BABAN KAWATA

Baban Kawata chapter 3

by @smauta

Baban kawata page 3




Yan hostel ne suka zagaye manar da har lokacin take kyarmar sanyi ana tambayar ta ina taje ta kasa magana ga cannular a hannu tana kuka room mate dinta ce dake kuka akaje da sauri ana mata albishir da manar ta dawo da gudu halim ta duro daga gadon tayo waje inda taga mutane sun taru a wurin tayi tana zuwa ta tabbatar da manar ce basuyi wata wata ba suka rungume juna suna kuka mai tsumaya zuciya…………





Manar kiman mgn dagani saike a dakin nan wani abu sam'an yayi maki manar idan har wani abun ya faru bazan yafema kaina ba manar dana barki kika tafi wurin sam'an ya hannunki da cannular kiman bayani ko zuciya ta zata samu saukin abinda nakeji a cikinta yanzu manar,sai lokacin manar ta kalli kawar tata daduk duniya bata kamar ta a yanzu bata taba ƙawance da kowa ba sai kawota makarantar nan ta hadu da halim tazamar mata uwa uba kawa kuma garkuwa a gareta………….






Halim na'am ba abinda ya faru dani sai alkhairi kuma a yanzu ina cikin wani irin farin cikin da bankawo kwana kusa zanyi shi ba halim,ina tunanin rayuwa ta ce tazo ƙarshe koban kashe kaina ba zan zama marar amfani a cikin al'umma zan zama wacce batasan ciwon kanta ba,bansan taya zan farama mutane explaining taya wannan hoto ya fita ba'a son raina ba amma dayake Allah Allah ne Allah buwayi gagara misali sai yajefoman da wanda zai taimakeni ya ceceni ya cireni daga kuncin da sam'an ya sakani a lokaci kaɗan halim,nan ta kwashe komi tasss taba halim labari…………






Kuka sukayi tayi itada kawar ta halim kukan dadi kukan farin cikin da basusan na meye ba a haka har bacci yayi awon gaba dasu,can tsakar dare cikin bacci halim taji manar na kiran oga tana wani irin nishi😳😲😳😳😳 hankalin halim tashi yayi ta kasa tashin manar dake wasu irin sabbatu cikin baccin ta,manar manar ke manar na'am oga tayi firgigi a baccin tashi halim tayi wayar ta ta kunna tace manar nice oga??????







Waye oga manar mafarkin me kikeyi kuma,duk kunya ta rufe manar tsaf abinda ya faru a mafarkin kedawo mata sabo dal,magana nake halim bakomai fa a'a manar da komai kinji yadda kike moaning kina kiran wani daban sanshi ba waye shi, innalillahi wainna ilaihir rajiun kar abinda nake tunani manar shi kika aikata saboda pressure da sam'an ya sakaki a ciki ce ta saki shiga wani halin da bansani ba……………..





Kuka manar ta fashema halim dashi wlh halim ba haka bane abinda kike tunani akai bashi bane halim wanda ya taimakeni ne jiya tunda nadawo da tunanin shi na kwana a raina da kyar bacci ya saceni kowane moment nawa dashi idan na tuna nakanji wani irin sanyi yana ziyartata, kardai keceman mutumin nan mai bindiga manar ki rufama kanki asiri tunanin shi akan me har kike mafarkin shi?meye sunanshi halim wannan ne bansani nadaiji wanda ya maidoni yace mashi oga bansan yazanyi ba karki dauka wani abu ne ina crushing dinshi ne😻😻😻😻😻😻😻😻😻😻😻😻😻😻 







Halim tayi wata daria tace crushing manar bazaki raba kanki da crushing ba ko,ince nan sam'an zuwa kikayi kikaceman kina crushing akanshi harda kukanki mukaje muka sameshi daga karshe ga abinda yayi maki,wannan din kinsan halin shi kinsan waye shi da zaki saka zuciyar ki a inda bazata amfaneki da komai ba sai wahala,kiyi focusing akan karatun ki,ya taimakeki ne saboda Allah kuma inada tabbacin da yardar Allah ladar shi tana wurin Allah bayan wannan banga dalilin da zaki saka mutum a ranki ba har kina mafarkinshi irin haka jarababba kawai🙄🙄🥱







A tare sukaima juna daria manar ta tashi tashiga toilet ruwa ta sakar ma kanta ko ta samu saukin abinda takeji a ranta daga farkon dare zuwa tsakiyar dare ta rasa gane kanta sonshi takeyi taimakon ta da yayi ne yasa taji ya kwanta mata a rai ko kuwa wata zuciyar tana gudar mata halin dana sani daga baya da tunani kala kala falll a ranta ta fito,har halim ta koma bacci blanket ta shimfida kasa dan jikinta gaba dayan shi ciwo yake mata dayake akwai gajia a tare da ita batai minti biyar ba bacci yayi awon gaba da ita…………….






Dukkansu gajiye suke ya kama kuma da weekend ba lectures koda sukayi sallah asuba sabon shafin bacci suka dasa sune basu tashi ba sai kusan ɗaya na rana as usual yadda suka saba tare sukayi gyaran daki manar tace halim yaufa kece da girki,bazan ba manar na bakin toilet tace bangane bazaki ba?wai haka zakiyi aure bakison girki nidai banison maganar nan manar muyi wanka muje muci abinci,manar ta lumfasa kawai ta shiga toilet tana tausayin kanta amma tana tausayin halin da kawar ta halim ke ciki……………….






Tana wanka tana tunanin halim kudi dai ba matsalar ta bane amma ita bada wani wanda zai kirata yaji ya lafiyar ta yake,saidai babanta shima sai tayi wata biyu ba tareda sunyi mgn dashi ba😪idan ta tuna ita marainiya ce ba uwa ba uba kakar ta kadai guda ɗaya ta rage mata a duniya amma babu ranar Allah da zatazo ta wuce basuyi waya ba taji ya lafiyar ta take,halim mahaifiyarta ta rasu amma dangin mahaifiyarta sun kasa rike ta sbd tsanar mahaifin halim da sukayi………….







Tana cikin tunanin ne taji muryar halim na mata balai ke wlh koki fito ko in shigo har 2 ta kusa kina wanka sai kace mai canza fata shiyasa kullum ma sai kodewa kikeyi sbd ruwa a gurguje ta ida wanka tayo waje halim ta fada koda tagama shirinta tsaf tasa kaya kanta ta kalla a madubi wasu hawaye suka shiga zubo mata,tana tunanin makomar ta da nude dinta sun fita hannu ta daga tace Allah nagode maka Allah ka tsare shi ka kare shi a duk inda yake………………






Daga bayanta taji halim tace amin bazaki raba kanki da tunanin gayen nan ba ko?kai tsaye ta kalli halim tace bazan iya ba halim ki tayani da addu'a kawai bazan tayaki ba wlh,ya bansan mutum ba idan mugu ne in tayaki addu'a Allah ya amsa maki kishiga cikin wata damuwar addu'a daya zan maki Allah yayi maki zabi nagari bayan wannan bazan so in ganki a wani yanayin ba eh😭








Tare suka fito gwanin sha'awa wanda jiya basu samu ganin manar ba sunata mata sannu dan bayan halim ba wanda yasan menene ainahin abinda ya fitar da ita cikin ruwan nan gaban wani restaurant sukaje shigar su keda wuya aka kawo masu menu zabar halal food sukayi sukaci suka koshi halim ta biya bills din kusan 200k sukaci zama daya,manar ta riko hannun halim zatayi magana tayi sauri tace nasan mezakice kiyi shiru kawai manar idan ban kashe kuɗin nan bansan mezanyi dasu ba kullum daddy saiya turoman kudi……………….







Mu hadu a next page pls don't forget to like share and comment It's me SM AUTA💃💃💃💃💃