Baban kawata chapter 1
by @smauta
BISMILLAH DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI……
Zamu fara wannan littafi mai suna *BABAN KAWATA NE (my besties daddy)* suna ko hali yayi kamanceceniya da wani ko wata arashi ne ban yarda a canza man littafi ba ta kowace siga and this book is free💃💃💃 wannan littafin kyauta ne daga marubuciyar ku SM AUTA👍👍👍👍let's goooooooooooooo💃💃💃💃💃😔
BABAN KAWATA page 1…
Wata katafarirayar makaranta dake kasar sin china ana tsaka da ruwa mai ƙarfi ga iska na kadawa,kowane lungu da sako na makarantar haske ne ya karade shi,daga tsakiyar wani katoton building inda nake kyautata zaton nan ne hostel na hango wata tsaleliyar yarinya danya shakaf tana wani irin mahaukacin kuka,ga ruwa mai karfi yana dukanta…………
Bata duba inda take jefa kafarta gudu take kawai ba abinda ranta da zuciya ke raya mata illa ta fice daga makarantar gaba daya haka akayi kuwa koda tazo bakin gate security sun tare ta amma halin da suka ganta a ciki yasa suka barta ta wuce domin kasa ce da kowa yasan ƴancin shi,koda ta fito gate tsayawa tayi domin neman abun hawa………
Kusan mintin ta ashirin ba wani mahalukin da ya wuce ta gabanta yasa ta yanke hukuncin ta cigaba da gudunta,gudu take ga kuka ba kakkautawa takalmin da ke kafar ta ne ya tsinke anan inda take ta duke tana wani irin kuka mai tsuma rai ta sake mikewa ta cigaba da gudunta tayi gudu ya kusa na minti talatin kafin ta iso gaban wani club jikinta ya jike sharaf da ruwa………….
Daga nan inda take tsayen tana kuka tana kwalama wani matashi kira dake cikin club din Sam'an Sam'an Sam'annnnnnnn tun kiran sunashi na farko yaji sarai yasan kuma wacece yana kuma expecting zuwanta a wannan lokacin shiyasa ya dakatar da shigar shi ya tsaya a entrance jiran zuwanta, budurwar da hannun shi yake makale dana juna ya jawota zuwa jikinshi ta fado kan kirjin shi tare da sakin wata yar kara irin wanda suka dade a yawon duniya tace auucchhhh,wanda aka kira da Sam'an ya kalli budurwar da kyau sannan yace sorry baby………………
Bakin club din ya fito tareda budurwarsa inda ya tarar da yarinyar tsaye ruwa na dukanta tako ina amma tana tsaye kyammmm kamar soja a gurin kallo daya yayi mata ya cije lips dinshi,sannan yace gani yayi mata alamar tambaya da hannu?kamar jira take ta tsugunna ta hade hannunta biyu tace Sam'an karkaman haka,ka rufaman asiri kamar yadda Allah ya rufa naka………….
Marainiya ce na taso bansan iyayena duk da ban dandani rashi na wani abun duniya ba amma na dandani rashi na rasa mahaifana,karka zama kaine sanadiyyar rusa sauran farin cikin da nake dashi ka dubi girman Allah sam'an karka yaɗa tsuraicina a duniya na rokeka da Allah karka wulakantani, wallahi wallahi ban taba aikata zina ba ko a mafarki balle a zahiri………………
Ta cigaba da kuka tana rokon shi,rarrafowa tayi tazo har kusa da kafar shi tasa hannunta farare tasss ta rike masa kafa ɗaya ta kara fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya sam'an na rokeka pls don't do this to me Ka tuna soyayya ta dakai ka tuna halin da zan shiga bayan kayiman haka,ka tuna haƙƙin Allah tsakanina dakai, sam'an banki baka kaina ba dan haka nan ba sai dan kiyaye dokar Allah………….
Wallahi niba yar iska bace kamar yadda kake tunani ka taimaka man dan Allah duk wannan abun dake faruwa sam'an na tsaye rungume da budurwar shi,sai lokacin ya kalleta da kyau yafara da cewa keeee tunanin ki na soki har kike hada kanki dani sunan saurayi da budurwa to bari kiji in gayamaki kuma ki bude kunnuwanki da kyau idan sunyi datti ki goge su Manaar ya kira sunanta a gadaran ce sannan yace ban taba son ki ba koda na minti daya neeeeeeee………….
Ban taba maki kallon wacce nakeso ba kullum ina maki kallon sha'awa wanda idan da kin bari na samu abinda nakeso manar daba wannan zancen akeyi ba,amma tunda kinki yarda da bukatata mu zuba mugani nidake wazai kwasa,duk wannan abun da ake manar na zube ne a ƙasa kan kafafunta tana rusa kuka mai tsumaya zuciya…….
Kinada sauran minti talatin ko ki yarda da bukatata kokuma kinga ya nuna mata securities dake tsaye a bakin kofa yace zansa su daureman ke a shigo dake a cikin club in kasaki kamar yadda kikasan ana kasa gwanjo a Nigeria in fadi amount na kudi danake bukata a samu mai sayen ki nan take yaci ki a gaban bainar jama'a,keda za'ayi ma tsirara kowa yayi video son ranshi mene abun tada hankalin ki akan hoton ki dake wayata………….
Kinsani ba abinda mazan nan na turawa suke darajawa akan mace sama da ace Virgin ce kinsan a daren nan miliyoyi nawa zan samu a tare dake zabi ya rage naki koki bani abinda nake bukata daga gareki kokuma in sayar dake ga wanda baisan zafin ki ba ya kwaci budurcin da kike takama dashi ta karfin tsiya a gaban kowa meya rage daga ranar saka hijabi ya kare maki…………
Budurwar tashi ya kara jawota gaf da bakin shi tana wani lumshe ido ya manna mata kiss a baki caf ta cafke ta shiga maida mashi manar na tsugunne tana kuka da hannu sam'an yayoma securities din wurin alamar suzo dayake sun saba dashi babban customer ne na VIP yasa da gudun su suka iso take her kawai yace masu ya bada baya suka cimimiyi manar da har lokacin motsi bata iyawa da karfin tsiya suka mikar da ita tsaye tsammmmm……………
Tassss tassss sukaji karar harbin bindinga har so biyu yasa dukkansu suka waiga wanine da bata iya daga fuskar ta duka ta kalle shi daga iya hannun shi kawai idonta ke hange sanye da bakaken kaya ya tunkaro su gadan gadan da bindigar tashi dake hayaki ai da gudu securities din suka ɓace nan manar ta kara zubewa kasa sharaf,da Izza sam'an ya juyo ya kafe mutumin da ido………….
Hannun shi yasa ya dago manar dakyar batai wata wata ba ta fada jikinshi koda bata kalli fuskar shi ba tanaji a jikinta zuwanshi taimako ne a gareta,tafiya ya farayi da ita har bakin motar shi prado baka steps dayaji a bayanshi yasa ya dakata da saka manar a motar, sam'an ne ya taho a zafafe yakai mashi duka yasa hannu ya tare, cigaba da naushin sam'an yayi saida yayi mashi likis kafin ya bude motar yashiga da manar yabar shi kwance jina jina a wurin……….
Ajiyar zuciya manar ta sauke sai lokacin ta kara yi mashi kallo na biyu duk da manar nada kyau amma sai taga wannan kamar ma yafita kyau kura mashi ido tayi har batasan kallon da take mashi ba ya wuce shari'a saida taji hannun shi akan idon ta tadawo duniyar tunanin da take,gefen titin yayi parking ya kalleta da kyau fuskar shi ba alamun wasa yace waye wancan yaron?me kikai masa?a ina kike?kuma meya fiddo ki cikin ruwa sosai???????
Tana kuka ta fara cewa saurayina ne koda yaji kalmar saurayi tsuke fuskar shi yayi tsammm,yayi amfani da wata dama daya samu a lokacin dana kone a cikina da bayana bana iya saka kaya ina gadon asibiti yayiman hoto jikina dagani sai ta kasa ida ƙarshen sbd kuka dayaci karfin ta,ko bata fada ba ya gane me zatace ta cigaba da kuka tana cewa………….
Tun bayan na warke ya fara bijiroman da sainazo mun hadu dashi kuma ni wlh ban taba aikata alfasha ba ko a mafarki,kin tabbata wannan labarin naki gskia ne idan na bincika nagano gskia ba haka bane kinsan mezan maki da sauri tace idan harba gskia na fada maka ba wlh na yarda ka kasheniiiiiiiii,sai lokacin ya kalleta tsaf yarinya ce karama shakal,yace mata how old are you?17 years ta bashi amsa…………….
Me kikeyi a china?ankawoni makaranta ne anan,shima student ne?eh amma senior na ne jinjina kanshi yayi kawai ya tada motar bai kara tanka mata har suka iso wani wuri da wurin kamar tashar mota ce yayi parking dashboard dinshi ya bude ya ciro kudi masu yawa yace take, hannunta na kyarma ta ansa sannan yace fita ki hau mota acan ki koma school dinku daga yau wannan yaron bazai kara takura maki ba………..
Wasu zafafan hawaye suka shiga zuboma manar, bakinta na kyarma ta furta mashi kalmar nagode kasan zuciyar ta kuma tanajin kamar bazata iya fita daga motar ba sbd tsoron abinda hakan iya zuwa ya dawo,ya gane hakan sarai ya bata karfin gwiwa kije ba abinda zai sameki am with you,wannan kalmar ta kara tsaya mata a rai kamar ya yana tare da ita dama ya santa ne?da sauri kawar da tunanin nooo kawai zai taimakeki ne tana tsaka da wannan tunanin taji yace what's your name?bakin ta na kyarma tace ma ma manarrrr,good manar you can go now…………
Tsuluf ta fito daga motar ta isa gaban motoncin hayar dake parking a wurin ta samu wanda zai kaita makaranta a daren,har lokacin bai tafi ba yana nan yana kallon ta a mirror samun kanta manar tayi da sakar mashi murmushi tana mashi waving hannu,saida yaga tashiga mota an tayar sun tafi sannan ya taka wani mahaukacin reverse…………..
Jama'a ya zata kaya mu hadu a next page pls dont forget to comment like and share💃💃💃ITS ME SM AUTA