Baban Kawata chapter 2
by @smauta
Baban kawata page 2
Dawowa yayi gaban club inda yabar sam'an a yashe nan ya sameshi wani uban burki ya taka a gabanshi sannan yazo ya ciccibo shi ya jefa mota sai a lokacin budurwar tashi ta fito da abokan su dake cikin club din,ganin mutumin ne ya kara dawowa yasaka sam'an mota yasa ta kara fashewa da kuka bindigar dake gefen jeans din ya fiddo ya kara harbin iska kan kace kwabo kowa ya watse a wurin yaja motar sa yayi gaba………
Tafiya yayi ba wata mai tsawo ba ya iso wani mini apartment da anan ya sauka dan harkokin shi bude kofar motar yayi,ya karayima sam'an kallon tsanna sannan yace get down kafin inzo in idasayin ƙasa ƙasa da kashin ka,da sauri ya fito bakin shi na fitar da jini koda ya fito faduwa kasa yayi sharaf jikin shi ba karfi ga ƙarfin jini da ya zubar yana sake dibar shi………….
Janshi kasa yayi kaiiii har tsakiyar parlour gidan sannan ya wurgashi kanshi ya bugu da centre table sam'an halinda ya tsinci kanshi a ciki yanzu rayuwa ko mutuwa,a bangaren manar kuwa sai yanzu ta ankara da ina take tunda tashiga motar take kuka koda ta dago kanta bata gane wane hanya ce wannan yake tafiya da ita ba,da karfin gaske tace ina zaka kaini Tsinghua zanje fa…..……
Bai tanka mata ba ma sai kara karfin gudun motar da yakeyi ta ankara da mutumin ma bakin fata ne,gudu yake na wuce ka'ida da ita a mota wayar sa tayi ringing bugu daya ya dauka ok sir in the next 10 minutes i will be there shi kadai ne abinda ta iya ganewa,kuka take tana bashi hakuri kan ya ajeta bai zame ko ina da ita ba sai wani gida uffan bai ce mata ba ya bude mata kofa kin fitowa tayi hakan yasa ya duko ya jawota a motar har bakin kofar parlour ya kawota sannan yace enter…………
Batada kuzari hakan yasa ta kasa bude kofar daga ta cikin parlour aka bude kofar bataga wanda ya bude ba saidai wanda idanta yaimata tozali dashi kwance cikin jini ne yasa ta zabga uban ihu tayi baya luuuuuu sumamma,mutumin dazu ne tagani da sam'an kwance tsakiyar parlour cikin jini wani uban tsaki ya buga a zuciyarsa yace kome aka haɗa da mata sai sun baka matsala………..
Wannan wanda ya kawota ne ya dauko ta nuni yayi mashi da bedroom ya sakata a ciki ya fito gefe guda kuma parlour wasu Chinese ne nagani zaune da computer a gabansu suna aikin su cikin kwarewa kusan hour akayi sannan suka tashi ogan suka ba hannu bayan sun gaisa ya dauko wasu makudan kudi ya mika masu……….
Jude wanda aka kira da Jude ne ya juyo call dr baa kara mintina talatin ba dr ya iso nuni yayi masa da inda aka kai manar shida jude suka shiga har lokacin a sume take,da sauri dr ya karasa gaban gadon ya tsaya aune aune ya fara da kyar ya shawo kan ciwon nata ya daura mata ruwa da allurai suka fito dr yayi ma oga bayani kan halin da manar take ciki zuciyar ta ce ta fara collapse amma idan aka dage da therapy zata dawo daidai………….
Jimmmm yayi ba abinda ke mashi ringing akai sai lokacin da yake cikin mota yakejin tana rokon sam'an ni marainiya ce ka rufaman asiri kallon inda sam'an yake kwance yayi ya kara jin wani bakin ciki ya taso masa,tun yaushe ya fara mata barazana da hoton ta,baici a ce abinda ya faru yau ba yasata zuciyar yin collapse ba,da kafar shi ya daki table dake gefen sam'an firgigi ya mike da hannu daya ya jawo shi gabanshi ya durkusar dashi idon shi jawur ba alamun sassauci a tare dashi……………
Karar buga table ya ta manar innalillahi wainna ilaihir rajiun shine kawai abinda take iya furta wa da karfi tun daga dakin suke jinta har parlour jude ne ya kalli ogan nashi yaimashi alama da fito da ita,zaune ya sameta da hannu ya kirata ta fito har gaban oga yakawota ya koma gefe sai lokacin ta kalli waye take tsaye gabanshi mutumin daya ceceta dazu ne, ajiyar zuciya ta sauke da duk wanda yake parlour saida yajita…………..
Zunbur ya mike tsaye yazo gaban manar ya tsaya hannun shi rike da bindiga ya saita kan sam'an da sauri manar ta rike mashi hannu tana kallon sam'an da har lokacin jikinshi ke kyarma kyaf kyaf kyaf yace apologise to my woman,Dan Allah manar kiyi hakuri ba zan kara ba kuyiman rai na tuba kit kit ya kara saida bindigar akan shi sannan yace manar,tana rike da hannu shi ta baya tace na'am did you hear it??…………
Langwabar da kanta tayi tace mashi no harzuka yayi ya dumfaro sam'an yace louder i want the whole room hear who you are,ko yanzu a dauki gawar ka mushe,da karfi sam'an ke kuka yana rokon manar ta yafe mashi ya juya ya kalleta da kyau yace now,manar tace yeah now i hear it wayar shi dake cikin aljihu ya fitoo ya cire security ya tsugunna gaban sam'an yace,idan kaga dama picture dinta ka kara nemo shi ka maido shi a wayar ka kuma ka cigaba da mata barazana dashi………..
Ni kuma nayi maka alkawarin daga ranar ko ina kake ko kasan kasa ka boye alƙawari nayi maka niiiiiiiii sai naga bayanka wayarshi dake hannun shi ya daga mashi ya nuna mashi wani abun tracking yace zabi ya rage naka duk motsinka ina tare dakai ba dare ba rana in har bazaka bar yarinya ta lumfasa ba to kaima kasani kana jan lumfashin ka na ƙarshe a duniya remember this night remember her face,take your phone and leave my house now,wayar sam'an dake kan tebur ya dauka jiki na kyarma ya tashi yana godiya yana gudu yana faduwa kasa ya fito daga gidan…………..
Lokaci daya manar ta saki wani makirin murmushi sai hawayen dadi suka shiga zubo mata kasa ta zube gaban oga ta cigaba da mai godiya da yabo na yadda taga ya tsaya mata tsayin daka wajen kare mutuncin ta,baice mata uffan ba sai hannu daya daga mata yace enough shuru tayi ya kalli jude dake tsaye take her to school,koda taji haka tashi tayi ta kalli hannun ta da har yanzu yake daure da cannular ta kara cemashi Nagode😭😭😭😭
Mu hadu a next page salon namu ba irin nasu bane You can chat me direct on WhatsApp *** don't forget to like share and comment💃💃SM AUTA