Miji goma(ba uba goma ba ne)

Chapter 7

by @sadiyaabdulrazak954

PAGE 7


    A zuciye sosai Nazifi ya ƙarasa gidan, ko sallama bai yi ba ya banka ɗakin Maryam, ba ta ɗago ta kalle shi ba ta ci gaba da aikinta ranta fess, ya ce"Ke Maryam akan wane dalilin kika watsawa babata ruwan ƙazanta?"

Ta ɗago tana hararar shi cike da tsiwa ta ce"Ƙila tare mini hanya ta yi".

Tass! Ya ɗauke ta da wani zazzafan mari, ta tsaya tana mamaki ya ƙara sauke mata wani, yana nunata da yatsa a fusace kamar zai tsokane mata ido ya ce"Wallahi uwata ta fi kowa a wajena, ke ba ki kai wacce za ta wulaƙanta uwata ba, duk duniya ma babu indai ina raye ina kuma da ikon rama mata..."

Ta katse shi da faɗin"To ai ba ka rama mata ba, wanke-wanke za ka yi ka watsa mini ruwan na yi tsumu-tsumu kamar an tsoma kaza a ruwa shi ne zan san ka rama mata".

Tana rufe baki ya naushi bakin nata, ya ce"Wallahi ni dai na yi asarar kuɗi da lokacina wajen aurenki, maza ki tattara gayyar tsiyarki ki bar mini gidana".

Har ya juya zai tafi, sai kuma zuciya ta ciyo shi, ya tuna yadda ya dinga sintiri a ƙofar gidansu yana yi mata wahala, yana yi mata ladabi kamar uwarsa, ya tuna kuɗin da ya kashe a kayan lefe, da shagalin bikin, da ya san wacce zai aura ai da a kasuwa ya saka kuɗin ya ƙara jari ya ciji leɓe, sannan ya dawo kamar an jeho shi, tana duƙe tana haɗa kaya, ya yi mata wani dundu a bayanta, sannan ya rufe ta da duka ta ƙo'ina yana cewa"Wallahi sai na daki kuɗina, ƴar wahala wacce ba ta san halacci ba!".

Maryam ma ta taso tana kai masa duka daidai iya ƙarfinta, sai dai ƙarfin ba ɗaya ba ne, idan ta dake shi ma ita ce take jiggata hannunta saboda ƙaƙƙarfan ƙashi kawai take duka, don haka cikin ƙanƙanin lokaci Nazifi ya yi mata lilis ya tara mata gajiya, fuskarta kuwa har ta kumbura, dama naushin da ya yi mata bakinta ya fashe, bai bi ta kan ashar ɗin da take ƙundumawa Gwaggo ba, ya fice daga gidan, saboda idan ya biyewa zuciya sai ya kashe ta, tun da ta lura bakinta ba zai yi shiru ba.

 Kuka sosai Maryam ta ci kafin ta saka hijjabi ta tafi gida, don fasa haɗa kayan ma ta yi, yana daga runfar maƙotansu a zaune, dama jira yake yi ta fice ya zo ya rufe gidan, sai da ta yi nisa sannan ya shiga, sai ya ga kayan duka a baje ba ta haɗa ba, nan ya yi tozali da tarin kayan lefen da ya haɗa mata, zuciya ta faɗa masa ya ragewa kansa zafi a kansu, ai kuwa ya ɗauki atamfofi guda biyar, leshi guda biyu, ya kwasarwa Yasmin kayan kwalliya, sannan ya rufe ɗakin ya tafi gidan Gwaggo, a hanya ya tsaya ya samu leda ya zuba kayan, ya zauna a gaban Gwaggo cike da kunyar abin da matarsa ta yi mata ya ce"Gwaggo don Allah ki yi haƙuri, na ja miki tozarci, wallahi inda na san haka za ta faru da tun farko ma ban yi auren nan ba".

Gwaggo ta ce"Ba komai Nazifi, kowa da irin halinsa, ba ga shi na bar mata gidan ba? Yanzu sai ku zauna lafiya".

Ya ce"Haba Gwaggo, ai ko ita ta gwal ce wallahi ba za ta yi miki wannan abun na iya ƙara kwana ɗaya da ita ba, na sake ta".

A ranta ta ji daɗin yadda ɗanta ya nuna tana da muhimmanci a wajensa, ta ce"Na gode Nazifi, Allah Ya shi albarka, amma da ba ka rabu da matarka ba, tun da na tafi ƙila ku ci gaba da zaman lafiya, dama fa ba lallai ne sai matarka ta so danginka ba, wata nagartar tata za ka duba sai ka yi haƙuri da wani halin nata".

Ya ce"Haba Gwaggo ina nagarta ga wacce za ta iya wulaƙanta mahaifiyarka? Ba fa zama za ki yi a gidan nan ba, kin ga idan sun gama kwashe kayanta sai ki koma, ba na son su zo wani ya ganki ya zage ne, amma da a yau ɗin za ki koma, gara na haƙura da auren matuƙar za ki zauna lafiya".

Ta yi murmushi ta ce"Ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba,nan gaba sai ka ga ka samu wacce za ta bi ra'ayinka".

Ya ce"To Allah Ya sa, ga wannan kayan Gwaggo kya ɗinka".

Ta karɓi ledar da ya miƙo mata, tana cewa"To daga ina kuma? Na ga sallah da saura".

Ya ce"Na lefen yarinyar nan ne, na kwaso saboda na rage asara".

Gwaggo ta yi ƴar dariya ganin yadda ya yi maganar bil haƙƙi, ta ce"Nazifi kenan, idan ka yi wani abun sai ka ce yaro ƙarami, yanzu dai ka san wannan wata fitinar ka siyo ko? Lefenta ai haƙƙinta ne ka je ka mayar mata, ni ba yafe".

Zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta ce"Ka je ka mayar".

Ya ce"To".

Daga nan suka shiga fira, ta ba shi abinci ya ci, sai tara da rabi ya koma gida, washegari da safe ya haɗa kayan shi ya saka a ɗakin Gwaggo ya kulle, ya ɗauki kayan da ta ƙi karɓa ya tafi da su kasuwa, sai ya bawa wani mai kanti dake kusa da su mukullin gidan, ya ce idan wasu sun zo ya ba su.

 Ita kuwa Maryam da kuka sosai ta shiga gidan nasu, lokacin Baba yana tsakar gida yana cin abinci, Uwani da take ta jiran dawowar tata ta miƙe tana rafka salati kamar ba ta san komai ba ta ce"Ba dai yaron nan sakinki ya yi ba?"

Baba ya yi mata wani kallo bai ce komai ba, tun da ya san dama sakin suke so.

Maryam ta shige ɗaki tana ƙara sautin kukanta, Uwani ta mara mata baya, tana cewa"To ai ya isa haka, na ji daɗi da kika shigo da kukan kissar nan wallahi, kin ga babanki zai ce ba da son ranki komai ya faru ba".

Ganin Maryam ta ƙi daina kukan kuma ta ƙi ɗagowa sai ta sha jinin jikinta, ta ce"Maryam to ko dai kina son mijinki?"

Sai a lokacin ta ɗago, Uwani ta yi arba da kumburarriyar fuskarta, ta ce"Innalillah wa inna ilaihi raji'un! Faɗuwa kuka yi a adaidaita sahun?"

Tana kuka ta ce"Dukana ya yi".

Uwani ta ji daɗi a ranta, ta ce'Allah Ya ƙara, kaɗan ma kika gani'.

A fili kuwa ta ce"Duka!? Duka dai wanda na sani?Me kike yi da ba ki ɗauki turmi kin rotse shi ba?"

Sai ta yi waje tana"Malam! Mun shiga uku...".

Baba ya katse ta da faɗin"Kun shiga uku dai".

Ta ce"Shigo ka ga fuskar yarinyar nan, bayan sakin da ya yi mata, har da yi mata dukan kawo wuƙa, fuska ta kumbura kamar an saka mata yis".

Baba ya ci gaba da cin abincinsa bai ce komai ba.

Ta ce"Ga duka ga tsinka jaka? Wallahi ba zata saɓu ba bindiga a ruwa, sai na bi mata kadinta!".

Ta shiga ɗakin, ta tashi Maryam zaune tana cewa"Bar kukan haka, wallahi sai na ƙarti daidai da shi sun yi masa duka, ke dai tun da kin rabu da ƙaya Alhamdulillah!".

Ta fita ta kunna wuta, ta ɗora ruwan zafi, daidai nan Sunusi ya shigo, Baba kuma ya fita, ko sallamar da ya yi ba ta amsa ba, ta tare shi da faɗin"Sunusi ka ga abin da wannan tambaɗaɗɗen yaron ya yi wa ƴar'uwarka? Ya yi mata dukan mutuwa sumanta uku, kuma ya sake ta, da ƙyar ta kawo kanta gidan nan tana jiri tana faɗuwa".

Ya ce"Subhanallah! Ya sake ta kuma? Ko fa sati ba a yi da auren ba, gobe Lahadi shi ne zai cika sati ɗaya cif".

Uwani ta ce"Ubanka kai da satin, ina maka zancen duka wato kai mutuwar auren ce ma ta dame ka!".

Ya ce"To babarmu kin san wane tudu da gangare suka hau har ya dake ta? Kin san fa Maryam ba ta da kunya, ƙila zagin shi ta yi".

Ta ce"Kai dalla gafara, kar na gwabje ka, ashe dai bayan raina ba za ka iya ƙwatarwa ƙannenka ƴanci ba, Allah wadaran naka ya lalace".

Sunusi ya buɗe ɗakinsa ya shige, ita so ta yi ya fusata ya kwashi abokansa a daren su je su yiwa Nazifi duka, ashe ba zai iya komai ba.

Sai da ruwan ya yi zafi sosai sannan ta juye a baho ta kai banɗaki, ta shiga ɗakin ta taso Maryam ta ce"Maza ki je ki yi wanka, ki gaggasa jikinki sosai da zani, idan ba haka ba ba za ki iya bacci ba, Allah Ya saka miki".

Maryam ta yi wanka, ta zuba mata abinci ta ci, ta kwanta nan take kuwa sai bacci ya ɗauke ta.

 Washegari Uwani ta kira ƙawayenta da maƙota suka je suka kwashe kaya tass, a ranar kuwa ta siyar da su aka ajiye kuɗin. Sai bayan kwana biyu da Maryam ta nutsu sannan ta gane an kwashi wasu daga cikin kayan lefen, amma dai ta yi shiru ba ta ce komai ba, don ta fi tunanin a cikin masu kwaso kayan ne wata ta ɗiba.

 Nan fa ta gyara zaman idda, ta manta da ta taɓa rayuwa da Nazifi, kullum Uwani ƙara koyar da itw darussa take yi, ita kuma tana kwashewa tana adana su a kanta, a haka har ta gama iddarta, ta ɗiɗɗinka kayan lefenta, tana shiga tana fita, sai Uwani ta ba ta shawarar ta fara sana'a don zawarci sai da sana'a, da fari Baba ya hana ya ce ba za ta yi ba, to akwai ƙawarta da take siyar da abinci a tashar kusa da layin nasu, Maryam sai ta tsiri cin kwalliya ta je ta zauna kawai a wajen, suna kwashewa da maza, Baba ya yi faɗan har ya watsar, ƙarshe abokinsa ne ya ba shi shawarar gara ma ya barta ta fara sana'ar don a san zaman tashar nata mai dalili ne, don haka ya barta, ta fara dafa shinkafa da taliya tana kaiwa tashar, uwar kwalliyar da take ci da tsaftarta, uwa-uba kuma yadda take ƙawata abincin, da yadda take sakin baki su yi ta fira da maza shi yake ƙara janyo mata hankulan maza, da ta fito za ta siyar ta koma gida, ta ƙirga ribarta cass ta adana, nan da nan kuwa zawarawa suka fara tururuwar zuwa wajenta, amma sai Uwani ta nuna mata kar ta sake ta ce za ta yi aure yanzu, ta bari sai ta tara wani abu tukunna, don haka duk wanda ya zo da zancen aure sai ta saita masa hanya, wanda kuma dama su ƴan a bi yarima a sha kiɗa ne, ƴan rage dare sai ta yi ta cin kuɗinsu, amma hakan ba ya saka ta bawa wani jikinta, sai dai ta yi ta maka wayo, har ka gaji ka kama gabanka.

 Ta kusa shekara a gida, ta haɗu da wani Hamza, lokaci ɗaya ta ji tana ƙaunar shi, kuma za ta iya auren shi, don haka duk yadda Uwani ta so nuna mata ba yanzu ba, ba ta yarda ba, ƙarshe dai ta rabu da ita, suka sasanta tsakaninsu, babu jimawa Hamza ya turo manyansa, bayan gabatar da bincike an ga ba shi da matsala aka saka ranar aurensu wata biyar, suka ci gaba da soyayyarsu suna kuma shirin aure.