Miji goma(ba uba goma ba ne)

Chapter 10

by @sadiyaabdulrazak954

PAGE 10


***


      Hamza sai ya bushi iskarsa yake leƙowa gidan har aka yi arba'in ɗin Al'ameen, ga wani raini da ya yiwa Uwani, saboda yawan roƙon shi da take yi, da yadda take raina ƙoƙarin shi, har wani kallon gani-gani yake yi mata idan ya je gidan. Uwani tana sane ta ce Maryam arba'in biyu za ta yi, saboda ta dinga ja masa rai har ya gaji auren ya sire masa, ba ta san kamar an zuga zugagge ba ne, don shi ma ba son ci gaba da zaman yake yi ba, Baba da ya yunƙuro a kan sai ta koma ɗakinta Uwani ta sanar masa ba ta da lafiya fa, ɗinkin da aka yi mata sanadin haihuwar nan bai warke ba, kuma likitocin sun yi gargaɗi da kakkaurar murya a kan kar ta koma sai bayan wata uku, su kuwa yaran zamani masu do a tsakar ka idan ta koma sai dai komai ya faru, don haka Baban ya ƙyale su ya zuba ido.

 Watanta biyu a gida Hamza ya zo da daddare, sun gaisa yake cewa"Maryam yaushe za ki koma ne? Sannan ina ga fa sai dai ki koma gidanmu da zama..."

Ta katse shi da faɗin"Ban gane ba!".

Ya ce"Ai ganar da ke nake yi".

Ya ce"Kin ga dama kuɗin hayar ya ƙare, kuma ni ba ni da kuɗin da zan sake biya, sannan ma ina son tafiya wata ƙasar neman kuɗi, ana kan yi mini hanya, kuma ko ba wannan ba ni dama fa a zamanmu haƙuri kawai nake yi da ke, saboda tsakani da Allah ba ki da kunya, ba ki da tarbiyya ba ki san girmana ba a matsayina na mijinki".

Maryam ta yi mamaki sosai, don ko da wasa ba ta taɓa tunanin gidan nan ba na shi ba ne, sanda yana neman aurenta ya ce mata na shi ne ya gina tun da jimawa sai ya saka ƴan haya a ciki, yanzu ya tashe su tun da ya yi aure, ta ce"Hamza idan za ka kore ni ba sai ka yi mini ƙarya da gida ba naka ba ne, idan ka yi haƙuri dama ni ma wannan zaman da nake yi ba ni da niyyar komawa, saboda haka ka sallame ni kafin ka tafi inda za ka je".

Ya ce"Wallahi ba gidana ba ne, ki tambaya ki ji, kuma sannan ni fa ba ni da manufar rabuwa da ke, sai dai idan ke ce kika zaɓi hakan".

Ta ce"E ni ce na zaɓa ɗin, ka sake ni".

Ya ce"To gobe zan aiko miki saƙo".

Ya tashi ya fice, a tsakar gida ya samu Uwani zaune, ta ce"Ka fito?"

Ko kallonta bai yi ba ya yi dogon tsaki ya fice.

Ta shiga ɗakin dafe da ƙirji tana cewa"Na shiga uku ni Uwani, Maryam me zan gani? Mijinki ne yau ya yi mini tsaki, a gobe kuma sai duka, wallahi saura zagi da duka, Maryam wa kika kwaso mana ne haka?"

 Jin shigowar saƙo wayarta ya sa ba ta kula Uwani ba, tana dubawa ta ga daga shi ne, ya rubuto mata ya sake ta saki ɗaya, ta nunawa Uwani wayar ba ta ce komai ba, ta ce"To rubutu nake gani, kuma kin san ni ba iya karatu na yi ba, na mene ne?"

Ta ce"Shi ne ya turo mini saƙo wai ya sake ni saki ɗaya".

Uwani ta sauke ajiyar zuciya ta ce"To Alhamdulillah! Tsaki da ya yi mini kuma ya je don kansa, tun da dai ya sallame ki ni ya biya ni!"

Ta zauna tana cewa"Maryam ki kwantar da hankalinki, wannan ba komai ba ne, in sha Allah nan gaba za ki samu miji na kere sa'a, wanda za mu yi alfahari da aurenki".

Maryam ta ce"Allah Ya sa".

 Bayan kwana uku da sakin sai ga babar shi ta zo gidan, Uwani ta yi kicin-kicin ta tarbe ta a tsiyace, saboda kar ma ta yi zancen kome, irin yadda take amsa mata gaisuwa a daƙile kamar mai gyambo a maƙoshi har Maryam ɗin sai da ta ji babu daɗi, saboda ta zauna da matar lafiya ba ta da wata matsala, babar Hamza ta ce"Ashe haka abu ya faru, ɗan yau dai ka haife shi ba ka haifi halinsa ba, wallahi Hamza bai yi shawara da ni ba ya yanke hukunci, don Allah ku yi haƙuri".

Uwani ta ce"Ai ba komai ba ne a wajenmu, duk wanda ya rasa Maryam shi ke da asara, don haka shi za ki bawa haƙuri".

Ta ce"Ai kuwa ba a ce ba komai ba ne, aure irin wannan da albarkarsa har an fara samun rabo..."

Uwani ta katse ta da faɗin"Cewa za ki yi har an samu rabo, idan kika ce an fara da saura kenan za a ci gaba, kin ga mun gode amma don girman Allah ki ƙyale yaron nan sa hukunci shi, don ba a yi wa yaran zamani dole".

Ta ce"Haka ne, to Allah Ya rufa asiri".

Uwani ta gyara zama ta ce"Dama ai jira nake a cika sati na ga ƙarshen abun, da ba ki zo ba dama zan zo".

Babar Hamza ta ce"To lafiya dai ko?"

Uwani ta ce"Ƙalau, dama a kan wannan yaron ne, na ce ya za a yi da shi? Za ki karɓa ne ko kuwa biya za ku dinga yi tana shayar muku da shi?"

Ta ce"A haba dai ga uwarsa a raye ai bai kamata a raba shi da nonon uwa ba, sai a dinga ba ta wani abun".

Ta ce"To nawa za ku na badawa? Kin ga bayan shayarwa ma a kwai omo, sabulu, famfas kafin kuma ya fara cin abinci".

Maryam da duk matar ta ba ta tausayi ta ce"To babarmu ai ba sai an wani tsadance ba, ko me suka kawo Allah Ya saka masa albarka, ni ma fa ɗana ne".

Uwani ta galla mata harara, ita dai ta yi musu sallama ta tafi, ta ce gobe za ta dawo idan suka yi magana da Hamza.

 Tun daga nan duk sati biyu sai babar Hamza ta zo ta gansu, wataran kuma ta tiso shi a gaba su zo tare, su ba su kuɗin shayarwa. Babu laifi Maryam ta samu kulawa sosai a wajen Uwani, yanzu hankalinta a kwance yake tana ra rainon ɗanta da yake ta ƙara girma da wayo. Al'amin yana da wata biyar ta ce za ta fara bussiness da kuɗin da ta siyar da kayan ɗakinta, Uwani ta so daƙile ta, ta nuna mata wannan fa duk cake ne ba samun ciniki ake ba, har gara ma siyar da abincin, ita kuma Maryam ta ga ya za a yi ta sana'ar abinci da ƙaramin ɗa, to da yake Uwanin ta san idan Maryam ɗin ta coge ba a iya ture ta sai ta rabu da ita, ita take zuwa kasuwa da kanta tana yo sarin abubuwa iri-iri, ta tallata a maƙota da kuma status kuma Alhamdulillah Allah sai Ya sakawa abun albarka, Uwani tana kallo take ƙirga ribarta tana adanawa.

 Da ta yaye Al'amin sai ta daina zuwa kasuwar da shi, ta fara ɗaukar wanka don shirin fara zawarci, ai kuwa zawarawan suka fara layi, tana ta cafke musu ƴan canji,domin ta koyi roƙo sosai, idan ma kai faƙiri ne ko marowaci soyayyarku da Maryam ba ta taɓa yin ƙarko, bani-bani ne zai kore ka, idan gari ya waye dare ya yi ba su ci kaza ko balangu ba ita da Uwani to sai dai idan ita ce ba ta so ba, ma'ana idan ba ta bawa kowa damar zuwa ba, amma muddin ka ce ga ka nan tafe to za ta lissafo maka abin da za ka taho da shi, ai kuwa har wata ƙiba ta fara yi, ta yi kyau abunta.

Ba ta tsayar da mijin ba, tana ta tantancewa dai, yayin da ƴan'uwanta ƴaƴan Uwani suke yawan yi mata nasiha kan auren shi ne rufin asirinta, idan a gaban Uwani ne kuwa nan za ta hayayyaƙo tana cewa su ba su san ƙaddara ba? Ai ita Maryam ƙaddararta kenan, shi ma Baba ya fara matsa mata, don haka ta tsayar da wani Nasuru, a kasuwa suka haɗu, ya faɗa mata ya taɓa yin aure ƴaƴansa biyu suka rabu da matar, Nasuru ba shi da rowa, sosai yake sakar mata kuɗi, kuma ba shi da wata makusa a halitta, ta ji tana son shi za ta iya auren shi, don haka ta ba shi dama ya turo bayan ta gama shirinta.

 A wannan karon wata biyu aka saka, aka ɗaura aure, aka mayar da Al'amin wajen babar Hamza ta ci gaba da kula da shi, a wannan karon Uwani ta san babu buƙatar yiwa ƴar tata wata huɗuba domin ta riga ta haddace karatunta, musamman ma a wannan zawarcin da ta yi ta ƙara samun gogewa ta rayuwa, don haka hankalinta kwance yake, ta san yadda ta tafi haka za ta dawo.

 An kai amarya lafiya, zamansu da Nasuru lafiya ƙalau babu wata matsala daga farko, haka kuma shi yana son haihuwa ba kamar Hamza ba, don da ta samu ciki ya nuna mata kulawa sosai, bai taɓa nuna ƙosawa da yanayin laulayinta ba. Yaran shi suna zuwa gidan, wani lokacin ma har su kwana biyu idan sun zo ranar Juma'a sai ya mayar da su ranar Asabar, a yadda ta lura da alamunsa yana son yaran su zauna a wajenta, ita ma kuma ba ta ɗauki hakan a komai ba, tun da ba ƙananu ba ne sosai ballantana ta ce za ta ci kashinsu da fitsari, babban shekararaa tara, sai ƙanwarsa shekararta baƙwai, to da yake komai na gidan aurenta a tafin hannun Uwani yake ita ce ta nuna mata sam kar ta sake ta riƙe masa ƴaƴa, ɗan kishiya ruƙon mai haƙuri ne, ta zuga ta a kan idan ta haihu tana kallo zai yi ta fifita yaran a kan wanda za ta haifa, saboda an fi marmarin ɗan fari, haka dai ta harhaɗa mata raunana hujjoji marasa tushe bare makama, sai ta hau kai ta zauna ta fara baya-baya da yaran.

 Nasuru ɗan kasuwa ne, dole ba zai rabu da mata a waya ba, musamman yanzu da kasuwancin ya koma na online, sannan da daddare ne yake samun damar zama ya nutsu ya duba saƙƙonnin da bai duba ba, sannan ya yi ta saka hotunan kaya a groups ɗin shi, ita kuma Maryam wannan karkata da yake yi a kan waya yana mugun ba ta haushi, ko kuma ta ga wata ta kira shi suna magana, duk da ga shi a zahiri tana ji zancen kaya ake yi, amma sai ta yi ta yi masa tijara tana cewa ƙarya yake yi alaye yake yi mata, kurman baƙi ne kawai suke yi saboda a gabanta ne, kuma da fari ba haka take yi ba, ta yarda da shi sosai, nan ma Uwani ce ta zuga ta ta ɗora ta a keken ɓera ta ce duk ƙarya ce, dama ƴan kasuwa ba a isa a raba su da mata ba, ga su da watsewa da masu abinci, har da cewa Allah Ya sa ma bai ɗebo mata alaƙaƙai ba.

Tun daga ranar da Maryam ta ji haka shikenan ta kasa zaune ta kasa tsaye a gidan aure, ta matsewa Nasuru lamba take tuhumarsa babu dare babu rana, dayake yana sonta haka yake ba ta hujjojin kare kansa, daga ƙarshe ma ta ce munafurci ne yasa yake saka password a waya dole sai ya cire, kuma ta cire ɗin saboda a zauna lafiya, don haka ta samu damar bincikar wayarsa kullum, tsakar dare za ta tashi ta ɗauki wayar ta fice falo ta yi ta bincikenta, yana kallonta amma bai damu ba tun da ya san babu komai ba rashin gaskiya da za ta gani.

 Ana haka ne ya sayi wata waya sakan a wajen abokinsa, ya ɗora wani daga cikin layinsa a kai, da yamma ya karɓi wayar bai ma duba ya ga mene ne a ciki ba, ashe da fina-finan batsa kala-kala, ta ɗauki wayar ta duba ta gani, shi ne ta tashe shi tsakar dare suka yi tijara har ya sake ta, tana ganin ba komai ba ne don aurenta ya mutu, sai kuma ta dawo a ranar ta san matsayinta da gadar kwalin da Uwani ta sakawa rayuwarta ta hau kai ta kwanta a rashin sani.


 Wannan shi ne abin da ya faru a baya, yanzu za a ci gaba da labari.


***