3
Ya abin yake?
Daban yake da sauran.
Da sauri Sadiya ta fincike wuyanta haɗe rai sosai tayi ta ce "kada ki fara kada kiyi wannan kuskuren, ko ina yarinya ban yarda da dambe da kishiya ba, balle yanzu da nake da ƴaƴa da jikoki har da surikai."
A zafafe Ammi ta ingijeta tare da ɗaga hannu zata zabga mata mari dai-dai lokacin da drivern Didi ya danno hancin motarsa cikin gidan tare da sakin gigitaccen horn, bisa bin umarnin Didi don sanar da masu gidan zuwanta, wanda hakan shine tambarinta.
Cak Ammi tayi da hannunta cikin matuƙar ɓacin rai da haushin bayyanar jarababbar tsohuwar, tayi tsaki ta fice daga sashen Mahmahn da sauri don ta san tabbas Didi tazo ta tarar da wannan tashin hankalin ranar na lahira ma sai yafi ta jin daɗi. Mahmah tayi murmushi kafin ta furta “Gaba da gabanta”da ki tsaya mana. Sannan tayi azamar fita don tarar Didin.
Fuskar Didin a washe take kallonta, da duk jama'ar gidan tana amsa gaisuwarsu cike da murnar samunsu lafiya, ahalin Sakina ne kawai bata gani ba. Bata damu kanta ba ta san dalilinsu na ƙin zuwa bai wuce ba sa son tayi musu gorin rashin aure ba, alhali ba mijin suka rasa ba suna dai jiran wanda ya ci ya tada kai.
Murya a cunkushe ta kalli Sadiya ta ce"Ita hakimar kishiyar taki tana ina?" Mahmah ta ɗan yi jim kafin ta ce "Ina ji sallah take tunda baki ganta ba." ta samu kanta da gillara ƙarya duk don ta gyara lamarin. Didi ta kalli agogon hannunta kafin ta ce "Sallahr walaha take Kenan da sha biyun rana? Sadiya kenan kishiya kike karewa don kada nayi mata sababi? ai ba tun yau na san Sakina bata ƙaunar taga nazo gidannan ba, saboda bata son na sawa yaranta ido to wannan karan a shirye nazo tsaf wallahi ba zan bar gidannan ba sai na aurar da iyayen matan da ta girke a ɗakinta, su ba zawarawa ba su ba ƴan mata ba, shi kuma soloɓiyin mijinku ya saka mata ido sabida baya son laifin balarabiya."
Sunkuyar da kai Sadiya tayi kafin ta ce "Kiyi haƙuri Didi ai aure lokacine da zarar lokacinsu yazo ko suna so ko basa so sai sun yi."
Dai-dai lokacin da Ammin ta shigo kuma duk wani sababin Didin akan kunnenta take yi ranta ya sake ɓaci shikkenan wannan matar zata zo ta ɗaga mata hankali.
Fuskarta ba yabo ba fallasa tayi sallama haɗe da faɗawa cikin parlourn. Didi ta zuba mata ido tana jijjiga kai ganin yarda Sakinan ta cono ɗankwali har gaban goshi,alamar dake nuni da cewa a shirye take da amsar duk wani rashin mutunci na Didin. Murya a cunkushe ta fara gaisheta Didin ta yamutsa fuska kafin ta ce "Ai Sakina da kin bar gaisuwarki tunda ba dole nace sai kinzo kin gaisheni ba, ba buƙatar ta nake ba gaisuwar da za'a yiwa mutum ana faman ɗaga hanci dai-dai nake dake wallahi, ki bini a hankali kafin ki kaini bango." Sakina dai ɗan murmusawa tayi wanda direct zan iya kiransa dana rainin hankali ta miƙe cike da izza tace "A huta lafiya Didi" daga haka ta kaɗa zaninta ta wuce ta bar Hajja Didi da hangamemmen baki don kuwa ta hango raini tsagwaronsa a fuskar Sakina, girgiza kai tayi kawai tana kallon Sadiya tace "Shahara iyye! Cabd’i jam" girgiza kai itama Sadiyar tayi ita kanta tana mamakin yarda Sakinah ta fetsare har haka? Didin da ko ido mutane basa iya haɗawa da ita idan tana magana. Ita dai murya a sarƙafe ta hau bata haƙuri sannan ta miƙe don ta bawa Didin waje ta huta har ta kai bakin ƙofa Didin tace "Ina Hamda ne ban ganta ba ko bata gama gallafirin makarantar kwanar bane?" Sadiya ta girgiza kai ta ce tana ɓangarena bata da lafiya ne yau ma aka yi discharging ɗinmu daga hospital ai da tuni kin ganta ta fito."
"Subhanallahi me ya sameta haka? Yanzu haka shaiɗaniyar uwarta har yau bata san annabi ya faku ba ko? Wannan mata sai kace wacce tazo a zamanin jahiliyya ƙiri-ƙiri ka ƙi ƴarka ba laifin tsaye ba na zaune, muje in ganta ai gwara da aka mayar da ita ɓangaren naki, naga uban da zai ce sai ta koma gurin wulaƙantacciyar matar can da ta zamewa mijinki matar jaraba." Ita dai Sadiya murmushi kawai ta saki ta bi bayan Didin tana tafe tana riƙe zaninta da yake shirin faɗuwa.
A kwance suka sameta idanunta a lumshe lokaci guda ta sake zabgewa dama ita ba jikin arziki ba kyalan-kyalan take tamkar ta faɗi ko don bata da kwanciyar hankali ne Allahu ya alamu. Didin da sauri ta ƙarasa gefen gadon ta zauna tana dafa goshin Hamdan, da kyar Hamdan ta buɗe idanunta da suka zama tamkar garwashi ta zuba su akan Didi tana sakin wani malalacin murmushi, tana shirin miƙewa Mahmah ta ce "Koma ki Kwanta Ke da ba kya jin daɗi." Wani kallo Didi ta zabga mata kafin ta ce "Ta zauna a ina? Bayan Allah ya kawo ni, ke tashi dahalla mu wuce idan banda kafirin iyayi na Sadiya me ye haɗinki da ita da har zaki rabamu? Sadiya ta gumtse dariyarta ta ce "Ayi haƙuri Didi bari na taimaka mata ta koma ɓangarennaki" "Ya dai fi, in banda shegantaka ba ita take taya ni hira ba, sai kuma a barni can a zaune ni kaɗai kamar wata mayya dama ku gidannan ba wani yawan arziki ba kowacce ta tsaya ragwanta daga haihuwa biyar kawai ni sai da na haihu sau goma sha huɗu ke da kanki kin sani zama ne kawai Allah baiyi zasu yi ba, Huɗu kacal Allah ya raya min na kuma gode masa a hakan ma, muje dahalla kin tsaya min wani iyayin banza."
Ammi da take tsaye a jikin window ta hango fitowarsu ana rirriƙe da Hamda wani abu mai kama da tausayi yaso shiga ranta amma sai tayi tsaki kawai ta saki labilan zuciyarta na sake ɓacin ran ƙin barinta ta cigaba da wahalar da Hamda da aka yi, yarinyar da ko sunanta bata son ji bare karo da baƙar fuskarta.
Didi suna shiga ɗakin ta hau damawa Hamda fura da nononta mai kyau da tazo da shi, sai garin fura mai ƙanshi da aka yi mata dakan hannu sai zabga ƙamshi yake. Sosai damun yayi kyau sai ƙamshi take bata saka mata sugar ba sai zuma farar saƙa.
Da kyar Hamda ta miƙe ta karɓi furar ta fara sha dama Allah ya zuba mata son fura don dai bata samu ne sai Didi tazo, don wani lokacin da gangan Ammi take dama furar kuma ta hanata ta bawa masu aiki saboda ta san tana tsananin son furar. Ta lumshe ido tana jin daɗin zuwan kakartata da ta tabbatar soyayyar da take mata babu algus. Sosai ta samu ƙwarin jikinta har ta miƙe da kanta ta shiga toilet tayi alwala tazo ta tada sallah a gefen Didin da take sallahr itama.
Suna idarwa suka jiyo sallamar su Muneerah Najma da Nasma fuskar Muneerah ce kawai a washe banda ta su Najma da suka yi kamar an aiko musu da saƙon mutuwa.
Muneerah da sauri ta isa wajen Didin tana gaisheta, itama cike da kulawa take amsawa tana son Muneerah musamman da yake ita sunanta taci "Ina kika shiga tun ɗazu ban ganki ba?" Muneerah tana ɗibar fura ta ce "Wallahi Didi Islamiyya naje da na gaji da tsimayin zuwanki.".Didi ta ce "Masha Allah ubangiji ya bada nasarar karatu. Ku kuma asararru ina kuka shige ana nan dai ana haɗa kafaɗa da iyaye an ƙi aure ko? To ku kwana da saninku wannan karan da shirina nazo inma ku fitar da miji ko ni na fitar muku acan Gwarzo cikin dangi ko abokan arziki, na baku wata ɗaya kacal wallahi wannan karan ba zan karɓi uzirinku ba ko kun wuce azimi ba zaku wuce sallah ƙarama ba insha Allah ku haƙura ku zaɓi ko waye tunda govenor da shugaban ƙasar har yau ba su ganoku ba, sai ku rungumi haƙuri kafin furfura ta fara bayyanar muku a gida, don kyan da kuke taƙama da shi zagwanyewa zai yi matuƙar babu aure shashashai kawai." suna gama gaisheta suka miƙe ransu a. ɓace da tijarar da take musu suka ƙarasa wajen Ammi Suna shiga taga alamun Didi ta kunnosu tsaki tayi kawai tayi kafin ta tambayesu mai ya faru? Najma ta zauna tana zuba tagumi ta ce "Jarrabar tazo yaushe zamu ga dai-dai daga zuwanta har ta fara zancen aure wai mu zata haɗa da ƴan gwarzo kurt da kuwa sai ta gwammaci kiɗa da karatu wallahi don ba mai saka ni auren mutumin ƙauye." Tsaki Ammi tayi kafin ta ce "Ya zama kuwa dole na tashi tsaye wajen samo muku mazaje na kece raini ko da kuwa zanyi yawo tsirara burina naga kun auri mazan kece raini da zanyi tunƙaho dasu a matsayin surukai tunda dai Allah bai bani yara mazan da nake burin naje gidansu na baje mulkina ba, kamar yarda waccan tsohuwar take baje nata, tun ina yarinya ban fi shekara sha shidda ba nasa wa raina son haihuwar ƴaƴa maza ganin yarda yayar Mamma na take baza mulki a gidajen ƴaƴanta maza Ita kuwa Ummi mu kawai ta haifa mata bata da inda take zuwa tayi tunƙaho sai daga baya ta haifi ƙaninmu shikkenan na sawa zuciyata burin haihuwar maza amma Allah bai cika min burina ba, duk da ƙoƙarin da nayi tayi akan haka."
Tana faɗar haka hawaye ya shiga gangaro mata akan fuskarta wanda hakan yake nuni ƙarara da zallar ɓacin ran da yake zuciyarta.
Ko da Abbu ya dawo zancen dai ɗaya ne Didi ta tareshi da shi ta kuma tabbatar masa wannan karan da gaske take dole ne ta aurar dasu da son su ko ba son su, su suka kawo mijin ko akasin haka ta sake jaddada masa "Idan har kaga hakan bai faru ba tabbacine na rashin rayuwata, amma ko sharafa nake a gadon asibiti sai na aurar dasu banda tsiya ko Munirah da Hamda sun kai munzalin aure. Shima kuma Hammad ka sanar dashi ya tattara ya dawo gida Yaro shekara sha uku yana can zube a ƙasashen masu jajayen kunnuwa yayi sammakal ko matarsa yana can aka Kai masa ita, ai barewa ba tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba. To wannan karan da shirina nazo ƙwal uban kowa zan ci har shi Hammad ɗin da ku iyayensa." Abbu dai sunkuyar da kai yayi yana jaddada mata za'a yi yarda take so.
Haka nake so Didi, ki soyawa kowa gyad’arsa a hannu y’an k’wal uba.. [11/21, 2:17 PM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE
YA ABIN YAKE ?
LIttafin Nazeefah Nashe.
***
Follow me on ArewaBooks
@nazeefah https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e
ELEGANT ONLINE WRITERS
(Haɗin kai shine takenmu.)