CIN AMANA BOOK TWO 2 JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ZUZU

CIN AMANA BOOK TWO 2 JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ZUZU

by @juwairiyyamahboo331


CIN AMANA BOOK TWO 2 JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ZUZU

Dukkkan yabo da godiya sun tabbata ga allah madaukakin sarki mekowa me komai wanda yabani iko da damar rubuta wannan littafi CIN AMANA allah yasa yanda nafara asa'a nagama asa'a tare da temakon ubangiji.

page ....11

KADUNA

Aruk ya yi saurin fita daga office dinsa. Jabir da Mustapha suka bi bayansa ba tare da sun yi wata magana ba.

Duk wanda ya ga yadda Aruk yake tafiya zai fahimci cewa akwai wani abu da yake damunsa

Suna isa gaban office din Daddy, sakatariyarsa ta miƙe tsaye

Barka da shigowa sir

Kai kawai ya gyada mata

Ta buɗe masa ƙofar.

Aruk ya gyara rigarsa sannan ya shiga.

Daddy yana tsaye a bakin tagar office dinsa hannayensa a baya. Idanunsa suna kallon gine-ginen kaduna, amma tunaninsa yana wani wuri dabam.

Shiga yayi da sallama

Saida yadauki mintuna .

Sannan ya juya a hankali ya kalli Aruk.

"Zauna."

Aruk ya zauna.

Daddy ya koma kujerarsa, ya buɗe wani files da ke gabansa.

Ya tura shi zuwa gaban Aruk.

"Karanta."

Aruk ya ɗauki file ɗin.

Yana buɗewa, idanunsa suka sauka kan manyan haruffa da aka rubuta a saman takardar.

TAFIDA GROUP OF COMPANIES CONFIDENTIAL REPORT

Ya fara karantawa a hankali.

Yayin da yake ci gaba da karatu, fuskarsa ta canza.

Ya ɗago kai.

"Daddy... wannan gaskiya ne?"

Daddy ya haɗe hannuwansa.

"An kawo min shi ne da safen yau."

"Wa ye kawo?"

"Wani mai bincike da na ɗauka watanni biyu da suka wuce."

Aruk ya sake kallon file din .

"Daddy..."

Daddy ya katse shi.

"Ka karanta page din ƙarshe."

Aruk ya juya zuwa page din ƙarshe.

Da ya kai ƙarshen bayanin, ya yi shiru.

Na kusan 30 minutes

Sai ya ajiye file ɗin a hankali.

"Taya ma yarda dawannan."

Daddy ya kalle shi.

"Ni ma ban yarda ba."

"Saboda babu wata hujja ."

Daddy ya gyada kai.

"Hakane."

Ya ɗan yi shiru.

"Amma da ba za mu yi watsi ba."

Aruk ya jingina da kujerarsa.

"Ya za ayi?"

Daddy ya miƙa masa wani ƙaramin takarda.

I nagama tafiyar nan tadawo gobe

Aruk ya jinjina kai shikenan daddy.

Daddy ya miƙe daga kujerarsa.

Ya matso kusa da Aruk.

Ya ɗora hannunsa a kafaɗarsa.

"Ka kula da kanka."

Aruk ya yi murmushi.

"Daddy, tafiyar aiki ce kawai."

Daddy ya sauke numfashi.

"Na sani."

Abin da bai faɗa wa Aruk ba shi ne...

A bayanan da aka samu ɗin ya nuna cewa akwai wanda ke ƙoƙarin lalata sunan kamfanin Tafida.

Kuma mai binciken ya yi zargin cewa wannan makircin yana da alaƙa da reshen da za a buɗe a Kano.

Daddy bai so ya tayar wa Aruk hankali ba kafin ya tabbatar da komai.

---

Aruk ya fito daga office din Daddy.

Jabir da Mustapha suka taso daga inda suke zaune.

"Lafiya?" Jabir ya tambaya.

Aruk ya yi murmushi kaɗan.

"Tafiya zuwa Kano ce tadawo gobe."

"Gobe?" Mustapha ya tambaya

"Eh."

Jabir ya ce,

"To ni fa?"

Aruk ya ɗan yi dariya.

"Ka zauna nan ka kula da company."

Jabir ya ce.

"Ah ah gaskiya

Mustapha ya ce,

"Ka bar shi ya je ya yi aiki."

Jabir ya girgiza kai.

Ah ah inaso inje."

Aruk ya yi dariya.

"Kwana biyu ne kawai."

CIN AMANA BOOK TWO 2 JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ZUZU

ALQALAMI ✍️YAFI TAKOBI 🤺


page.....12

KADUNA

Aruk ya koma ofice a hankali. Ya rufe ƙofar, ya zauna a kujerarsa yana kallon file ɗin da Daddy ya ba shi.

Ya sake buɗe shi.

Ya karanta wasu bayanai karo na biyu.

Sai ya rufe idanunsa na ɗan lokaci.

A zuciyarsa ya ce,

"Duk wanda yake son ya lalata sunan company, ba zai yi nasara ba, In sha Allah."

Yana cikin wannan tunanin ne yaji knock na door

"Shigo."

Mustapha ne ya shigo.

Dauke da wani ƙaramin littafin rubutu da computer.

Zama yayi , na gama shirya duk takardun da za ka buƙata."

Ya miƙa masa wani babban file .

"Wannan ya ƙunshi bayanan filin aikin, kwangiloli, sunayen engineers kuma jadawalin tarurruka."

Aruk ya karɓa.

"Sannu da qoqari."

Mustapha ya yi murmushi.

Sai ya ɗan yi shiru.

"Aruk..."

"Na'am."

"Ka yi taka-tsantsan."

Aruk ya ɗago ya kalle shi.

"Me ya sa ka faɗi haka?"

Mustapha ya ɗan yi tunani.

"Ban san dalili ba. Amma tun bayan zuwan Alhaji Bashir da kuma bayanin da aka samo zuciyata ba ta kwanta ba."

Aruk ya yi murmushi.

. Kadena yawan tunani haka.

Mustapha ya ɗora da cewa,

"...kakula sosai pls

Aruk ya miƙe ya matso kusa da shi.

Ya dafa kafaɗarsa.

"Na gode. Zan kula."

Mustapha ya gyada kai.

"Shi kenan."

Ya miƙe ya fita.

---

Bayan fitar Mustapha, sai Jabir ya shigo

"Na san Mustapha ya gama yi maka doguwar nasiha."

Aruk ya yi dariya.

"Ka san shi ai."

Jabir ya zauna yana murmushi.

"Ni kuma na zo da wata magana."

"To ina ji."

"Ka ɗauke ni mu je Kano."

Aruk ya girgiza kai.

"Jabir."

"Na'am."

"Wannan tafiyar aiki ce."

"Ni ma ai zan yi aiki."

"Wane aiki?"

"Duk abin da ka ce."

Aruk ya yi dariya.

"Da gaske nake."

Jabir ya haɗe fuska.

"Wallahi ban taɓa zuwa Kano ba."

"Shi ya sa kake son zuwa?"

"Eh."

Aruk ya ɗan yi tunani.

"To bari in fara tambayar Daddy."

Jabir yasaki murmushi

"Da gaske?"

"Amma ban yi maka alƙawari ba."

"Ko hakan ma ya isa."

Ya miƙe tsaye yana dariya.

"Thank you so much

Da ya kai bakin ƙofa sai ya juyo.

"Amma..."

"Me kuma?"

"Ina qaunarka.

Aruk ya ɗaga biro ya yi kamar zai jefe shi.

Jabir yana dariya yafuta

Aruk ya girgiza kai yana murmushi.

---

Da yamma.

Aruk ya isa gida.

Tun daga farkon get din gidan ya lura akwai motoci da be saba gani ba

Lokacin da me gadi yabude masa katafaren get din gidan nasu

Me gadin gidan yayi saurin qarasowa tare da fadin

Barka da zuwa sir

Gyada kai yayi kawai

Parking space yawuce.yayi parking motar

Yafuto

Ya shiga cikin gidan.

Da ya isa babban falo, ya tarar da Daddy da Ammi suna zaune tare da wasu dattawa

____________KANO__________

– JA'EN

Asubahin gari ne a unguwar Ja'en da ke cikin birnin Kano.

Kafin hasken rana ya mamaye sararin samaniya, an riga an fara jin sautin kiran sallah masu zuwa masallaci na zuwa.

Wani qaramun gidane madaidaici wanda daganinsa kasan masu gidan ba wasu masu hali bane

Wani mutum ne yafuto sanye da kodadden farin yadi amma wankakkene tas harda guda masallacin dake kusa da unguwar yanufa don gabatar da sallar asuba

Malam Mudassir kenan.

Mutum ne mai kamun kai, mai ilimi da tarbiyya. Duk wanda ya san shi a unguwar Ja'en yasanshi mutum ne da bayason hayani shiyasa befiya shiga harkar mutanen unguwar ba seta kama mutane na girmama shi saboda gaskiya da riƙon amana.

A cikin gidan kuwa…

6am .

Wata kyakkyawar matashiyar budurwa ce ta fito daga ɗakinta

Sanye da riga da zani na atamfa tarufe kanta me dauke da kwantaccan gashin da ya rufe mata rabin goshinta

Subhanallahi ahsanul kaliqin nikaina se seda naqara kallonta ashe da kallon tsoro nakeyi mata

Siririya sedai tana da shape me daukar hankali ataqaice dai irin shape dinnan na Coca-Cola

Kyakkyawa ce irin kyawunnan da ya amsa sunansa kyau don duda kasancewarta a gida na masu qaramun qarfi hakan besa jikinta canzawa daga kyau da Allah yayi masaba fara ce irin farinnan me daukar idanu tana da doguwar fuska me dauke da dogon hancin dabya qara qawata fuskarta sannan tana da wani shape na baki da ake kira silly shape se manyan dimples dinta a kawanne bangare na kumatunta se yalwatacciyar bakar gashin girarta me sheqi da daukar ido

Ta gyara mayafinta, ta ɗauki tsintsiyar shara ta nufi tsakar gida.

Daga yanayinta zaka gane tana da nutsuwa, da tarbiyyar da ba kowa ke da ita ba.

Tana gama share tsakar gida, sai ta nufi kitchen

Ta kunna wuta , ta ɗora tukunya domin girkin safe

A daidai lokacin ne mahaifiyarta, Maryamu, ta fito.

Ta yi murmushi ZAHRA

"Kin tashi tun ɗazu kenan,

Zahra ta juyo tana murmushi.

"Eh Mama. Na ga kina gajiya kwanan nan, shi ya sa na ce bari na yi aikin."

Maryamu ta matso kusa da ita.

"Allah Ya albarkace ki, 'yata."

"Amin."

Mama tace bari nima na kama wani abun

Suna hakane sukaji muryar

Malam Mudassir daga cikin ɗaki.

"Maryamu..."

"Na'am."

Sakin aikin tayi taje kiran dayake mata

Bayan tashiga dakin da sallama

Malam Mudassir yadubeta yace.

"Ina Zahra?"

"Tana nan kitchen"

Futowa yayi

Lokacin da yafuto, ta yi saurin ƙarasawa gabansa.

"Ina kwana Baba."

"Lafiya lau,

Ya zauna a wata kujera da ke tsakar gidan.

Ya kalli Zahra.

"Zahra

"Na'am Baba."

"Na san rayuwa ba ta mana sauƙi."

Zahra ta yi shiru tana sauraro.

Ya batun aikin naki

Inanan dai ina qoqari akai

Jiya naje wurin hajiyar tace in bari se yau

Toh shikenan

"Amma ki tuna..."

"Duk wahalar da muke ciki, ko ina zakije kada ki taɓa miƙa hannu zuwa abin da ba naki ba."

Zahra ta gyada kai.

"Insha Allah, Baba."

"Mutunci shi ne babban arzikin da mutum yake da shi."

"In sha Allah, zan ci gaba da riƙe tarbiyyar da kuka koya min."

Malam Mudassir ya yi murmushi cikin jin daɗi.

Toh haka yayi tayimata nasiha bayan sun gama girkin

Zahra tazubawa kowa

kunu ne na dawa shima ba wani me yawa ba

Toh misalin qarfe 4pm mama da Zahra na zaune a tsakar gida suna jiran Baba don tun kunun safe babu abunda suka ci.

"Assalamu alaikum..."

Sukaji sallama

Amsawa Zahra tayi tana mikewa

ta ɗaga kai ta kalli ƙofar.

Ta gane muryar.

Fuskarta ta ƙawata da murmushi.

"Lahhhhhj... Husnah ce?"

CIN AMANA BOOK TWO 2 JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ZUZU

ALQALAMI ✍️ YAFI TAKOBI 🤺


page......13

Zahra ta ƙarasa bakin ƙofar cikin nutsuwa.

Ta ɗan buɗe ƙofar.

wata mata ce me kimanin shekaru arba'in da biyar, sanye da baqar lafaya hannunta riƙe da ƙaramin jaka.

Fuskar matar ze tabbatar da gajiyar datayi.

Gaisheta Zahra tayi

Matar ta amsa

"Bismillah, shiga."

Matar ta girgiza kai.

"A'a 'yata, ba zan shiga ba. Malam Mudassir nake nema."

"Amma bayanan"

Kafun taqarasa fada Sega Malam Mudassir yadawo

Zahra takarbi ledar hannunsa

Sannu da zuwa Baba.

Ya amsa da yawwa

Tashiga cikin gidan

Matar tace yawwa dama kai nake nema yanzu take cewa bakanan ashe kana hanya

Baba yace eh amma bangane kiba

Matar tayi murmushi dama nasan baka sanni ba

Dama wata magana ce takawoni

Akan Zahra.

Baba yakalleta .

Toh Allah yasa ba lefi tayiba.

Ah ah batayi komaiba, Toh musical daga ciki .

Shiga sukayi.

Mama dake zaune a saman tabarma

Takalli matar tare da cewa

"Sannu da zuwa."

"Yauwa."

Suka zauna matar ta nisa tare da cewa

"Sunana Hajiya Rabi."

Ina zaune a tarauni

Ta ɗan yi shiru kafin ta ce,

"Na zo ne saboda wata magana."

Malam Mudassir ya ce,

"Ki shigo mu zauna."

Suka shiga falon gidan.

Falonsa ƙarami ne, amma mai tsafta sosai. An shimfiɗa tabarma mai kyau, a gefe kuma akwai ƙaramin ɗakin karatu da Malam Mudassir yake ajiye littattafansa.

Zahra ta kawo musu ruwan sha.

Ta ajiye sannan ta koma kitchen don Dora abincin da baba ya kawo

Maryamu ta ce,

"Hajiya Rabi, muna sauraronki."

Ta gyara zamanta.

"Munyi magana da hajiya binta akan neman aiki da Zahra takeyi

Tacemun ita bata da gurin dazata kai Zahra amma in temaka in dauketa.

Nace toh toh yauma nazo barka nan unguwar shine nace bari na qaraso

"Shi ya sa na zo."

Malam Mudassir ya ce,

"To, muna ji."

Hajiya Rabi ta ce,

"Ina da wata ƙanwar mijina. Tana da makarantar ɗinki da koyon sana'o'i."

"Tana neman yarinya mai gaskiya da riƙon amana da za ta taimaka mata a makarantar. Shiyasa nayanke shawararar tuntubarku naji ko zatayi

Malam Mudassir ya yi shiru.

Maryamu ta kalli mijinta.

Hajiya Rabi ta ƙara da cewa,

"Ba aikin wahala ba ne. Kuma za a riƙa biyanta albashi duk wata."

Shiru ya sake ratsa falon.

Ba don ba sa son Zahra ta yi aiki ba.

Sai don Malam Mudassir ya kasance mai matuƙar kula da tarbiyyar 'yarsa.

Ya ɗan gyara zamansa sannan ya ce,

"Za mu yi shawara da ita. Idan ta amince, za mu sanar da ke."

Hajiya Rabi ta yi murmushi.

"Shi kenan."

---

Bayan tafiyar Hajiya Rabi Zahra tana zaune tana gyara itacen da take dafa abinci

Mama ce tashigo takalli Zahra tace. "Zahra."

"Na'am Mama."

"Kizo.

Zahra ta ɗago kai.

"To?"

CIN AMANA BOOK TWO 2 JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ZUZU

ALQALAMI ✍️ YAFI TAKOBI 🤺


page. .....14

Ajiye maficin da take fifita wutar tayi tanufifalon.

Malam Mudassir kam yana zaune inda yake. ya jingina da matashin kai da ke gefensa, ya yi ɗan shiru kamar wanda yake nazarin wani abu mai muhimmanci.

Maryamu ta kawo masa ta ajiye a gabansa.

Ta zauna kusa da shi.

"Me kake tunani ne?"

Malam Mudassir ya sauke numfashi.

"Maganar aikin Zahra."

Maryamu ta gyada kai.

"Ni ma shi nake tunani."

"Rayuwa ta yi tsada, Maryamu."

"Hakane."

"Amma duk da haka, ba zan taɓa bari 'yata ta shiga wurin da zai lalata mata tarbiyya ba."

Maryamu ta yi murmushi.

"Ka san Zahra. Tun tana ƙarama ba ta taɓa ba mu abin da zai sa mu ɗaga gira ba."

Malam Mudassir ya ce,

"Na sani. Amma iyaye dole su kula."

A daidai lokacin ne Zahra ta shigo falon.

Zama tayi tare da cewa

"Baba."

"Na'am, 'gani

Ya kalle ta cikin nutsuwa.

Wannanmatar datazo tazone saboda tana buqatar wacce zata runga temakon qanwar mijinta a gurin sa'a."

Taduba taga kece wacce tadace da wannan aikin.

Shiyasa nakiraki naji

"mene ne ra'ayinki?"

Zahra ta sunkuyar da kai.

"Baba..."

"Na'am."

"Ni duk abin da kuka ga ya dace da ni, shi zan yi."

Malam Mudassir ya yi murmushi.

"Ba haka nake nufi ba."

Ta ɗago ta kalle shi.

"Ina so in ji abin da ke ranki."

Zahra ta yi ɗan shiru.

"Gaskiya Baba, ina son in koyi sana'a. Domin ko da mutum babu sana a abun bazeyuba , ya kamata ya kasance yana da abin da zai dogara da shi."

Maryamu ta yi murmushi tana kallon mijinta.

---

Da yamma...

Baba yakira hajiya rabi yake fadamata sun amince da maganar aikin Zahra.

Zahra da mama suna kitchen mama na tuna Tywardreath Zahra na goga kubewa.mama ta nisa tace.

"Zahra."

"Na'am Mama."

"Gobe za ki fara zuwa wurin aikin nan idan Allah Ya yarda."

"In sha Allah."

"Amma ki tuna da abin da Baba ya gaya miki."

Insha Allah mama zan kiyaye.

---

Washegari...

Tun kafun akira kiran sallar asuba tafarka Zahra ta farka.

Ta yi alwala, ta idar da sallah, sannan ta zauna tana karatun Alƙur'ani cikin nutsuwa. Muryarta mai laushi ta cika ɗakin da wani irin kwanciyar hankali.

Da ta gama, ta ɗaga hannayenta sama.

"Ya Allah, Ka sa ranar nan ta kasance mai alheri. Ka ba ni ikon riƙe mutuncina da tarbiyyar da iyayena suka koya min."

Ta shafe fuskarta da tafin hannunta.

Toh misalin qarfe 7 mama tagama shirya breakfast

Malam Mudassir ya fito cikin farar jallabiya mai tsabta.

Ya zauna sannan ya kalli fatima dake zaune tashirya cikin wata blue black din doguwar riga da mayafi baqaramun kyau kayan sukayimata ba .

Ya sauke numfashi tare da fadin

"Kin shirya?"

"Eh Baba."

Mama takawo mata farar taliyar data dafa da kunu

"Ki fara cin abinci."

"Mama, zan makara."

Ta girgiza kai.

"A'a. Ba na son ki fita ba tare da kin ci komai ba."

Zahra ta yi murmushi.

"To."

Ta zauna suka ci tare cikin natsuwa.

Bayan sun gama, Malam Mudassir ya zaro kuɗi daga aljihunsa.

"Ga wannan."

Ta karɓi kuɗin cikin ladabi.

"Nagode Baba."

"Kada ki manta da addu'ar fita."

"In sha Allah."

Ta durƙusa ta gaishe su.

Maryamu tace

"Allah Ya dawo da ke lafiya."

"Amin."

Zahra ta fito daga gida.

Ta lumshe ido safiyar yau baqaramun dadi tayi mata ba.

Ta kalli mutane kowa da abunda yakeyi

Masu buɗe shaguna suna ta gyara kayansu.

Masu kosai da masu kunu sun fara duk sun futo.

Masu adaidaita sahu suna ta kai-komo.

Tafiya tafarayi har ta isa bakin titi.

Ta samu adaidaita.

Sannan tace

"Barka da safiya."

Direban ya amsa.

"Ina za mu?"

"Unguwar Sabon Gari."

"Shiga."

Motar ta fara tafiya.

Zahra tana ta kalle kalle

Bayan kusan mintuna talatin...

Adaidaitan ya tsaya a gaban wani katafaren gini mai rubutu da manyan baƙaƙe:

BAHIJJA SKILLS AND FASHION CENTER

Zahra ta sauka.

Tamiqa masa kudin

Ta gyara mayafinta sannan ta shiga harabar gurin

A ciki ta tarar da wasu 'yan mata suna ta koyon ɗinki, wasu kuma suna koyon makeup

Hajiya Rabi na tsaye tana ba da umarni.

Da ta hango Zahra, sai ta yi murmushi.

"Maraba da zuwa."

"Nagode Hajiya."

"Kin zo da wuri."

"Eh."

"Toh sannuda zuwa"

Yawwa ta amsa dashi

Ta nuna mata wani ƙaramin office.

"Zo, bari na nuna miki wurin da za ki riƙa zama."

Suka shiga office din

Hajiya Rabi ta fara bayyana mata yadda aikin yake gudana, da yadda ake kula da ɗalibai,

CIN AMANA BOOK TWO 2 JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ZUZU

ALQALAMI ✍️ YAFI TAKOBI 🤺


page ....15

BAHIJJA SKILLS AND FASHION CENTER

Zahra ta bi bayan Hajiya Rabi zuwa cikin babban ɗakin koyon ɗinki.

Ɗakin ya kasance mai faɗi, an jera kekunan ɗinki cikin tsari. Da yammata da waya aciki Wasu 'yan matan suna koyon yadda ake yanka , wasu kuma suna ɗinki ƙarƙashin kulawar malamansu.

Da suka shiga, Hajiya Rabi ta ce,

"Ku dakata kaɗan."

Kowa ya yi shiru.

Ta nuna Zahra.

"Wannan ita ce Fatima Zahra. Daga yau za ta fara aiki tare da mu. Ina fatan za ku ba ta haɗin kai kamar yadda kuke ba juna."

Dukkaninsu suka amsa da murya ɗaya.

"In sha Allah."

Zahra ta yi murmushi

Sannunku

Daga cikin 'yan matan, wata mai fara'a ta taso.

Ta ce,

"Sannunki da zuwa. Sunana Amina."

Zahra ta yi murmushi tare da cewa

"Ni kuma Fatima Zahra."

Amina ta yi dariya.

"Ta ruqo hannunta suka zauna

Zahra ta yi murmushi.

Nagode. ---

Hajiya Rabi ta nuna wa Zahra ƙaramin tebur.

"Daga yau wannan shi ne wurinki."

"Nagode Hajiya."

"Da amina ta hada ta don tafara koya mata

---

A wannan lokaci kuwa...

Jirgin da Muhammad Aruk Tafida yake ciki ya fara sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano International Airport.

Aruk ya ɗauki jakarsa.

Sanye yake cikin wata baqar shadda ta alfarma wadda akayiwa ado da zaren azurfa wacce ta kwanta luf a farar fatar jikinsa taqara masa kyau da kwarjini hannunsa daure da agogo omega fuskarsa kuma ta qawatu da wani hadadden prada glass kafarsa kam sanye take cikin wani hadadden prada loapers yayi kyau sosai.

Jabir ya bi bayansa yana murmushi.

Yaudai gani a kano

Aruk ya yi dariya.

"Amma ka tuna abin da na gaya maka."

Jabir ya ce,

"Na sani. Aiki muka zo yi."

Mustapha bai zo tare da su ba. Ya rage a kaduna domin kula da wasu manyan ayyukan company.

Wasu manyan motocine qarar bugatti se wata guda daya qirar Land Cruiser sunzo daukarsu

Dasauri mutanen dake ciki suka futo cikin girmamawa suka amshi kayan hannunsa tare da fadin

"Sannu da zuwa sir."

"Yauwa."

Motar suka shiga suka dauki hanyar daze sadasu da katafaren ginin company nasu.

Aruk yana ta kallon garin ta cikin glass din mota.

Bayan mintuna talatin suka isa sabon ginin reshen Tafida Group.

Ma'aikatan company duka sun futo suna jiran isowarsu .

Bayan motocin sun qaraso direct parking space suka nufa drives din suka futo suka bude musu motar ahankali yafuto daga motar .

Nan mutane suka qaraso suna yimasa sannu da zuwa.

Shiga cikin babban office din company sukayi

Aruk yasa aka kira masa manager

Babu jimawa yaqaro .

Bayan sun gaisa yace sir sunana. Musa Idris, ya miƙa masa wasu manyan files

"Waɗannan su ne bayanan aikin."

Aruk ya fara dubawa.

Bayan ɗan lokaci ya ɗaga kai.

"Akwai wasu bayanai da ba su yi daidai ba."

Duk ɗakin ya yi tsit.

Musa Idris ya ce,

"Mun lura da hakan, amma ba mu gano inda matsalar take ba."

Aruk ya rufe file ɗin.

"Za mu bincika komai daga farko."

---

A wannan lokaci kuwa...

A bahijja Skills and Fashion Center, Zahra ta fara aikinta.

Tana koyon dinki sosai don yanzu har ta iya yanka .

---

Se wurin 5pm su

Aruk da Jabir suka isa katafaren gidansa dake GRA.

Babban gidane me bene wanda yaqawatu da flowers masu daukar hankali .

Tsayawa fadamuku tsaruwar gidan ma bata lokacine domun ya hadu iya haduwa

Koda suka shiga dakinsa yawuce jabir kam a saman manyan sofers din dake makeken falon ya kwanta wai yagaji.

Aruk ya kallesa bafa music wani aiki ba

"To idan wannan ba aiki ba ne, me za ka kira aiki?" .

Wanka yasiga be jimaba yafuto daure da kimono rob zama yayi a bakin mirror lotion kawai yashafa xloset yashiga bawasu kaya yasakaba boxes yasaka da farar riga tsakiyar gadon yahau tare da janyo computer ya fara duba takardun da Musa Idris ya ba shi.

Yana nazarin bayanan ne sai ya lura da wani abu.

Ya qara zooming screen din computer. Wayarsa yadauko jabir yakira

Babu jimawa yashigo dakin aruk yace

"Jabir."

"Na'am?"

"Zo ka ga wannan."

Jabir ya taso ya matso.

"Me ya faru?"

Aruk ya nuna masa wasu numbers kuɗi.

"Duba nan."

Jabir ya yi shiru yana karantawa.

Bayan wasu mintuna ya ce,

"An canda adadin kuɗi."

Aruk ya gyada kai.

"Ba sau ɗaya ba."

"To wa ya yi?"

"Shi ne abin da zan gano."

Ya rufe computer a hankali. Tare da fadin

"Duk wanda yake wannan aikin, ya san abin da yake yi."

---KANO

_____________MEDILE____________

zaune yake akan manyan kujerun dake falaon.

gabansa cike yake da kwalaben drinks da manyan files

Sunansa Alhaji Kabiru Dantala.

Mutum ne mai kuɗi, amma zuciyarsa cike take da son zuciya i da kwaɗayi.

Wayarsa ta yi ƙara.

Ya ɗaga.

"Na'am."

Daga can aka ce,

"Alhaji, mutumin nan ya iso Kano."

Kabiru ya yi murmushi.

"Muhammad Aruk Tafida?"

"Shi ne."

"Yana ina yanzu?"

"Yana gidansa dake GRA"

Kabiru ya jingina da kujera.

"Ku ci gaba da sa ido a kansa."

"To Alhaji."

Ya kashe wayar.

Sai ya kira wani.

Bayan an ɗaga wayar, ya ce,

"An fara wasan."

Muryar wani mutum ta fito.

"Ka tabbata ba za su gano mu ba?"

Kabiru ya yi dariya.

"Ko sun gano, zai zama ya makara."

Ya kashe wayar.

Ya miƙe ya nufi window dake ɗakinsa.

Yana kallon fitilun dake gidansa

A hankali ya ce,

"Muhammad Aruk... wannan karo ba za ka hana ni abin da nake so ba."

---

---

Da daddare...

Aruk ya kasa barci.

Bayanan da Daddy ya ba shi da kuma bayanan da ya gani a company dake kano sun cika masa kai da tunani.

Ya tashi ya buɗe window ɗakinsa.

Iskar dare tana kaɗawa.

A lokaci guda.

Yafi 30mint ahaka kafun yakoma saman godon takwanta kafun wani nannauyan bacci yadaukeshi.

To masu karatu .

Shin waye alhaji kabiru dandala?

Meze faru da aruk nan gaba?

Meyake faruwa da company's din tafida?

Waye ke kwashe kudin?

Duka kubiyoni acikin wannan littafi na CIN AMANA na JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ZUZU

***

Ku tuntube ni a wannan number 👆 Don shiga group dina na WhatsApp ko samun damar karanta littafina a arewapen