ƘABILA

BABI NA ƊAYA

by @sadiyayusufishak133

Kauyen Ugwueme da ke Jihar Enugu ƙauye ne mai cike da tsaunuka masu korayen bishiyu, manyan bishiyoyi da ke ba da inuwa, da ƙananan rafuka masu tsaftataccen ruwa. Da sassafe ana jin ƙarar zakaru suna cara, yayin da hayaƙin girkin itace ke tashi daga gidajen laka da aka yi wa rufin kwano. Mutanen ƙauyen mutane ne masu son zaman lafiya, masu girmama al'ada da mutunta na gaba. Kowa ya san kowa, kuma farin ciki ko baƙin cikin mutum na zama na al'umma baki ɗaya. A wannan ƙauye ne aka haifi Chioma Emeka, yarinya mai nutsuwa, biyayya da son taimakon iyayenta. Tun tana ƙarama ta saba da wahalar rayuwar ƙauye. Duk da haka, ba ta taɓa yin korafi ba, domin ta taso tana ganin rayuwa haka take. Mahaifinta, Emeka, manomi ne mai ƙwazo. Kullum tun kafin fitowar rana yake fita gona da fartanya a kafaɗarsa. Duk abin da ya samu daga noman rogo, doya da masara shi ne yake ciyar da iyalinsa. Mahaifiyarta kuwa, Ifunanya, mace ce mai haƙuri da tausayi. Bayan kula da gida, tana sayar da kayan miya a kasuwar ƙauye domin ƙara wa mijinta taimako. Su biyar ne 'ya'yan gidan. Babban yayan Chioma shi ne Chikanso, wanda ya fi kowa ɗaukar nauyin taimaka wa mahaifinsu a gona. Sai Chioma, sannan ƙannenta uku: Peter, Paul, da ƙaramin cikinsu Philimon, wanda kullum yake sa gidan dariya saboda shagwaɓarsa. Ko da yake ba su da dukiya, amm gidan cike yake da ƙauna. Da sassafe kafin hasken rana ya mamaye ƙauyen, Ifunanya kan tashe su. "Chioma, tashi ki je ki debo ruwa kafin mutane su cika rijiyar." Ba tare da gardama ba, Chioma kan ɗauki bokiti ta nufi rijiyar ƙauyen tare da sauran 'yan mata. Daga nan sai su dawo su share harabar gida, su wanke kwanukan da aka yi amfani da su da dare, sannan su shirya zuwa makaranta. Makarantar gwamnati ce da ke da tazarar kusan mintuna talatin daga gidansu. Duk safiya sukan yi tafiya a ƙafa suna hira da dariya. Duk da cewa takalmanta sun tsufa, kuma jakar makaranta ta fara yagewa, Chioma ba ta taɓa jin kunya ba. Burinta shi ne ta yi karatu sosai ta fito daga talaucin da ya dabaibaye iyalinsu. Malamai suna son ta saboda hazakarta. Sau da yawa idan aka yi jarabawa, sunanta yana cikin na farko. Mahaifinta kan ce mata, "Chioma, ilimi shi ne gadon da zan iya bar miki. Ba ni da kuɗi, amma ina da addu'ar Allah Ya sa ki zama abin alfaharinmu." Kowace rana idan ta ji waɗannan kalamai, sai zuciyarta ta cika da ƙwarin gwiwa. Ta yi alkawarin cewa wata rana za ta canja rayuwar iyayenta. Rayuwa ta ci gaba cikin kwanciyar hankali. Bukukuwan gargajiya, shagulgulan aure, da lokutan girbi suna ƙara wa ƙauyen armashi. Babu wanda ya yi tunanin wata guguwa na shirin sauka a rayuwar wannan iyali. A lokacin ina aji biyar na sakandare, shekaruna ba su wuce goma sha shida ba. Burina kawai shi ne in gama makaranta cikin nasara, in ci gaba da karatu a jami'a, sannan in taimaki iyayena su huta daga wahalar rayuwa. Sai dai ban san cewa ƙaddara ta riga ta rubuta wani shafi daban ba a cikin rayuwata. Wata rana, wani al'amari ya faru da ni—al'amarin da ya sauya rayuwata gaba ɗaya. A cikin lokaci kaɗan, farin cikin da nake ciki ya rikide ya zama tsoro, hawaye da ruɗani. Na tsinci kaina cikin wata irin jarabawa da ban taɓa tsammanin zan fuskanta ba. Tun daga wannan rana ne rayuwata ta ɗauki wata sabuwar hanya... hanyar da ta cika da sirrika, ƙalubale da raunukan da ba sa saurin warkewa.