MATAR GIDA PAGE 3
MATAR GIDA 003
SHUUKRAN/022
P3
Sudais ne ya fito daga mota yazo ya tsaya kusa da Fauziyya dake tsaye gefin Ɗalha ya ƙarewa Rayyan kallo kafin ya ce ''kullum haka ya ke duk sanda zamu ji islamiyya sai ya ce baiga rigarsa ba ko wando wata rana sai Mumy ta kaimu islamiyya zai ce ya manta Ƙur'ani a gida, uniform ɗinsa yana ɗakin Mumy cikin saif ɗinta har Kur'anin sa duk a can take ajiye masa'' shi dai Rayyan banda kuka babu abinda ya ke wani tsawa Ɗalha ya daka masa ya ce ''ka yiwa mutane shiru kafin na make ka'' nan take Rayyan ya yi shiru yayin da Sudais ya koma cikin gida ɗakin mahifiyaru ya kwasowa Rayyan uniform da kur'ani,bayan Ɗalha ya sauke su islamiyya ne Fauziyya ta fara kuka ita sam baza ta zauna ba wajen Mumy take son zuwa nan Ɗalha ya shiga aikin rarrashinta,wata malamar islamiyya ce ta karɓi Fauziyya hannun Ɗalha,tana faɗin ''ƴar Mumy yau Dady ne ya kawo ki?"ita dai Fauziyya sai faman kuka take tana ƙokarin zillewa daga hannun Malamar,malamar ta kai hannu kunci Fauziyya ta ji ya yi zafi hakan yasa ta mayar da dubanta ga Ɗalha ta ce ''jikinta ya yi zafi kamar bata da lafiya'' Ɗalha ya sosa kai ya ce ''eh rashin nono ne yau aka yaye ta'' baki buɗe malamar ke kallon Ɗalha kafin ta ce ''bai kamata ka kawo ta makaranta ba,sai ta yi zamanta a gida ko zuwa jibi ne sai tazo in jikin ya yi mata sauƙi,mamarta bata ji zafin jikin yarinyar bane?ta shirya ta'' nan Ɗalha ya fara kame kame ya rasa me zai cewa malamar sai kawai ya ce ''itama bata ji daɗe bani tana asibiti'' nan malamar ta jajanta masa,daga haka ta miƙo masa Fauziyya ta ce ya maida ta gida a siya mata maganin zazzaɓi da kuma wanda zai sata cin abinci,Ɗalha ya yi mata godiya kafin ya bar kofar makarantar bai tsaya ko ina ba sai wani pharmercy inda ya yiwa mai pharmercy bayanin condition ɗin Fauziyya mai pharmercy ɗin ne ya bawa Ɗalha shawarar siyawa Fauziyya maganin barci wanda da ta kwanta sai safe amma ya tabbata ya ɗaga ta cikin dare ya bata wani abu ta ci ko da ruwa ne,Ɗalha ya yi na'am da shawarar ana cikin haɗa masa magunguna ne wayarsa ta fara ƙara alamar shigar kira a tunaninsa Amirah ce ke kiransa sai yaga Unaisa ce ke kira rejecting kiran ya yi kafin ya yi silencing wayar,shagon provission dake gefin pharmercy ɗin ya shiga,shopping ɗin kayan ciye ciye sosai ya yiwa Fauziyya da sauran yara daga nan ya kama hanyar gidan su Unaisa daidai juction ɗin gidan su Unaisa Fauziyya ta fasa kashi cikin mota,wari ne ya cika motar lokaci guda, hakan yasa Ɗalha faka mota gefin titi ya fara ƴan dube cikin mota yana faɗin ''wannan warin na meye ne'' ita dai Fauziyya ta yi shiru tasa kai ƙasa bata ce masa komai ba,shiru ya yi yana dubanta kamar zai yi kuka ya ce ''what the hell is wrong with you Fauziyya ba ki iya magana bane?" Fauziyya ta yi wiƙi wiƙi da ido tana shirin kuka wani irin tsawa Ɗalha ya mata nan take ta haɗe kuka,sai kuma ta basa tausayi hakan yasa ya yi ƙasa da murya ya ce ''princess'' haka ya ke kiranta wani lokaci duk yaran ita kaɗai ta fita Amirah sak babu inda ta baro Amirah hakan yasa duk cikin yaran Ɗalha ya fi sonta cike da kulawa Ɗalha ya ce ''duk sanda za ki popo ki yi magana kin ji?" Fauziyya ta ce ''umm'' daga haka Ɗalha ya tada mota,a daidai kofar gidan su Unaisa ya yi parking mota,gida ne na masu rufin asiri ɗakuna huɗu jire sai kitchen da banɗaki daga can gefi,farfajiyar gida bata da wata girma sosai bishiyar lemo dake tsakar gidan da aka kewaye da randunar ƙasa ya baiwa farfajiyar gidan inuwa mai sanyi da dadin zama,Unaisa ce zaune karkashin bishiyar hannunta riƙe da wayarta tana kallon video a tik tok,daga can kofar kitchen mahaifiyarta ce zaune tare da wata makwabciyarsu suna hira,magana suke kan bikin Uanaisa,Ɗalha ya jingina bayansa da kujerar mota,daga azahar zuwa yanzu gaba ɗaya ya gaji har ya fara tunanin anya kuwa zai iya riƙon yaran nan kafin lokacin auren sa,warin kashin Fauziyya ne ya fara ɗaga masa hankali hakan yasa ya buɗe kofar motar dan iska ya samu damar shiga ya zira ƙafarsa ɗaya waje,layin Unaisa ya kira sai da kiran ya kusa tsinke kafin Unaisa ta amsa a takaice Ɗalha ya ce ''ki fito ina jiranki'' ba tare da ɓata lokaci ba Unaisa ta fito daman zaman jiransa take tun safe ya ce zai zo ya kaita ice cream planet su sha ice cream su dauki hotuna
Unaisa kyakkyawar yarinya ce ajin farka Allah ya yi mata baiwar kyawun fuska da kuma dire komai a jikinta masha Allah tana da haske daidai gwargwaɗu,kyawunta yasa Ɗalha kara macewa cikin soyayyarta,sanye take cikin wata doguwar riga materail gray colour anyi masa ado da fararen fulawa fuskarta dauke da murmushi ta fito,tun daga nisa Ɗalha ya kafeta da ido kamar zai cinye ta,ji yake kamar ya maida ta ciki tsabar so,bakinta dauke da sallama ta iso wajen Ɗalha ya amsa mata sallama nan ta gaida shi ya amsa mata har sannan idonsa a kanta sai wani binta yake da ido,wani wari wari ne ya dake hancin Unaisa nan take ta fara rufe hanci tana bin wajen kallo tana neman daga ina warin yake,bayan ta gama dube dube ta mayar da dubanta kan Ɗalha ta ce ''beby kana jin warin nan kuwa?" numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya ce ''ƴar ki ce ta ɓata jiki da popo'' sai a sannan hankali Unaisa ya kai kan Fauziyya dake barci hankali kwance gaban mota,da sauri ta cire hannu daga hanci ta ce ''kamata ya yi ka kaita gida couze babu yadda za'a yi mu fita da ita alhali ta ɓata jiki,babu wanda Ɗalha ya faɗawa ya saki Amirah har Unaisa,shiru ya yi na wasu ƴan sakkani kafin ya ce ''mamansu bata nan'' Unaisa ta yi saurin tarar numfashi sa ta ce ''ina ta je?'' Ɗalha ya gyara zama ya ce ''na turata gidansu ɗazu da safe,and l don't think zan dawo da ita nan kusa maybe sai mun gama cin amarci'' ya kare magana yana sakarwa Unaisa murmushi,nan take annuri dake fuskar Unaisa ya ɓace fuskarta babu alamar wasa ta ce ''wani amarci za'a ci? amarci da ƴaƴa bakwai? "magana ta gaskiya ka maida matarka saboda ni ba zan iya reno ba'' cike da mamaki Ɗalha ke kallon Unaisa,kamar bazai yi magana ba sai kuma ya ce ''munyi magana da ke last week kin ce za ki riƙe min yara tamkar ke kika haifi su'' Unaisa ta yi magana cikin gatse ta ce ''sai na ce ka saki uwarsu? yara da mahaifiyarsu ka maida su marayu ba fa zai yiwu ba,tun wuri ka je ka yi bikon matarka'' ta yi magana tare da kawar da kai gefe,shiru ne ya biyo baya kowanne su da tunanin da yake,sosai Ɗalha ya yi mamakin yadda Unaisa ta nuna sam baza ta riƙe masa yara ba,a tunaninsa zata yi farin ciki bayan ya sanar da ita ya saki Amirah amma sai ya ga akasin haka,Unaisa ta shirya za su sha soyayya sosai bayan aurensu,ga kuma alƙawarin da Ɗalha ya mata na tafiya kasar Poland cin amarci,yanzu ya saki matarsa ba lallai ya kaita Poland ba ita da ko airport bata taɓa zuwa ba,hakan yasa ta ci burin tafiyar sosai gashi duk ƙawayenta ta yi masu hiran za su poland honeymoon shikenan sai ta ƙare honeymoon a hidimar yara,sam haka ba zai yiwu ba
Ɗalha ya mayar da dubansa ga Unaisa ya ce ''je ki gyara mata jiki daga nan sai mu wuce na siya maki ice cream ɗin'' galala Unaisa ta yi ta buɗe baki tana kallonsa ta saki wani irin murmushi kafin ta ce ''da wa ka ke magana? wai ni?" ta kare magana tana nuna kanta zuwa yanzu Ɗalha ya gama karaya da lamarin Unaisa hakan yasa ya yi shiru bai ce mata komai ba kawai ya rinƙa kallon ta can ya ce ''what is really wrong with you Unaisa ɗa fa na kowa ne beside Fauziyya ƴata ce and nan da wasu ƴan kwanaki za'a daura mana aure da ke me matsalar ki,pls bana son jin wata magana ki dauki yarinyar ki je ki gyara mata jiki ban son jin komai'' wani irin dariya Unaisa ta yi harda shewa kafin ta ce ''ka yi hakuri bazan iya ba'' Ɗalha na shirin magana ya jiyo muryar Aisha inda ta ce ''barka da yamma ango'' fita Ɗalha ya yi daga mota ya nufi inda Aisha ke tsaye cike da girmamawa suka gaisa inda Aisha ta tambaye sa ya yara ya ci mata duk suna lafiya daidai lokacin idonta ya kai kan Fauziyya dake barci hankali kwance cikin mota amma kana ganinta zaka san barcin wahala take daga yadda ta kwanta,Aisha ta ce ''tare kuke da yaran?Ɗalha ya ɗan sosa kai kafin ya ce ''a'a bata jin daɗi ne shi yasa na fito da ita'' Aisha ta ce ''allah sarki, Ubangiji ya bata lafiya,in babu damuwa zan yi mata shimfiɗa cikin gida kafin ku gama'' Ɗalha ya ƙirkire murmushi kafin ya fara magana cikin in'ina ya ce ''daman..daman ta ɓata jikinta ne'' Aisha ta ce ''to Unaisa ki shiga da ita ciki sai a gyara mata jiki'' wani kallo Unaisa ta yiwa Aisha da yasa Aisha faɗin ''ba ki ji ba?" cikin sanyin murya Ɗalha ya ce ''ta ɓata jiki da bayan gida ne'' cike da mamaki Aisha ta kalle Unaisa kafin ta ce ''saboda ta ɓata jiki da bayan gida shine baza ki dauke ta ba?" shiru Unaisa ta yi,ta kawar da kai gefe tana ƙananun maganganu ita kaɗai gudun kar a yi abin kunya yasa Aisha daukan Fauziyya bayan Ɗalha ya buɗe mata kofar mota cike da dabara ta fidda Fauziyya daga cikin mota,sallama dauke a bakinta ta shigo gidan,a tare Mama da makwabciyarsu suke amsa sallamar da ido Mama ta bi Aisha daidai lokacin da Aisha ta dire Fauziyya bakin fanfo Mama ta ce ''wannan kuma fa daga ina kika samu ta duk ta ɓata jiki da kashi?" numfasawa Aisha ta yi kafin ta ce ''ƴar Ɗalhatu ce wai bata jin daɗe shine ya taho da ita zance suna hanya ta ɓata jiki da kashi''
SHUUKRAN