Baban kawata chapter 4
by @smauta
Baban kawata page 4
Manar tun tana yar shekara hudu a duniya Allah yayima iyayenta rasuwa ta taso a hannun kakar ta wacce ta haifi mahaifiyar ta,ba masu hali bane suna zaune a cikin garin suleja,tun tana yarinya Allah yayi ta da kwalwa ga hazaka hakan yasa tana ss2 gwamnati tana bi makarantun gwamnati ana daukar yara masu hazaka Allah yasa da sunan ta ciki…………….
Ko candy batayi ba gwamnati tai masu jumping,abunka da gwamnati ba'a dauki wani dogon lokaci ba aka tura list ɗin sunayen su kowa da kasar da zaije yayi jami'a sunan manar ya fada a kasar sin dake china ranar murna wurin hajia kaka da manar karku tona,wata daya aka basu su kimtsa komai nasu domin da jakadan gwamnati za'a kaisu a damka amanar su a makaranta da suka samu……………
Bayan wata daya
Yaushe ranar da ta kama su manar zasu tafi makaranta har gida akazo da mota aka daukesu harda kaka aka ɗauka tayi masu rakiya har airport tana kuka suka rabu da yar jikallenta an kuma yimasu alkawarin duk bayan shekara biyu zasuzo ganin gida kuma gwamnatin tarayya zata dinga basu kudin kashewa ba'a buƙatar komai daga wurin iyayensu,haka kaka naji tana gani manar ta tafi suka rabu suna kuka da jikar ta daya tilooooo………………..
Wannan ne karo na farko da manar ta fara hawan jirgi a rayuwarta tsoro da fargaba duk ya cika ta haka suka shiga jirgi aka lula dasu kasar china sun sha zaman jirgi kafin su sauka tun a airport ta tabbatar da tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda yayi birni da kauye yau itace a kasar china,ko a mafarki bata taba ganin kanta a wata kasa ba impact ma tasan basuda kudin da za'a sakata University amma yau gashi itace ta tsallake kasar ta Nigeria tazo china da sunan University a ranta tace kai Alhamdulillah……………….
Watan manar daya a china ta gane ko ina aka kawo halim babanta da kanshi ya kawota makarantar yayi mata komai,wata ranar Monday tana zaune ita daya halim ta fito daga Library taga manar zaune,kusa da ita tazo ta zauna Assalamu alaikum manar na duke kan wayar ta tana browsing ta dago waalaiki salaam ta mikama halim hannu suka gaisa……………
Tunda nazo sai yau naga yar uwata baka halim tana dariya manar ta kalli kanta ina take da baki idan ta shiga cikin ƴan Chinese din nan ma sakewa take dasu sbd farinta,halim dince baka, dariya tayi dan ta gane neman magana ne takeyi 😂😂 ummmmm gashinan kinsamu,halim tace sunana halimatu amma daddy na da friends dina suna ceman halim ni yar Nigeria ce a Abuja kefa?
Murmushi ta sakar ma halim hakanan taji surutun halim ya mata tace sunana Manar Shehu,a suleja nakeda zama halim tace what suleja tamu ta abuja gyada mata kai manar tayi alamar ehhh,halim batai wata wata ba ta rungume ta alhamdulillah wlh yau sati na daya bansan kowa ba garin ba dadi can we be friends?manar tayi daria yesss nan fa aka cigaba da labari kamar sunsan juna…………..
Haduwar halim da manar yau kimanin sati biyu kenan kullum halim na dakinsu manar dan ita babanta hostel din ma mai single bedroom ita kadai ya kama mata,bakowa sai ita kadai shiyasa kullum tana like wurin manar suna hanyar su ta dawowa ne wani black beauty matashi mai kyau yasha gabansu halim ce ta kalle shi malam lafiya,yes lafiya da kawarki nake mgn,sai lokacin manar ta dago ta kalleshi nikuma malam eh ke to inaji, I'm sam'an i like u,dummm gaban manar ya fadi dakyar tace thank u ta rabashi zata wuce ya jawo hijabin ta…………….
Da sauri halim tace ahh mlm lfy zaka riketa,budar bakin sam'an yace inason ta ne,dan kana sonta sai akace ka dinga janta haka dalla malam saketa halim tasa hannu ta bige nashi hannun manar na tsaye na kallon ikon Allah,kama hannunta halim tayi suka wuce sam'an bai hakura ba saida ya biyo su har bakin hostel yayi kasa da murya yace sister halim ta kalle shi do me a favour and help a brother pls wlh sonta nake sosai ba tun yanzu ba kibari muyi magana da ita,halim ta kalli manar zakiyi magana dashi?samun kanta tayi da daga mata kai gefe ta koma ta basu wuri………………
Sam'an yashiga tsara mata kalaman shi na karya har yayi nasarar kamota tareda zuciya ta,a cikin sati daya manar da lalace a soyayyar sam'an abinda da wanda bai taba soyayya ba idan ya fara sai Allah da malaman gari,kullum sam'an na tareda su duk inda sukasa kafa yana biye dasu halim tun bata sake mashi harta fara saboda taga yadda manar ta saki dashi,amma Allah yasani dama can ita baiwani kwanta mata a rai sosai ba…………….
Wai manar menene haka sai rokonki nake kinki yarda bakin yarda nayi ba halim,yan dakinmu zasuga kamar na gujesu sbd na sameki,halim taji haushi sosai kema fa idan kikabar dakin zakiji dadi manar kinga sun haɗa kansu sun ware ki,kinaji fa jiya a laundry muka kamasu suna cewa ke yar scholarship ce bakida kudi meye amfanin zama dasu nidai yanzu damun koma zanzo mu dauki kayanki ki dawo dakina kawai ba ruwanki dasu,shikenan halim Allah yasa haka shine alkhairi Amin…………….
Bayan komawar ta dakin halim da kwana biyu tautsayi ya fada kan manar inda tana kwance kasa sun dora ruwa kettle ya mungulo mata ya kone mata ciki da baya sosai,hankalin halim ya tashi,da sauri taje admin din makaranta tayi reporting clinic din makaranta aka kai manar ta kone sosai a jiki, sam'an ne farkon wanda ya fara kira ta fada mashi halin da ake ciki amma a nata mamakin ko akan wayar bataji yayi wata rudewa ba……………..
.
Tun bayan zuwanta makarantar so daya tayi waya da daddyn ta saidai kullum zataga an turo mata kudi daga Companyn,kirrrr tashiga kiran daddy bugu ukku ya dauka,halim ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tace daddyyyyyy meeeee,bakayi missing dina ba sai kai daya a gida ummm nabar zama gidan sosai halim sbd bakya nan na saba ko fada ne muyi idan kina nan, yanzu kana ina daddy office sometimes ma anan nake bacci,tabbb daddy haka kake sona daman😂……………………
Daddy ummmm halim room mate dina ta kone da ruwan zafi yanzu haka muna clinic,room mate ya maimaita?eh daddy bansan zama ni daya na samo wacce zamu zauna tare nan ta zayyana mashi tun daga haduwar su har kawo yau badai kece kika ɗora ruwan zafin ba ko?Yes daddy ajiyar zuciya ya sauke dan yasan kasashen waje da binciken kwakwaf kar a juya zance su kama mashi diya…………….
Allah ya bata lafiya kinada kudi for her treatment,ahh daddy scholarship ce komai free akeyi mata, Allah ya bata lafiya kit ya kashe wayar,kallon wayar tayi tana murmushi koba komai tanason mahaifinta shi ya raine ta tun tana yarinya harta girma kulawa da uwa zata ba ɗa bata samu ba babanta ya zamar mata uwa uba kanwa yayye duk shine yau ga karatu ya raba ta dashi,duk da suna yawan samun sabani da baban nata sbd wasu halaye nashi da batasoooo………………..
Mu hadu a next page it's me SM AUTA don't forget like share and comment 💃💃💃💃💃💃