JODAH

30

by @sadisakhna


 

______👑 *JODA* 👑_____ 

 

             

 

Na  

 

*Sadi-sakhna* 

 

Ƴar mutan Jama'are 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

@sadisakhna on Arewapen 

@SAKHNA03 On Wattpad 

*** on Whatsapp 

 

LITTAFI NA 1 

 

👑*WarÆ™a ta Æ™arshe(30)*👑 

 

 

Fitowa ta daga banÉ—aki kenan Daga kasuwancinnawa wato fitsari naji ana maidamin saÆ™on cewar ana sallama dani. Jimm kaman banji ba,dan yanzu magana ma ba sosai nakeyi ba,duk na zama wata iri a kwanaki kaÉ—an. Jiya kuwa dana dawo bayan wannan abun yafaru ko bacci kasa runtsawa nayi,ina rufe idona saidai na kalli Ummata ana janta a bayan doki dakuma kallon da Hammar yake aikamin a wajen. 

 

FaÉ—awa É—aki nayi ina shirin kwanciya akan tabarmata,don Allah yaga banason koma wanene naje na ganshi,kowa ma yafita takaina a yanzu. Babu abinda ke raina saita ta wacce hanya zanbi na kubutar da ummata,sannan kuma ya zanyi da É—an talikin dake cikina wanda babu wanda yasan dashi dagani sai mahaliccin daya ajiyeshi a ciki. 

 

"Joda bakiji bane ance ana nemanki a waje,abinda yafaru tabbas bashida daÉ—in tuni,amma kullum inaso ki Æ™ara ganewa rayuwarmu fah haka take,naga alamar har yanzu baki buÉ—e idonki kinsan wacce rayuwa muke ciki ba,kada ki dunga mantawa baiwar da Allah yayi miki da kyar ta iya siyamiki matsayin dakike fata a wajensu,saima hankalin su dazai Æ™ara kawowa kanki wajen suga sun mallakeki,dan haka ki je kiga wanene. Duk da hakan kuma ki godewa Allah da matsayin dakike dashi É—in,saboda kin kalla duk cikin jami'ar nan yanxu babu wata baiwa tamkarki,kowa fata yake ko makusancinki ya zama. Ki rage saka damuwa a ranki kar wani abu yasameki,duk mai nemanki da sharri Allah yafishi" 

 

Adda Rahilah ta Æ™arisa maganar tana dafani cikin kulawa,daren jiyan na zayyanemusu duk abinda yake faruwa dani,domin nakai gabar da bazan iya rikewa ni kaÉ—ai ba. Sun tayani kuka sosai,sannan sunyi mamaki danace musu mahaifiyata yakama a dole sai ya mallakeni. Babu abinda zasuyi min amma kukan da suka tayanin ba Æ™aramin daÉ—i yayimin ba. Sannan ga shawarwari da suka bani masu É—an sanyaya zuciya,shine na fawwalawa Allah lamarina domin dukkansu yafisu. 

 

Banason yimata musu,dan haka na zari mayafina na lulluba na fita. 

 

Musa nagani a tsaye can gefe da Æ™ofar sansanin namu,yana kallon fitowata ya taho da sauri, É—auke kaina nayi har ya iso wajen,dan a yanzu duk wani abu daya shafi Hammar É—in haushinsa nakeji. 

 

"Kiyi haÆ™uri Joda,haÆ™ika abinda Yallabai yayi miki jiya bai kyauta ba,duk da cewar yana jin haushinki amma baici ya shareki ba,saidai kinsan AlaÆ™ar ku ba abune bayyananne ba,kuma ya ganki ne tareda yerima kabeer shiyasa abin ya harzuÆ™ashi,idan bazaki damu ba dan Allah kiyi haÆ™uri kizo wai inda kuka saba haÉ—uwa yana jiranki a wajen zakuyi magana domin gobene zamu É—aga zuwa kasarmu tunda mun gama abinda yakawomu" 

 

"Hmmm sallama zaimin kenan tunda yagama abinda yakawoshi,ciki harda waina rayuwata dayayi,yanzu yagama abinda yakeso zai tafi kohhhh" 

 

Banaso yakalli hawayen daya taru a idona,dan haka wusheshi nayi nabi hanyar daya fito É—in. Kai tsaye lambun damuke haÉ—uwa na nufa,zuwa lokacin yamma tayi liÆ™is rana ta fara haramar faÉ—uwa. 

 

Ko gabana bana gani saboda tafasar da zuciyata takeyi,badan zuciyata ta haddace bin hanyar ba daba lallai Æ™afafuna su kaini ba. 

 

A zaune yake wannan karon akan darduma da kayan marmari a gabansa,tuffa ce a hannunsa yake gutsira hankalinsa kuma yana kallon ruwan dayake gabansa. 

 

Ko kaÉ—an bayyimin kama da hammar É—ina ba wanda na bawa darajata,rayuwata da kuma zuciyata,sai yamin tamkar basaraken daya fito shaÆ™atawa yin kilisa. A haka na Æ™arisa inda yake tareda tsayawa a bayansa. 

 

"Uhmmm tarayya da É—an sarki yasa yanxu kenan kin daina tsugunnawa idan kinyi laifi,saidai ki tsaya a bayana ko Joda?" 

 

Matsawa nayi nesa dashi kaÉ—an a gefe na durÆ™usa kaman yanda sauran bayi sukeyi na sunkuyar dakaina kana nace. 

 

"Kayi haÆ™uri ya shugabana ka gafarceni, idan na bata maka rai ka gafarceni." 

 

Nasan kallona yakeyi da mamakin abinda nayi,bai amsamin ba sai gani nayi ya É—auki ayaba ya miÆ™omin. 

 

ÆŠan matsawa nayi kaÉ—an tareda cewa. 

 

"Kayi haÆ™uri amma matsayina na baiwa ban cancanci nuna sanayya kokuma karbar abu daga gareka ba,aikina shine faranta maka,da shimfiÉ—a rayuwata a gabanka kabi takanta yadda kakeso. Gangar jikina da zuciyata sallamace gareka ranka ya daÉ—e" 

 

  

"Idan da gaske ne hakane matsayinki to na umarceki ki karba kici" 

 

ÆŠagowa nayi na kalleshi,so nake na karanta saÆ™on fuskarsa amma yaÆ™i bani damar hakan,dan haka nima na tamke tawa fuskar na karbi ayabar. Barewa nayi nafaraci,ko gama taunawa banyi ba naji wani tashin zuciya da amai ya tasomin. Da sauri na jefar da ayabar hannuna na koma gefe nafara amai. Saida na zubar da duk abincin ranan danaci har yazaman Æ™oÆ™odonne kawai nakeyi. Lokaci guda duk na galabaita na fita hayyacina. Bayan na gama ina maida haki nakalli ya miÆ™omin hannu,ashe tunda na fara aman yake tsaye a kaina. 

 

Ture hannunsa nayi tareda fashewa da wani kuka daya daÉ—e yana cin raina sai yau nasamu na zazzage shi. 

 

"Karka tabani babu ruwanka dani,dagani har abinda yake cikina babu ruwanka damu,meyasa ka shiga rayuwata,wato saboda kaga inada abin baka shine bari ka karba sannan ka bayyanamin matsayina koh?" 

 

ÆŠagoni yayi daga tsugunnen yazamana muna kallon juna,har sannan sheshsheka nakeyi na kukan danayi. 

 

"Ya isa ki daina wannan maganganun wanda nasan ko nayi miki bayani bazaki fahimta ba, ki gasgatamin maganarki naji kince kina keda abinda yake cikinki,kenan kina É—auke da juna biyu?" 

 

Yayi min maganar a sigar tambaya 

 

"Shine abinda nazo faÉ—amaka idan ba haka ba babu abinda zaisa na dunga tako Æ™afata ina zuwa neman ka,har ka nemi cimin fuska a cikin mutane" 

 

"Wai ke kaÉ—ai akayiwa laifine a lamarinnan,kin manta kamaki nayi ido huÉ—u kin sulale kintafi wajensa har bayan jami'ar nan,sannan idan na tambayeki kuma bazaki bani amsaba,ko kin manta sauyamin dakika farayi a kwanakinnan,sannan jiya dana ganki a tareda shi mai kikeso nace miki,mai yakaiki wajensa tun farko, kindai san keba baiwarsa bace bashida iko dake,amma mai yasa komai yace kiyi zaki dungayi. Ko kina tunanin banida labarin saÆ™onnin dayake aiko miki a kwanakinnan. Yanzu ma so nake na tambayeki shin cikin jikinki nasane ko nawa. Saboda idan banawa bane babu yanda za'a yi na tafi dake Kasarmu dashi a jikinki" 

 

Wani kallon mai yake faÉ—a nayi masa. 

 

"Hammar abin har yakai haka? Kai kanka kasan a yanda ka sameni,sannan banyi tunanin alaÆ™ar dake tsakaninmu zaisa ka zargi haka ba,shin kodai dama kallon haka kakemin kai. Sannan wanne zuwa Æ™asarku kake faÉ—a. Dama haka yarjejeniyarmu tace ,cewar zaka jani zuwa kasarku a matsayin baiwa nacigaba da biya maka buÆ™atarka?" 

 

"Ba haka nake nufi ba,amma tunda kinada ciki kam dolene ai na tafi dake kinsan da haka,sannan bazayyiwu na Æ´an taki naje dake da ciki ba,idan ba haka ba sai wata matsalar ta bayyana,saboda matsayina ya wuce............" 

 

"Kaga bar maganarka basai ka Æ™arisa ba hammar,naji iya wanda zanji kuma na fahimta. Wanne mai matsayine mai irinnaka a yanzu zai amshi É—a daga baiwa,ko ya jata zuwa Æ™asarsa ayi masa dariya idan aka ganshi da ita.....to na hutasarka,dama haƙƙinkane na sanar dakai amma bance ka amsa kaine ubansa ba,matsayinka yafi gaban haka. Nima bazan bika ba akwai abinda yake buÆ™atata wanda nawane,kuma inaso na tsaya tsayin daka wajen ganin na kareshi. Idona ya waye haka sakamakon dana karba a soyayya yasa na farka daga baccinta,dan haka bazan sake irin wannan rayuwar mafarkin ba kuma" 

 

Kama hanya nayi nafara tafiya zan bar cikin lambun,idona har wani dishi dishi yake gani saboda bacin rai. 

 

"Joda idan kika saka Æ™afa kika fita daga cikin lambunnan,kuma har kike faÉ—a a fuskata zaki koma ga wancan mutumin to ina mai yimiki albishir da cewar zan hanaki yancin danayi miki alÆ™awarin samu kuma........ 

 

Waiwayowa nayi na kalli cikin idanuwansa... 

 

Wai mai yake nufi ne,shi ya halicceni komai. Yarabani da mafarkina,yarabani da budurcina,ya rabani da farincikina yanzu kuma so yake a sanadiyyar sake yi masa biyayya na rabu da mahaifiyata ma,inaaaaa hakan bazai taba yiwuwa ba,koda Gadar kifiyace kona garwashi inajin zan iya takawa domin na isa gareta. Kan mage ya waye haka,bacewa nace inason Æ´an ci danna halaka ba,ina sonsa ne domin na rayu kuma na kare abinda yake nawa,bawai na sadaukar da komai dominsa ba. Yaje da Æ´an cinsa na yafe,idan rayuwar bauta Allah yazabamin na karba hannu bibbiyu. 

 

Batareda na furta kalma ko É—aya ba nake kallonsa da jajayen idanuwana ina wannan tunanin. Juyawa nayi cikin zafin zuciya dakuma dauriya na fara takawa ina barin wajen.  

 

Kowanne taku danakeyi ina jin zaren daya É—aure zuciyoyinmu waje guda yana É—ashewa,zogi da raÉ—aÉ—in hakan yana ninkuwa a zuciyata,amma hukuncin dana riga na yanke bazai taba barina na waiwayaba. Da haka harna bacewa ganinsa batareda nasan wanne hali yake ciki ba. Wanda inada yaÆ™inin bazai taba kasancewa mai kyau ba. 

 

****    ****    **** 

 

Tana barin wajen ya riÆ™e Æ™irjinsa wannan yake bugawa da Æ™arfi kamar zai faso waje. YunÆ™uri yayi kaman  zai bita Sai bakinsa ya feso da aman jini harda guda guda. Tun yana gani kaÉ—an kaÉ—an har duhu ya lullube ganinsa. 

 

*****     *****   

 

    

Washagari da safe saÆ™on yerima Kabeer ya iskeni na Keken doki na jirana Æ™arfe shida na yamma a bakin Jami'ar, babu wanda na faÉ—awa cewar a yau zan tafi,domin banajin zuciyata ta shirya miÆ™a musu bankwana. 

 

ÆŠakin ajiye litattafai na sulale na shiga,na É—auki litattafai kusan guda biyar masu daraja a bangaren magani,nasan sata ce nayi musu amma ko wannan É—in bai isa biyana abinda nayi musu ba. Suma dukka haushinsu nakeji. 

 

Dakin magani shima nashiga,babu wanda yahanani domin daman wajen shigatane. Duk wani magani danasan zayyimin amfani saida na É—auka,suma na ajiyemusu duk wani bayani danake haÉ—awa na cirar magani da sarrafashi wanda nasan zai musu amfani sosai suma.  

 

Saida na bari yamma tayi sosai kafin na haÉ—a duk abubuwan danake buÆ™ata,ban É—auki kaya da yawa ba,sannan wasu kyautukan duk na barwa su addah rahila su. Ina kuka haÉ—eda share majina haka nagama haÉ—a kayan.  

 

ÆŠauka nayi na nufi sansanin su hammar,a can zan jira har lokacin dazan bar jami'ar, idan da rabo nasan zan sake haÉ—uwa dasu,amma yanzu banason damun rayuwarsu da damuwar dani kaÉ—ai tashafa, hakan yasa na zabi rubutamusu iya wasikar inda nake kawai na ajiye musu. 

 

Tura Æ™ofar É—akin nayi nashiga,ko kaÉ—an na gagara tare hawayen dayake zubowa daga idona,abubuwa da dama suna tariyowa a cikin kaina. Tun ba'aje ko ina ba na fara nadamar irin rabuwar da mukayi da Hammar. Shafa cikina nayi inajin yanda zuciyata tayimin nauyi. 

 

Akan wata wasiÆ™a a naÉ—e da take kan gadonsa idona ya sauÆ™a. Gadon da komai ya faru akansa gadon da bazan taba mantawa ba, Kenan yasan zanzo shiyasa ya ajiyemin. 

 

Tsugunnawa nayi na É—auka,amma a halin yanzu banida Æ™arfin halin buÉ—eta ballantana na kalli mai ta Æ™unsa,tunda nasan koma mai yake ciki to bazai taba dawowa da hannun agogo baya ba. 

 

Tattara duk wani guntun abun dayake nasa a cikin É—akin nayi nasaka a kayana,irin su sauran takardu,alÆ™alami harma da wani mayafinsa. 

 

Ina nan durÆ™ushe a É—akin ina kuka har rana ta faÉ—i kafin na binne rayuwar danayi a cikin Jami'ar a Æ™arÆ™ashin zuciyata na kuma nufi hanyar fita. 

 

Kaman fita ta wancan karon yauma buÉ—emin kawai sukayi batareda sunce komai ba. Nima da Æ™ullin kayana aka na kama hanyar fita daga jami'ar. 

 

 

Kaman yanda ya faÉ—a da mai keken doki naci karo,ina zuwa na hau yakama hanyar masauratar dani a karo na biyu. 

 

Tafiya mukeyi da tunani kala kala a cikin raina. Kallon wasiÆ™ar dake hannu na nayi,wanda na tamke ta kamar wani zai kwacemin. 

 

Banso budeta ba,amma saboda kawar da tunani yasa nafara wareta a hankali wani hatimine yafaÉ—o daga ciki irin wanda yake kan Æ™irjinsa. An rubuta Keita Hammarou a jiki. Sunansa ne y  yankeshi zuwa Hammar.  

 

Ware wasiÆ™ar nayi tareda fara karantawa. 

 

.......idan wasiÆ™ar nan tasameki to lallai kin je masauÆ™inmu Joda bayan rabuwar da mukayi batareda bankwana ba. Bazan iya binne sonki ba,domin rayayyene dayake zaga dukkan zuciyata. 

 

Ina tunanin kin manta kalmar dana furtamiki a daren dana maidaki cikakkiyar mace.... 

 

("Ina Azabtuwa da kasancewar ki a taredani,amma nesantarki dani yafi komai Illata rayuwata. Kula wani dazakiyi a rayuwarki bayanni Alhali ina numfashi abune na bazan iya yafewa zuciyarki ba Joda,Ba so nakeyi miki ba abinda yafi So ruhina yakeyi miki.") 

 

To yanzu ki Æ™ara da nabaki umarnin karemin jinina dayake jikinki,ban yafe ba idan kika bari wani yazubawa É—ana dayake jikinki najasarsa,wannan hatimin dana baki alamace da ke mallakina ce ni kaÉ—ai,babu wani daya isa a kaff faÉ—in duniyar nan yace ke mallakinsa ce sai idan na yarje masa. Nasan wancan Lusarinne yashiga tsakanina dake,ke kuma kika boyemin saboda wani dalili naki, bazan tilastaki ba,amma ko bayan raina ban amince miki dashi ba har abada. Kaman yanda zanyi ta tunaninki a kullum kema nasan dole kiyi hakan. Wannane hukuncinmu na hawa dokin zuciya dakuma fincike soyayyar da bata nuna ba daga jikin zuciyoyinmu. A kowacce dama idan na samu shine zanyi yanda zanyi ki dawo gareni. Kizama cikin shirin faruwar hakan JODA" 

 

Kuka na Æ™wace dashi musamman dana kalli yanda wasiÆ™ar tabaci da jini,na tabbata aman jini yakeyi lokacin daya rubuta,ko ya yake ji a lokacin. Rawa nima nawa jikin yakeyi,tun ba'a je ko ina ba nafara nadamar barinsa, anya kuwa ban tafka babban kuskure ba kuwa,in ban tsaya dan soyayyar mu ai na tsaya domin jininsa na jikina,gashi ko a wasiÆ™ar yaÆ™i faÉ—amin koshi waye,kullum faÉ—i yake bazan taba fahimta ba. Ballantana na nausa cikin duniya nemansa. Lallai aiki jaaaa yakamani. 

 

 

......nace nima aiki ja yakamani na cigaba da rubutu,haka kuma masu karatu aiki jaaaa yakamaku na ku tsaya kuji yaya haÉ—uwar wannan masoyan zata kaya?  

 

 

.....shin wacce rayuwace take jiranta ? 

 

......shin tayi daidai kuwa data bar wanda suka tsayamata tamkar ahali a lokacin da batada kowa?. 

 

 

.....Ya labarin Hammar shi wanne irin zaren Æ™addarane mai Æ™arfi dazai yi silar janta izuwa gareshi,bayan batasan a wacce Æ™asa yake ba. 

 

........idan sun haÉ—u shin a wanne matsayi zasu tsinci kansu,da gaskene yafi Æ™arfinta kuma ya manta da ita a rayuwarsa. Kokuma kaman yanda yafaÉ—a a wasiÆ™ar yana dakon haÉ—uwa da ita. 

 

.......ina labarin baÆ™in asirin dayake jiransa shin zai illah tashi kaman yanda akace. 

 

.........Zaleekah zata bar Joda ta zauna lafiya bayan tasan itace wacce yerima kabeer yakeso. 

 

 

.......wacce hanya joda zatabi tayi maganin Yerima kabeer dama marasa mutuncin cikin masarautar..... 

 

 

.......Wacce gwagwarmaya ce zata auku a masarautar Mali yayin zabar sarauniya?  

 

 

.....miye makomar cikin jikinta da wanne Æ™alubale zaizo...... 

 

Dukka dama wasu chakwakiyar a cikin littafin JODAH book 2 ..... 

 

 

Ku tutuntubeni ta wannan layin idan kun shirya ayi tafiyar daku....karku manta dukka kamun bakin zare akayi ba'a ma fara labarin ba tukunna.  

 

*** 

Zaku iya cigaba da bibiya a AREWAPEN 

1K A WHATSAPP 

700 A TELEGRAM  

SAINA JIKU