BIYU A ƊAYA

Chapter 13

by @barista

BIYU A ƊAYA 
     Don't judge a book by its cover)

Page 13

Sayyada barrister 
***
YOTA 13 
TEAM FIVE INK LEGENDS 


Washegari Bilqees ta tashi jiki ba kwari, ga zazzaɓi da ta ke ji da ciwon kai, da ƙyar ta shirya cikin uniform na aiki, ta fito ta tadda Mamanta zaune tana jiran fitowarta su yi breakfast. 

Ta zauna ta kurawa abincin idanu tana jin ba za ta iya ci ba, amma zata ɗaure ko don kada Mamanta ta fahimci wani abu, a hankali ta ke iya taunawa jollof ta shinkafa ce...

"Bilqees lafiyar ki?"

"Lafiya Mama"

"To kamar ba ki son cin abincin"

"Bana jin yunwa ne"

"Me ki ka ci? Ba abin da ki ka ci tun da ki ka tashi kuma ki ce ba ki jin yunwa"

"Ki dai ci abinci sai ki tafi"

"To Mama"

A daddafe ta ci abinci, ta mik'e ta kammala shirya wa sannan ta yi wa Mamanta sai ta dawo ta fice, yau Alaja bata jira ta ba ta yi tafiyar ta. Mashin ta hau kamar yadda ta ke yi, ya kawo ta Alaja restaurant a lokacin har an fara aikace-aikace, ta shigo side nasu na Server's ta ajiye jakarta ta sannan ta fito ta shigo kitchen gaisuwar jam'u ta yi da yawa sun amsa waɗan da basu amsa ba, ba su da yawa, ta kama aikin da ya zamto nata ne, Majada ta taimaka mata, suka ci gaba da shirya wa bakin breakfast.....


******************************

International hotel

Zaune yake akan dardumar sallah, yatsar sa maƙale da counter yana lazimi, tun da ya yi sallah bai koma bacci ba, ya yi addu'oin sa ya shafa ganin gari ya soma haske ya tashi ya dawo kan bed ya kwanta nan bacci ya ɗauke sa....

Sai 9:00 am ya tashi, ganin kiran Oga yasa ya ɗaga, bayan sun gaisa ne yake sanar dashi za su je cin abincin safe ya shirya. Sannan ya katse wayar, Dr Waahab ya mik'e ya faɗa toilet ya watsa ruwa, ya fito ya shirya cikin manyan kaya, shadda mai ruwan madara ya yi matukar kyau sai ƙamshi yake yi, ya sanya farin glass sannan ya ɗaura agogon hannunsa, yaji ana nocking ya bada izinin shigowa, Dr Faisal ne ya shigo tare da cewa 

"Special doctor barka da safiya"

Murmushi ya yi tare da cewa 

"Barka dai Dr Faisal, an tashi lafiya"

"Lafiya fah sai godiya"

"Ya yi kyau, ya amarya"

"Beb tana nan lafiya mun shirya ne za mu je cin abincin safe yunwa mu ke ji"

"Mun yi waya da OG ya faɗa min, shine ma na tashi na shirya"

"Eh wai cewa ma yayi za a iya kawowa duk wanda ba zai iya tafiya cen ba breakfast nan"

"Ok wannan ma ai dabara ce, ko ni dole ne yasa zan fita"

"Ai ni na fi son mu ci da Beb a cen don ta zaɓi abincin ranta"

"Masoya"

Dariya Dr Faisal yayi ya fice, Dr Waahab ya kammala shirin sa ya fito ya tadda har su Dr Isma'il da sauran ma sun fito harabar hotel ɗin, suna shirin shiga zungureriyar motar su Dr Faisal da matar sa suka iso nan suka shiga, kai tsaye sai Alaja restaurant.

Kasancewar zuwan dare su ka yi jiya yasa basu karewa wajen kallo ba, sai suka ga kusa da hotel ɗin da suka sauƙa ne, sakanin ba nesa, mota na parking suka fito sai kallon wajen suke, nan ALAJA ta fito tana musu maraba da zuwa suna amsawa, ma'aikatan ta maza su ka yi musu jagoranci zuwa dining area, nan kowa ya zauna duk da ba dukkanin su suka taho ba, wasu za a kai mu su breakfast nasu masauki.....

Tawagar Hafsuh shugabar Server's ta fito da team nata suka kama shirya musu duk abinda suka buƙata, Bilqees ta iso inda Dr Faisal yake zaune da matarsa ta ce

"Bonjour Dr Faisal"

Nan fah ya sosa keyarsa, don ba wai bai iya bane tsoron sa kada a ci gaba ya ƙaƙare, ya ja dogon numfashi tare da cewa

"Bonjour yarinyar"

Dr Isma'il ya tuntsure da dariya, Dr Faisal ya harare shi ƙasa ƙasa, Bilqees ta ce

"Uhm do you need something?"

Ta ke tambayar su ko suna buƙatar wani abu, Dr Faisal ya ce

"Perhaps later, comment Ca Va?"

Ya ta ke yake tambayar ta, how are you? Ta sauke numfashi cikin sakin fuska ta ce 

"Ca Va Bien!"

I'm good ta faɗa, tana lafiya, ya danna full stop kada ta ƙure shi ya juya wajen Beb yana tambayar ko tana buƙatar wani abu ta ce a'a bata buƙata, Dr Waahab ya ɗan ɗago ya kalli in da su Dr Faisal suke zaune yaji yana yaren French da ma'aikaciyar RESTAURANT ɗin, ganin yarinyar tabar wajen yasa ya sauke numfashi yana buƙatar shayin gargajiya gashi kuma bai shaida fuskar yarinyar da ta kawo masa jiya da daddare ba, da ya ce ta sake kawo masa....

"Kana buƙatar abu ne?"

Ya ɗan ɗago yaga yarinyar da suke magana da Dr Faisal ce, ya sauke numfashi tare da yin magana a hankali 

"Shayi nake buƙata in akwai ko coffee"

"Shayi irin na jiya?"

Ya yi saurin ɗagowa ya kafe ta da idanun sa masu kaifi da ƙwarjini, da sauri ta ɗauke nata idanun, mamaki ya yi wacce yake neman ta kawo masa shayin gargajiya ashe ita ce...

"Eh"

Ya faɗa ta bar wajen, ya ci gaba da latse latsen wayarsa. Bilqees ta shigo kitchen ta wuce ta ɗaura shayin gargajiya, Majada ta iso tare da cewa 

"Special chef me ki ke girkawa?"

"Shayi ne"

"Oh! Ya yi kyau, Alaja ce ta ke so?"

"A'a ɗaya daga cikin bakin ne"

"Uhm that's right"

Bilqees ba ta sake cewa komai ba, ta ci gaba da dafa shayin gargajiyan, tana kammalawa ta juye kamar yadda ta yi jiya ta fice.

"Majada"

Cewar Laraba, da sauri Majada ta iso wajen tare da cewa 

"Yes Aunty"

"Yau za ki yi mana aiki"

"Ok da me zan fara?"

"Ke shashasha kawai, daƙiƙiya, wa ya ce girki za ki yi, aiki akan Bilqees ne?"

Cewar Jummai cikin ɗaga murya, jikin Majada ya soma rawa, cikin rawar murya ta ce

"Don Allah...

"Majada dole ki aiwatar da abin da muke so"

Cewar Laraba, Jummai ta ɗaura da cewa 

"Yau da daddare ki tabbatar da kin tarwatsa dining area, har sai farin cikin Alaja ya gushe"

"Na shiga uku, yau za a kore ni a wajen aikina"

"Dalla gafara cen, doluwa kawai, wa ya ce miki ke za ki aikata? So mu ke ki yi yadda ki ka yi rannan wa Bilqees a dining area har Alaja ta yi fushi da ita, ke in takama ma ta kore ta"

Cewar Laraba cikin ɗaga murya.Hawaye Majada ta soma zubar wa, tsam bata son ganin Bilqees cikin damuwa, amma babu yadda ta iya dole sai ta aikata abin da suke so in ba haka ba, za su hukunta ta...

"Daga yanzu za mu fara shirya plan namu zuwa dare ki aiwatar, in aka samu kuskure to ki sani, kashe ki za mu yi"

Waro idanuwa waje Majada tayi tana kallon Jummai tare da cewa 

"Kisa!"

"Eh za mu kashe ki"

Nan ta ji tsoro ta amsa da za ta yi duk abin da suka umurce ta dashi....

Bilqees ta kawowa baƙo shayin gargajiya ta ajiye masa, cikin sanyin murya ta ce

"Ga shi nan"

"Thanks"

Kawai ya faɗa yana cin abinci a hankali, ta juya ta bar wajen.

Basu jima a wajen ba, suka koma hotel, masaukin su, abincin rana a hotel za a kawo musu. DR Waahab ya dawo ɗakinsa ya rage kayan jikinsa ya watsa ruwa ya fito ya sanya kaya mara sa nawi ya ya hau bed ya kwanta tare da lumshe idanunsa, ringing wayarsa ce ta sa ya buɗe idanunsa tare da kurawa screen na wayar idanu kamar me karantar Number ganin ba suna, a hankali ya ɗauka tare da karawa a kunnensa ya yi sallama aka amsa jin muryar Ashfat ne yasa ya sauke numfashi ta gaida shi ya amsa sannan ta ce 

"Ya Waahab ya aiki"

"Sai godiya, ya mutan gida?"

"Kowa yana lafiya"

"To ya yi kyau, ya school?"

Ta yi farin ciki da ya bata hankalin sa, ta ce

"Alhamdulillah mun kusa gamawa"

"Ya yi kyau, Allah yasa a gama lafiya

"Amin Ya Waahab, na gode"

"Mentioned not"

Cikin farin ciki ta katse wayar.

Ya lumshe idanunsa nan bacci ya ɗauke sa.


Sai 11:00 am ya farka, duk ya gaji da kwanciya yana so a fara program ɗin nan ko zai daina jin kaɗai ci, ya iso ya tsaya a daidai window dake ɗakin a hankali ya yaye labule ya kurawa waje idanu yana kallo da mamaki har titi yake hangowa, har zai juya kuma ya kalli inda  ya zauna jiya da daddare yaga yara suna wasa hankali kwance suna ta nishaɗi. Ya yi mamakin ganin yara a wajen, bashi da yawan bincike, don haka kawai ya yi tunanin komawa kan bed, yana ƙoƙarin sauke labule don ya koma, sai yaga yaran sun mik'e suna murna tare da rugawa a guje, suka iso wajen wata mace me sanye da bakaken kaya fuskar ta rufe da niqab. 

Yaran suka kewaye ta tare da rungume tana suna mata maganar da shi baya ji amma kuma yadda suke yi kamar suna cikin damuwa. To ko dai yaranta ne ta fito nemosu ta same su bakin hotel, to in dai yaranta ne waɗan nan ai suna da yawa. Kamar zai juya kuma yaga ta ɗauki yarinyar ƙarama daga cikin su sannan suka koma kan dakali tana yi musu magana, cen yaga sun yi layi tana raba musu abu, suna murna, sai kuma jim kaɗan yaga tabar inda suke ta yi bakin titi ta tari machine ta hau suka bar wajen. Ya jinjina kai da abin da ya gani, yana tunanin akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin wannan yaran da matar nan....

Wayar sa ta yi ringing ganin sunan OG ne yasa ya ɗauka, nan ya sanar da shi ya ce wa sauran duk su zo su same shi. Haka ya yi ya tara su baki ɗaya a wani ɗakin taro suka gabatar da meeting.


***********************************

Kasancewar abincin dare bakin za su ci yasa aka shirya musu abinci na musamman a wannan daren, don har da manyan ogannin su za su zo Alaja restaurant, don haka Alaja ta sanya su gaba suka shirya dining area.

8:00pm suka iso, ganin yadda aka shirya wajen gwanin sha'awa, suka zauna, cikin farin ciki kowannen su ya ke cin abinci suna hira suna nishaɗi, Bilqees ta iso wajen bakon nan me son shan shayin gargajiya ta iso cikin girmamawa ta ce

"Barka da warhaka?"

Ya ɗan ɗago tare da cewa 

"Yawwa"

"Akwai buƙatar na kawo maka shayi?"

"Eh"

Ya faɗa ta yi saurin barin wajen ta wuce cikin kitchen daman already ta dafa ta ajiye, ta ɗauko ta iso cikin dining area tana ƙoƙarin isowa inda bakon yake saura kaɗan ta ƙarisa ta zame ta faɗi ƙasa, nan take madaidaicin plate dake ɗauke da tea flask da madaidaitan cups suka zuɓe ƙasa ba ki ɗaya suka tarwatse ruwan shayin sai a hannun Dr Faisal da wasu likitoci da suke zaune kusa dashi ragowan ya dawo jikin Bilqees sabar azaba ta saki ƙaran da ya jawo hankalin ƴan wajen, suka mik'e a sora  ce suna kallon ta.

ALAJA dake Corido tana waya jin wannan ƙarar yasa ta iso cikin sauri kamar ta kifi don son sanin wannan ƙarar daga ina ta ke. Aiko tana shigowa dining area taga wajen ya hargitse wasu suna tsaye, wasu suna zaune, wasu kuma sun taru waje guda suna magana ta iso idanunta suka sauƙa kan Bilqees dake zaune kan ties tana rawan jiki saboda tsoro da tashin hankali, ita ce mata sannu da suke yi ma ƙara firgita ta yake...

"Ina me baku hakuri, don Allah ku zauna ku ci gaba da cin abincin ku cikin kwanciyar hankali, accident ne"

Cewar ALAJA, jin haka yasa wasu suka koma suka zauna, Bilqees jin muryar Alaja tana bada hakuri yasa kaɗan ta saki fitsari shikenan ta mutu ta lalace, ba ayi solving wancan case ɗin ba ga wani nan ya sake faruwa, ta kalli baƙo me shan shayi taga wani ya iso yana goge masa jikinsa. Bilqees jiki sai rawar ɗari yake yi saboda tsoro gashi kuma manyan mutane ne, ya za ta yi. Cleaners suka su iso wajen tare da fara tsaftace wajen, Dr Faisal ya ce

"To ku taimaka mata ta tashi mana ba ku ga taji rauni bane?"

Da kyar wata cleaner ta taimaka mata ta mik'e tare da isowa kusa da Dr Waahab bakinta na rawa, idanunta akan hannunsa da ta kula yana ɗan riƙe wa lokaci zuwa lokaci ta kurawa ido tana kallon wajen, tabbas shayi ya ƙone saboda ja da taga wajen ya yi kasancewar farar fata ce dashi....

"I'm really sorry Sir"

Ta faɗa tana jin azabar raɗaɗi da zugi, kasancewar ta ƙone da yawa, bai ɗago ba, amma ya ce

"Noted"

Zata juya kuma ta taka glass na cups da suka farfashe, nan ta sanya ƙara, tana riƙe wajen, cleaner ta cire mata. ALAJA kamar tayi hauka sabar ɓacin rai da takaici kamar ta rufe Bilqees da duka, ta ci albarkacin waɗan nan bakin ne amma da ta shaƙota a gaban su. Bata so mutuncin ta ya zube nan da danne abin da yake damunta ta ce a shigar da Bilqees ciki. 

Nan ta dinga bi tana basu hakuri su ci gaba da cin abinci tsautsayi ne, su kuma cewa suke ai ba komai ta sa a duba yarinyar ita ma taji rauni, a cikin zuciyar Alaja cewa take ba rauni ba Allah yasa buguwa ta yi.

Dr Waahab ya zauna, yana jin zafin inda shayin ya ƙona sa, dole sai ya sha maganin rage zugi, kasancewar shayin da zafi sosai dole ya ƙone mutum, kuma yarinyar ma ta ƙone sosai...

"Alaji kana buƙatar wani abu ne?"

Cewar ALAJA, a hankali ya ɗago ya kalleta tare da cewa 

"A'a"

"Ok we are so sorry woo, ya faru ne cikin rashin sani, tsautsayi ne"

"Ba komai hakan yana faruwa ai, ku yi gaggawar treating yarinyar taji ciwo"

A ran Alaja ta ce, kai dai bari ni naji ciwo ba ita ba, ai wannan ciwon da ta ji ma kaɗan ne da abin da zan yi mata........

Bilqees da ƙyar ta kawo kanta ɗaki, ga ƙafarta dake mata zafi, ta janyo jakarta ta saɓa a baya, tana so ta bar cikin restaurant ɗin tun kan su yi ido hudu da Alaja, don yau muddin suka haɗe kashinta ya bushe, ta zauna tana sauke numfashi jin zafi da tafin ƙafarta yake mata, ta duba ganin glass ne a maƙale a wajen yasa ta saka hannu ta cire nan da nan jini ya barƙe ta waro idanuwa waje tana kallon yadda jinin ke fitowa duk da ƙaramin glass ne ta taka, ta ajiye jakarta tana kallon wajen gashi ba damar ta tashi ta yi wa kanta agaji, sannan babu kowa a kusa.....

"Ai wannan ma kaɗan ki ka gani, ni da ma ɓalle miki ƙafar ya yi ba ki ɗaya kowa ma ya huta"

Ta saurin ɗagowa, ta kalli bakin ƙofar ganin Aunty Laraba yasa ta ce

"Don Allah ki taimaka keni ki bani tissue"

"Hehehe, ba ki da hankali, in dai ta ni ne ki shekara goma a zaune"

Tana gama faɗin haka ta fice, Bilqees me za ta yi ban da hawaye....





Comments and share fisabilillah