwu ka ƙi aure saboda ni ba, wallahi so ne yasa na zaɓi zama a kusa da kai, ka sani duk cikinku na fi sonka, ba zan so abin da zai takura rayuwarka ba, saboda haka gara na tafi ɗin kawai tun da haka ta zaɓa".
Ya ce"Gwaggo wallahi ba za ki tafi ba, indai ba za ta zauna da ke ba a gidan nan, to tabbas zan haƙura na sake ta kamar yadda ta ce".
Gwaggo ta ce"A'a kar ma ka fara, ba zai faru ba ma, tun da ka ce sai na zauna to zan kwashe kayana daga kitchen ɗinta, sannan zan dinga girkina a murhuna, idan ta ga dama ma ko gaishe ni kar ta yi, tun da ba zamana take yi ba, indai hakan ya yi mata shikenan".
Ya ce"Wallahi da na san haka Maryam take da ba zan fara aurenta ba"
Gwaggo ta ce"Ka daina yiwa kanka baki, ai idan ka lura har da ƙuruciya da rawar kai irin ra yaran zamani, Allah dai Ya kyauta".
Ya ce"Amin, bari na siyo miki tuwon".
Ta ce"To kai me ka ci?"
Ya ce"Tun kunu da na sha a kasuwa".
Da sigar tsokana ta ce"Kai dai sunanka angogu ba ango ba, to ko ƴar taliya za ka dafa mana? Ka ga Yasmin tuwon rana da ka siyo ma ba ta ci ba, ka ganta ta yi lakur ko motsin kirki ba ta iyawa saboda yunwa, ba mu iya kunna gas ɗin ba, kuma matarka ta ce za mu babbake, na ce to mu bar shi tun da ba mu san kalar kaifin bakinta ba".
Ransa a ɓace ya ce"Kamar ya za ku babbake?"
Ta kwashe labarin yadda aka yi da Yasmin ta zo kunna gas ɗin ta faɗa masa, ya ce"Tabb ai kuwa da kun babbake ɗin, gaskiya kar yarinyar nan ta sake gwada irin wannan tsautsayin, nawa take da za ta ce za ta yi girki?"
Ya tashi ya shiga kitchen ɗin, sai bai ga kayan abincin ba, ya koma ɗaki nan ma bai gani ba, saboda Maryam a cikin sif ta loda su ta kuma rufe ta zare mukullin ta tafi da shi, abun ya ba shi mamaki, kamar ya kira ta ya tambaye ta, sai kuma ya ga ai ba shi ya siyo ba dama gararta ce, don haka ya fita ya siyo taliyar ya dafa musu, suna ci suna fira cike da nishaɗi kamar suna gidansu na da.
Ƙarfe tara ya yi mata sallama ya tafi ya kwanta, sai dai ya kasa baccin, ya shiga tunanin yadda rayuwar aurensa ta fara da ƙalubale, yana son Maryam sosai, har zuciyarsa yake son ƙare rayuwarsa da ita, sai dai ya fara tunanin ita ba son shi take yi ba, tun da har wannan ƴar matsalar za ta saka ta ce ya sake ta, wajen goma da rabi ya kira ta a waya, har sau uku ba ta ɗaga ba, ya kunna data ya ganta a online, kamar ya yi mata magana sai ya fasa, ta ajiye wayar yana jira gobe ta yi, ya je ya ji yadda za su kaya da ita, don shi dai bai shirya rabuwa da ita ba.
A ɓangaren Maryam kuwa bayan tafiyar Nazifi, Uwani ta saka ta a gaba da zuga, tana nuna mata ya zama dole ta haƙura da auren nan indai tana son kanta da arziƙi, ta na ta nuna mata mutuwar aure ba komai ba ce, ballantana ita da ba ta haihu ba ma, nan da nan wani da ya fi shi zai fito ya aure ta, ta nuna mata da ka yi rayuwar aure cikin ƙunci da rashin ƴanci gara a ce ka ƙi zaman auren ma, ai dai ka san kana da cikakken ƴancinka.
Shi kuwa Baba bai sake bi ta kanta ba, ya zuba ido ta ga gudun ruwansu.
Tsaf ta kwashe karatun da aka biya mata, don haka har ta fara jin tsanar Nazifi shi da auren nasa duka, ta kuma saka a ranta ba za ta koma ba, dole ya sake ta, shiyasa tana kallon kiransa ma ta ƙi ɗagawa, lafiya ƙalau ta shari baccinta sai ta ji kamar dama ba aure ta yi ba, unguwa kawai ta je ta kwana biyu ta dawo gidan babarta mai ƙaunarta.
Washegari Nazifi tun safe ya kira ta a waya ba ta ɗauka ba, haka dai ya tafi kasuwa, sai la'asar ya tashi ya dawo gida ya yi wanka ya canza kaya ya tafi gidan nasu, da ita ya fara cin karo bayan ya shawo kwanar kayin nasu, tana tsaye a ƙofar gidan kusa da su, ta yaye hijjabinta ta baya gabaɗaya bayanta a waje, ga shi riga da siket ɗin jikinta sun ɗame ta sosai, tsaye take a kan yarinyar da take soya awarar siyarwa a ƙofar gidan, ta ɗauki ɗaya a cikin ɗan kwandon, ta kai bakinta kenan suka haɗa ido da Nazifi wanda ya tsaya yana kallonta ransa a ɓace cike da takaici.
Wani haushinsa ya kamata, ta tsaya tana ƙare masa kallo kamar yadda yake kallonta, Nazifi dogo ne siriri, baƙi ba wani kyakkyawa ba ne, shi ba kuɗi ba, sai yau ma ta ji haushin kanta, ta fara tunanin me yasa ma ta aure shi? Kamar wacce aka yiwa asiri, idonta ya rufe saboda ganin son da yake yi mata.
Ta yi tsaki bayan ta karɓi awarar da yarinyar ta miƙo mata, ta juya ta fara tafiya, kamar ba ta san wajenta ya zo ba.
Ya bi bayanta yana kiran sunanta, ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya ƙarasa ya tsaya a gabanta yana kallonta zuciyarsa cike da sonta, ya ce"Amma Maryam kar ki manta yanzu ke matar aure ce fa, bai kamata ki ɗage hijjabinki haka a titi ba, duk wanda ya kallar mini ke a haka wallahi ya cuce ni".
Ta yi masa wata kafirar harara ta ce"Malam me yake tafe da kai?"
Ya daure ya yi murmushin yaƙe ya ce"Ango ya zo wajen amaryarsa a tambaye shi dalili? Zuwa na yi mu tafi mana".
Ta gyara tsayuwarta ta ce"Nazifi kana son kanka da arziƙi? To ka taƙaitawa kanka wahala ka sake ni, zan faɗa maka a taƙaice, wallahi ko sama da ƙasa za ta haɗe, ko uwata za ta taso daga ƙabari ba zan koma gidanka ba, ka ga wannan bayanin da na yi maka? Indai ba ka fahimce shi ba, to ba za ka taɓa fahimta ba, ka ga kenan ba ni da lokacin ɓatawa wajen sauraronka".
Ransa ya ɓaci, a ɗabi'arsa shi mutum ne mai saurin fushi, amma yakan danne zuciyarsa idan yana gaban Maryam, ya ce"Ki yi haƙuri Maryam, indai a kan Gwaggo ne ta amince da wannan sharuɗan da kika kafa da farko, za ta dinga girkinta, kuma ta ce ma za ta kwashe kayanta daga kitchen ɗin".
Ta yi wata shegiyar dariya ta ce"Yanzu da kuka ji uwar bari kenan! To sai ka koma ka faɗa mata kun makaro, ita dama sau ɗaya take zuwa a rayuwa, da ace ka amince tun a lokacin da an yi hakan, amma ka yi sake yanzu auren duka ya fita daga raina, kuma wallahi babu wanda ya isa ya saka ni na ci gaba da yi, don Allah Nazifi idan ba takarda ka zo kawo mini ba kar ka sake zuwa wajena, ni zan fi so ma ka turo min da sakin ta waya saboda ba na son ganinka".
Ganin ya daskare ya kasa cewa komai, sai ta yi tsaki ta shige gidan, ya rasa ma me yake yi masa daɗi, me kuma zai ce mata ta yarda ta koma? Ya lura ita ma babarta ba son ci gaban auren take yi ba, don haka ya yanke ba sai ya sake tuntuɓarta ba, kawai sai ya zauna a ƙofar gidan yana jiran Babanta ya dawo, ya saƙa wannan ya ware wancen har aka kira magriba, ya shiga masallaci ya yi, ya dawo ya zauna, babu jimawa kuwa sai ga Baban ya dawo.
Ya tashi da sauri, ya rusuna yana gaishe shi, Baba ya amsa yana cewa"Kamar Nazifi ko?"
Yana rusunar da kai ya ce"Ni ne Baba".
Baba ya ce"Sannu da zuwa".
Ya ce"Yawwa".
Ya ce"Wajen Maryam ka zo? Ka shigo daga ciki".
Nazifi ya ɗan sosa kai ya ce"Ai wajenka na zo, ita mun yi magana tun ɗazu, kai na zauna jira".
Baba ya ce"To shigo daga zaure".
Suka shiga, Baba ya shiga cikin gidan ya ɗakko tabarma, ya dawo ya shimfiɗa suka zauna, Baba ya ce"Wai mene ne yake faruwa tsakaninku?"
Nazifi ya zayyana masa komai, sai Baba ya ji akwai ragi a maganarsa ba kamar yadda Uwani ta faɗa masa har da dukan Maryam mahaifiyarsa ta yi ba, ya ce"Sun sanar da ni, to kai yanzu wane mataki ka ɗauka?"
Ya ce"Ita Maryam ɗin tun farko ita ce ta ce ta yarda za su zauna da Gwaggo amma kowa ya yi harkarsa, kowa ya yi girkinsa, to da farko ban amince ba, shi ne abin da ya tada tarzomar, duba da ganin mahaifiyata ce, tana da cikakken iko a gidana, kuma ta cancanci mutuntawa daga matata, amma da na ga hakan ya ƙi kawo maslaha sai na ce na amince da sharaɗin nata, ita ma kuma Gwaggon ta amince, amma dai har yanzu Maryam ɗin ta ƙi ta nuna saki kawai take nema".
Baba ya ce"Saki!? Kai ɗan yau ka haife shi ba ka haifi halinsa ba, ka ga ni fa shiyasa ba na saka baƙincikin ɗan yau a kaina, sai su kashe ka a banza, kuma dama Maryam ta fita da ban da ƴaƴan gidan nan, za ta aikata, auren ma da ya ta yi?"
Nazifi ya ce"Sai haƙuri Baba".
Baba ya tashi ya ce"Jira ni kaɗan".
Ya shiga cikin gidan ya ƙwalawa Maryam kira, har ta tashi Uwani ta mayar da ita ta zaunar tana tsuke fuska ta ce"Malam lafiya?"
Ya shigo ɗakin yana cewa"Uwani wannan wane irin shirme ne haka? Ya za ki ɗaurewa yarinya ta samu saken cewa ba za ta koma ɗakin mijinta ba?"
Maryam kamar za ta yi kuka ta ce"Baba ni fa wannan zaman ba zai yiwu ba".
Ya ce"A kan me? Ba matsalar babar shi ba ce? Ai ya karanta mini komai, ya ce zai bi sharaɗin da kika kafa da farko, ku zauna da uwar tashi ba ruwan kowa da kowa, sai kace wasu facaloli, kai Allah Ya shirya yaran zamani, maza saka hijjabinki ki wuce ku tafi".
Uwani ta ce"Haba Malam don ka ga ba ni na haifi yarinyar nan ba, shiyasa ba za ka ƙyale ni na ƙwatar mata ƴancinta ba?"
Ya ce"Ko wacce kika haifa ce haka zan yi mata, ni ba na ma taɓa sakawa a raina ba ke kika haifi Maryam ba, tun da ba kya wani abu na nuna bambanci, amma kin san wannan zaman nata ba shi da wata fa'ida".
Ya kalli Maryam ya ce"Ba ki tashi kin saka hijjabin ba?"
Ta tashi a zabure kamar wacce za ta kai wa wani duka, tana turo baki da haɗe gira ta saka hijjabin ya fita ta bi bayansa, ya ce"Ina akwatin?"
Ta ce"Gobe a kawo mini".
Uwani takaici ya rufe ta, sai take jin kamar da zuciyarta za ta tafi, sam ba ta so hakan ba, so ta yi a yita ta ƙare, auren nan ya mutu a cikin satin nan, duniya ta shaida.
"Maryam!" Ta ƙwala mata kira murya a shaƙe.
Ta koma ɗakin tana share hawayen da ya zubo mata, idan ta tuna haka za ta tsufa cikin bauta da rayuwar ƙunci sai ta ji har gara mutuwa a kan gidan Nazifin.
Uwani ta ja hannunta har ƙuryar ɗaki ta ce"Ba kuka za ki yi ba, ki koma ɗin amma ki ɗaura ɗamarar yi musu gashin ƙuma shi da uwar tashi, kada ki sake ki saurara musu, musamman ita uwar, saboda idan ta ga abun ba na ƙare ba ne, ita ce za ta saka dole ya sake ki, sannan kada ki sake yarda ku haɗa shimfiɗa, idan kuma kin je kin sakar masa jiki kin samu ciki kin ga kanki kika cuta, ki yi zaman zawarci da ciki".
"Ke Maryam!" Muryar Baba ta katse musu tattaunawar.
Wannan karon tare suka fito Uwani tana cewa"Allah Ya ba da sa'a Maryam".
Suka tarar da Nazifi a zaure, Baba ya ce"Tashi ku tafi Nazifi, Allah Ya rufa asiri".
Ya tashi ya naɗe tabarmar yana cewa"To Baba na gode, Allah Ya saka".
Ya yi gaba, Maryam ta bi bayansa, sai da suka ɗan yi nisa da gidan suka kusa kai wa titi sannan ya tsaya har ta ƙaraso, saboda su samu damar jerawa.