SANADIN HIJIRA

Page 26

by @ummufadeela01

SANADIN HIJIRA

       


   By 

Ummu Fadeela




26....

END OF BOOK ONE.






Dariya yake kyakyatawa kamar jikan boka yana saita wukar saitin wuyar Uwa. Wani irin shocking jikin Uwa ya dauka kafin daga bisani wani fitsari mara control ya fara sulalowa daga jikinta kamar sauk'ar ruwan sama...

Dagowa yayi yana baza idanu a kanmu karaff idanunshi ya sauka a kaina hannuna dana matse na Maahh dashi ya bi da kallo yana studying yanayina, "Ke! tashi matso ki danne min kafafunta zan yi aikin Allah.(Subhanallah)."
Ko ban dago ba na san dani yake amma yadda jikina ke rawa sai na kasa tashi, wata irin razaninniyar tsawa mai tsinka yan Hanji wani ya min "Ke waye Amir namu yana magana kina zaune" hantsilawa nayi da azabar karfi na mike ba tare da nasan sadda hakan ta faru ba sai ganina na yi ina tafiya toward him.


"Dakata" wadda aka kira da Amir ya fada yana takowa, "Me kika sanya a cikin hijabin naki yake rawa haka kamar reshen bishiya?"

"Babu komai Wallahi Allah ban 'boye komai ba hijab dina ne kawai" na fada ina cigaba da rawar jiki hakama sauran matan dake durkushe a wajen. Matsoni yayi sosai har ina jin yadda hamamin warin dake tashi a jikinsa da ya haddasa min tashin zuciya amma haka na hadiye abuna...."dage hijabin in gani" yayi maganar in a serious tone. Nan fa ake yinta dan kam na rike kasar Hijab dina da nake mishi kallon mutunci da darajata na diya mace. duk irin yadda suka min tsawa akan in cire hijab din na kiya dan sai naji zuciyata ta kekashe saitani da bakin bindiga wani yayi akan inbi umarnin ogansu amma ko gezau ban yi ba, daga mishi hannu ogan yayi barta Hassan, yatsu biyu ya daga sama ya buga da karfi, da gudu wasu biyu suka zagaye ni ban ankara ba sai saukar hijab dina naji zuwa kasa, ihu na yi ina kankame kirjina da rumtse idanu na ce, "Allahumma ajjirni fi musibati, wa'akhlifni khairan minha,Rabbana innaka jami'un nasi liyaumin laraiba fihi, Allahumma akhfiniheem bima shi'ita".

Kowa a wajen sai da ya firgita gabadaya mun dauka fyade zasu min. Jin shiru har tsawon minti biyu ban kara jin motsin kowa a wajen ba na bude idanuna a hankali. Akan Amir din nasu na sauke yana tsaye sai kallona yake yi yana lasar baki a lokaci guda yana figar gashin dake gemunshi da hannu. Kankame idanu na kumayi lokacin da naji muryarsa yana magana cikin sanyi kuma irin maganar ustazai. "Hassan kaga abun da nake gani a gabana kuwa? Gata dai baka kirin kamar ba'kin zunubi amma gabadaya kayan alatun nata ne yaseen, wai tirkashi, kai kaga yadda suke juyawa a cikin hijabi? a cikin riga kuma sun tsayar min da numfashi na minti biyu, a zahiri kuma inaga sumar dani zasuyi, wai zillaziya ke nan. Sannan muryarta kuma ya sanya ni jin ina yawo a cikin gajimare. A adana min ita wannan tawa ce har abada" Kafin hassan ya ce wani abu wani a cikinsu yace, 

"Shakka babu Oga kayi kyakyawan zabe, na tabbata ba karamar sharholiya zaka sha a nan ba dan daga yadda komai suka nuna lallai rijiyar ma cike take dam da romon dimokuradiya kasha har kayi wank... "Bai karasa ba ya ji saukar bindiga tushhhh a goshin sa, take a wajen ya fadi ko shurawa bai yi ba.... "Karya kake matsiyaci, ka yi kadan Kamar Amir ya yi yabon mace kai ma ka yabeta" cewar Hassan yana taka kafar wanda aka harben amma shima deepdown kyarma yake, dan mutum baya kaiwa matsayin Amir har sai an yarda da sahihancin rashin imani da kuma zaluncin sa,(wa'iyazubillah) dan haka suke tsoron wannan Amir din domin shi din mugune na karshen zamani kuwa... A fusace Amir din ya juya kan Uwa dake kwance magashiyan har lokacin ta kasa ko motsi dan dukkan mu mun yi suman wucin gadi ne sakamakon karar harbin da Amir din ya yi.) yana dariyar mugunta ya kuma tunkarota, wani fitsarinne ya kuma kecewa Uwa da ta tabbata wannan yana isota shi kenan sai dai wata ba dai Uwani ba....


Dukkansu d'aga kai suka yi sama jin wasu jirage suna shawagi a sararin samaniya da masifar karfi, ga karar harbe harbe daga gefe da ke tabbatar da jami'an sojin sama da na 'kasa ne sukayi hadin guiwa.!

Cikin daga murya Amir d'in ya ce "Hayya! Hayya!!" dukkan su suka kwasa a guje suna barin cikin gidan. Da rarrafe Uwa ta fara tafiya tana ambatar Alhamdulillahi Allah,a fili da zuciyarta. Sauran mutanen dake wajen ma sai a lokacin jininsu ya fara narkewa daga daskarewar da yayi sakamakon ganin mutuwa kuru kuru. "Jama'a bamuga ta zama ba fa, duk tsiya dole mu bar yankin nan ko da zamu fita missing bu*llet ya tabamune mun gwammaci a haka akan ai mana kisan gilla, sannan tunda sun rigada sun kyallara idanu akan abun da suke so dole ne zasu dawo" cewar yakura..
"kwarai kuwa uwa uba kuma wannan shegen jirgin dake shawagi a sama, shifa ba ruwanshi baya tantance wannan yan ta*addane wannan fararen hulane kawai da zarar yaga dandazon mutane a waje guda wuta kawai zai zubo muku daga sama" cewar Iya da ta amshe maganar hankali a tashe, bayin Allah sun yi hijira daga garinsu sun dawo nan, an biyo su an kashe musu mazaje da y'ay'a ba:a barsu sun yi zaman takaba kamar yadda Allah ya ce ba gashi ana farautar tasu rayuwar bayan an haddasa musu tsoro da firgici cikin zuciyarsu, MATA ke nan a kullum idan ana rikici su abun ya fi shafa.


Kalmar Yakura ta "Ko da tsiya sai an bar garin nan da shi muka yi amfani, Maahh dai tana da ga gefe zuciyarta na jin kunan abun da akayiwa diyarta amma babu bakin magana, Uwa kuwa tsuru tsuru ta yi tana ta hada uban zufa dan har ta fara hasasota a cikin kabari. Kowa ta kansa kawai yake lokacin da aka yanke zamu kuma gwada jarraba fita bayan awa daya da fitarsu still ana ta bata kashi tsakaninsu babu abun ke tashi sai sautin bindigu da karar boma baman da wannan jirgi ke jefawa ta sama, shaguna da dama sun kama da wuta foli*ce station ya kone masallatai coci coci duk an kona, kamar almara muka jiyo faduwar abun fashewan da jirgi yayi missing a sashen su Ammah, bummmm haka wajen ya karba ya fara ci da azabar sauri. duk cikinmu babu wanda bai tsorata ba dan haka aka fara ranta a na kare ganin wuta yana ci bal bal bal,"Ammah ki taimaka min ki sanya min Maahh a bayana bazan iya daukarta ba dan girman Allah" na fada da sauri ganin kusan kowa ya fita Ammah ce ta karshe tana kokarin sa kai na rikota, maahh na jingine da bango daga gefe tausayin Fanne ya gama cinye mata zuciya idanunta sun yi jajur 

"Fanne baza ki iya goya Aminatu ba, bayan haka ciki gareta babba zaki illata abun da ke cikin" cewar Amma tana baza idanu a tsakar gidan, da sassarfa naga ta nufi wani bangare cikin second biyu ta juyo da wani amalanke wanda ya gama lalacewa amma dai yana tafiya, da kyar muka daga Maahh muka sanyata cikin amalanken." Maza turo mu bar gidan nan kada sauranmu su bacewa ganinmu Fanne" cike da dakewar zuciya da jarumtar da na arawa kaina na fara tura amalanken da Maahh ke kwance a ciki tana fizgar numfashi da masifar karfi dan ji take kamar nmfashinta yana komawa cikin cikinta ne a maimakon ya fito waje. Gudu kawai muke a hanya yayin da ni mai turawar da wacce ake turawar duk muka jigata muka galabaita, mun yi tafiya mai dan tsawo muka fara hango dandazon mutane a gabanmu suna ta gudu nafsi nafsi kawai ake, kowa yana ta kansa babu mai jin wani,.mata kananan yara tsofaffi gudu kawai ake wasu a mota, motar da zata iya daukar mutum bakwai sai ka samu Dan Adam fiye da ashirin a ciki. Wasu a kan babura. ya'ayyuhannasu irinmu akan kafa, gudu kawai muke yi alburusai na wucewa ta samanmu jajajur kamar garwashin wuta shuuuu shuuuuu haka suke wucewa.

Tashin hankali iyaka mun ganshi dan tsere muke yi a tsakanin rayuwa da mutuwa, idanun Maahh ne ya fara kakkafewa wani irin zufa yana feso mata a goshi nishi take yi iya karfin ta dan azabar da take sha, wani irin harbawa kirjina ya yi sakamakon hannun Maahh da na gani a kasanta tana mai da kan jaririn da tashin hankali da azaba ya sanya shi turo kai da niyyar fitowa duniya tun lokacin sa bai ba, innalillahi, duk irin azabar da ke tattare da nakuda da haihuwa amma haka Maahh ke tura kan dan tayin tana mayarwa cikinta a kokarinta na son hanashi fitowa dan wani tashin hankalin yafi gaban wani.


Maahhhhhhh!!! na fada da ihu ina sakin amalanken da take ciki na juyo gabanta da gudu, ban damu da alburusan dake shawagi a saman mu ba. Durkushewa na yi a gabanta, hakan ya yi dai-dai da wani azababben nishi da ta sake yi, a take jini ya feso gami da wanke min fuska kamar an kunna famfo hadi da fadowar jariri lokaci guda yana tsanyara ihu. Hannu nasa na katse jinin da ya min feshi hakan ya bani damar bude idanuna na sauke akan jaririn dake yashe a kasa tun kuka daya da yai bai kuma wani ba, duk da ban san haihuwa ba na san wannan da bai Isa haihuwa ba, irin sune ake kira bakwaini. Jikin Maahh babu abun da yake sai jijjiga har amalanken da take ciki Yana jijjiga, ga wani irin tauna da take yiwa harshen ta kamar ta samu nama idanunta suna juyewa zuwa fari sol jini kuma sai ambaliya yake a kasan ta. 

Maaahhh! na ambata can kasan makoshi domin a lokacin sunan ta ne kawai abun da yayi saura bai goge ba daga kwakwalwata, tabbas ina kyautata zaton na haukace dan ji na yi jinin dake circulating a cikin jijiyoyina ya tsaya caakk kana nau'rar dake kai sako wa kwakwalwata ta tsinke, bana iya jin komai bana ganin komai, nishi da fuzge-fizgen da Maahh ke yi tana taunar harshe da karfi yawu na gangarowa yayi dai-dai da fadowar wani makamin artilary kusa damu, wannan ya dawar dani duniyar mutane, zabura na yi gami da kamo dankwalina na fizge na janyo jaririn da mabiyar duka na rufesu da dankwalin na damke da kyau a gefen hannu guda hannu daya kuma na fara tura amalanken a guje da niyyar in kamo su Uwa dan tuni sun bace min ko akwai taimakon da zasu yiwa Maahh. Gudu nake yi iya karfina bani da bambanci da mahaukata gashin kaina Yana mikewa da kwanciya, kafata babu takalma, hannuna yana digar da jinin da jaririn da na rike ba tare da ko cibi an yanke mashi ba, Maaahhh ta dade da suma ba tare da na ankare ba gudu kawai nake ga mamakina na daina haduwa da mutane akan hanyar, sai ma karar sautin harbe harbe da nake jin yana dada kusanto ni. Ashe tashin hankali da firgici sun sanya ni canza hanya ban sani ba, su Uwa sun bi gabas ni kuma na bi Arewa, ban sani ba ashe cikinsu na fada tsundum. Ya yin da kaddara ta yi aikinta, a lokacinne mai afkuwa ta afku......!


Cigaba da gudu na ke yi ba tare da na San inda na ke jefa kafata ba. Wani irin kara na saki sakamakon wani azaba da ya ratsa damtsen hannuna dake rike da jaririn da Maahhh ta Haifa ,a take ya subuce zuwa kasa, lokaci guda Nima na bi jaririn bayan na saki amalanken da Maahh ke ciki, ban kai ga isowa kasa ba na ji ni kwance jikin mutum, a hankali na dago birkitattun idanu na da tashin hankali ya gama dagulasu na sauke a akan fuskarsa, babu abin da nake iya gani sai tsinin hancinsa da jajayen lips nashi da suka fito ta cikin hular sojojin dake kanshi, murya kasa kasa na fara karanto Kalmar shahada ina lumshe idanuna da addu'ar Allah ya sa mutuwata ita ce karshen wahalata.....!