HASASHEN SOYAYYA

Hs 25

by @legendspen

_Page 25_



Hannusu rike da ƙaramin bakko, da mamaki sosai take kallonsu har suka karasa shigowa,har ƙasa suka tsugguna tare da faɗin. "Ummah ina kwana?."


"Lafiya lau, ya mutan gidan?."


"Alhamdulilah Ummah, mun zo ne a amshi kayan Bhatool da mu a matsayinta na yar uwarmu" murmushi Umma ta yi sanan ta ce. "Sannunku da zuwa, ko shigo ciki." Bhatool dake ɗaki ce ta ce. "Ubam wa ya gayyace su, wallahi sai sun koma mumafukai." 


"Kar ki fara Bhatool wallahi." Yaya Karima ta tare ta. "Yaya idan ba munafunci ba mai ya kawo su?." 


"Ko ma munafuncin ne mene a ciki, ai sai ka kai za ayi maka munafunci, ke kina musu ne?." 


"Me zai sai na yi musu munafunci, sai ka ce mara aikim yi?."


"To kinga ke kenan kin kai su yi miki, dan Allah idan sun shigo karki yi musu rashin kirki." 


"In sha Allah." Bhatool ta faɗa, sai kuma can ta ce. "Yaya yanxu nan zan zauna har su su zo." 


"A'a, zai dai ki shirya ku je gidansu Na'ima idan sun buƙaci ganinki sai a kiraku." 


"Okay, daman Amrah ta ce mun tana hanya ma." 


"Yawww to, Allah ya kawo ta." Yaya Karima ta faɗa dai dai lokacin da su Furee da Hari suka shigo, da mutunchi Yaya Karima ta karbesu haka ma Bhatool ɗin, faran-faran a kawo musu abinci da na sha, suma kuma suka miƙe aka shiga aiki da su har zuwa lokacin da Amrah ta zo, Jannah ba ta sami zuwa ba. Ko da a ka ce su tafi gidansu Na'ima sai Amrah ta ce ita zata tsaya ta yi bidiyon shigowa da kayan ne. 



Shigarsu gidansu Na'ima kenan Senate ya kira wayarta. "Hello Fulani." 


"Na'am." Ta faɗa a hankali. "Sun isu?." 


"Bansaniba, yanzu na fito daga gidan." 


"Ina zaki kuma?." Murmushi ta yi sanan ta ce. "Kasuwa." 


"Wane kasuwa kuma, me zaki yi." 


"Abu zan siyo." Ta faɗa tana kunshe dariyarta. "Wai dagaske kike." 


"Dagaske mana ranka ya daɗe." 


"Gaskiyya ban yarda ba ki dawo." Dariya ta yi sanan ta ce. "Gidansu Na'ima fa na shiga, kasan dai ba a zuwa a sami mata a gidansu indai ba babban gida suke ba." 


"Auh, har na ji daɗi amma sun yi delay fa." 


"Na ji hayaniya kaman sune suka iso."  Ƙarar guɗa ce ta cika ko ina, kamar anan gidansu Na'ima akeyi domin mutanen unguwa gaba ɗaya su ka fito domin yi wa Mama kara kasancewarta mutuniyar kirki a unguwan, Furee ce ta ce. "Kunga bara dai na leƙa." Ba ta jira cewar su ba ta fita, motoci ne sunfi guda goma, sanan kuma ga wata katuwar mota irin a kuri kurar nan, guda biyu cike maƙil da akwatuna baki sake mutane ke kallon motocin, har aka fara suke kayan, manyan mata suka fara fitowa cike har da matar minista, masu bidiyo sai dauka suke suna ɗorawa live cikin ƙanƙanin lokaci Live ya zaga ko ina, dakin da Mama ta ajiye na tarbar baki da kayan lefe ya cika maƙil da kaya hakan yasa Anty Asabe kawar Mama ta ce. "Ku fito da kayan waje kawai, su shiga ciki." Hakam a ka yi suka shiga fito da kayan, manyan matan sun saki jiki babu ƙyama ko wani abu, haka su ka zauna falo suna ta gaisawa da maƙwaftan Mama, haka aka kawo musu kayyyakin da a aka yi order ɓasu yawa, hakanan suka buɗe suka fara cin abinda za su ci, daya cikinsu ta ce. "Akawo mana Amaryar mana."  Yaya Karima ce ta kalli Amrah da ke tsaye tana ta faman daukan hotona ta ce. "Amrah kuje ku shigo da ƙawarki."


"Tom Yaya." Ta faɗa tare da ajiye wayar ta fita zuwa gidansu Na'ima. "Ke ƙawatah kin gama yin goshi, akwati hamsin fa." Amrah ta faɗa bayan ta shigo. "Yoo aini na aza arba'in ne ma." Furee ta faɗa. "Hamsim ne cif, ki taso suna nemanki zasu tafi." Tsuke fuska ta yi sanam ta ce. "Yamzu dole sai naje." 


"Idan bazakije ba, ni sai na rufe fuskana na je." Amrah ta faɗa. Mikeww Bhatool ta yi suka rufa mata baya zuwa gidan, lokacin kowa ya fito daga dakin anbarsu su ka dai, makwaftan nata santin yawan kayan da aka kawo wa Bhatool. "Ki shiga ku gaisa." Yaya Karima ta faɗa bayan su Bhatool sun shigo. "Tom." Ta faɗa tare da shigewa ciki, Amrah ta bi bayanta. A hankali ta taka ciki, bakimta dauke da sallama, wanda suka amsa kowacce baki washe da fara'a. " ina yininku?." 


"Lafiya kalau Amarya." Suka amsa baki daya. "Buɗe mana fuskar mana." Daya cikimsu ta faɗa, ido Bhatool ta kai kanta kana ganinta kaga Mom. "Da alama ita ce ƙanwar Mom, Maman Anas." Bhatool ta faɗa a ranta, sanan ta kai hannu ta buɗe fuskar, dukkansu sun yaba da kyan Bhatool a ransu, haka kuma da irin tarbar da Mama ta yi musu, sai da suka dan jima sanan suka ce. "To zamu huce, kamar yadda lissafi yake saura kwama goma sha biyu tariyar, amma evennts ɗinmu saura kwana biyar In sha Allah mu fara." wanan mai kama da Mom ta faɗa. Yaya Karima ce ta ce. "To Allah ya nuna mana." 


"Amin ya Allah." Suka faɗa tare da ta shi suna ficewa. "Ya sunanki." Wacce ta yi mgana ɗazu ta faɗa tana kallon Amrah. "Sunana Amrah." 


"Amarah Allah ya yi albarka, Bhatool nice Maman Anas." Murmushi Bhatool ta yi sanan ta ce. "Aina gane ki kam." Myrmushi matar ta yi sanan suka fice da tawagarsu, bayan sun fita ne aka hau duna kaya ta ko ina, tun ana lissafa yawan atamfofi amma tun da aka zo kala ɗari biyu da hamsin kowa ya gaji, ƙarshe dai ansami atamfofo kala dari uku da goma, laces kala ɗari da hamsin, manyan shaddoji kala saba'in materials masu kyau da tsada kala talatin, dogayen riguna kala dari da goma sai kuma sauran kayyaki, ga Gold da kuna mukkullin mota. 


Cikin yan awanni zamce ya karaɗe media, kowa kiran Bhatool yake yana ta ya ta murna, haka shima Senate ko ina taya murna ne, wasu ma na cewa zasu daukar masa nauyin events kasancwwar shi na Mutane, yana da yawan taimako ko mai kuɗinka cikim abokansa, in dai yaji zakayi aure sai ya daukar maka nauyin wani abu mai girma, haka Mom wasu ƙawayen nata sai waya suka mata wai bata kyauta musu ba, Aminyarta Hajiya Shuwa ma cewa ta yi, Ajira na ta lefen yana zuwa gobe, gaba daya gida ya kacame ya rikice. 




"Bhatool, ya zamu yi da zancen ashobe ne wai events nawa za ayi?." Kallon Jannah da Amarh dake zaune ta yi sanan ta ce. "Wallahi nima bansaniba." 


"To ai ba a haka daya zaki haɗa da shj Senate ɗin ya haɗa ta da abokinsa a tsara komai, kina ji events ɗin fa saura gaba daya kwana 12 yanzu."  Amrah ta faɗa. "Hakane kam, amma Amrah sai dai ta haɗaki da abokin nasa gaskiyya, domin kinfi deserving komai you're a good friend." Jannah ta faɗa, domin ita kanta tana sarawa Amrah bisa yanda ta jajjirce a lamarin bikin Bhatool. "Eyh hakane, bara na kira shi ko." Bhatool ta faɗa dai-dai lokacin da Habi ta shigo, hannun ta rike da plast. "Gashi Bhatool." Amsa ta yi sanan ta ce. "Ni wanan masifa ta fara isata wallahi." Dariya suka yi baki daya sanan Habi ta ce. "Bara naje naƙarasa aikina, yanzu sai kiji baƙi tun da yanzu mu bama rasa baƙi." 


"Ai Bhatool ta jawo jama'a." Jannah ta faɗa tana dariya, sai da Habi ta fice sanan Amrah ta ce. "Wai wayanan zaman me suke yi basu tafi ba, basu ne marasa mutuncin nan ba?." Dariya Bhatool ta yi sanan ta ce." Ai sun canja wallahi, kuma Mama ce ta ce kawai su zauna har biki, jiya ta ce da Yaya Karima idan abun arzikin ta dore ai sai ta riƙesu kafin suma su yi aure, kinsan Furee bazawara ce to naji ma ta ce ita karatu take son komawa." 


"Ai kam dai Mama ta kyauta wallahi." In ji Jannah ita dai Amrah ba ta ce komai ba kiran Senate ya shigo,bayan sun gaisa ne ta ce. "Annur wai su Amrah ne ke tambayar Events ɗin sabida muna son fito da Ashobe." 


"Hakane Fulani, dazu mun yi magana da Mom ta ce ita dai nata events ɗin na kanta guda uku ne, sanan ƙawayenki gaba daya mutum sha biyar ake so, akwai Ashobe din da aka tanadar musu na dukka events ɗin, za aka wo su gida ko zuwa gobe, sauran kuma bansan yadda za ayi ba, mu guda nawa zamuyi?."


Follow for more update, Allah Ya saka da alheri. 



Legendspen ***