Page 2
by @zeeykumurya
*BARA A KUFAI*
*Zeey Kumurya*
2.
JURAIJ
Kaiwa da komowa kawai yake a cikin ƙaton bedroom ɗinsa cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, lokaci ɗaya ya zauna a bakin gado kamar wanda aka tsikara tare da ɗaukar wayarsa da ya yasar ya latsa ya ƙura mata ido, gabaɗaya fuskarsa ta sauya, jijiyoyin kansa sun fito raɗa-raɗa, a hankali ya sauke numfashi tare da lumshe idanunsa da suka yi ja, yana jin yadda zafin wutar da ke ci a zuciyarsa yake karaɗe ko'ina na jikinsa.
A razane Ramlah da ke kwance tana kallon shi da idanunta da ke cike da bacci ta tashi zaune, idanunta duka a waje ta ƙarasa kusa da shi tare da dafa kafaɗarsa, saboda gigicewar ganin yanayinsa bakinta har rawa yake gurin furta. "Man! Mine! Me ya faru? Me aka ce maka a wayar da assusuban nan na ga jikinka yana ta tsuma haka?" Bai ba ta amsa ba sai idanunsa da ya buɗe ya zuba mata, yanayin yadda ta ga idanunsa ya sa ta saurin ja baya a firgice tare da furta. "Innalillahiwa'inna'ilaihi raji'un!" A sukwane ya miƙe ya fara tafiya ba tare da ya amsa mata ko ɗaya daga cikin tambayoyinta ba, ta bi shi da kallo tare da sauraren takunsa da yake amsawa a duk ɗaga ƙafa da direnta da yake yi, dafe kai kawai ta yi cikin kaɗuwar rashin sanin damuwar mijin nata.
Zuciyarsa a cunkushe ya fito parkour ya haura sama, direct ɗakin Daddy ya nufa ya buɗe ya shiga.
Yana nan a kwance a miƙe samɓal tamkar gawa kamar kullum da kodayaushe, wani irin faɗuwa gabansa ya yi, bai san ya aka yi ba sai tsintar kansa kawai ya yi a bakin gadon da Daddy yake kai, jikinsa na tsuma ya kai hannu daidai saitin hancin Daddy, ƙaƙƙafar ajiyar zuciya ya sauke tare da zamewa ya zauna. Azkar ɗin safe ya fara karantawa a hankali yana tofawa a fuskar Daddyn, bayan ya ida ya ɗora hannunsa a kan goshin Daddy, murya a karye ya ce. "Allah ya ba ka lafiya ya nuna mini ranar da zan ga ka miƙe kana tafiya da ƙafafunka." Daga haka ya miƙe ya gyara masa kansa sannan ya fice daga ɗakin a hanzarce.
A bakin steps ya tarar da Ramlah a tsaye tana kallon inda zai ɓullo, kamar za ta kifa haka ta fara taka matattakalar tana faɗin. "Me ya samu Daddy? Ba dai jikin nasa ba ne ko?" Ta ƙarashe maganar tana hawaye.
Cike da kulawa ya kama hannunta ya ce. "Babu abin da ya same shi, yana nan a raye kamar yadda yake." Dogon numfashi ta sauke ta ce. "Alhamdulillah! Ubangiji ya tashi kafaɗunsa, amma har hankalina ya tashi ganin yanayinka, I thought wani abun ne ya same shi." Girgiza mata kai kawai ya yi.
"To me ya faru My na gan ka a haka? Ka san bana son abin da zai taɓa mini kai ko kaɗan? Bana ƙaunar ganin damuwa daidai da ƙwayar zarrah a kan fuskarka."
Sai da ya zagaye ta ya sauka daga kan steps ɗin gabaɗaya sannan ya ce. "Damuwa da numfashina a yanzu sun zamo manyan amininai, saboda dalilai masu tarin yawa da kika sani da kuma ciwon Daddy." Ya dakata daga tafiyar da yake ya juyo ya fuskance ta, fuska babu walwala ya ci gaba da faɗin. "Kin taɓa ganin kifin da aka ciro shi daga cikin ruwa ya ci gaba da rayuwa?" Ta girgiza masa kai a hankali, ya ce. "To tamkar haka lafiyar Daddy da farincikin rayuwata suke, idan kin ga na koma kamar yadda kike so to na ga Daddy ya fara takawa da ƙafafunsa, sannan kuma na cika burina akan abin da nake son cimmawa." A raunane ta ce. "Da yardar Allah Daddy zai warke ragal, burikanka ma gabaɗaya za su cika." Idanunsa da suka yi masa nauyi kawai ya lumshe ya ci gaba da tafiya. Da sauri ta bi bayansa har tana tuntuɓe.
**** ****
AHAYAN
Durƙushe take a bakin rijiya tana kuka mara sauti, jikinta sai karkarwa yake saboda sanyin da yake ratsa ta na ruwan da Umma Lantana ta kwara mata a jiki, saboda takaicin ba ta yi nasarar cilla ta cikin rijiyar ba kamar yadda ta so.
"Amma dai Lantana kin yi asara kin kuma cika mahaukaciya, haka kawai ki kama ki hankaɗa yarinya cikin rijiya, idan da tsautsayi ya sa ta faɗa ta mutu sai ki yi yaya kuma?"
Baba da ya fito daga ɗakinsa a guje yana saɓa babbar riga ya faɗa a fusace kamar zai kai wa Umma Lantana duka.
Tsaki ta ja ta ce. "To sai me don ta faɗa ta mutu? Ka fi kowa sanin ba ta da gatan da za a bi ta kan gawar tata ma bare a ba da bayanin yadda aka yi ta mutun, idan na kashe ta na kashe banza, kuma ko ba komai an rage mugun iri ai." Baba ya kufula ya ce. "To shikenan tunda haka kika ce, don Allah ki gwada ki gani idan za a bar ki da ranki, kar ki fasa, mahaukaciyar banza da wofi kawai wadda ba ta san abin da take ba!" Inno ta saki murmushi cikin jin daɗin yadda yayan nata yake wanke Umma Lantana a gaban yaran gidan da ihun Ahayan ya fito da su tsakar gidan. Kamar Umma Lantana za ta yi kuka ta ce. "Yanzu ni kake kira da mahaukaciya Malam saboda wannan agolar?"
"Ba saboda ita ba ne kawai, har da ja'injar da kika yi da Zulai, kuma na sha faɗa miki duk abin da ta ce shi za a dinga yi a gidan nan, amma saboda kunnen ƙashi ne da ke kin ƙi ji."
"Ba zai yiwu ba ne shi ya sa na ƙi ji, ba yadda za a yi ina matar wanta a ce sai abin ta shimfiɗa zan bi, wallahi ba ta isa ba, ta yi kaɗan!"
Ta ƙarashe maganar tana zullo kamar za ta kai masa duka.
Inno ta yi ƙasaitaccen murmushi ta dubi Baba ta ce. "Rabu da ita Baban Zeenat, ita ce za ta wahala ai ba ni ba, don wallahi za ta janyo na cire hannuna a komai na gidan nan ne, sai na ga a inda za ta dinga samun abin da za ta ci har ta samu energyn yi mini haukan da take." Da sauri Baba ya ce. "A'a ba ma za a yi haka ba."
"Ke Lantana ba za ki ɓallo mini ruwa ina zaman zamana ba, saboda haka biyayya ga umarnin Zulai ya zama wajibi a gare ki, tilas ne wannan, idan kuma ba haka ba na tattara ki ke da tsumman ƙazamin jikin ku bar mini gida."
Daga haka ya juya ya koma ɗakinsa a fusace, Umma Lantana ta rasa abin faɗa saboda tsabar takaici da baƙinciki, Inno ta saki siririyar dariya cikin shaƙiyanci tana karkaɗa awarwaron hannunta yana bayar da sauti.
"Dole ne a yi mini biyayya idan ana son a ci gaba da zama ana shan jar miya."
Harara kawai Umma Lantana ta iya zabga wa Inno tare da jan ƙwafa, Zeenat ta ja hannunta a zuciye suka koma ɗaki. Inno ma ɗaki suka koma ita 'yarta Husnah bayan ta zabga wa Ahayan mugun kallo. Ummi da ke tsaye a bakin ƙofar ɗakin Umma ta taɓe baki ta ja hannun Raudah suka koma ɗakin.
Ba tare da wani ya rarrashe ta ba ta goge hawayen fuskarta da hannunta ta miƙe ta janyo ruwa ta cika wa Inno bakitin kamar yadda ta saka ta, ta ɗauka ta kai mata har kusa da ƙofar ɗakinta, sannan ta dawo ta tsugunna ta ƙarasa wankin tukunyar da ta fara.
Tana ajiye tukunyar a ƙofar ɗakin Umma Laraba inda kwarfetonta yake ta ji kamar ana kallon ta, a hankali ta ɗaga kanta, gabanta ne ya yi mummunar faɗuwa lokacin da idanunta suka sauka a cikin nasa, saurin yin ƙasa da kanta ta yi tare da neman tsarin Allah a cikin ranta.
Kallon da ya saba bin ta da shi kamar sabon maye shi yake wulla mata a yanzu ma, muryarta na rawa saboda tsoro ta gaishe shi, da kai kawai ya amsa mata ya shige ɗakin Inno yana waigen ta.
Zeenat na duban Umma Lantana cikin damuwa ta ce. "Na sha faɗa miki Umma ki daina biye wa Inno tana saka Baba yana wulaƙanta ki a gidan nan amma kin ƙi ji, yanzu mene ne amfanin wannan zagin da kika janyo ya yi miki? Kuma abin da kika so ɗin dai bai samu ba."
"Abin ne da ciwo Zeenat, akwai tarin baƙinciki kuna rayuwa gida ɗaya da mace amma ta fi ka arziƙi da izza a gidan, abin takaicin ma wai ƙanwar mijinka."
Umma Lantana ta faɗa kamar za ta yi kuka.
"Ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa Umma, ba dai duk saboda 'yarta tana auren mai kuɗi ba ne? To in sha Allahu rabbi sai na auri wanda ya fi mijin Aunty Laure komai da komai, ai ba wata uwar ta fi mu ba."
Umma Laraba ta yi ƙasa da murya ta ce. "Shi ya sa nake son wanda Babanku ya ce zai zo ya zaɓi mata a gidan nan ya zaɓe ki, saboda na ji yana faɗawa ita uwar jin kan ba ƙaramin hamshaƙi ba ne." Da sauri Zeenat ta ce. "Ni zai ma zaɓa Umma, kar ma ki ɗaga zancen, ba dai kin ce malamin nan ya ce kina kawo kuɗin da ya buƙata zai yi mana aikin ba? To yanzu zan shirya na je gidansu Furera na ranto miki kuɗin, can ma zan fara zuwa kafin na je makarantar."
"Yawwa 'yar albarka, 'ya ɗaya tamkar da dubu, ni na san ban yi haihuwar asara ba da ma, na san sai kin share mini duk wani hawayena."
Zeenat ta ce. "Wannan rubutu ne akan dutse Ummata, bari na yi maza na shirya." Umma Lantana ta miƙe tana faɗin. "Ni ma bari na leƙa idan yarinyar can ta hura wutar na ɗora miki ruwan shayin, ki samu ki karya kafin ki fita." Zeenat ta ce. "To farar Uwata." Murmushi Umma Lantana ta yi ta fice daga ɗakin.
Sai da goma na rana ta wuce sannan ta kammala wankin, a matuƙar gajiye ta yi shanya saboda yunwa da ke nuƙurƙusar hanjin cikinta, jikinta babu ƙwari ta tattare gurin ta shige ɗakinsu.
A kwance ta tarar da Umma ta yi nisa a cikin tunanin da take, jiki a sanyaye ta tsugunna a gabanta ta ce. "Sannu da hutawa Umma." Kallon tsaf Umma ta yi mata sannan ta sauke numfashi ta ce. "Kin gama wankin duka?" Kai ta gyaɗa a hankali.
"Umma kina cikin gidan nan kuma idanunki biyu amma kina ji za a cilla ni rijiya ko fitowa ki duba ni ba ki yi ba bare ki tsawatar?"
"Ahayan ba ni da zaɓi sama da na abin da na yi, dole fa sai kin yi haƙuri a zaman gidan nan, na samu an kara ki ana riƙe min ke idan ban yi biyayya ba ya zan yi? In kuma so kike na yi magana a kore mu to, tunda ke kin fi son a yi ta maimaita magana ɗaya."
Hawayen da suka zubo mata ta share ta ce. "Amma Umma maganar kisa fa ake, da na faɗa rijiyar nan wallahi mutuwa zan yi." A fusace Umma ta ce. "Idan kin mutu Allah ya ji ƙan ki, amma dai duk abin da Zulai da Lantana za su yi miki a gidan nan ba zan taɓa magana ba, saboda ina son zama ban shirya yankar ticket ɗin zawarci da wahala ba, ke idan kin ga ba za ki iya zama ba ƙofa a buɗe take sai ki nemi wani gurin ki koma." Kallon Umma ta yi cike da rauni hawaye na tsere a kuncinta, tana jin yadda har yanzu zuciyarta ba ta daina bugawa ba na tsoratar da ta yi ɗazu ba, rijiya fa? Rijiyar ma irin tasu mai zurfi da ke cike da ruwa, amma shi ne Umma za ta ce ta yi haƙuri saboda kawai kar Baba ya sake ta? Ta san har da rashin maganar Umman yake saka su Umma Lantana yi mata kowanne irin cin kashi.
"Ba tsare ni za ki yi da ido ba, duka zan ji a jikina kawai kin rufe ni da shi, shi ne zan san kin fusata."
"Allah ya ba ki haƙuri."
Ta faɗa da rawar murya tare da yin ƙasa da kanta.
Kamar daga sama suka juyo Baba yana zabga sababi a tsakar gida, da sauri suka miƙe a tare suka leƙa.
Sabira ƴar autar Umma ce a hannunsa ya murɗe mata kunne, tana ta kuka da son ya sake ta amma ya ƙi.
"Sato kuɗin nake ko kuma haƙowa nake da za ku ishe ni da bani-bani? Yaushe na biya kuɗin makarantar da har za ki zo ki ce mini an koro ki? Shegiyar yarinya da ta yi gadon annamimanci a gurin uwarta, to ba zan bayar ba, daga yau ma kar ƙi ƙara zuwa makarantar tunda macuta ne kuma ɓarayi." Ya ƙarashe maganar tare da yin cilli da ita ta faɗi a ƙasa, tsawa ya buga mata akan ta yi shiru ko ya zane ta sannan ya koma ɗakinsa yana muzurai.
Da sauri Ahayan ta je ta rungume ta a jikinta tana rarrashinta, ko tari Umma ba ta yi ba ta juya ta koma ɗaki, Inno da Umma Lantana da ma ko leƙowa ba su yi ba tunda ba ɗansu ake duka ba, Ahayan ta bi ta da kallo zuciyarta a cunkushe da wani irin abu mai zafi.
"Aunty Ahayan ina son makaranta, ina son na zama likita, don Allah kar ki bari Baba ya cire ni."
"In sha Allah za ki yi karatu har sai kin cika burinki, ki yi haƙuri ni zan samo kudi na biya miki school fees ɗin da yardar Allah, tashi mu je ki ci abinci." Ta ƙarashe maganar tare da kama hannunta suka koma ɗakin Umma, ta tambaye ta abin kari ta ce Baba bai bayar ba ya ce ba shi da kuɗi, sai dai ta kai wankin da ta yi jiya da yamma gidan masu shi ta karɓo kuɗin sai ta siyo abin karin da shi.
Har Baba ya fita daga gidan bai daina banbamin faɗan kuɗin makarantar da Sabira ta tambaya ba, Umma na ta ba shi haƙuri kamar za ta yi kuka.
Yana fita ya ga wani maƙocinsu a tsaye a ƙofar gida yana jiran shi, bayan sun gaisa mutumin ya risina ya ce. "Alhaji taimakon dai da ka saba shi na ƙara zuwa a taimaka a yi mana, na tashi babu ko sisi ga gida ba abinci, yara ko makaranta ba su je ba." Da sauri Baba ya ce. "Kayya! Abu bai yi kyau ba, har ta kai yara su ƙi zuwa makaranta?" Mutumin ya ƙara rusinawa ya ce. "Wallahi Alhaji, shi ya sa ma na kasa haƙuri na zo na same ka ko za a yi abin da aka saba." Cike da alfahari Baba ya zura hannu a aljihu ya ɗauko kuɗi ya ba shi, sai da mutumin ya tsugunna sannan ya karɓa yana ta zabga godiya kamar zai ari baki.
******
JURAIJ
Tsaye yake a gaban mudubi yana ƙarasa shiryawa, har lokacin yanayin tsantsar ɓacin ran da yake ciki da damuwa bai bar fuskarsa ba.
A hankali Ramla take tafiya cikin yanga ta ƙarasa inda yake tsaye yana ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa. Tsayawa ta yi a kusa da shi fuskarta ɗauke da yalwataccen murmushi tana ƙare masa kallo.
"Good morning my Man."
Ta faɗa tana ɗaukar turaren da ya buɗe ta fara fesa masa a jiki.
"Morning."
Ya faɗa a taƙaice ba yabo ba fallasa.
"Ka yi kyau sosai Hubby!"
Ya yi mata murmushi kaɗan kamar mai rowarsa.
"Ba za ka yi breakfast ba ne wai na ga kana ta sauri da sassafen nan?"
Hannunta ya kama cikin kulawa ya ce. "Na faɗa miki ina nan ne kawai amma hankalina gabaɗaya ba ya tare da ni." Rausayar da kai ta yi ta ce shikenan, amma bari na haɗa maka kafin ka sauko daga gurin Daddy, idan ka je office ɗin ka samu nutsuwa sai ka ci." Ya gyaɗa mata kai kawai don ba ya son doguwar magana, ya san halinta ita kuma ba za ta taɓa ƙyale shi da batun abincin nan ba idan bai bi yadda take so ba. Zare hannunta ta yi daga nasa ta fice daga ɗakin. Mintuna biyu ya ƙara ya bi bayanta shi ma. A dinning area ya hango ta ita da wata dattijuwa mai aikin gidan, kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kai ya haura sama.
"Wai ke don Allah wacce irin dabbar mata ce? Sau nawa zan faɗa miki da zarar kin ga mijina ki dinga gaggawar barin gurin ki tafi inda kika san ba zai gan ki ba?"
Da rawar jiki Dattijuwar ta rusuna ta ce. "Don Allah Hajiya ki yi haƙuri, wallahi ban lura da shi ba ne, ban san ma ya fito ba sai yanzu da kika yi magana."
Ƙwafa Ramlah ta ja ta wurga mata murfin flaks ɗin da yake hannunta ta ce. "Munafukar banza kawai, sai an yi magana ki yi ta marairaicewa, na guji yara masu aiki ashe kuma tsofaffin an gudu ne ba a tsira ba, sai kun ga mijin mutum ku yi ta satar kallon shi." Ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsaki. Dattijuwar ta yi ƙasa da kanta kawai ba ta ce komai ba.
A wulaƙance ta nuna ta da hannu.
"Yau dai na ƙyale ki, amma wallahi idan irin haka ta sake faruwa a bakin aikinki."
Da sauri Dattijuwar ta tsugunna tana mulmula goshinta inda murfin flaks ɗin ya same ta, ta ce. "Na gode! Na gode sosai Hajiya! In sha Allah zan kiyaye, hakan ba za ta kuma faruwa ba."
Tsaki ta ja tare da zabga mata harara ta bar gurin. Matar ta raka ta da idanunta da ke cike da ƙwalla.
A hankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga bakinsa ɗauke da sallamar da ba ya fasa yin ta duk da ya san ba mai amsa masa, daga bakin ƙofa ya tsaya ya rungume hannayensa a ƙirji, ya ƙura wa Daddy ido cikin tsantsar damuwa. Ya ja sakanni a haka Kafin ya ƙarasa bakin gadon cikin ƙarfin zuciya.
"Allah ya ba ka lafiya."
Ya faɗa cikin sanyin murya da mutuwar jiki.
A bakin gadon ya zauna ya karanto addu'oi ya tofa a hannunsa ya shafa a fuskar Daddy, sai da ya gyara masa pillow yadda zai fi jin daɗin kwanciyar kamar ɗazu sannan ya tashi ya fice daga ɗakin.
A gaban steps ya tarar da Ramlah tana kallon matattakalar kamar ɗazu, murmushi ta sakar masa tare da kama hannunsa bayan ya gama saukowa.
"Na kai maka abincin da briefcase ɗinka mota, saboda na ga kana sauri kar tsayawa ɗaukar su ya ɓata maka lokaci."
Numfashi ya ja ya fesar ya ɗaga mata kai.
"Don Allah Hubby ka dinga rage wannan damuwar da kake yi, in sha Allah Daddy zai samu lafiya very soon, bana jin daɗi kullum idan ka je gurinsa na ga ka fito cikin wannan yanayin."
Hannunta da yake cikin nasa ya damƙe ya ce. "Na kasa sabawa ne, a duk lokacin da na gan shi abun sabo yake dawo mini, duk farincikin da nake ciki ina tuno halin da Daddy yake ciki sai na neme shi na rasa, idan kuma na shiga na gan shi sai na ji tamkar ban taɓa sanin wani abu nishaɗi ba a rayuwata!" Gefen fuskarsa ta shafa ta ce. "Na sani dear, amma dai ka dinga rage wannan damuwar don Allah kar wani ciwon ya kama mini kai, kuma ko shi ma Daddyn na san ba jin daɗin ganin ka a irin wannan yanayin yake ba, kawai don ba iya magana ne, amma na san da tuni ya furta maka."
Kai ya gyaɗa mata sannan ya zare hannunsa daga cikin nata ya nufi ƙofar fita daga parlourn, ta bi shi da kallo tana jin kamar ta tsaga zuciyarta ta saka shi a ciki ta ɗinke saboda yadda take jin shi a cikin ranta.
Har ya kai bakin ƙofa ya juyo ya dube ta.
"Kar ki manta da ba shi maganinsa akan lokaci."
"Abu ne da ba zai taɓa yiyuwa ba my Man."
Ya yi murmushi kaɗan.
"Na gode sosai da yadda kike kula da mahaifina ba tare da nuna gajiyawa ba."
Ta ɓata fuska ta ce. "Mahaifinmu dai, kuma kar ka ƙara mun godiya na faɗa maka amma ka ƙi dainawa ko?" Juyawa ya yi ya fice yana murmushi, murmushin da a irin wannan gaɓar kaɗai yake jin shi, ko a ina yake, ko me yake yana tuna ya bar mahaifinsa a hannun Ramlah sai ya sake shi, musamman idan ya hango yadda take rawar jikin yi masa hidima da dukkan lafiyarta da jikinta, wanda ko shi da ya haifa ba ta bari ya yi masa rabin abin da take masa.
"Marka! Marka!
Ramlah ta faɗa cikin ɗaga murya tana yatsina.
Da sauri Dattijuwar nan ta fito daga ƙasan steps inda ta rakuɓe ta zube a gaban Ramlah.
"Na'am Hajiya."
Ramlah ta bi ta da wani matsiyacin kallo ta ce. "Ki je waje ki zauna sai na kira ki, sannan duk wanda ya zo ki tare shi ki ce bana nan."
"To Hajiya in sha Allah" Dattijuwar ta furta da azarɓaɓi, da wani mugun kallo Ramlah ta raka ta da shi tare da sakin tsaki ta bi bayanta da sassarfa ta rufe ƙofar da key, sai da ta kashe light ɗin parkourn sannan ta haura sama a hanzarce.