Chapter 22
Madaidaicin gida ne irin na talakawan nan. Sai dai ba irin waɗanda talauci ya yi musu katutu ba ne, amma kallo ɗaya za ka yi wa gidan kasan cewar masu shi ba su da wani ƙarfi. Babban mutum mai kimanin shekaru hamsin, zaune yake a tsakar gidan saman tabarma, ya tsurawa wayar hannunsa ido, sai da ya gama kallon abin da ke cikin wayar sannan ya sauke ajiyar zuciya. Matarsa Rabi dake zaune a bakin murhu tana hura wuta ta ɗago da kanta ta kalle shi, ta ce "Malam wai me kake kallo a cikin wayar nan ne da ba ka son in gani? Kullum sai dai in ga ka tsura mata ido kana kallo, da zarar na matso sai ka rufe, ina lura da kai a duk lokacin da kake kallon wayar nan sai naga yanayinka ya canza, ƙarara nake ganin damuwa a fuskarka, wanda ko lokacin da ƴarmu ta ɓata banga kana shiga damuwa kamar haka ba."
Kallonta ya yi da idanunsa da suka canza launi ya ce "Ba za ki gane ba Rabi'atu, abin da ke cikin wayar nan ba za ki iya jurar ganinsa ba, ni kaina ba ƙaramar dauriya nake yi ba idan ina kallonsa. Ji nake kamar in zunduma ihu saboda firgici da tashin hankalin da yake cikinsa."
Rabi ta ce "Wai menene wannan abin? Don Allah ka nuna mini mana"
Girgiza kai ya yi, ya ce "Ba zan nuna miki shi ba, domin muddin kika gan shi za ki shiga cikin damuwar da tafi wadda kika shiga a lokacin da muka rasa ƴarmu." Kallonsa ta yi da kyau ta ce "To kai me ye amfanin barinsa a wayarka? Bayan kuma ba abu ne mai kyawun kallo ba?" Numfashi ya sauke ya ce "Akwai wani abin al'ajabi ne a cikinsa, wanda nake jin ba zan iya goge shi a wayata ba, saboda ina ji a jikina wata rana abin nan zai yi amfani, zai kawo mafita da haske a lokacin da duhu ya mamaye ko ina."
Rabi ta ce "Ikon Allah, ni dai Malam da za ka ɗauki shawarata ka goge abin nan zai fi." "Ba zan goge ba Rabi, ina jira ne Allah ya haɗa ni da wanda nake fatan haɗuwa da shi, domin in bashi wannan videon, saboda ina da tabbacin zai yi masa rana da amfani." Daga haka ya tashi ya kaɓa kai ya fita daga gidan, yana ji tana faɗin "To wai kai a ina ka samu videon?" Amma bai tsaya sauraronta ba ya fice.
.....
Ilham tun jiya da tasha magani Allah ya yi mata sauƙin ciwon kan nan. Bayan ta kammala girki ita da Zahra, ta zubawa Mammy a flakes Zahra ta je mata da shi, sai da ta yi wanka, ta gabatar da sallar azahar sannan ta je gurin Mammy, cike da farin ciki suka zauna suna hira, tana lura da irin kallon da Mammyn ke yi mata, amma sai ta basar. Mammy kuwa sai murmushi take yi tana hamdala a zuciyarta, domin kuwa kallo ɗaya ta yi wa Ilham ɗin taga alamun shigar ciki a jikinta.
Sudais na officer ya ji wayarsa na ruri, ko da ya duba Zuhura ce, share ta ya yi ya ci gaba da aikinsa, ganin da ya yi ta dame shi da kira ne ya sa shi ya ɗaga dole, bayan sun gaisa ne, suka ɗan taɓa hira sama-sama, da za su yi sallama ne Zuhura ta ce masa "Baby jiya mun haɗu da wata yarinya, sosai naga kuma kama da ita, sai da ma na yi tunanin sisternka ce."
Sudais ba tare da ya ɗauki maganarta da muhimmanci ba ya ce "Ok Allah Sarki" daga haka ya kashe wayar. Zuhura tabi wayar da kallo, a hankali ta ce "Da sannu za ka shigo hannuna. Duk abin da za ka yi mini ba zan ji haushi ba, tunda har kake iya ɗaga kirana, soyayyar ma na san zan samu wata rana."
....
Yau Jamila ta zo gidan su Ma'u domin ta sake yi musu ya haƙuri? Nan ta tarar da Ma'u cikin damuwar da tafi ta kullum. Cikin damuwa Jamila ta ce "Ma'u lafiya kike kuwa? Me yake damunki ne? Kinga yadda kika koma kuwa? Gabaɗaya kin rame kin fita hayyacinki, sai wani uban haske da kike yi?"
Kasancewar Inna na can waje ya sa Ma'u ta fashe mata da kuka hadda shasheka, dafe bakinta ta yi da sauri gudun kar Inna ta ji tana kuka, sai da ta samu kukan ya tsaya mata sannan ta ce "Jamila na ba ni, na lalace, Jamila na shiga uku." Ta ƙarasa maganar wani sabon kuka yana ƙwace mata. Cikin tashin hankali Jamila "Subhanallah! Ma'u me ya sa me ki?"
Ma'u ta ce "Jamila ji nake yi ina ma Allah zai ɗauki raina a yanzu, saboda tashin hankalin da nake ciki ya yi mini yawa, astagafirullah ba zan iya jurarsa ba." "Ma'u don Allah ki sanar da ni me yake faruwa ne, gabaɗaya kin ɗaga mini hankali."
"Mutuwar Abida ce ke damuna, Jamila abin nan ya tsaya mini a rai, haka kawai nake jin kamar akwai wani abu da ba daidai ba a tattare da mutuwarta, ga wannan abin da ya faru a gabana shi ma har yanzu na kasa mantawa da shi, ga rasuwar Anty Halima, abubuwa gabaɗaya sun rincaɓe mana, abu sai ka ce addu'ar maƙiyi." Ajiyar zuciya Jamila ta sauke ta ce "Haƙuri za ki yi Ma'u, bawa baya wuce ƙaddararsa, daga Anty Halima har Abida lokacinsu ne ya yi, addu'a ya kamata ki yi musu ba wannan kukan ba, abin da kuma ya faru da ku ƙaddara ce, don Allah ki yi haƙuri ki cire damuwar nan a ranki. Ni wallahi har kin sa hankalina ya tashi, na yi tunanin ko wani abin ne ya kuma faruwa."
Ma'u ta dube ta, ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Ki taya ni da addu'a kawai, domin a yanzu ita nafi buƙata fiye da komai." Tana yin maganar ta tashi da sauri tana faɗin "Ina zuwa, bari in yi fitsari." Daga haka ta bar ɗakin, tana fita taga Inna a ɗakin girki, don haka ba ta lura da yanayin da Ma'un take ciki ba ta shiga banɗaki, tana shiga ta fara yunƙurin amai, sai dai babu abin da yake fitowa daga bakinta saboda ba ta ci komai ba, haka dai ta yi ta yunƙurin da ƙyar ta samu abin ya lafa mata sannan ta kuskure bakinta, tare da wanke fuskarta ta fito. Ɗaki ta koma suka ci gaba da magana, Jamila sai rarrashinta take yi har ta samu ta ɗan sake jiki, suka taɓa hira kafin ta bar gidan.
.....
Bayan sati ɗaya, Ilham ta fara fama da yawan gajiya, da tashin zuciya, ga jiri da yake ɗibarta akai-akai. Uwa uba matsanancin ciwon ciki da take fama da shi, ga rashin cin abinci. Wani lokacin gefe ɗaya na mararta yake ƙullewa. Ba ta sanar da kowa hakin da take ciki ba. Duk da Sudais na ankare da ita, amma ganin ba ta yi masa magana ba ya sa shi yi mata shiru.
Yau ciwon cikin ya tsananta mata sosai. Zahra ce ta shigo taga halin da take ciki, da gudu ta je ta sanar da Mammy saboda lokacin Sudais baya gida. Ko da Mammy ta zo taga halin da take ciki, ba tare da ɓata lokaci ba ta ɗauke ta suka tafi Asibitin da suke ganin likita, suna isa aka karɓe ta da gaggawa saboda tana cikin mawuyacin hali. Sai a lokacin Mammy ta kira Sudais ta sanar da shi, yana tare da Uncle nan suka wuce Asibitin gabaɗaya.
Sudais ne da Uncle zaune a gaban Doctor, sun tsura masa ido suna jiran su ji me zai fito daga bakinsa. Doctor ya gyara zaman gilas ɗinsa ya ce "Bayan kammala duk wasu gwaje-gwajen da ya kamata mu yi mata, abin da sakamakon ya nuna shi ne, hantarta ta ce ta samu mummunar illa".
Da ƙarfi Sudais ya ce "What! Doctor me ka ce? Kamar yaya hantarta ta samu matsala?"
Doctor ya cire gilas ɗinsa ya dube shi da kyau, ya ce "Kamar yadda ka ji na faɗa hantarta ta samu matsala, sakamakon amfani da wani magani mai hatsarin gaske da ta yi, wanda ya kasance gurɓataccen magani ne da ba shi da kyau, kuma yana da matuƙar illa da hatsari a jikin ɗan Adam." Kallon juna suka yi shi da Uncle, Sudais ya ce "Magani kuma? Ilham ɗin? A yaushe ta sha maganin?"
Doctor ya nisa ya ce "A binciken da muka yi maganin bai wani daɗe a jikinta ba, kawai ƙarfin maganin ne da illarsa ya sa yake saurin tasiri a jikin mutum, wanda a yanzu ya yi mata mummunar illar da sai dai mu yi iya ƙoƙarinmu wajen ganin mun ceto rayuwarta, amma bamu da tabbacin za ta iya tsallake tarkonsa." Sosai hankalinsu ya tashi da jin abin da Doctor ya faɗa, musamman ma Sudais, nan ya fara tunanin yaushe ta sha wani magani? Kuma a ina ta same shi. Duk wani taimako da ya kamata a yi mata Asibitin sun yi, Mammy ce ta zauna tare da ita, Zahra kuma ta koma gida domin ta haɗo musu duk wani abu da za su buƙata. Uncle ya wuce gida ya sanar da Momy abin da yake faruwa, sosai hankalinta ya tashi, babu shiri ta shirya ta zo Asibitin, sai dai a lokacin da ta iso Ilham na ɗakin da a ke duba ta ba a fara fitowa da ita ba.
Sudais ne a tsaye yana bin ɗakin Ilham da kallo, tunani yake yi ta ina ma zai fara neman abin da yake son gani a ɗaki. A hankali ya taka ya buɗe wardrobe ɗinta, cikin natsuwa yake bincika kayanta sai dai bai ga komai ba, rufe ta ya yi ya taka gaban madubi ya jawo lokar madubin, cikin Sa'a yaga wata baƙar leda a ciki, ɗakko ta ya yi ya buɗe sai yaga kwalin magani ne kala biyu a ciki, ko da ya buɗa kwalin nan ya tarar da anfi shan rabin maganin ko wane, shiru ya yi yana bin maganin da kallo, ya juma tsaye a gurin sannan ya fita daga cikin ɗakin. Ɗakinsa ya shiga ya ɓoye sauran maganin, ya zauna tare da dafe kansa, yana fata Ilham ta farka yau domin ya tambaye ta ina ta samu maganin da ta sha? Kuma saboda me ta sha shi? Tunani ya fara yi yanzu idan ta rasa rayuwarta da wane idon zai kalli iyayenta? Bayan ya kasa kula da amanar da suka bashi, ya yi sake har rayuwarta ta salwanta saboda rashin kukawarsa. A fili ya ce "Allah ya tashi kafaɗunki Ilham, in sha Allah daga yanzu za ki samu dukkan kulawar da kike buƙata daga gare ni."
Momy ta daɗe a Asibitin sannan aka fito da Ilham daga ɗakin da aka shiga da ita, nan Doctor ya ƙara tabbatar musu da tana ɗauke da juna biyu na tsawon sati uku, sosai suka yi murna tare da fatan Allah ya ba ta lafiya.
Sudais ya dawo Asibitin tare da Faruk, nan Mammy ta sanar masa da abin da Doctor ya ce, wani irin daɗi ne ya mamaye zuciyarsa, ya dinga fatan Allah ya ba ta lafiya ya fito masa da wannan babyn lafiya, Faruk ma ya yi murna sosai. Mammy ta kalli Zahra dake zaune ta ce "Zahra, an ce Ilham magani ta sha mara kyau, narasa wane magani ne ta sha haka? Ko dai maganin nan ne na ciwon kai da aka bata, lokacin da kuka dawo daga gidansu Uncle ɗinku, a hanyaku ta dawo gida, saboda ciwon kai da ya uzzura mata kuka biya Asibiti aka ba ta shi ne bai karɓe ta ba?" Cikin damuwa Zahra ta ce "To Mammy wallahi ban sani ba, amma ba na tunanin shi ne gaskiya, sai dai a jira ta idan ta farka sai a tambaye ta ko ta yi amfani da wani maganin bayan shi?"
Mammy ta ce "To shikenan Allah ya ba ta lafiya" suka amsa da "Amin" sai wajen magriba Momy ta tafi gida, sai dai har ta tafi Ilham ba ta farka ba.
Dukan su suna Asibitin, Hanif ma ya zo ya duba ta, sai wajen sha ɗaya na dare sannan Sudais da Faruk suka yi wa Mammy sallama suka wuce gida, kuma har lokacin ba ta motsa ba. Sai dai kafin su fita daga Asibitin Sudais ya biya ta office ɗin Doctor ya sanar masa da idan ta kai gobe ba ta farfaɗo ba zai fita da ita waje. Doctor baya son yin musu da shi ne ya sa cewa "Babu matsala, in sha Allah za ta farka kafin ku dawo." Sallama ya yi masa, ya fita.
Wajen ƙarfe ukun dare, Ilham ta farka da wani irin ciwon ciki, jikinta har jijjiga yake yi. Da sauri Mammy ta je ta kira wani likita, ko da suka shigo tare Zahra na riƙe da ita tana kuka, Ilham kuwa sai dafe cikinta take yi, jikinta na karkarwa. Da sauri likitan ya ƙaraso gare ta, yana ƙoƙarin saka kayan aikinsa domin ya ba ta taimaka, ta riƙe hannun Zahra da ƙarfi ta ce "Mijina ina yake? Ku kira mini Yaya Sudais, ina son yin magana da sh..." Ba ta ƙarasa ba ta fara salati, tare da yin kalmar shahada. Tana gamawa sai ta yi shiru, jikinta ya saki. Ko da likitan ya duba ta nan ya tabbatar da Allah ya yi mata rasuwa, tun kafin ya sanar da su suka fahimci abin da yake faruwa, kuka ne ya ƙwacewa Zahra, Mammy kuwa babu abin da yake fita daga bakinta sai "Innalillahi wa inna ilaihim raji'un"
Likitan ya jawo zani ya rufe ta, sannan ya raɓa ta gefensu ya fice yana girgiza kai cikin damuwa.
Amanarcool
***