DANGAR WUTA

Chapter 1

by @maryamstar248

***
๐Ÿ”ฅ๐˜ฟ๐˜ผ๐™‰๐™‚๐˜ผ๐™ ๐™’๐™๐™๐˜ผ๐Ÿ”ฅ
            ๐˜•๐˜ˆ
๐˜”๐˜ˆ๐˜™๐˜œ๐˜‰๐˜œ๐˜Š๐˜๐˜ ๐˜ˆ
๐™ˆ๐˜ผ๐™๐™”๐˜ผ๐™ˆ ๐™Ž๐™๐˜ผ๐™โญ

๐Ÿ’ช๐™…๐˜ผ๐™…๐™„๐™๐™๐˜ผ๐™๐™๐™ ๐™’๐™๐™„๐™๐™€๐™'๐™จ ๐˜ผ๐™Ž๐™Ž๐™Š๐˜พ๐™„๐˜ผ๐™๐™„๐™Š๐™‰๐Ÿ’ช


๐™‚๐™–๐™—๐™–๐™ฉ๐™–๐™ง๐™ฌ๐™–
๐™’๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™–๐™›๐™ž๐™ฃ ๐™™๐™ช๐™ ๐™– ๐™–๐™—๐™ž๐™ฃ ๐™™๐™– ๐™ฎ๐™– ๐™ ๐™ช๐™ฃ๐™จ๐™– ๐™ ๐™ž๐™ง๐™ ๐™ž๐™ง๐™– ๐™ฃ๐™š, ๐™—๐™–๐™ฃ๐™ฎ๐™ž ๐™จ๐™๐™ž ๐™™๐™–๐™ฃ ๐™˜๐™ž๐™ฃ ๐™ฏ๐™–๐™ง๐™–๐™›๐™ž ๐™ ๐™ค ๐™ข๐™ช๐™ฉ๐™ช๐™ฃ๐™˜๐™ž๐™ฃ ๐™ ๐™ค๐™ฌ๐™– ๐™—๐™– ๐™ฃ๐™– ๐™ง๐™ช๐™—๐™ช๐™ฉ๐™– ๐™จ๐™๐™ž ๐™ฃ๐™š ๐™™๐™ค๐™ฃ ๐™ž๐™ก๐™ž๐™ข๐™–๐™ฃ๐™ฉ๐™ช๐™ฌ๐™– ๐™™๐™– ๐™›๐™–๐™™๐™–๐™ ๐™–๐™ฃ๐™ฉ๐™ช๐™ฌ๐™–, ๐™ž๐™™๐™–๐™ฃ ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ž ๐™—๐™–๐™ฃ๐™œ๐™–๐™ง๐™š ๐™ฎ๐™–๐™ฎ๐™ž ๐™ ๐™–๐™ข๐™– ๐™™๐™– ๐™ง๐™–๐™ฎ๐™ช๐™ฌ๐™–๐™ง ๐™ง๐™–๐™ฃ๐™ž ๐™ฉ๐™ค ๐™–๐™ง๐™–๐™จ๐™๐™ž ๐™ฃ๐™š ๐™–๐™ ๐™– ๐™จ๐™–๐™ข๐™ช.

๐™‚๐˜ผ๐™๐™‚๐˜ผ๐˜ฟ๐™„
๐˜ฝ๐™–๐™ฃ ๐™–๐™ข๐™ž๐™ฃ๐™˜๐™š ๐™ ๐™ช๐™ข๐™– ๐™—๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™–๐™ข๐™ž๐™ฃ๐™˜๐™š ๐™– ๐™จ๐™–๐™ง๐™ง๐™–๐™›๐™– ๐™ข๐™ž๐™ฃ ๐™ก๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™–๐™›๐™ž ๐™ฉ๐™–๐™ ๐™ค ๐™ฌ๐™–๐™˜๐™š ๐™จ๐™ž๐™œ๐™– ๐™—๐™– ๐™ฉ๐™–๐™ง๐™š ๐™™๐™– ๐™ž๐™ฏ๐™ž๐™ฃ๐™ž ๐™ฃ๐™– ๐™ฃ๐™ž ๐™ข๐™–๐™ง๐™ช๐™—๐™ช๐™˜๐™ž๐™ฎ๐™– ๐™—๐™–, ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™–๐™›๐™ž๐™ฃ ๐™ข๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ ๐™ž๐™ฃ๐™– ๐™ฃ๐™š ๐™ฃ๐™ž ๐™ ๐™–๐™™๐™–๐™ž.

๐™๐˜ผ๐™๐˜ผ
๐˜ผ๐™ก๐™ก๐™–๐™ ๐™ฎ๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ฃ๐™– ๐™›๐™–๐™ง๐™– ๐™ก๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™–๐™›๐™ž๐™ฃ ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ ๐™– ๐™—๐™–๐™ฃ๐™ž ๐™ž๐™ ๐™ค๐™ฃ ๐™œ๐™–๐™ข๐™– ๐™จ๐™๐™ž ๐™ก๐™–๐™›๐™ž๐™ฎ๐™– ๐™—๐™– ๐™ฉ๐™–๐™ง๐™š ๐™™๐™– ๐™ฃ๐™– ๐™ง๐™ช๐™—๐™ช๐™ฉ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ž ๐™–๐™—๐™ช ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™™๐™– ๐™ฏ๐™–๐™ž ๐™ฏ๐™–๐™ข๐™š ๐™ข๐™–๐™ฃ๐™ž ๐™ ๐™–๐™ก๐™ช๐™—๐™–๐™ก๐™š ๐™ ๐™ค ๐™ข๐™–๐™ฉ๐™จ๐™–๐™ก๐™– ๐™—๐™–๐Ÿคฒ.

๐˜ฟ๐˜ผ๐™‰๐™‚๐˜ผ๐™ ๐™’๐™๐™๐˜ผ ๐Ÿ”ฅ
   ๐˜ฝ๐™Š๐™Š๐™† ๐™Š๐™‰๐™€ ๐Ÿ“–1


001
*******
(Manzon Allah S.A.W ya ce. "Ba ฦ™arfi bane jarunta lallai abin da ke jarunta shine mallakar zuciya a yayin fushi.")

*******
Shimfiษ—ar labari.

   Da gudu motar ke cin hanya, yayin da iska ke kaษ—a bishiyoyin da suka yiwa hanyar ฦ™awanya da matsanancin ฦ™arfi, ta yanda ganyayyaki ke kaษ“aษ“ษ“owa musamman waษ—anda suka bushe zuwa ฦ™asa, ฦ™oฦ™arin matsa sitiyari ya ke da sauran ฦ™arfin daya rage ma shi, amma duk ฦ™oฦ™arin shi ya kasa, kwatsam motar ta sake cin karo da wata babbar bishiyar nan take motar ta soma jujjuyawa tana dukan bishiyoyin gaba da bayanta.
   Bai sare ba ya sake ฦ™oฦ™arin taka burki a karo na babu adadi sai ina motar ta rigada ta zame saboda gudun da take yi tana kai karo ko ina.
   Yayin da tayoyi suka yi ฦ™ara tare da jan ฦ™asa me razanarwa motar na tafiya streight ta wata hanya me duhuwa saboda bishiyun da suka lulluษ“e.
   Cikin rashin abin yi ya riฦ™e belt amma kuma lokaci ya riga da ya kure lokacin wanzuwar ฦ™addara marar tsammani ya soma.
   Cikin daฦ™iฦ™u kaษ—an motar ta yi mummunar karo da abin da ya zama na ฦ™arshe kuma maฦ™urar hanyar da take tafiya, Airbag ya buษ—e nan takr da ฦ™arfi glashin gana ya tarwatse, hayaฦ™i ya soma tashi daga ฦ™arฦ™ashin bonet, ฦ™ahon motar ya ci gaba da ฦ™ara ba tare da tsayawaba.
    Nan take sauran ฦ™warin gwuiwar daya ke da shi ya idasa rushewa, rintse ido yayi da ฦ™arfi yana jiran wa'adin wanzuwar ฦ™addara, ฦ™arar da motar ke yi na cike ฦ™ofofin kunnuwan shi suna hana masa jin sautin komi.
   A hankali ganin shi ya soma ษ—aukewa jin shi yayi nisa sosai ta yanda baya iya tantance abin da yake ji, duniyar shi ta yi shiru komi na shi ya tsaya cak ciki harda fitar numfashin shi.


Lokacin da wata ฦ™ara da basu taษ“a jin irinta ba ta soma karaษ—e ilahin dajin, nan take zaratan matasan suka soma darewa cike da shirin ko ta kwana, suka shiga saita kwari da bakar su cikin ฦ™warewa suna gurnan kamar zakuna, yayin da suka bubbuษ—e ฦ™ofofin jin su suna son tantance ainahin inda sautin ke fitowa suna magana da junan ta hanyar jujjuya kawunansu.
    Nan suka sake tarwatsewa wasu suka kalli gaba wasu baya wasu kuma gefe da gefe cikin salon iya tako na mutumin da ke rayuwa daga shi sai dabbobin daji.

     Bata manta da kashedin da mahaifinta yayi mata ba, haka kuma bata tsorata da abin da ta gani ba, bata da tsoro ta sani ita jaruma ce sai de kuma mahaifinta baya bata damar nuna jarumtakarta a sarari, yana tausarta ne da sanyin shi wanda ta ke ganin yayi yawa kuma yana cutar da su da tsoron shi.
   Yasar da ganyen maganin da ta ษ“ata awanni tana rarrashi  mahaifinta akan ya barta ta zo ษ—iba ta yi tare da yin shitin gudu cikin ฦ™warewa bayan ta zaro wani abu me kama da wuฦ™a wanda aka sassaฦ™a da itaciya me ฦ™arfi, kamar biranya ta soma tiฦ™a gudu tana tsallake madaidaitan bishiyu bata damu da yanda ฦ™afarta ke taka ฦ™ayoyi ba.
    Cikin abin da bai gaza sakanni arba'in ba ta isa wajen da hayaฦ™i ya soma tunuฦ™ewa, sam hayaฦ™in bai dameta ba ta matsa kusa da abin bata taษ“a gani ba tun da take a rayuwarta, bata yi tsammanin gani wani abu me rai ba amma kwatsam ta ji ฦ™afarta ta taka wani abu me laushi, tsugunawa ta yi tare da taษ“a abin wanda ta  ga yayi kama da hannunta, bin dogon hannun ta yi da kallo sai ta ga wata halitta me kama da irin tata halittar kwance cikin abin amma kuma yayi sadda kai sama a ฦ™asa ฦ™asa a sama.

 Dunฦ™ule hannunta ta yi cike da jarumta ta kaiwa glashin bugu, nan take ya idasa rarratsewa, sai ta tsuguna tare da zira kanta ciki, da sauri ta fiddo jin wani ฦ™auri mara daษ—i, sam bata fahimci abin da ya faru ba sai ta tashi tsaye ta ษ—auki wuฦ™arta ta bishiya ta soke a kunkuminta da ta zagaye da fatar Biri, jin ฦ™arar na ฦ™aruwa ga kuma ฦ™auri daya cika wajen ya saka ta sake hallon hannun sai kuma ta juya cike da rashin damuwa tana shirin wucewa, nan ta hangi wani abu me kama da kibiyar da aka harbo da tsakananin ฦ™arfi na tunkarota, da wani irin sauri ta kauce tare da durฦ™ushewa a wajen tana kaucewa harbin da ake yowa tun daga nesa cike da salon ฦ™warewa.

  Bata tsaya sanya ba ta soma jawo mutum da dukkan ฦ™arfinta da cikin tagar motar har ta yi nasarar janyo shi gaba ษ—aya, cike da jarumtaka ta duฦ™a tare da saษ“arshi a lokaci guda kuma tana kare harbin kibiyar da aka yo da hannunta, inda mashin kibiyar ya soke ta a hannu cike da azaba ta yi wani irin gurnani wanda amon shi ya karaษ—e ilahin dajin.
 
    Jin sautin gurnanin da ta yi ya shelantawa mutanen da ke yo hardi lallai koma minene a wajen to ษ—an ฦ™abilarsu ne, hakan ya saka suka soma yin tsalle suna gudu kamar wasu bururruka, sai tsallake bishiyu suke yi cike da ฦ™warewa.
   Ta yi tako ษ—aya biyu, uku, huษ—u ana biyar ษ—inne wata ฦ™ara ta ziyarce ta, a tattare da ฦ™arar kuma akwai wani huci me kama da zafin wuta.
   Yana saษ“e a kafaษ—arta ta durฦ™usa akan gwuyagunta ta durฦ™usar da kanta tana maimaita wasu kalamai, a kuma daidai lokacinne waษ—annan maharban suma suka iso wajen, irin yanda ta yi suma suka yi cike da ฦ™asฦ™antar da kai suka soma furta irin kalaman da ta ke furtawa suna yi suma ษ—aga hayyanensu sama.


Bayan wani lokaci.
Tafe su ke tun daga nesa sun yo gungun suna dogara mangan itatuwa suna dukan ฦ™asa da tsananin ฦ™arfi, duk inda suka gifta sai ฦ™asar ta amsa da ฦ™arar buga itatuwan da suke yi, yayinda suka lanฦ™wasa harsunansu ta sama laษ“ษ“ansu na ฦ™asa suna fitar da wani sauti wanda ya maida hankalin ilahirin jama'ar da ke yanki.
      A daidai wajen da al'ummar yankin suka tattaru manyansu da yara, a tsakiyarsu kuma wani baฦ™in mutum ne marar fasali da kyawun gani, kamar yanda sauran mutanen suke a jikunan su babu tufafi amma kuma sun zagaye ฦ™ugunansu da fatocin dabbobi, matayensu kuma suna ษ—aure da fata a ฦ™ugu da kuma saman ฦ™irjinsu inda sauran jikinsu ya ke a buษ—e, gasunan su sun ci ado da furanni yayinda wasunsu suka yi ado hannu da ฦ™afa da ฦ™ananun jijiyoyin itaciya.
   Mazan kuma kawunan wasunsu sanye da ฦ™ahunna wasu na ragon daji wasu kuma na Giwaye, damatsansu ษ—aษ—ษ—aure da wasu abubuwa dana gagara tantance ko minene.
      Wata irin magana suke yi wa junansu cikin wani yare dana gagara gane kan shi.
    Isowar mutanen wajen ษ—auke da wannan mutumin wanda suke yiwa kallon halitta ta daban a cikin su ya saka wajen yi tsit babu me magana.
    Kai tsaye suka aje shi kamar wani kaya a gaban wani baฦ™i jibgegen wanda ke zaune akan wata iriyar kujera da aka  yiwa ado da gwarangwal ษ—in kawunan Zakuna dana Damusoshi.

****
"Mtswwww aikin bamza ฦ™iba a kunne, ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta munafurcin banza da wofi kawai."
   Cewar wata farar mata data ci ado na gani na faษ—a ta hakimce akan lafiyayyar kujera tana taunar chewingum.

   Nan take sautin kukana ya tsaya, amma hawaye basu daina tseren gudu daga idanuwana suna bin kumatuna ba, yayinda maganar da ta yi ta sake soso raunin da ke zunda jini a zuciya ta, ban yi niyyar kulata ba amma kuma bana daga cikin mutane masu barin magana a ciki dan haka sai nima na ce da ita ina shesheฦ™ar kuka.
    "Malama ban kasa da ke ba banga dalilinki na ษ—auka ba, kiyi safgar gaban ki nima inyi tawa bana da lokacin ษ“atawa a  kanki ciwon rashin mijina kaษ—ai ya ishe ni ba sai kin ฦ™ara min da naki ba."
    Na faษ—a ina kallonta a hasale ina jin tsananin takaicin yanda sam bata nuna damuwa akan abin da ya faru da mu, hasalima sai nike gani kamar farinciki take da hakan.
    Kallona ta yi a ษ—age tana karkaษ—a ฦ™afa sannan ta kuma cewa.
   "Kyaji da shi yarinya dan za ki yi bayani yanzu babu jimawa bara dai su Hajja su ฦ™araso dole za ki faษ—i ฦ™ulla-ฦ™ullar da kika yi kika sace min miji, yau za ki gane kuren ki a gidannan da ni kike zancen."

Kalamanta sun yi tasiri matuฦ™a wajen ฦ™ara ta'azzara wutar tashin hankali haษ—e da tsoron da ke mamaye a ฦ™albina, har wani jirin tashin hankali nike ji na ษ—ibata daga zaune, yayinda zuciyata ta shiga hasaso min irin baฦ™in artabon da za'a tabka muddin su Hajja suka iske ni cikin gidanan, to amma kuma ai bani da wani zaษ“i dolene in tsaya ayita ta ฦ™are domin hakan shi ne masalaha a gare ni, to wai idan ma na fita na bar gidan ina zan je, bayan na gama tabbatar da yanzu duniya ta gama sanin abin da ke faruwa, bama wannan ba ฦ™arฦ™ari in ce zan tafi gidanmu, gidanda shiga ta cikin shi a tsakiyar wannan lokaci yake daidai da kai ni kushewa, cikin rasa abin yi na ษ—ora hannuna a kai na sake rushewa da wani sabon kukan.

    "Hehehe kya yi kya gama yarinya, ni ce ajalinki wallahi a cikin gidannan da ni kike zancen wallahi sai na koya maki darasin da ko harafin farko na sunana kika ji an ambata sai kon saki fitsari a wando."

    Juyawa na yi gaba ษ—aya na  ina kallonta, cikin sautin kuka na soma faษ—in.

 "Ki yi min rai, dan Allah ki yi min rai Yusra ki rufa min asiri ki barni inji da abin da ya dame ni, ba laifina bane, sam bani da laifi ko kaษ—an akan abubuwan da ke faruwa, ki taimake ni ki faษ—i gaskiya kar ki jaza min wani bala'in bayan wanda nike ciki dan Allah."
    Na ฦ™arashe ina dafa ฦ™afafuwanta da ke sanye cikin takalmi plat me kyau wanda ya hau da suturar jikinta.

    Sunkuyowa ta yi yana fuskanta ta yayinda ta maida fuskarta very serious sannan ta soma faษ—i tana kallon fuskata da hawaye da majina suka haษ—e min duna firgice.

    "Zan taimake ke in kuma rufa maki asiri in cire laifinkina cikin case ษ—in ษ“atan Alhaji Ahmad amma kuma sai idan kin yi min alฦ™awarin za ki cika min dadaษ—en burina da kika riga da kika sani, mudun kika amince to zan tabbatarwa su Hajja sam babu hannunki a ciki, domin kuwa ni kaษ—ai ce shaidar ki a yanzu, ni ce zan gaษ—i a yadda."
    Da wani irn sauri naja da baya ina soma girgiza kaina, ษ“acin ran kalamanta da kuma damuwar da nike ciki suka taka rawar gani wajen cunkushe zuciyata, yayinda wani malolo yayi min tsayuwar wata a maฦ™oshina, ina zunda hawaye na soma faษ—in.
    "Allah ya fiki Yusra tir da baฦ™ar aniyarki, na yadda kiyi nasara a kaina a wannan karon amma ki sani ba zan taษ“a aikata abin da kike so ba har gaba da abada."

Saka hannunta ษ—aya ta yi ta janyo yuwan hijabina a ฦ™asฦ™ance tana aika min da mummunan kallo ta ke faษ—in.

    "Bazan taษ“a saurara ma ki ba har sai kin amince da buฦ™atata, zan ci gaba da dangana ki akan DANGAR WUTA ina gana maki nau'o'in azaba har sai ke da kan ki kin amince min akan abin da nike da muradi, mu zuna mu gani ni da ke shege ka fasa." 
Ta hankaษ—a ni bayan ta gama faษ—in abin da ke ranta ta wuce har tana take hannuna ta barni nan a wulaฦ™ance.
      Sai da na ci kuka san raina har sai da idanuwana suka soma zafi haษ—i da ฦ™aiฦ™ayi sannan na tsagaita, a nan wajen barci ya kwashe ni cike da mafarkai akan mijina da ya ษ“ata yau kwana biyu.


     Hangame ฦ™aton get ษ—in aka yi wasu arnan motoci guda biyu shigo gidan, me gadi ya maida get ษ—in ya rufe yana tahowa da ษ—an gudun shi ya nufi motocin, ta gaban ya soma buษ—ewa murfi sannan ya koma ya buษ—e ta bayan kamar zai yi musu sujjuda tsabar sunkuyawa.

    Wata farar Datijuwa ce ta fito fuskarta sanye da glashi fari ta haษ—e gabas da yamma, ko bi takan Me gadin da ke ta faman gaishe da ita bata yi ba ta huce tana tunkarar cikin makeken gidan gadan-gadan, sauran mutanen da suke tare na take mata baya.

      Sauti ya ษ—auke shiru ya ratsa ko ina  babu ฦ™ara ko hayaniyar komi, da cikin wannan duhuwar me cike da ban tsoro ni ke iya ganin gasken ฦ™wayar idanuwansa da take jazur, kafin ya buษ—e waskeken hannunsa wani haske me shiga har can cikin kai ya bayyana tare da kore duhun, dubana na kai wajen da yake yi min nuni a zabure na miฦ™e tsaye da nufin in isa wajen sai de kash sarฦ™oฦ™in da aka ษ—aษ—ษ—aure hannaye da ฦ™afafuwana basu bani damar koda yin taฦ™i ษ—aya ba, cikin rasa abin yi na saki wata iriyar ฦ™ara me firgitarwa wacce ta karaษ—e ilahin filin da muke ciki, filinda sam bai yi min kama da duniyar mutane ba.

    Shurin da aka kaimin a karo na barkatai a gefe cikina ya saka na farka a razane duk na haษ—a gumi sai sambatu nike irin na wanda yayi magarki me firgitarwa.
  Na dawo nutsuwata ne sanda na ji dirar sautin muryar Hajja, nan take hantar cikina ta kaษ—a na soma ja da baya a firgice sam bana cikin nutsuwata.....โœ๐Ÿป
A nan zan ษ—isa aya ina fatan zaku kasance tare da ni domin lasar zumar daษ—in da labarinan ya ฦ™unsa, kudai ku biyo ni kawai dan jin yanda zata kaya.

Littafin Dangar wuta littafin kuษ—i ne, ki kasance tare da ni domin faษ—akantuwa gami da nishaษ—antuwa a cikin wannan zazzafan labarin me abin mamaki.

Ina fatan zaku taya ni yaษ—a wannan labarin a groups ษ—inku na whatsapp da facebook nagode sosai ni ce yaku har kullum.

MARYAM STAR ฦณAR BAIWA KUMA SARAUNIYAR JAJIRTATTU WRITER,S๐Ÿ’ชโœ๐Ÿป 

0912636748