BABI NA HUƊU
Tun bayan zuwan Malam Abubakar Gidado makarantar, Chioma ta fara lura da wasu halaye daga garesa wanda ba ta saba gani ba. A duk lokacin da aka yi hutun rana, maimakon ya shiga hirar banza ko ya yi zaman banza kamar wasu malamai, sai ta ga ya ɗauki ƙaramin tabarmarsa ya nufi wani wuri mai natsuwa a bayan ofishin malamai. A can yake yin alwala, sannan ya tsaya cikin nutsuwa yana gudanar da sallarsa. Wannan hali ya ba Chioma mamaki. Ba don bata ta taɓa ganin Musulmi ba, amma ba ta taɓa kusantar wanda yake bin addininsa da irin wannan tsari da natsuwa ba. Wata rana, bayan an tashi daga makaranta, ta tarar da shi yana zaune yana karanta wani littafi mai rubutun Larabci. "Sir..." Ya ɗago ya yi murmushi. "Chioma, ya karatu?" "Lafiya, sir." Ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "Sir... wannan wane littafi ne?" Abubakar ya kalli littafin da ke hannunsa. "Alƙur'ani ne." Chioma ta gyada kai. "Shi ne littafin Musulmi ko?" "Haka ne." Ta sake yin shiru na ɗan lokaci. "Sir... ina mamakin yadda kuke yin Ibada kullum ba tare da gajiyawa ba." Abubakar ya yi murmushi. "Idan mutum ya fahimci abin da yake yi, sallah ba nauyi ba ce. Hanya ce ta kusantar Allah." Kalaman suka shiga zuciyar Chioma. Tun daga wannan rana, duk lokacin da ta ga yana sallah, sai ta tsaya daga nesa tana kallonsa cikin mamaki. A hankali ta fara sha'awar sanin addinin Musulunci. Wata rana bayan an gama darasi, ta ce masa, "Sir... idan mutum yana son ya san wani abu game da Musulunci, me zai yi?" Abubakar ya ɗan yi tunani kafin ya amsa. "Abu na farko shi ne ya yi karatu, ya tambaya, ya bincika. Addini ba abin tilastawa ba ne. Dole mutum ya fahimce shi da kansa." "Za ka iya ba ni littafin da zan karanta?" "Zan nemo miki littafin da yake bayani cikin harshen turanci mai sauƙi." Bayan kwanaki biyu ya kawo mata ƙaramin littafi da ke bayani kan ginshiƙan Musulunci da kyawawan ɗabi'u. "Ki karanta. Idan akwai abin da ba ki fahimta ba, za ki iya tambayata." Chioma ta karɓa cikin girmamawa. Amma ta san cewa idan iyayenta suka ga littafin, za su yi mamaki. Saboda haka ta ɓoye shi a cikin littattafan makaranta. Da yamma, bayan ta gama ayyukan gida, sai ta shiga ɗakinta tana karanta littafin a hankali. Duk lokacin da ta gama wani shafi, sai ta yi tunani mai zurfi. A hankali zuciyarta ta fara jin wani irin natsuwa da ba ta taɓa ji ba. Domin ta sami damar yin tambayoyi ba tare da an hana ta ba, sai ta gaya wa iyayenta cewa makaranta ta shirya ƙarin darasi domin shirin jarabawar WAEC da NECO. Ifunanya ta ce, "To ki yi ƙoƙari sosai. Muna son ki ci jarabawa." Emeka ma ya amince. "Ki dawo gida da wuri kada ki riƙa yawo." A duk lokacin da ta je wajen Malam Abubakar, abin da suke yi shi ne tattaunawa kan abin da ta karanta da kuma amsa tambayoyinta game da Musulunci. Wani lokaci kuma idan ta buƙata, yakan nuna mata yadda ake furta haruffan Larabci domin ta fahimci abin da take karantawa. Abubakar kuwa kullum yana tuna mata da abu guda. "Ki tabbata duk abin da za ki yanke shawara a rayuwarki, ya kasance saboda kin gamsu da gaskiya, ba don wani mutum ba." Chioma kan gyada kai. Amma ba ta san cewa ɓoye wannan al'amari daga iyayenta zai iya haifar da manyan matsaloli a nan gaba ba.