HASASHEN SOYAYYA

Hs 24

by @legendspen

kar ku manta ku yi following dina, domin samun update akai akai. 

_Page 24_



Waya ya ɗauka ya kira lambar Bhatool, dai-dai lokacin da ta gama shiryawa bayan ta fito daga wankan da ta shiga, ɗaga wa ta yi tare da faɗin. "Hello, salamu alaikum." Wani sanyi Senate ya ji cikin ransa, sai da ya rufe ido  sanan ya amsa da. "Amin wa'alaiki salam, Fulani Barka da safiya."


"Barka dai ina kwana?." 


"Lafiya kalau Alhmdlh, ya su Mama?." 


"Kowa lafiya, ya su Mom?." 


"Alhmdulillah, gani ƙofar gidan Yaya Karima zan shigon sai kuma na tuna kina gida." Dariya ta yi sanan ta ce. "Ko zaka zo nan ɗin?."


"Ina son zuwa, amma ina jin kunyar Ummah."


"Hahaha ita Umma ɗin, bara naje na faɗa mata." 


"A'ah Fulani, ban saki ba fa." Dawowa ta yi ta zauna sanan ta ce. "To kawai ka zo." 


"Tom Fulani, zan ɗakko Anas sai muzo kawai." 


"Ni da kai kaɗai zaka zo Allah." Ta faɗa kaman za ta yi kuka. "Shike nan Fulanina zan zo kin ji." Daga haka suka fanjama duniyar soyayyarsu.




~~~~~~~~Hausari




Fure da Habi ne xaune sun rafka uban ta gumi, abin duniya duk ya ishe su. "Wai yanzu haka zamu zauna mu zubawa su Bhatool idanu, sun abinda suka ga dama suna ta samun duniya." Habi ta faɗa. "Ni kinga Habi duk jikina ya mutu gaba ɗaya, jikina ya na bani kawai na je gidansu mucu arziƙi tare." 


"Eyh lallai ne asararriya, amma kin ji kunya wallahi." 


"Ba zancen jin kunya Habi, tun da sun fi mu nasara a rayuwa sai mu haƙura, faɗan da yafi ƙarfinka sai ka masshe shi wasa."  


"Kin san yaranan 'yan iska ne wulaƙantamu za su yi, amma wallahi da sai muje kawai." Itama Habin ta faɗa. "Ai a hankali zamu shiga jikinsu, muci arziƙi mu yi ɓulɓul ko zamu samu masu kuɗin nan kamar su." 


"Hakane kuma, yanzu kawai mu shirya muje gidan yau." 


"Ke Habi matsalal ki rawar ƙafa, mu bi a hankali mana." Furee ta faɗa tana tunani, sai kuma can ta ce. "Mu sami kuɗi muje kasuwa mu siyo su bulugari da turmi da kujeru na katako mu kai gudumawa, sai muje da yamma kinga sai muce dare ya yi mu kwana ɗaya." 


"Gaskiyya Furee kina da lissafi, ayi hakan kawai."


"Wai Uban me kuke tattaunawa ne, kun ƙunshe a ɗaki?." Goggo larai ta faɗa. "Bakomai Goggo muna fira ne kawai."


"Har kuna da nutsuwar yin fira yanzu, iyayen ku suna can asararru sun biyewa abun duniya, sun ba da auren Bhatool, shine ku xaku zo nan kuna wani fira." 


"To mu Gaggo mene ruwanmu a ciki?." Habi ta faɗa. "Yoo kema ai irin uban naki ce marar hankali sha-sha-sha." 


"Bawani Goggo, mu yanzu ya za ayi ace mun zauna muna baƙin hali kamarku mu tsani mutane kuma ga shi sai samun ci gaba suke."  Furee ma ta faɗa tana hararar Goggo laran. "Sai ku yi asararru." 


"Kema sai ki yi." Suma suka faɗa. 



~~~~~~~Nyan'ya. 




Kwalliya Bhatool ta ɗauka cikin wani arnen lace da ya matuƙar amsar jikinta, fuskanta ta sha ta ɗau light make-up. "Wai Bhatool wanan kwalliyan na mene haka?." Ummah da ta shigo ɗakin ta tambayeta. "Baƙo zan yi." Kallonta kawai Ummah ta yi sanan ta fice, a ranta ta na nemawa Bhatool shiriya. Sai bayan salkan Magariba Senate ya zo gidansu Bhatool, lokacin Bhatool ta cika ta yi fam, jira kawai take yazo ta sauke mai kwamdon rashin mutunchi, a ɗakIn Abdul na zaure aka sauke shi, da kayan ciye-ciye da na sha. 



Yana zaune ya kafe ƙofa da idanu yana jiran shigowarta, a hankaili ta tako cikin ɗakin bakinta dauke da Sallama. Ba tare da ya jira ta gama shigowa ba ya ta shi da sauri yana faɗin. "My Amarya." Ƙasa ta yi da kanta a karo na farko da ta ji tana kunyar haɗa ido da Senate, xama ta yi kan abun zama daga ɗan nesa da shi sanan ta ce. "Ina yini." 


"Lafiya kalau Fulani Amarya." Murmushi ta yi kafin ta ce. "Yasu Momy." 


"Kowa lafiya kalau, Momy anyi bixi shirye-shiryen biki." Shiru ta yi bata iya cewa komai ba, sai shi Senate ɗin ke ta zuba, ya kamo wancan xancen ya kamo wancan. Ya daɗe sosai kafin sukayi sallama ya tafi bayan ta gaisa da Ummah. 



A cikin yan kwanaki aka ci gaba da shirye-shiryen biki, ƙawayen Mom sun yi matukar kokari da kara, sun haɗa akwati 36 sanan abokan Senate sun haɗu nasu 12 wayanda suma suke maƙil da kayayyaki masu tsada, ganin haka yasa Dad ya ƙara cika wasu biyan da manyan laces masu tsada daya kuma da manyan shaddoji, baya ga mukullin mota ƙirar GLK da ya sa a cikin kayan, kallo ɗaya zaka yi wa kayan kasan ankashe masu gidan rana, komai very Expensive su kansu akwatunan masu tsada ne sosai baya ga kayan da suke ciki. 



An sanar da su Bhatool ranar da za a kawo kayan, hakan yasa Abdul da Yaya karima suka saki kuɗaɗe wajen yin abinda suma zasu fita kunya, duk da basu san adadin kayan da za a kawo ba amma dai sun san manyan mutane zasu kawo kayan. Haka bangaren Bhatool da ƙawayenta sun shiga hada hada na hidima, duk da Bhatool ta daina zuwa makarata, amma su kanzo gidansu ayi shirye-shirye, sun he gidan Suhaima sau ɗaya ita ka ɗai ce fitar da ta yi, kuma Senate ya kai ta da ddare yazo ya dauke ta, Jannah da Amrah dai kullum sai sun zo, Amrah ce a matsayin babbar ƙawa, ita ke fitar da kowwnne bayanai a social media, gaba ɗaya Yobe State ta ɗauka Maganar auren Senate da Bhatool. 



Yau ta kama ranar da xa a kawo kayan lefen, tun safe ake gyaran gida da sauran abubuwa, duk wwni Abu da za a ci ko a bawa masu kawo Kaya Abdul da Yaya Karima ne suka ɗauki nauyi, kuma order su kayi, Ummah na zaune tsakar gida bayan ta gama turaren huta ta ji anyi Sallama, ba ta gama tantance mai Sallanar ba ta ga Hari da Furee sun shigo.  




Legendspen ***