Page 5
Ina macen datake fama da ciwon mara in mijin yana saduwa dake kirinka jin xafi to kixo kimallaki female care
Ina masu fama da basir constfree tea yana magnin basir yana gyara fata tayi kyau
Royal jelly ya gyara mace yafito mata da shafe dinta kama daga breast hips duwawo
Fat bunner yana rage kitse ina wanda kitse ya mata yawa a jiki kigarxayo kimallaki naki ***
Gamai bukatan yin register xai iyayi yasaya afarashin company
Company ght zakiyi registered akan 4500 kikawo mutun biyu suyi siyaya company zatabaki 36000 inbaki shiryaba karkimin mgn ngd
**************************** _Mu d’in ba wasu masu wadata bane sai dai muna cikin ni’imar ubangiji, don bamu rasa ci ba, bamu rasa sha ba, Kakanku a tsaye yake sosai akan iyalinsa ta yarda duk abinka baka isa ka hango gazawarsa ba, ya tsaya sosai musamman ga karatun iyayenku, burinsa a kullum bai wuce yaga sun samu nagartaccen ilimi ba, na boko da na muhammadiyya, Musamman Babanki Umar. Sanda ya gama secondary School Allah ya taimake shi har jami’a yaje can zaria inda yayi karatunsa a ‘bangaren Zane-Zane kasancewarsa mai hazaƙa wata rana kawai yazo min da labari mai dad’i wai Gwamnati ta d’au nauyin karatunsu ‘kasar waje can ‘bangaren larabawa ‘kasar Jordan zasu je su yi babban degree a can. Mun yi murna sosai sai dai Kakanku ya ce bai isa ba, ba zai tafi ba sai da aurensa, amma mahaifinku ya turje ya kuma kawo uzurin gwamnati tace ba zata d’au masu mata ba saboda ba zasu d’au nauyin mutum sannan su d’au nauyin iyalinsa ba, har da ce mana sunce sai dai ya hak’ura Haka dai dole muka k’yaleshi ya tafi ashe tafiyar zata zame mana jangwamgwam domin dai a can ya had’u da alak’ak’an uwarki ya aura.
Tafiyarsa da wata uku yayi mana aike akan ya samu mata zai yi aure a can. Ai kuwa na rufe idona na ce bai isaba, hakan ya tashi hankalinsa sai gashi ya dawo k’asar ba shiri lokacin watansa shidda da tafiya. Da Allah da annabi da saka malamai suyi mana wa’azi muka amince da yayi auren amma da sharad’in ni da kakanku zamu je muga tushe da asalin yarinyar. Bai wani damu ba ya ce mana ya yarda. Nan muka fara cuku-cukun tafiya kakanku ya siyar da gonarsa d’aya muka tafi har da k’aninsa da suke ciki d’aya wanda kuke kira Baffa Mamman.
Mun samu tarba Ta mutunci daga iyayenta,babu aibu sam a tattare da su dattawa ne sosai, don shi kansa Umarun a gidansu yake zaune kuma yana d’an aiki a kamfanin mahaifinsu mutumin kirki shima daga Nigeria yaje karatu sai ya had’u da uwarta mutuniyar Jordan d’in ta nuna bu’katar aurensa shikkenan zamansa ya koma can don haka da yaga Umar bahaushe ne ya ja shi a jikinsa, ya shiga farin ciki, ko da yarinyarsa ta nuna tana sonsa take ya amince ya bashi aurenta.
Hankalina ya kwanta da naga ubanta bahaushe ne, kuma har kwatancen gidan su yayi mana a garin Niger (Minna) cikin unguwar limawa nan ce mahaifar Kakanku na wajen uwa, ta daina muku fankamar wai asalinta balarabiya ce, asalin uwarta dai.Kakanku ya ce zai bincika ya gani, ai Niger ba bak’on waje bane a wajensa.
Ba mu dawo ba sai da aka d’aura auren, amma jikina ya yi sanyi da na lura da uwar Sakina ce take kula da al’amuran gidan shi uban nasu ba shi da ta cewa sai abinda Ta d’aurashi a kai, kuma yarinyar da naji suna kira Sakna ni ce nan na mayar mata da sunanta Sakina har yanzu a garinsu Sakna ake kiranta, kaf halayen uwarta ne a tare da ita bata ganin mutane da gashi. Gaisuwa kanta sai taga dama take min gashi iyayen suna ji da ita tamkar masifa ko don itace babba.
Satinmu biyu muka baro garin daga nan umara muka wuce, na kuwa dad’e a d’akin Allah ina kaiwa Rabbil Izzati kukana akan aurennan na ubanki don sam zuciyata ba wai ta gama yarda da auren d’ari bisa d’ari bane, na yarda ne dai don Malam yafi ‘karfina.
Dawowarmu Nigeria muka dinga zuba idon ganinsu sai dai kamar mun shuka dusa ba amo ba labarinsu.
Hankalina ya tashi matuk’a da gaske ga gari ba kusa ba kuma lokacin wayar hannu bata zo ba iyakaci ta landline ce shima ba waje mai nisa ake kira ba.
Ganin tashin hankalin nawa ya yawaita hakan yasa Malam ya shiga addu’a da a lokacin ake kiranta addu’ar kiranye. A lokacin har aka yi bikin k’anwarsa amma bai dawo ba. Na haifi autata lauratu shima bai dawo ba.
Kwatsam wata rana muna zaune da hantsi sai ga sallamarsu ina d’aga Kai suna shigowa da hakimar uwarku tana wani cin magani tana yatsina kamar ta shigo gidan da ake tsubire himulin kashi, ba mu bi ta kanta ba muka shiga murnar ganin Umaru da duk yayi ‘kiba ya zame min babban mutum kuma duk da a lokacin ko shekaru talatin bai rufa ba. Na shige rumfa ina musu lale marhabin ku shigo mana. D’aki na tsaf yake duk da dai ba kujeru amma malale yake da sabuwar leda sabuwa dal don mun fara shirin azimi daga gefe kuwa fanka ce Ta tsaye sai dadduma da tum-tum irin na gidan sarauta.
kuma bana mantawa a lokacin k’amshin turaren tsinke yake da na kukkunna a duk wata kusurwa da take d’akin, ya kuma sha Fenti da farar k’asa kamar yarda malam yake k’o’kari duk shekara a watan sallahr tsofi yake shafe gidan da farar k’asa.
Duk da wannan abin amma Sakina yamutsa fuska kawai take, ta d’ofana d’uwawunta akan tum-tum d’in da yake gefe sai sannan Umar ya kalleta ya ce “Ki gaisheta mana.” Fuskarta kamar ta zunduma ihu cikin gwarin hausarta da ko fita bata yi a lokacin ta ce “Ina kwana?” Ina murmushi na ce mata “Lafiya k’alau Sakina.” Ji nayi tana masa magana da turanci ban dai fahimci abinda tace masa ba amma tabbas naji ta ce Sakna da Sakina a cikin zancen nata. Sai naga yayi murmushi ya ce “Didi sunanta ba Sakina ba Sakna sunanta.”
Na kuwa daddage na jefe shi da umbola na ce nak’i nace Saknan ka gaya mata ba zance ba Sakina zance Au nan k’arata Ta kawo don rashin Ta ido? gaisuwar ma ina ce sai da kace ta gaisheni, kai Umaru!ni dai ka tak’aitan da ba ka auro mai jin hausa ba balle ta fahimci masifar da nake mata ja’ira fuska kamar jan k’osai.” Kallona kawai take tana ta’be baki ni kuwa na mik’e ina kallon Ummaru da yake ta guntse dariyarsa nace “Sai ka kawo mana bak’uwa ba sanarwa yanzu mai kakeso mu bata? Ga d’akin naku ma ba a gyare yake ba.” Na k’walawa Ali kira yana zuwa nace “Gadanga sai ka tattara kayanka ka dawo d’akin nan na tsakargida sai a gyara musu can d’in tunda d’aki ne da rumfa har da makewayi a ciki.” Ali cikin farin ciki ya shiga aiki ma’kota kuwa tuni aka fara shigowa ganin Amaryar Ummaru ana mamakin yarda ya auro balarabiya sai da nayi musu jan ido sannan suka fice na saka sakata a Zauren gidan ina sake tsinewa k’auyanci banda haka meye na dandazon zuwa ganinta abinda gobe zan saka ta zaga gida-gida su gaisa dasu.
Abincin da muka yi na rana shinkafa da miya da salak na juye musu kaf na bawa gadanga ya siyo kifi sukunbiya na saka musu, har da dafaffen k’wai wai duk don na karramata. Na zuba musu zo’bo mai sanyi har da fura da yake ina siyarwa k’aton firiza ne dani a tsakrgida, nake sararwa da mutane zo’bo da fura mai sanyi kuma cinikin ya kar’beni sosai.
Reras na jere musu langunan abincin har da cokula na sababbi gal dasu.
Umaru yayi saurin jan tray d’in abincin ya fara k’o’karin zuba musu, gani nayi tayi wuf Ta ri’ke hannunsa tana girgiza masa kai sai kuma naji tana ambaton hotel da nuna masa lokaci ta hanyar kallon agogo. Sai naga ya mayar da abincin ya rufe yana sakar min murmushi ya ce “Didi ai wucewa ma masauki za muyi mun riga mun kama d’aki a hotel.” Ban san sanda bakina ya zunduma masa zagi ba nace “Ba Otel ba Otalo kai har kayi kud’in da ba zaka iya ajiye iyalinka anan ba? to wallahi baka isa ba nan d’in da take ‘kyama anan zata zauna ba gidan uwar da zata je, ina kallo da ma tun d’azu kallon rainin da take wa gidannan to ka gaya mata nan kwana nan yini don uwarta ba inda zata je ga d’aki can na saka gadanga yana gyara muku, kuma ko dawowa kayi gaba d’aya ga ‘bangarenka can malam yasa ana gina maka anan d’in zaka zauna. Ni za’a kawowa fi’ili da zancen banza.” Ina kallo tana tambayar me nake cewa naji ya ja ajiyar zuciya yana mayar mata da harshen da tafi wayo a kansa kawai sai naga yarinya ta saka kuka ta mi’ke tana d’aukar jakarta tayi hanyar waje da sauri Umaru ya bita dai-dai lokacin da malam yayi sallama ya shigo.. kamar zata bangaje Malam, Umar d’in yayi sauri ya rik’ota ai kuwa munyi kallo don fad’awa jikinsa tayi tana kuka sosai kamar yarinya cikin kukan babu abinda nake ji sai furucin Back da kuma Jordan sai kuwa wata kalma da take yawan maimaita Ta wai now now. Malam ya saka salati tare da furta “Umaru saukar yaushe naji kuma amaryar taka tana ita Jordan zata koma? Ku muje ciki naji me yake faruwa a tsanake.” Umaru ya ja hannunta ko kunyarmu bai ji ba ya saka ta a gefen hammatarsa yana goge mata k’wallar idonta. Sosai takaici ya kumeni nama kasa magana zuwa lokacin da suka shigo Malam ya sake tambayata na bashi labarin kaf abinda ya faru. Take shima na ga fuskarsa ta sauya da yanayin ‘bacin rai amma da yake namiji ne sai bai nuna ba kalmar Ashsha kawai yake fad’i sai kuma ya girgiza kansa ya kalli Umaru ya ce “Kai kuma don sakarci sai ka biyewa matarka ka ‘batawa uwarka rai? Meye da gidannan d’in da ba zaku sauka ba? ka gwammace Ku kama Hotel ina ce kaima a gidan ka rayu?” Kasa cewa komai yayi ganin ran mu ya ‘baci ina kallo yana ta fama da hakimar tasa kan ta ha’kura amma taja ta turje akan sai ta tafi abincin da na kawo musu ma ko ci ba suyi ba. Bama ta kalleshi ba ran Malam a ‘bace ya ce masa su wuce su tafi sa dinga lek’omu kafin su tafi. Abin mamaki Umaru kuwa ko ja da lamarin baiyi ba yaja matarsa suka wuce ba abinda ya dameshi balle ya gane Malam gatse yayi masa.
Bayan fitarsu Mun dad’e muna ta’ajibin abin, mamaki kuwa kamar ya kashe mu haka yasa Malam yanke shawarar aura masa yarinyar mak’ocinmu Sadiya, Yarinyar da kowa ya shaida da nagartar halayenta ga son ibada kamar me. Ubanta Aminin Malam ne. Murna na shiga yi da shawarar Malam na karb’eta d'ari bisa d’ari muka kuma ce ba za mu sanar dashi ba sai dai yaji an aura masa aure da ita dole kuma ya amsheta matsayin mata.
Malam bai bari sai kashegari ba a daren ranar yaje wa da Talle amininsa zancen, Talle yayi farin ciki sosai don babu wanda zai k’i had’a zuri’a da Malam sai marar rabo, take suka saka lokacin aure Sati biyu masu zuwa. Malam ya cigaba da ginin da yakewa Umaru a gefe guda a gidanmu. D’aki biyu ne da babbar rumfa sai makewayi ‘d’aya da yake dangar rumfar daga can gefe.
Kashegari Umaru shi kad’ai ya zo don hakimar ta ce ba zata Biyoshi ba, ban ko tambayeshi ba shi yake rattabo min bayani, na ta’be baki na ce ta sha zamanta ai ni ba na nemanta, don na gane k’yank’yamun mu take kuma tayi Ta banza don kwanannan zata gane kurenta.”
Bai wani da’de sosai ba ya tafi.
Da ku’dina da na Malam har da na gadanga da Y’ar uwarsu da tayi aure muka ha’da aka yi lefen kishiyar Uwarki Sadiya.
Da yazo yaga ana had’a lefen bai kawo komai a ransa ba ranar ma bai dad’e ba kuma nan ma bata biyoshi ba sai wasu dogayen riguna na k’asar da Ta aiko min dasu da na k’annensa ni kuwa duk na tattara na zuba a lefen Sadiya....
To fa! Ko me Ummaru zai ce idan ya Samu labarin aurensa da Sadiya? Shi da yake da tsaleliyar Balarabiya [11/21, 2:17 PM] Nazeefah Nashe: Alk’alamin JIKAR NASHE
Ya Abin Yake?