MATAR GIDA PAGE 4
MATAR GIDA 004
SHUUKRAN/022
P4
Shiru Aisha ta yi na wasu ƴan sakkani kafin ta ce ''Mama ki yiwa Unaisa nasiha da alama bata san abinda ta ke ba, wai yarinyarnan na ce mata ta dauki ƴarinya ta wanke mata jiki amma Unaisa ko motsawa bata yi ba daga inda take na yi mamaki sosai walh a gaskiya za'a samu matsala da Unaisa ya za'a yi ki so uba ki ƙi ƴaƴansa a ina aka taɓa yin haka,wlha Mama ƙi ja mata kunne gwara tun wuri ta gyara kar tasa ya fara tunanin bata son ƴaƴansa'' tun sanda Aisha ta fara magana Mama kallon ta kamar baza ta yi magana ba sai kuma ta ce ''shirmen Unaisa ya yi yawa amma da ta shigo zan mata magana na ji dalilin da yasa ta yi hakan'' ita dai Aisha bata sake cewa komai ba ta mayar da hankali kan wankewa Fauziyya jiki ita ko Fauziyya sai tsala ihu take tana kiran Mumy haka Aisha ta wanke mata jiki tsaf har wanka ta yi mata soso da sabulu ta wanke ta tsaf,ta shirya ta cikin kayan ƴarta Nana ƴar 2 years ta fesa mata turare mara ƙarfi,zafin da jikin Fauziyya ya yi yasa Aisha kiran ɗanta Auwal mai shekaru sha uku da shigan sa kenan daga shago ta ce ''kaita wajen babanta a waje ka ce masa jikinta ya yi zafi sosai ko zai maida ta gida wajen mamanta ta bata magani,kuma ya aiko gobe a ƙarɓo uniform ɗinta'' ta kare magana tare da kunna fanfo inda ta fara wanke uniform ɗin Fauziyya
Kamar yadda mahaifiyarsa ta faɗa masa hakan ya yi,Fauziyya ko da gudu ta nufi inda Ɗalha ke tsaye ta ɗaga masa hannu alamar ya dauke ta,daukan ta ya yi yana shafa fuskar jin yadda jikinta ya yi zafi sosai ya mayar da dubansa ga Unaisa ya ce ''l think zan wuce kawai she is runnig temperature'' da kyar Unaisa ta iya buɗe baki ta basa amsa tsabar yadda ranta ya ɓace ita da ta shirya daukan hotuna ta sa a status amma wannan yarinya mai ido kamar ƙwai da shegen fari kamar uwarta ta ɓata masa plan duk wannan magana cikin zuciyarta take muryar Ɗalha ne ya ya katse mata tunani inda ya ce ''kar ki ji komai zan tura maki ƙudin sai ki siya kwai'' bai jira cewar ta ba ya buɗe motarsa ya shiga Fauziyya ta yi lamo jikinsa yana jin yadda zafin jikinta na ƙaruwa,bai tsaya ko ina ba sai kofar gate ɗin gidansa lokacin karfe biyar da mintina goma ledar magani ya dauko ya fita daga motar,ya kulle motar ba tare da ɓata lokaci ba ya cire key daga aljihunsa rigarsa ya buɗe kofar entrance,nan parlour ya samu waje ya zauna ya shimfiɗa Fauziyya kan ɗaya daga cikin kujerun parlourn zuwa yanzu jikinta ya fara week,Ɗalha ya buɗe ledar magunguna kenan ya ji alamar zuban ruwa daga ɗakin Sumayya da Ummu Abiha tashi ya yi ya nufi hanyar ɗakin bayan shigar sa ɗakin ne ya buɗe kofar bathroom, idonsa ya sauka kan bathtub dake cike da ruwa ga wani kumfa dake saman ruwan,wani doguwar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke kafin ya shiga cikin bathroom ɗin ya kashe famfo bathtub,hannun rigarsa ya naɗe daga nan ya zura hannusa cikin bathtub ya ɗaga stopper nan take ruwan dake cikin bathtub ya fara raguwa,yana shirin barin bathroom ɗin ne idonsa ya sauka kan siter yaga duk sun ɓata da kashi ko flushing basu yi ba,bai bar bathroom ɗinba sai da ya tsaftace shi tsaf kafin ya fito yana share zufa,fitar da magunguna ya yi ya ɗiba kowanne kamar yadda aka rubuta jikin kwalin maganin a hankali ya ɗaga Fauziyya ya zaunar da ita,idonta ne ya sauka kan magunguna,nan ta sake wani kuka ta fara magana cikin hausarta da bai fita ta ce ''Dady ban ca a'a ban ca'' nan Ɗalha ya shiga rarrashinta yana faɗin ''no..no.. no my princess za ki sha ba ki da lafiya jikin ki ya yi zafi you have take your medicaton'' ita dai banda kuka babu abinda take sai faɗin Dady ban ca take,ganin da gaske baza ta sha ba yasa Ɗalha daura ta kafarsa inda ya riƙe hannayen ta da hunnusa ɗaya,ɗaya hannu kuma yana riƙe da magani,ya daura ƙafarsa ɗaya kan kafafunta duka biyu yana faɗin ''buɗe bakin ki,comm on open your mouth my girl'' ko da wasa Fauziyya ta ƙi buɗe baki hakan yasa Ɗalha ya sakin hannunta ya matse mata baki da kyar ya samu ta buɗe bakin bai tsaya ɓata lokaci ba ya zuba mata magani a baki,har cikin zuciyarsa ya ji ɗadi ganin ya samu ya zuba mata magani a baki,yana shirin daukan dayar magani Fauziyya ta fesar da maganin da ya zuba nan ƙasan tiles,wani irin zafi zuciyar Ɗalha ya yi ji ya yi kamar ya kai mata duka amma sai ya fasa ganin yadda idanunta suka yi ja sosai numfashinnta na fita da zafi,nan take wani irin tausayinta ya ziyarcesa bai san sanda ya fara magana shi kaɗai ba kamar wani zararre ''yanzu ya ya zan yi da ke Fauziyya ba ki da lafiya amma kin ƙi shan magani wannan wata irin musiba ce? Amirah ba ki kyauta min ba ki kyauta wa yaran nan ba innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya rabbi'' ya ƙare magana cikin karayar murya bai hakura ba ya sake gyarawa Fauziyya zama ya dauki ɗaya daga cikin murfin magunguna ya sake ɗura mata a baki nan ma ta fesar wannan karon a fuskarsa ta fesar,cike da jin haushi ya kuma daukan ɗaya ya ɗura mata,da sauri ya kama lips ɗinta duka biyu a dole sai ta haɗe maganin Fauziyya taga azabar da bata gani ba sai mutsu mutsu take da kafafunta Ɗalha ya ƙi sakar mata baki,bayan wani ɗan lokaci ya samu ta haɗe maganin,a hankali ya sake lips ɗinta cike da jin daɗin shan maganin da Fauziyya ta yi ya saki wata murmushi ya ce ''that's good my princess'' bai gama rufe baki ba Fauziyya ta fara wani irin tari,kafin Ɗalha ya ankare ta kwarara amai nan ƙasan parlour ta ɓata gaba ɗaya jikinta har shi ta ɓata masa jiki,ji ya yi kamar ya zai yi hauka harda rashin lafiya take tsabar ɓacin rai Ɗalha bai san sanda ya ɗaga hannu ya duke ta ba nan ta ƙara kwala wani uban ihu tsabar yadda marin ya yi mata zafi bata san sanda ta miƙe tsaye ba ta shiga zaga parlour tana ihu tana kuka,ko kallo bata ishe shi ba ya tashi zuwa bedroom ɗinsa ya gyara jikinsa,bayan fitarsa daga bedroom ne yaga Fauziyya kwance ƙasan parlour har ta yi barci nan kusa da amai da ta yi,shiru ya yi yana tunanin ta ina zai fara,ɗazu kafin Amirah ta bar gidan saida ta gyara ko ina har turare ta kunna cikin burner amma in few hours yaran sun ɓata gidan gaba ɗaya,gida ya koma kamar anyi sati ba'a share ba,tun daga parlour har ɗakunansu sun ɓata ko ina ko ina kaca kaca wasan da suka fita ɗazu ne sun kwaso datti a kafafunsu ko ina alamar kafarsu haɗe da datti,ga kayan wasa ta ko ina,kusan duka toys ɗinsu suka watsar a parlour
Bayan dogon nazari Ɗalha ya dauke Fauziyya ya kai ta bathroom ya gyara mata jikin barinta ya yi cikin bedroom ɗinsa saboda sosai take runnig temperature,gyaran gidan ya fara,da parlour ya fara bayan ya gama share parlour ne yana shirin moping wayarsa ta fara ƙara alamar shigar kira,ganin shugaban islamiyyar su Sudais ke kira murya can ƙasa ya ce ''shirt l almost forgot about them''daga haka ya masa kiran bayan sun gaisa ne shugaba islamiyyar ya ce ''Alhaji ba'a dauke yara ba muna shirin ƙulle makaranta magriba ta ƙarato'' nan Ɗalha ya fara kame kame sai kuma ya ce ''motata ce ta samu matsala amma ina hanya'' bai jira cewar shugaban makaranta ba ya katse kiran tare da yin wurgi da mopper murya can ƙasa ''da ni ki ke Amirah a tunanin ki zan ƙaraya ne na dawo da ke? dan kawai kin bar min yara bazan taɓa dawo dake ba'' yana gama faɗin haka ya wuce ɗaki daukan Fauziyya ya yi ya fita ya sata a mota lokaci guda wani mugun wari ya ziyarce hancin sa sai yanzu ya tuna bai wanke inda Fauziyya ta ɓata da bayangida ba ɗazu,hakan yasa ya mayar da ita back seat,daidai lokacin da aka fara kiran sallar magrib Ɗalha ya yi parking kofar islamiyya Sudais tare da ƴan uwansa suka nufi motar Dadynsu yadda shugaban islamiyya ya ba Ɗalha hannu suka yi musabaha cike da mutuntawa Ɗalha ya ce ''a yi mana afuwa Mallam'' Malamin ya ce ''a'a babu komai Allah ya kiyaye gaba Ɗalha ya amsa da ameen,bayan komawarsu gida Ɗalha ya cewa yaran su shiga ciki shi kuma ya tsaya wanke seat ɗinda Fauziyya ta ɓata ɗazu,ya dauki kusan mintuna ashirin kafin ya gama wanke seat ɗin,daga haka ya shiga gida dan gabatar da sallar magrib,idonsa ne ya sauka kan tiles ɗin parlour da ya gama share moping kaɗai ya rage masa so yake ya yi magana amma ya ƙasa furta komai wani tunani ya faɗo masa hakan yasa ya yi shiru ya yi wucewar sa bedroom ɗinsa,ya gabatar da sallar magrib,ya so ya zauna ya yi azkar ɗin yamma da ya saba yi kullum amma gaba ɗaya ya ji bashi da nitsuwa gani ya ke in ya ƙara koda minti ɗaya ne za su iya ɓata gidan gaba ɗaya hakan yasa ya shafe addu'a ya fito parlour wani irin tsawa ya yi masu duk suka natsu sun mayar da duban su garesa,fuskarsa babu alamar wasa ya ce ''maza kuji ku yi alwala ku yi sallah babu musu suka yu hanyar ɗakunan su,kwalbar maganin da ya siyawa Fauziyya wanda aka ce masa na barci da sa cin abinci ya gani a ƙasa kwalbar ta fashe duka maganin da ke cikin kwalbar ya zuba dafe kansa ya yi zuwa yanzu ya fara karaya gani yake kafin safe yaran za su iya yin ajalinsa,ba tare da ya yi magana ya dauke tsintsiya ya share kwalbar ya sa mopper ya goge wajen zama ya yi kan ɗaya daga cikin kujerun parlourn ya na tunanin ta ina zai fara abinci zai dafa masu ko gyaran gida,ga Fauziyya ta ƙi shan magani kuma ga dukkan alamu akwai yunwa a cikinta,wani tunani ya faɗo masa hakan yasa ya dauki Fauziyya tare da sauran magungunan ta ya fita daga gidan,ya nufi hanyar gidan Mama Uwani makwabciyarsu,zaman mutunci suke da Amirah, da Mama Amirha da yaranta ke kiran Mama Uwani,sallama Ɗalha ya fara yi tare da kwankwasa kofar gidan Mama Uwani,ya dauki a ƙalla mintuna shidda tsaye kafin Mama Uwani ta buɗe masa kofa ganin Ɗalha yasa Mama Uwani faɗaɗa fara'arta tana faɗin ''sannu da zuwa son'' haka take kiran Ɗalha ta ce ''bismillah shigo'' har cikin parlourn Mama Uwani Ɗalha ya shiga
SHUUKRAN