4
*******************************
Da asubar fari, da tayi sallah bata koma ba, tana zaune gefen Didi suka yi azkar kafin ta karanta abinda ya sawwaƙa daga Alƙur'ani mai girma. Bata koma barcin ba, kasancewar ta ɗan ji sauƙin jikinta gyara sashen Didin tayi tas. ta wanke toilets uku da suke sashen ɗaya a Parlour biyu a sauran bedroom ɗin da suke sashen Didin inda ta mayar da ɗayan bedroom ɗinnata duk da dai Didin bata yarda su raba ɗaki ba tare suke kwana. Tas gurin ya fito sai zabga ƙamshi yake farin ciki ya lulluɓe Didi yana daga dalilin da yasa take son Hamda, sam bata da ƙiwa ko kaɗan. Wanka Didi ta shiga tana faɗin kema sai ki shiga kiyi wanka ga sabbin kaya nan da na ɗinko miki don na san waccan gallafirin uwar taki ko kayan ubanku yayi muku ba bari take ki saka ba, ta gwammaci ta haɗaki da gwanjo ina nan Ina jiran ranar da zata zo tana neman gafarar ki, to ko cikin shegen Ki tayi ai iya ɗiban albarkar da zata yi kenan, balle laifinki ɗaya wai kinzo a mace, shikkenan tun ranar da aka haifeki ake gumurzu da ita bari muyi walaha mu karya na baki labarin da kika daɗe kina son ji na san yanzu shekarunki sun kai sha bakwai tsab kwanyarki zata ɗauki labarin takaicin uwarki mai hali kwatankwacin na jahiliyya, na tabbata ita da kanta banda an saka mata ido tsaf zata iya hallakaki a lokacin, kai mun ga tashin hankali Ƙiris fa ya rage ta zauce sabida masifa.
Daga haka ta shige wanka wannan damar Hamda ta samu tayi saurin ficewa tana mamakin surutun Didin.
Sashen mahaifiyarta ta shiga, dama da spare key a hannunta ta buɗe a hankali, shiru ta tarar da parlourn da alama barci suke tabi gurin da kallo duk datti ɗan kwana biyun da tayi bata yi shara ba. Dama ita Ammi sam taƙi yarda ta ɗau mai aiki don tace gata bata buƙatar wata mai aiki. Ta ɗaure Hijabinta a ƙugunta ta shiga wanke kwanukan kitchen ɗin ta gyarashi tsaf burinta ta faranta mata ko ta samu ta goge tabon ƙiyayyarta a zuciyar Ammin.
Kan kace me? Ta gyare gidan tsaf banda ɗakunan barcinsu ta wanke har toilet ɗin parlourn sannan ta saka turarukan wuta a burner da humidifier tuni gidan ya ɗau wani irin Ƙamshi daga haka tayi sauri ta fice ta koma sashen Didi.
A saman sallaya ta tarar da Didin da alama sallahr walaha tayi, ita kanta Didin ita Ta koyar da ita sallahr walahar, tana sake jaddada mata ɗimbun ladan da yake cikin Sallahr walahan da tarin nutsuwa da mai yinta yake samu a zuciyarsa, ga shi Allah yana amsa addu’arsa ba da jinkiri ba.
Wankan itama ta shiga ta yiyo sannan ta ɗauro alwalarta ta saka tsaleliyer atamfarta da Didin ta ɗinko mata kaya ne kala goma dama ta saba duk sanda zata zo sai tayi mata don ta san kafin tazo nata sun mutu tunda ba wata sutturar arziki uwar take barinta ta saka ba. Idan ka shigo gidan ma zata zaka yi ƴar aiki ce, Saboda tsabar yarda zaka ga kayan sun ƙojale don tsufa ga kanta da baya samun cikakken gyata fatarta ma don dai Allah yayi ta cikin jinsin mutane masu taushin fata ne, da duk wahala bata jemewa tabbas da ba ta kai haka kyauba.
Tayi kyau sosai ɗinkin kuma ya zauna a jikinta tamkar ba daga ƙauye aka ɗinko mata su ba. Ta cukuikuye gashinta ta danna cikin ɗankwali don rabon da ta tajeshi har ta manta balle ta saka man kitso, ko wanke shi tayi haka take barinsa.
A gefen Didi da take lazimi da jug ɗin furarta a gefe ita ma ta tada sallahrta cikin nutsuwa. Sai da ta idar tayi addu’ointa Didin Ta tura mata cup cike da fura tace “Maza kwankwaɗeshi tas ki bani cup don na san waɗannan mashiriritan kafin su kawo abin karyawa sai goma ta gifta shi yasa wannan karan zan saka ya kawo min kayan abincina kaf da kaina zan dinga girki ba zan iya zaman jira ba, girkin da sai an ga dama sannan ake yin mai daɗi ko a zabga mai da maggi to bana ba dani ba kowa ta riƙe banzan abincinta."
Ita dai Hamda murmushi ta saki kawai tana kai cup ɗin furar bakinta. Ta shanye tas zuciyarta cike da farin ciki. Har zata kishingiɗa ta kwanta sai kuma ta miƙe ta ce "Didi baki ba ni labarin ba." "Ƴar nema ashe kina so bari mu ɗan runtsa tunda yau ba islamiyya sai na baki anjima yanzu kam idanuna har yaji yake.” Duk da ba haka ta so ba haka ta hakura don ta san idan ta matsa Didin zata iya cewa ta fasa.
________________________________
Ammi na fitowa ta ga parlournta tsaf sai baza kamshi yake da sauri Ta isa bedroom ɗin ƴan matanta don a tunaninta su suka yi sharar tunda Ta san Hamda na can ɓangaren Didi turus tayi ganinsu sheme suna barci har Muneerahn da take zaton ita tayi.
Jikinta a sanyaye ta juya don ta tabbatar Hamdan ce dai tayi, wani abu ya Tsirga a ranta mai kama da tausayin uwa ga yaranta, sau tari tana tunanin sassautawa Hamdan sai dai tuni shaiɗan yake rinjayar zuciyarta wajen tunanin Hamdan a matsayin wata tashin hankali ce wanzuwarta a rayuwarta, mutuwarta a zahiri ita tafiye Mata alheri shi yasa take takura mata ko don wataƙil zuciyarta ta buga ta rasu ta huta da baƙin cikinta, don tabbas idan Hamda bata mutu ba nan gaba kaɗan akwai tashin hankalin da bata so ya afku tana da rai wanda zai zamo tamkar tozarci ne mai girma a gareta da zuri’ar D’an Borno gaba d’aya. Ta sha auna kashe Hamdan a ranta sai dai tana fasawa gudun fallasuwar asirinta da kuma tonuwar sirrin da ta riga ta bisne a cikin ƙasa.
Ta ja ajiyar zuciya bayan ta zauna ta nutse a cikin kujerar three seater ɗinta samfurin royal da take girke a babban parlourn, idanunta akan tv tamkar mai kallon labaran da ake yi sai dai gaba ɗaya zuciyarta ta Lula can tunanin wani zamani da ya shuɗe.
_____________________________
Barci sosai su kayi bayan idar da sallahr walahar akan faffaɗar daddumar Didin mai laushin tsiya da take ambula mata turare kullu yaumin don son tsaftace wajen ibadartata da yake can kusurwar ɗakinta. Bugun ƙofar da ake yi ne ya farkar da su daga barcin Hamda ta miƙe don taga waye itama Didin miƙewa tayi tabi bayanta da hanzari don bata da jiki ko kaɗan shi yasa bata jin nauyin jikinta.
Saliha ce mai aikin Mahmah ta shigo hannayenta ɗauke da manyan warmers bayanta kuma Humaid ne yake biye da ita da flask ɗin tea. Didi ta dinga amsa gaisuwarrsu tana girgiza kai haɗe da duba agogo "Ba shakka, wannan abincin da mai za'a kirashi kenan na safe ko na rana? Kai jama'a ayi mata da shegen lalacin tsiya, to ni ba zan yarda da wannan tujarar ba bari wanda ya ajiye su yazo na faɗa masa ya jawa matansa kunne dama kada wacce ta sake ɗora sanwarta dani, su riƙe abincinsu can, zan dinga yi da kaina naga acan gwarzon ma da kaina nake yi to name za’a dinga wahalashsheni Allah na tuba abincin ma da ba ɗanɗanon arziki." Ta faɗa tana buɗe coolerr abincin faten dankali ne da ya sha busashshen kifi da alayyahu sai ɗaya coolerr farfesun cow-tail ne ɗayar kuma gurasar larabawa. Baki ta taɓe,dan ta tabbatar dai abincin ba makusa sannan ta ce Hamda ta kwaso plates ta zuba musu.
"Ku tashi kuje ku ke kallona kamar kun samu akwatin kallo, kai kuma me ya hanaka zuwa makaranta." Humaid da yake duk a tsorace da faɗan tsohuwar ya ce "Hutun independent day muke." kallo ta watsa masa kafin ta ce "Wani abu ne kuma indafadan?" Ba Humaid kaɗai ba har ta Hamda sai da ta tuntsire da dariya Didi Ta ce “Kaji min aikin banza faɗar tawa kuke wa dariya? Aikin kawai to turancin faɗar annabi ce da sai na iya? ka tashi kaje kace ina son ganin ubanka tunda gaisuwar ma sai na roƙa." Humaid ya fice yana dariya Ƙasa-ƙasa a zuciyarsa ya ce "Drammer Queen"
Abincin suka ci sosai kafin Hamda ta kai kwanukan kitchen ta ɗaurayesu sannan ta dawo.
Man zafi ta ɗauko tana shafawa Didin a ƙafarta. Didin ta ce Alhamdulillah tunda ciki ya ɗauka bari na baki labarin asalinmu ciki da bai, da yarda aka yi auren uwarki da ubanki ba bisa son raina ba.....”
_____________________________
Asalin kakanku haifaffen garin maiduguri ne kasuwanci ya kawoshi kano Ƙauyen Gwarzo, inda anan Allah yayi arzikinsa yake kuma anan ya had’u dani ya aureni har muka hayayyafa duk a Ƙauyen Gwarzo. Haihuwata sha huɗu sai dai a ciki huɗu ne suka rayu mahaifinki Umar ne babba sai Aliyu kafin na haifi Aliyu kuwa yara uku na haifa tsakaninsa da mahaifinki sai dai basu zo da rai ba.
Daga Ali gadanga ƙusar yaƙi sai Gwaggonku Asma'u da take zaune a can ƙasar dubai da mijinta daga ita kuwa haihuwa biyar nayi ba rai kafin na haifi autata lauratu wato Ammanku Ta Janbulo daga nan ne fa haihuwar Ta tsaya min bayan nayi biyu ba rai. Ni kad’ai ce wajen kakanku Usmanu dan Borno bai sake aure ba duk da baloƙoƙon da danginsa suke masa wajen son ya ƙara auren acan gida borno har mata aka bashi amma yace ya yafe ni kad’ai na isheshi tunda ina yi masa duk abinda yake so baya son yazo ya had’a tashin hankali a gidansa yana zaune lafiya.
Haka suka gaji suka zuba masa ido duk da surutun da suke masa yasa auduga ya toshe kunnensa ya ce ba zai ƙara aure ba. Ni nan da kike gani na macece mafaɗaciyar gaske da ba na barin ta kwana in dai ka takaleni ka taɓo masifa bana shiga shirgin kowa amma fa bana yarda a taka ni. Hadizatu nake mutane da dama suna kirana wargi kike dai-dai Ƙugun kowane ɗan iska. Shi yasa duk garin Gwarzo in dai kika je kika ce kina neman Didi matar D’an Borno to kin gama samu na saboda shaharar da nayi a masifa, wanda bakomai bane sai zallar fad’ar gaskiya da mutanenku basa so yanzu. Ko iyayenki Shakkata suke, saboda bana sakar musu fuska kamar yarda Kakanku yake sakar musu. Ba yabon kai ba dole Kakanku ya kasa aure sabida na riga na siye zuciyarsa da girki tunda shi in dai cikinsa zai d’auka to kin gama masa komai, idan kinga masifarsa to ya dawo gida ban gama abinci ba. Sannan ba yabon kai ba ina da tsafta dai-dai gwargwado, ga kwalliya kamar me don idan na cab’a kwalliya irin Ta mutanen da baki ga yarda yake zama yayi ta kallo na ba, na tabbata da yanzu zan yi wannan kwalliyar wasu ma mahaukata za su d’aukeni. Idan kuwa kika shigo gidana ba abinda zaki fara jiyowa sai k’amshin turaren wuta da na tsinke d’an Borno, don sana’ata kenan duk da ba wani ciniki nake ba kasancewar jama’ar garin mu basu damu da k’amshi ba. Ke na fa zabga iyayi ina yarinya Wani suna suke kira na da shi Delu iyayi har na haihu Umaru ya cigaba da kira na wai Delu, bisa tilas na koya masa cewa Didi shikkenan sai sunan ya bini. Idan kakanku yayi fushi wuyartana shafe baki na da jan jambaki nayi d’igo-d’igo a gefen k’uncina na ja siririyar jagirata, na bad’e fuskata da hoda pankeke shikkenan zaki ga ya daina fushin yana bina da ido yana fad’in Indiyana ni kuma kaina yana kumbura duk da ko a layin bak’ak’en India ba za’a saka ni ba, gashinta k’ak’k’arfa ne irin na hausawa, haka nan ba wani idon arziki gareni ba ga ni bak’a kamar yarda kika ganni d’in nan, amma don son ran kakanki yake kira na Indiyana ni kuma ina amsawa Cike da izzar nafi sauran mata, duk da wani ko a k’afa aka k’ulle masa ni ina tabbatar miki sai ya kunce ya arce ni da y’ar dab’as... wata dariya ce ta kufcewa Hamda, ganin duk suffofin da ta zayyana Haka zubinta da fasalinta yake, sam bata da tsaho ko kad’an...
Hajiya Didi tamu.... [11/21, 2:17 PM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE
YA ABIN YAKE ?
LIttafin Nazeefah Nashe.
***
Follow me on ArewaBooks @nazeefah https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e
✍✍✍📖📖📖📖📖✍✍✍
ELEGANT ONLINE WRITERS
(Haɗin kai shine takenmu.)