MAFARIN QADDARA BOOK ONE 1 JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ZUZU
1 MAFARIN QADDARA BOOK ONE 1 ***JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM *** (ZUZU)
Dukkkan yabo da godiya sun tabbata ga allah madaukakin sarki mekowa me komai wanda yabani iko da damar rubuta wannan littafi MAFARIN QADDARA Allah yasa yanda nafara asa'a nagama asa'a tare da temakon ubangiji
Naware lokaci don miqa godiya ta ga uwata mahaifiyata madubina (hjy zainab Muhammad)dakuma
Bangona majinginata abun adona mahaifina (mahboob ibrahim)
Jinjina gareku manyan yayuna da qannena allah yashiga lamarinku ameen 🙏
Wannan littafin banyishi Dan wata ko wani ba idon yayi kama da labarin ki/ka ina me bada haquri
MAFARIN QADDARA …….1
_____________JIGAWA_____________ Unguwar SHUWARIN dake a dutse jihar jigawa
Matashiyar budurwace yar kimanin shekara 17 sanye take cikin wata doguwar rigar atamfa da hijabi cike da nutsuwa take tafiya har takawo dede wani qofar gida ahankali ta tura kofar sedai tamayar da kyawawan fararen idanunta ta lumshe sakamakon tashin hayaniyar datakeji na “yan gidansu ahankali takama leben ta taciza don inda sabo tasaba jin irin wannan hakazalika muryar fiddausi tafi ta kowa tashi ko tantama batayi tasan dasu takeyi qarasa shiga gidan tayi fiddausi ce tsaye tana wurga hannuwa da idanu cike da zallar rashin kunya take fadin oho dai idon anyi zuciya adawo dasu tunda ba samarin gantalallu ne suka kawo ba ehe..
Lumshe idanu taqarayi lokacin data hango suhaima tafe da wata kodaddiyar dari biyu 200 tana tunkaro fiddausi da'alama bata kudin zatayi miqa mata kudin suhaima tayi fiddausi ta fuzga tana fadin dangin mayu ai nayi tunanin bazaku kawo daga ku har waccan tsohuwar… sedai kafun taqarasa taji saukar kyawawan maruka asaman fuskarta tamkar saukan aradu haka suka tsinkayi sautin marukan guda biyu qarar da fiddausi tasaki shize tabbatar daba qaramin shigarta marukan sukayiba wanda yayi sanadiyyar futowar baba sarai(mahaifiyar fiddausi)baki asake take kallon SULAIMA kafun taqaraso tana fadin yau ni naga shegiyar yarinya ubanki tayi miki don tayi magana akan kudin saurayinta toh ku kuyi zuciya ku kawo naku samarin mana sekuma tajuya kan fiddausi da fadin kema dai kinji kunya yarinya “yar cikinki zaki bari tadaga hannu tamareki dajin haka fiddausi tayi kukan kura tayo kan sulaima kafa tasa tayi wurgi da ita atsakar gidan cikin nuna alamun ko inkula da halin data sakata cike da zallar jarumta daze tabbatar da bata shakkar kowa take nuna fiddausi da yatsunta duda kasancewar ba iya girman jiki fiddausin tafita ba har shekaru ma tabata cikin alamun gargadi take fadin . Ke fiddausi ki kiyayeni idon kina cin kasa to kikiyayi ta shuri domun wallahi ni ba suhaima bace da inaji kina cin mutumci uwata nakyaleki don haka ki kiyaye fiddausin qara tasowa tayi a harzuqe ta tawo da niyyar marin SULAIMA sedai kafun taqaraso mama da idar da sallarta kenan tafuto tajanye sulaima suhaima ma bun bayansu tayi baba sarai ta lailayo wata ashar tayi tana fadin qaramar marakunya mara farinjini kwantan maza kitsaya mana sulaima tajuyo zatayi magana mama ta doke bakinta turn baki gaba tayi tana hararar suhaima datakeji kaman ta maketa don haushi ita wannan sanyin halin nata nabata haushi sekace babu zuciya ajikinta tayi kwafa har suka shiga daki sunajin ashariyar da baba sarai keyi zaunar da ita tayi itama tazauna mama tabita da ido tana fadin sulaima so nawa zan fada
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU)
REAL PERPECT WRITER'S ✍️
ALQALAMI✍️ YAFI TAKOBI 🤺
MAFARIN QADDARA ….2
miki kidena shiga harkar “yan gidannan ko me zakiji sun fada Kirabu dasu akwai lokaci tura baki tayi gaba tana fadin umma kijifa abunda suke cemiki to mene damuwarki idon sun fada ze futomun ne.
To washe gari takama juma'a “yammatan gidan kowa yayi kwalliya sulaima nazaune tana yanke farce suhaima kuma tana tsince shinkafa tsaki sulaima tasaki sakamakon jin muryar hajja agidan suhaima tayi murmushi wanda yayi sanadiyyar futowar fararen haqwaranta don tasan sulaima da hajja basa shiri ko daya ko yaushe zamu dena ganin wannan wariyar oho bugo qofar wajansu da'akayi ne yasata dawowa hayyacinta ko bata dagoba tasan hajja ce sulaima ko dako dagowa batayi ba ballantana tanuna tasan da zuwan hajjan tamike da niyyar shiga daki ta tsunkayi muryar hajja na fadin to futsararriya mara kunya wacce basu gaji azzukiba dangin mayu murmushi sulaima tayi tare da juyowa takalli hajja tare da fadin babu wanda yahalicci kansa ko kuma ubangiji yanemi shawararsa gurin tsarin kaddara ko kuma talauci nasaba ko kuma asali kowa tashi yayi yagansa a'inda allah ya ajiyesa ubanki nace futsarariyar yarinya mara kunya ina uwar taki tanaji kina gayamun magana tayi shiru adaki yau naga munafukar mata abba da shigowar sa kenan yaji abunda sulaima ke cewa yasaki murmushi shikanshi yana qara godema allah dayaba maryamu(mama) “ya kamar sulaima gyaran murya yayi wanda yasa hajja tsayawa da maganarta juyowa tayi tana fadin au kana tsaye kana kallona ah ah hajja yanzu nazo harara ta wurga masa tare da fadin to wannan tsintacciyar magen ta turo futsarariyar “yarta ta daki fiddausi fiddausi kuma abba yaqara tambaya eh ita saboda haka ni nazo da shawara tunda basu da mashinshini kuma sunfitini al'umma nayanke shawararar hada aurensu da malam tijani don wannan mara kunyar sedai malami yayi mata rukiyya ko aljanu ne ke damunta ita kuma wannan jafaru dangidan kawata zanbama abba yayi shiru yana kallonta ko bakajine ah ah hajja naji atoh seka shirya zasuzo neman aurensu tana gama fadar haka tafuce daga wajen sulaima da suhaima da sukayi tsaye suna jiran amsar abba jin babu abunda ya iya cewa yasasu kallon juna dama sunsan indai hajja tayi magana to dawuya yatsallake kallon umma yayi dake bakin qofa arakube ya girgiza kai kawai ya futa
Hajja kam dakin su fiddausi tawuce nan take fada ma baba sarai hukuncin data yanke guda ta rangwada tana fadin shiyaa nakeyinki hajja gara arabamu da baqaqen tandu kafun yamma labarin auren su sulaima ya karade gidan TANTAN (gidansu su sulaima)masu habaci nayi masu kunna kida nayi za'a rabasu da bakar qaya .
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU)
REAL PERPECT WRITER'S ✍️
ALQALAMI ✍️YAFI TAKOBI 🤺
MAFARIN QADDARA. ……3
Sulaima kwance take akan yaloluwar kujerar dake falonsu gefenta suhaima ce take faman kuka dagowa tayi tana fadin wai ke kuka zakiyi ko kuma zaki kwaci “yancinki ni yau naga ragwanta allah banda kamarmu se Ince an canzaki a asibiti kizama mace mana aure fa akace ba kasheki za’ayiba yo baki da baki da kafa ne dabazaki qwaci kanki ba ni angaya miki maganar tsohuwarnan tadagamun hankali ne kirabu dasu allah yakaimu lokacin..cikin kuka suhaima takatseta da cewa to yanzu kuma me zakiyi kijifa abba babu abunda yace harara ta watsa mata batare da tace komaiba takoma takwanta
mama tunda hajja tabar wajan tashiga daki tunanin duniya kawai takeyi gabadaya duniyar tayi mata zafi tanajin inama mutuwa zata dauketa wato tana yarinya batatsiraba tagirma ma haka tayi aure bata tsiraba ta haifi “yaya ma bata tsiraba wannan wacce irin jarabawa ce tafada hawayen datake maqalewa sukayi nasarar saukowa tuna abubuwan da suka faru shekaru ashirin baya tayi tare da share hawayenta futowa tayi ganin bacci ya dauki su sulaima yasata futowa alwala tadaura kasancewar magariba takusa takoma ta tashesu suma sukayi alwala
Tom kwanci tashi asarar me rai yau akasaka ranar sulaima da malam tijani suhaima da jafaru sulaima bata taba jin sarewa da tsoro irin wannanba bata taba tunanin lamarin zezo ahakaba ya'ilahi allah kafutar da mu sulaima tafada hawaye na zubo mata kallonta suhaima tayi tabbas du abunda zesa sulaima kuka baqaramun abu bane mama ta kallesu tasaki wani kyakykyawan murmushin da yaqara futo da asalin kyawunta na bafulatanar asali “yan biyun mamansu mene na kuka kuma kallonta sukayi atare murmushi taqara sakar musu tana fadin kuyi sallah ku roqi ubangiji ku nemi zabunsa goge hawayen sukayi tare da mikewa alwala suka dauro suka tada sallah Baba sarai kuwa kamar tazuba ruwa aqasa tasha don murna za'a rabasu da qaya har dije tadauko tayi guda tajuya cike da murna da farinciki
MAFARINQADDARA.........3
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU)
REAL PERPECT WRITER'S ✍️✍️✍️
Alqalami✍️ yafi takobi 🤺
____________ ABUJA ______________ ASOKORO
Unguwace mafi tsada a Abuja wanda yawancin “yan siyasa da “yan kasuwa ke zaune acikinta
Sojoji ne majiya qarfi tundaga farkon titin dazai sadaka da wasu manyan gine gine har zuwa katafaren dogon ginin da'aka rubuta GIWA'S HOUSE wasu manyan g_wagones sukayi Horne akatafaren gidan da bishiyu hadi da furanni sukayiwa qawanya budewa megadin gidan yayi yayin da motocin suka shiga ciki dasauri sojojin dake a sauran motocin majiya qarfi wanda kallonsu kawai ze iyasakaka futsari suka fara durowa suna qamewa daya daga cikinsu da ake kira David shiyazo yabude musu motar ahankali yazuro kafafunsa dake sanye da cover sheo din Sojoji yasaka face marks afuskarsa tayanda babu abunda ake iya gani se kyawawan idanunsa masu dauke da eye lashes yanayin tsayuwarsa sanye yake cikin kayan sojoji wanda suka qara futo da zallar jarumta hadi da qasaita tare da quruciyar daze tabbatar da ba wani babba bane shidin sedai ko ayanayin tsayuwarsa ze tabbatar da shidin cikakken namijine me jini ajika tare da zallar jarumta murdaddiyar surar jikinsa ze tabbatar da hutu da jin dadi yazauna masa wayar sace tahau qara yalumshe lumsassun idanunsa tare da ware su akan wayar hannunsa ammi nah shine ke rubuce akan screen din wayar murmushin da ba koda yaushe ake iya gani afuskarsaba yasaki tare da dagawa yakara akunnensa yafara takawa ahankali cike da qasaita daga cikin wayar matar tace my son lumshe idanu yayi tare da budesu batare da yace komaiba takuma cewa kana fushi da niko batare da ya amsataba yace ammi ina abuja murmushi tasaki da har yajiyo sautinsa kafun tace tare Kake da arif gyada kai yayi tamkar tana kallonsa kafun yace eh Tom kahuta zamuyi waya anjima katse wayar yayi batare daya juyaba yace da arif tsayawa zakacigaba dayi ko zaka tawo bejira amsar saba yayi gaba murmushi arif yayi yana mamakin hali irin na AKIM idon yayi wani abun tamkar shine babba kasancewar arif yagirmi aruk din amma bawani sosaiba
Abokan junane tun suna yara har yanzu allah yahada jininsu don idon ba saninsu kayiba zakayi tunanin “yan uwane komai nasu daya sedai shi arif yana da wasa da dariya sabanin aruk da ko haqwaransa ba a gani se ta kama shima sojane kyawawan matashi ga fara'a
Akim kam koda yashiga kayansa yarage yashiga bathroom wanka yayi yafuto daure da bathrobe se karamin towel yana goge kwantacciyar sumar kansa da taji gyara ganin arif zaune yana danna system yasashi girgiza kai bebi ta kansaba yanufi closets dinsa qananun kaya yasaka da p_cap yadaga kyakykyawar fuskarsa data qawatu da kwantaccen sajen daya qara qawata kyakykyawar fuskarsa yadan qifta ido kadan wanda yakasance al adarsa akoda yaushe .daidai futowarsa yaji arif na waya da'alama da ammi yakeyi baki yatabe yadauki p_cap din sa da face marks don bayason asan yana garin abuja futa yayi yanajin arif nayi masa magana amma yayi banza dashi koda yafuta parking space yanufa wata hadaddiyar farar corolla yashiga dasauri sojojin dake tsaye sukazo sedai bebi takansuba yafuce a 360 direct wani hadadden restaurant yanufa takeaway yayi musu yadawo yana cikin driving wayarsa tahau ringing ganin number ce yasa bebi takan taba yacigaba da driving dinsa jin kiran yaki qarewa yasashi dagawa afusace cikin ladabi Jessica tafurata good afternoon sir madam said i should come and continue from where i stopped on my work sir will i start today or i should keep it till tomorrow. Yanumfasa ahankali bayasan surutu dayawa ahankali yafurta if you have a time today you can come. Yana fada yakatse wayar yana sauke numfashi koda ya qarasa gida yatarar da arif zaune still da system ahannunsa sojan dake tsaye tamakar gunki afalon yace sir will i help you kallonsa yayi yana girgiza kai kitchen yanufa yaduko plates guda biyu zubawa yayi yafaraci ahankali cike da yanga wanda idon basaninsa kayiba zakayi tuanin yana sane
__washe gari bacci sukayi sosai saboda gajiya se wurin 12pm suka tashi shima ringing wayarsane yatadashi sunan ammi dayagani yasashi dagawa magana tayi masa shiru yayi tamkar bayason magana kayi shiru son yanumfasa ammi meyasa kike roqana just do what's best for us murmushi tayi tare da fadin allah yayi muku albarka ameen yafurta yana katse
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU)
PERPECT WRITER'S ✍️✍️
Alqalami✍️ yafi takobi 🤺
MAFARIN QADDARA …..4
wayar arif yashigo kallonsa yayi yana fadin yanzu ammi takirani akan.. kafun yaqarasa magana yakatsesa da fadin nima yanzu takirani kuma munyi magana da ita arif ya gyada kai beyi tunanin akim ze yarda dawuri hakaba murmushi yayi yana fadin yabatun shirye shiryen murmushin shima yayi yana dauke kai batare dayabashi amsaba __misalin qarfe 4pm akim ne zaune kan wasu building chairs dake akatafaren lambun gidan yajingina da bangon kujerun idanunsa alumshe yayin da sanyayyiyar iskar dake kadawa alambun ke ratsa ɓarko da sassan jikinsa kyawawan tsuntsayen dake lambun na faman safari da marwa tunani yakeyi ahankali yabude idanunsa sakamakon dafasa dayaji anyi arif ne harara yawatsa masa murmushi yayi yana fadin bazamu zaga gariba mtss yaja tsaki tare da fadin you're not just my headache you are also my problem wai meyasa kakeson takura mun dariya ya kyalkyale da ita tare da fadin haba (mie love)yakuma kyalkyalewa da dariya harararsa yakumayi yana mikewa zaune tare da fadin naga alamar kai ka qosa Tom bara nakira nafada mata yafada yana daukar wayarsa kwace wayar yayi yana cigaba da dariyarsa Bebi takansaba yamiqe yanufi hanyar futa arif dinma rufa masa baya yayi .
______________JIGAWA_____________
Tafe suke suna fira suhaima cike da tsokana take fadin ummm Mrs malam tijani hhhhh tahau dariya kallonta sulaima tayi tare da fadin hmm su sukaga zasu iya wai bakiga inayawan qure umma da abbah da idoba suhaima ta gyada kai hmm to kallonsu nakeyi inajin dadi kafun kwanakin da tsara su cika don wallahi banga dalilin dazesa ina da quruciyata na auri tsoho ba kuma na rantse senayi maganin wannan tsohuwar tafada tana kwafa kallonta suhaima tayi tana fadin ban fahimci mekikeson fadaba suhaima kenan to guduwa zanyi zaro manyan idanunta tayi tana fadin kaiiii gaskiya karki fara harararta sulaima tayi tare da fadin dama ke da shegen tsoro to seki zauna ayimiki auren dole .
Ruko hannunta suhaima tayi cikin taushin murya tafara fadin,sulaima kinsan cewa mukadai ne muka ragewa mama mutake gani tayi farinciki meyasa zakiga bataso kina shiga lamarin “yan gidanmu saboda bataso wani abu yasamemu mune rayuwarta kamar yanda muma itace rayuwarmu ko ina zamuje dole umma tana ranmu muma muna ranta yanzu idon muka gudu umma tazo takamu da wata cutar allah baze kyalemuba kuma muma bazamu yafema kanmuba pls sulaima karki tafi I beg you 🙏. Dariya sulaima tayi tana fadin yau ni naji wa'azi hhhhh to waye yafada miki zan iya barinku to nagudu naje ina wasafa nakeyi ni wallahi tun abun nadamuna har yazo yadena damuna
JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM (ZUZU)
REAL PERPECT WRITER'S ✍️
ALQALAMI ✍️YAFI TAKOBI 🤺
MAFARIN QADDARA ……5
see your face tafada tana dariya yayin da kyawawan dimples dinta suke lotsawa ahaka suka qarasa gida Gaba daya ‘Yammata gidan da matan gidan suna zaune a katon tsakar gidan nasu ko kallonsu basuyiba suka nufi hanyar wajensu muryar murja sukaji tana fadin sufa bakar tulu za'ayi aure za adena zagaye dakunan maza buri yacika se aje ayi me lasisi wani burki sulaima taja tana niyyar yin revers umma ta janyota zuwa ciki rule qofar tayi suko su murja dariya suka saka mama ce ruqe da hannun sulaima tana fadin AISHA dasauri sulaima tadago don rabon da umma takirata da sunanta andade don batata iya tunawaba. mama tacigaba da cewa yakama kirunga sakawa zuciyarki ruwan sanyi ki koyi danne fushi da ɓacin rai saboda gaba rayuwar dazakiyi anan gaba tabanbanta da wannan aure zakiyi. Yanda umma keyimata fada setakejin zuciyarta tayi nauyi jikinta yayi sanyi ba'itaba hatta da suhaima jikinta yayi sanyi mama tacigaba da magana cikin taushin murya da qarfafa gwiwa tace zaku hadu da mutane daban daban masu hali daban daban don haka ku koyi sarrafa fushi da iya zama da mutane kunjini suka amsa da eh
Kwanci tashi babu wuya awurin allah yau yarage saura sati daya bikinsu sulaima kuma yau ne za'akawo lefe tunsafe mutane da matan gidan wato matar baba umar(babasarai)matar baba halliru(babar su murja)sedai shiru har wurin isha nan fa mutane akafara tofa albarkacin baki kowa da'abunda yake cewa baba sarai ko cewa takeyi da mutane ai dama sadaka aka bada su lefenma anyafemusu nanfa aka hau shewa umma kam ko ajikinta sulaima da suhaima ma baccinsu sukesha basusan wainar da ake soyawaba
Hausawa nacewa rana bata karya sedai uwar diya taji kunya yau takama juma'a kuma yaune aka daura auren su sulaima da suhaima .
Tundaga masallacin da'aka daura auren jafar ke faman gudu har tuntube yakeci tamkar ze fadi tacikin mata yarunga bi har zuwa wajensu baba sarai data ware mp suna tiqar rawa saboda farinciki ji takeyi kamar tazuba ruwa aqasa tasha ganin jafaru da gudu yasata tsayawa tana fadin kaiko lafiyarka cikin haki yake fadin umma wallahi bada malam tijani aka daura ba da wani me kudine ke kinga motoci sunfi 10 wallahi baba sarai ta galla masa harara tana fadin maqaryaci ya….bata qarasaba sakamakon shigowar fiddausi itama tamkar zata fadi tace umma zo tama kasa magana se janyo ta takeyi futowa sukayi akwatina ne kala kala akefaman shiga dasu ɓangaren mama baba sarai da gumi yagama jiqata tafara fadin kodai makuwa sukayi bunsu tayi da niyyar ganin kwakwaf sedai abunda yasa baba sarai suman tsaye bakowa bace face mama sanye take cikin wani danqareren less na alfarma hannunta sanye da zoben goal se sheqi yakeyi wuyanta ma daure da sarkar goal tana murmushi tana kallon mutanen da suka kawo kayan
TOFAH JAMA'A WANNAN SHI'AKE KIRA DA RUDANI
TO SHIN DASUWA AKA DAURA AUREN SU SULAIMA DA SUHAIMA
WACECE MAMA
DUKA KUBIYONI ACIKIN WANNAN LITTAFIN (MAFARINQADDARA)
TAKU AKULLUM JUWAIRIYYA MAHBOOB IBRAHIM ( ZUZU)