HASASHEN SOYAYYA

Hs 22

by @legendspen

_Page 22_


"Ka na ji Abdul." Barrister ya faɗa. "Ina jinka." 


"Mu zaunar da su nan ɗakin ka na zaure kawai, su wayanan ɗin zan yi magana da Karima ta san yadda zata riƙe su da surutu ko abinci ne ta da fa musu, kar dai ta bari su fito kuma kar ayi hayaniya." 


"Hakan ya yi bari na buɗe musu." Abdul ya faɗa yana nufar ɗakin, shi kuma ya yi cikin gidan. Yaya Karima ya kira ya sanar da ita cewa ta san yadda zata kula da su, kafin su gama da yan uwan su Senate.


"Shikenan yanzu zaku tafi ne ko kuwa zaku jira a gama abincin ne kawu?." Yaya Karima ta faɗa bayan mijinta ya matsa. "Ita kuma maganar da mu ka zo da ita fa?." Goggo Larai ta faɗa. "Yanzu Abdul ya hau dokin zuciya ya fice, mijin ya bi shi kuma kun san ba zai ta ɓa fahimtar ku a haka ba." 


"Shikenan dafa mana abincin mu ci mu tafi, gaba ma dawo." Ita dai Umma da mamaki take kallon abinda Karima ke yi. "Umma me kike da shi?."


"Shiga Kitchen ɗin ki duba." Shigewa ta yi ɗaki ta sami Bhatool zaune. "Wai Yaya girkin me zaki yi mu su?." Bhatool ta tambayi Yaya Karima. "Ke dalla malama yan uwan Senate ne su ka zo, kin san idan aka bar su hauka zasuyi musu." 


"Hakane kuma wallahi." Ta shi Yaya Karima ta yi ta fice zuwa kitchen ta shiga haɗa musu abincin.


A ɓangaren su Abdul kam bayan ya buɗe ɗakin ya yi musu iso su ka shigo, yan mintuna kaɗan Barrister ma ya shigo, bayan gaisuwa ne Alhaji khamisu ƙanin Dad ya fara magana. "Da farko dai mun zo nemawa ɗan mu Usman Yunusa aure ne na ƙanwarka Bhatool, sai dai zuwan namu ya kasance ba tare da sanarwa ba, hakan yasa bamu buƙaci ganin wasu cikin dangin mahafinku ba tun da mun sami labarin shi mahaifin naku Allah ya yi masa rasuwa, mun yu bincike sosai kafin zuwan mu nan." Murmushu Abdul ya yi tare da yin godiya ga Allah sanan ya ce. "Gaskiyya na yi farin ciki kuma na ji matuƙar daɗi da hakan, sai dai a yanzu ma muna cikin wata matsala da dangin mahaifin namu, rabun mu da su tun lokacin da su ka amshi gadon mahaifinmu, sai yau ɗinan su ka zo wai zasu ɗaura mun aure da wata yarinya sanan zasuyi Bhatool ɗin ma aure da wani yaronsu kangararre,  ko zasu samu ya dawo kan hanya." Cike da mamakin wanan rashin hankali na yan-uwan mahaifinsu Bhatool Alhaji Habu Naira ya ce. "Ikon Allah, kuma suna cikin gidan yanzu babu kunya?."


"Wallahi suna ciki yallaɓai." 


"Kira mana su." Justice Audu ya faɗa, miƙewa Abdul ya yi ya shiga ciki yana mamakin dalilin da yasa suka nemi ganinsu, bayan ya ta shi ne Justice ya ce. "Ai tufkar za'ayiwa hanci kawai, rabon a ɗaura auren Senate da Bhatool yau ne ya kawo mu." Dad dai yana zaune bai ce komai ba, kamar ba shi ne mahafin Senete ba. Tun da ya shigo gidan zuciyarsa ke ma sa wani irin bugu, kallon Abdul kawai yake yana ganin kammanin Habiba a tare da shi, Abdul na shiga cikin ya ce da su Iliyasu. "Ku zo kuna da baƙi." 


"Su waye?." Goggo Larai ta tambaya. "Ban sa dake ba, su mazan." 


"Kar da ka ce zaka zageni dai." Banza ya yi da ita shi dai. "Kai su waye su ke kiran mu?." 

"Baƙi ne a waje, harkar samun kuɗi ce kar ku rasa." Daga haka ya fice, har rige-rigen ta shi suke su bi bayanshi. 


Baki sake suke kallon manyan mutanen dake cikin ɗakin,kallo ɗaya zaka yi musu kaga arziƙi a tare da su. "Ku zauna?." Justice ya faɗa, zama su ka yi babu wani musu. "Barkan ku." Ɗan-ladi ya faɗa. "Barka dai, nasan baku gane mu ba ko?."


"Eyh sai kun yi mana bayani."


"Mune masu nemawa ɗan mu auren 'yar wajenku Bhatool." 


"Wanan zancen banza ne, mun riga da mun yi wa Bhatool miji." 


"Muna so a janye wanan mijin akan naira dubu ɗari biyar." Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Ɗan-ladi da su Iliya, can kuma Iliya ya ce. "Ba sadakin ta ba ne wanan?."


"Ba sadaki ba ne, naku ne kawai." 


"To Mun bayar." Hannu Alhaji Habu Naira ya sa cikin aljihu ya fito da dollors ya miƙa musu sanan ya ce. "Muna so za ayi komai yau har da ɗaurin Auren." 


Daga nan aka shigo  hada hadan ɗaurin aure, har da gayyato mutanen unguwa suka shaida ɗaurin auren, Usman Yunusa Ahamd (Senate) da Kuma Fatima Ahmad ishak (Bhatool) 'yan cikin gida na zaune sai ji suka yi ana shafa fatiha, tare da yin Allah yasanya alheri. 


Bayan ɗaura auren Abdul ya ce da su. "Ya kamata ku shigo cikin gidan ko?." 


"A'a ma shigo wata rana." justice ya faɗa, dan ya fuskanci Dad fa ya fara rasa ƙwarin gwiwarsa na haƙura da Habiba. "Shikenan mun gode sosai." Abdul ya faɗa sanan suk rakasa zuwa motococinsu shi da Barrister, Bayan sun tafi ne Abdul ya kalli Barrister sanan ya ce. "Ka ga bayin Allanan ko?." 


"Hakuri za ka yi Abdul, ƙannen mahafinka ne kuma iyayenka ne, sanan rabon ɗaura auren Bhatool da senete yau ne ya kawo wu su gidan." 


"Hakane kam." Abdul ya faɗa suka shige cikin gidan,

 lokacin su Ilaysu sun koma ciki suna cin Abincin abun su, bakuma su ce da kowa ga abinda ya faru ba. "Wai baxaki faɗi abinda ya faru ba ne?."


"Larai bari su shigo dai su yi muku bayanin kawai."  Ɗan-ladi ya bawa larai amsa, tsaki ta ja kawai ta ci gaba da kai lomar abinci bakinta. Bayan su Abdul sun shigo ne Barrister ya ce. "Toh Alhamdulillah, babu abinda zamu ce da Allah sai godiya, a yau dai an ɗaura auren Bhatool." A zabure Bhatool ta fito daga ɗaki ta na faɗin. "Wace Bhatool ɗin?." Goggo Larai ce tasaki guɗa tare da faɗin. "Kai mun ji daɗi Saddiƙu an angwance." 


"Ba fa da Saddiƙu aka ɗaura ba." Ɗan-ladi ya faɗa. "Bamgane ba fa, kar ku raina mun hankali." 


"Mu ba da Saddiƙu muka ɗaura auren Bhatool ba, mun ɗaura shine da dan gidan Alhaji Yunusa."


"Ai wallahi ba isa ba, anyi kaɗan wallahi." Goggo Larai ta miƙe tsaya tana faɗi. "Kinga ki zauna idan zaki zauna, idan ba zaki zauna ba ke kika sani, ni ma fasa cin Abincin ma baki ɗaya." Iliyasu ya faɗa tare da ficewa. "Nima haka." Ɗan-ladi ya faɗa, ai duk sai mazan su ka miƙe suka fice, aka bar Goggo larai da saddiƙu, sai Habi da Fure. "Kutamma dumadu, Goggo kinga avinda akamun?." 


"Yi shiru Saddiƙu, ai babu asararre sai ubanka." Goggo Larai ta faɗa tana ficewa, ba shiri Furee da Habi suka bita, shima Saddiƙun ya fice.


"Wai mene ya faru a wajen, ku yi mun bayani." Umma ta tambaya, zama su ka yi sanan Barrister ya ce. "Umma daman akwai wanda suke soyayya da Bhatool anan unguwarmu."


"Eyh nasan da shi, mun yi maganar da Karima."


"To yanzu fitar da Abdul ya yi sune su ka yi sallama da shi sun zo neman auren, bayan ba su labarin abinda ke faruwa cikim gidan shine ɗaya cikin abokan mahaifn  yaron wanda yake abokim kasuwancin Abdul ya buƙaci kawai a ɗaura auren, gudun wata matsala." 


"To amma ta ya akai suka amince?." Yaya Karima ta yi wanan tambyar. "Da farko sun fara rashim arzƙin na su, shine akayi musu tayin hamsin-hamsin suka amince." Abdul ya faɗa. "Kai Allah ya sawaƙawa mutanen, ni naga sunkasa zama, ashe tsoron kar Larai taga kuɗin ne?."


"Wallahi fa Umma." Yaya Karima ta bawa Umma da ta yi maganar amsa. Ihu suka jiyo daga cikin ɗaki na Bhatool, tare da faɗin. "Wallahi bana so." 


Arewapick din mu ya kusa sauka, idan ya sauka ba zaku ci gaba da ganin littafin a sama ba, ku yi following ɗina yanda zaku dinga ganin notification da zarar na ɗaura



Legendspen ***