HASASHEN SOYAYYA

Hs 23

by @legendspen

_Page 23_



"Mene bakya so?." Yaya Karima ta tambayeta, bayan ta shigo ɗakin. "Aure, ni ba yanzu ba." 


"Dalla mahaukacya, ba taimakokin su ka yi ba, da wayanan ɗin sun ɗaura miki da Saddiƙun ai kyayi kukan na gaske." 


"Ni dai Allah ba yanzu ba."


"Kyaji da shi." Yaya Karima ta faɗa tana jan tsaki, tare da ficewa. Ta shi Bhatool ta yi zaune, tare da faɗin. "Wai yanzu na zama matar aure, matar Senate?." Wayarta ta ɗauka ta duba lokaci, ganin sha biyu ma rana ga kuma tarin Missed call ɗin su Jannah ya sa ta tuna da ɗaurin Auren Suhaima, da sauri ta ta shi ta fita tsakar gida.


Suna nan zaune ta huce su ta ɗibi ruwa ta yi toilet, a gaggauce ta yi wanka ta fito suna zaune suna kallonta, yan mintuna kaɗan da shigarta ta fito  sanye da riga da skert na lace, ta yafa mayafinta mai ɗan girma ba ta yi wani makeup ba. "Ina zaki kuma?." Yaya Karima ta faɗa. "Ni wallahi duk na sha'afa da daurin auren nan?.


"Ɗaurin auren wa?."


"Suhaima mana." Ta faɗa hankalinta na waje. "Wai Bhatool baki da hankali ne?." Ummah ta faɗa. "Me na yi Umma?." 


"A ɗaura miki aure yanzunan ki ce zaki wwni tafi biki, baki da hankali ne ko bakisan me ya faru ba?." 


"Me ya faru Umma?." Ta faɗa tana dawowa kusa da Umma ta zauna. " Bhatool ke fa yanzu matar aure ce, fita ai ba naki ba ne?." 


"Ko na tambayesa?."


"Wai me yasa baki da hankali, ɗaurin aure fa kawai aka yi ba ayi wani abu ba." Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ita ba ta gane kan wanan al'marin ba, wayarta ce ta fara ringing kira na shigowa. "Hello Suhaima." Ta faɗa tana mikewa tsaye bayan ta ɗaga kiran. "Suhaima ba zan samu zuwa ba wallahi." Ta ƙara faɗa. "An ɗaura mun aure fa yanzun nan." Sai a lokacin Muryar Suhaima ta fito. "Ki bana son iskanci." 


"Wallahi Suhaima daga zuwa tambaya." 


"Ka Alhamdulillah, amma Bhatool naji daɗi sosai wallahi." Daga cikin wyar Amrah ta tambaya. "Ba zata zo ba, me yasa." 


"An ɗaura aurenta ita ma da Senate." Jannah ce ta ƙwace wayar tare da faɗin. "Bhatool da gaske! ?." 


"Walahi dagaske Jannah, daga zuwa tambaya." 


"Kai! Allah Alhamdulillah Bhatool, Allh yasanya alheri yanzu zamu tawo nan." 


"Dan Allah ku zo ina gida, nasan ma bazan koma gidan Yaya Karima ba." 


"Yanzunan in sha Allah." Jannah ta faɗa tare da katse wayar.





~~~~~~~Red bricks.


Tun fitar su Dad, Mom tasanarwa da Senate an tafi nema masa aure, sai faman washe baki yake zai auri Bhatool. Suna nan zaune su Dad suka shigo gidan shi da Justice, bayan sun zauna ne Justice ya ce da. "Ango." Murmushi ya yi tare da yin ƙasa da kai. "Allah yasanya alheri, yasa abokiyar rayuwa ce ta har abada." 


"Amin Uncle." Ya faɗa kansa na ƙasa. "Alhmdulillah, an gama komai kenan?." Mom ta faɗa ta na washe baki, dariya Dad ya yi sanan ya ce. "Ai har sai kin ba ni tukwici." Dariyar ita ma ta yi sanan ta ce. "Na baka." 


"To dai Senate Allah ya yi, ba iya nema masa aure a ka yi ba har da ɗauro auren duk anyi." 


"Bangane ba." Mom ta faɗa. "Daga zuwa neman aure mu ka ɗauro auren baki ɗaya, a taƙaice dai an ɗaura auren ɗan lelenki da Bhatool." Justice ya yi wa Mom wanan bayanin. "Kai Alhamdulillah, Alhamdulilah." Mom ta faɗa tana hawaye. "Wai Dad kana nufin yanzu an ɗaura mana aure da Bhatool?." 


"Eyh tabbas haka ne, yanzu ka zama mijin Bhatool." 


"To Daddy tana ina?."


"Tana gidansu mana, yanzu za a zo a shirya duk wasu abubuwa da ake yi a kai wa iyayenta, sana a tsyar da lokutan shalin biki kamar one month haka."


"One month kuma daddy, ina laifin one week haka?." 


"Kaci gidanku, jimun ja'irin yaro." Dariya suka yi baki ɗaya, sanan Mom ta ce. "Ai kam dai ba za a huce two weeks ba har tarewar amaryar, yanzu kam sai a sanar da ɗaurin auren."


"Ai wanan aikin ki ne." Dad ya faɗa. "Ai kam dai nawa ne, yanzu zan yi shela." Dariya suka yi baki ɗaya, daganan kowa ya ta shi zuwa ɗakin shi. Senate na shiga ɗaki ya fara kiran abokansa ya sanar da su, cikin ƙanƙanin lokaci su ka cika gidan nasu, haka ma ɓangaren Mom ta hau snaar da mutane. Cikin 'yan awanni zancen auren ya fara zaga gari baki ɗaya.



Bayan abokansa sun tafi ne ta dau waya ya kira Bhatool, wacce itama su Jannah da Amrah ba su daɗe da tafiya ba sabida zasu je kai Suhaima, har da kukan Bhatool tasan ita da fita yanzu sai Baba ta gani, ɗaga wayar ta yi ba ta ce komai ba. "Bhatool." Ya kira sunanta a hankali, kuka ta fashe da shi wanda dama yana ranta. "Bhatool mai ya faru?." Kukan ta ci gaba da yi a hankali wanda ke ratsa zuciyarsa. "Me ya faru wai, Bhatool?." Ya tambayeta. "Bakomai, kawai ina yi ne." 


"Bhatool godiya ya kama ta mu yi wa Allah ko?." 


"Hakane." Ta ba shi amsa, gaba ɗaya jikinta ya mutu, sai ka ce ba Bhatool ba. "Ki ta shi ki yi alwala ki yi sallah, nima yanzu zan yi." 


"Tom." Ta faɗa tana mikewa bayan ta kashe wayar, su Umma na zaune tsakar gida, sai dai babu barrister ƙila ya tafi aiki. Huce su ta yi zuwa banɗaki ta ɗaura alwala ta dawo, bayan ta idar da sallah ne ta yi godiya ga Allah, sanan ta roƙa musu zaman lafiya da soyayya mai ɗaurewa. 


Bhatool tana ji tana gani Yaya Karima ta tafi ta barta wajen Ummah, ta sha kuka sosai mussaman da Yaya Karima ta ce mata."Ke Bhatool yanzu ai kinga ma kwana gidana in sha Allahu." Kukan ta ci gaba da yi har Yaya Kariman ta tafi, daddare ma sun sha waya da Senate ɗinta sosai da sosai, har zuwa sanda ta yi bacci. 


Ƙarar kiran wayarta ne ya tashe ta daga baccin da take, hannu ta kai ta ɗaga wayarta tare ba tare da ta kula da lambar da ke kiranta ba. "Hello." Ta faɗa bayan ta ɗaga wayar. "Bhatool." A furgece ta miƙe zaune tana faɗin. "Na'am." 


"Kin yi aure ko?." 


"Eyh na yi." Dan ita ta fara gajiya da lamrin Dr ɗinan, mutum kamar mai aljanu. "Ni kike cewa kin yi?." 


"To me zance maka malam, na yi aure sai ƙaƙa?." Cike da mamaki yake saurarun ta, sai ji ya yi taƙara cewa. "Shirun da nake maka bafa tsoro ba ne, ni Bhatool wallahi ba kanwar lasa ba ce, kainuwa nake dashen Allah, sai gani sai hange." Ta na gama faɗi ta kashe wayarta, dan koma mene yanzu ta riga ta yi aure ta huce duk wani sharrinsa, saukowa ta yi sa gadon ta fito tsakar gida tare da nufar banɗaki.



~~~~Red bricks. 



"Yanzu wayanan laces ɗin duka ta bayar akawo mun?." Mom ta faɗa tana tambayar wata mata dake zaune kan kujera. "Eyh Hajiya, cewa ta yi wai aƙara a cikin lefe." 


"Kai Ma sha Allah, matar minster ta cika 'yar halak wallahi, mgde sosai." Mom ta faɗa tana ƙara duba tsaddadun laces ɗin da suke baje a gabanta, wayanda sun fi kala 30 kuma dukkanin su masu tsada ne, dan babu na ƙasa da dubu ɗari biyu. "To Hajiya zamu tafi, driver na jiranmu." Matar da ta kawo kayan ta faɗa. "Ah, Ina zuwa." Mom ta faɗa tana ta shi ta nufi cikin ɗakinta, a hanya ta ci karo da senate yana shirin sakkowa. "Yawwa Senete je falo kaga kayan da Hajiya Na'ima matar minsta ta aiko da shi, wai asa a lefe." 


"Okay Momi, daman nasan ke ai bazaki rasa irin wanan ba, domin duk lokacin da 'ya'yan ƙawayenki suka ta shi aure haka kike musu." 


"Hakane Senete, amma wayanan fa suna da yawa sosai, ka je ka gani banma san me zan bawa wanan mai aikin na ta ba, da ta kawomun." 


"Bara na gani." Ya faɗa yana sauka ita kuma ta haye samanta, shi kan shi senate ya yi mamakin yawan laceses ɗin da kuma tsadarsu, domin kana ganinsu kasan masu tsada ne. Yana nan zaune mom ta sakko da wata ƙatuwar leda a hannunta cike da kaya, ta miƙawa matar tare da faɗin. "Ga shi wanan naki ne." Karɓa ta yi tana faɗin. "Na gode Hajiya, Allah yaƙara buɗi." 


"Amin-amin." senate ya faɗa yana ciro daloli daga aljihunsa shima ya ba ta, bayan ta fita ne shima ya ce da Mom. "Amma kayan da yawa gsky." 


"Nima haka na ce, gashi jiya sai da na yi order wasu laceses ɗin wajen 50pcs."


"Kai Mom, nima fa na yi nawa order ɗin kar kayan su yi yawa." 


"Senate wane kayane zasuyi yawa, kasan kuwa wa za a aurar, Senete The whole Alhaji Yunusa's Son." Murmushi ya yi a ran shi yana tunanin anya Mom ba ta fi shi Murna da wanan auren ba kuwa?


"Me ake ta tattaunawa ne?." Dad dake sakkowa ya faɗa. "Barka da safiya." Senate ya faɗa yana duƙawa. "Barka Lil Son, an ta shi lafiya?." 


"Alhamdulillah Dad." 


"Ya kwnana Amarya?." Ƙasa ya yi da kai, ya hau sosa ƙeya yana murmushi. "Kaga abinda matar minster ta aiko da shi, wai asa a lefe." Mom ta faɗa tana nunawa Dad. "kai Ma sha Allah, an gode sosai." Ya faɗa yana kallon kayan. "Wai yaushe ne xa a kai musu kayan?." Mom ta tambayi Dad. "Ai wanan kuma naku ne, mu mun yi namu mun gama, sai dai ko shi Angon?." Ta shi Senate ya yi ya fice, dan shi kunyar Dad ɗin ma yake ji. 



Yana fit ya nufu gidan Yaya Karima, sai dai bai ƙara sa ba ya tuna da cewa jiya Bhatool ta ce mai an hanata komawa gidan, ga shi yana son ganinta amma yana jin kunyar Ummah. 


labari fa ya fara ɗaukan zafi, ya kamata ku fara comments, sannan ku yi following dina, domin samun notification da zarar na daura. 



Legendspen ***