Page 27
SANADIN HIJIRA
*2*
By
Ummu Fadeela
27
****
*Al'ameen*
Tun da yake a rayuwarsa na aikin soja bai taba experiencing tashin hankali irin wannan ba, yak’i suke irin na sunk'uru ba bu mai kallon dan uwansa cikin kwana ukun nan har wani rama ya yi na mussaman, duk yadda suke zaton yaran sun wuce tunaninsu. Ga sojojinsu dake ta mutuwa duk kuwa da irin kwarewar da suke dashi ta bangaren yaki.
Yanzu ma kamar ko wanne lokaci fafatawa suke cikin tsananin duhuwa, tuni sun zubar da motoci sun shiga cikin surkuki in da maboyar yaran yake. Kusan awa shida kenan suna abu daya amma babu nasara ta gefensu ga yaran sai zubar musu sojoji suke, Musty ne ya taba Al'amin da ke gefensa yana mishi wani yare irin na su na sojoji. Girgiza kai ya yi ya ce, "No Musty, don't do this plsss, ba mu kai wannan matakin ba tukunna".
"Wannan ce kawai mafita Dude, idan bamu yi hakan ba duk mutuwa zamu yi.
Capt ka yi duba akan manufata. "Musty ya fada da dan fushi fushi, a tsawace Al'ameen ya ce," I said nooo,wannan risky ne"
Shima Musty a harzuge ya ce, "Dole ne muyi taking wannan risk din Capt. Daga haka bai ba Al'amin damar cewa wani Abu ba ya finciki wata jaka dake bayan Al'ameen ya fita daga cikin surkukin duhuwar da wani irin gudu kai kace zai fire sama ne, zabura Al'ameen ya yi kana ya bi bayansa a guje shima da wani irin speed.
Daniel dake ta fakon duk wani motsin Al'ameen din dama kawai yake jira ganinshi ya fito fili ya sai ta bindigarsa dai-dai kan Al'amin din gami da sakin kunamar bindigar, a dai-dai lokacinne kuma Fanneh ta iso wajen bul*let din ya yi nasarar ratsa damtsen hannunta ya shige ciki, babu shiri ta saki jaririn dake hannunta da kuma amalanken da Maahhh ke ciki ta sulale zata fadi.
Al'ameen da tashin hankalin abun da Musty zai aikata ya rikitawa kwakwalwa, ganin mace a tsakiyar wajen ya kara dagula mishi lissafi da hanzari ya tarota ganin saura kiris ta kai kasa, rikon da yai mata ya yi dai-dai da sakin bull*et na biyu da Daniel ya yi wanda ya sauka akan shoulder din Al'ameen. Rumtse idanu ya yi da karfin gaske kafin ya bude su ya kuma saukewa akan yarinyar dake rike a hannunsa har lokacin, manyan idanunta da suka kada jajir zube fes akan fuskarshi sai dai babu alamun numfashi a tattare da ita.
Daniel yana harbi Al'amin shima wani harbi from no where ya sauka a keyarshi ya fito ta gaban goshin sa, take ya fadi a wajen.
Gudu Musty ya ke yi da wani irin karfi a lokaci guda yana fitar da wasu abubuwa cikin jakar da ya karbe a bayan Al'ameen, saura bai fi taku shida ba tsakaninshi da yaran ya fara balle bakin abubuwan masu kama da balloons Yana jefawa a cikinsu douumm, douummm. Haka sound din yake tashi, ihu Al'ameen ya yi da karfi azaba yana ratsashi yake kiran Noooo nooo musty don't do this noooo. Daga haka ya fadi kasa shima Fanne da jikinta ya dade da saki dama ta fada kan damtsen hannunsa
UWA.
Gudu kawai suke yi da sauran jama'a, cikin su babu wadda ya lura cewa Fanne bata tare dasu. Sun yi nisa sosai har sun fara fita daga gari kwatsam suka hadu dasu akan babura uku,
"Ina zaku je?".Tambayar da daya daga cikinsu ya jefo musu kenan, dukkansu aka kasa samun wacce zata iya furta ko da kalma daya, sai kyarma na tsoro da suke yi. Suna dayawa sosai masu gudun amma ga yaran da basu fi su biyar ba,sun tsaida su.....
Duk ku tsugunna ku kama kunne, kuyi ta tsallen kwado har sai kun koma Inda kuka fito"!
Wani a cikinsu ya yi maganar, babu musu jiki na rawa dukkansu suka fara tsallen kwado kamar yadda suka saka su suna komawa cike da tunanin makomar su idan sun koma, iimnduk inda imanin mutum ya shiga a lokacin idan ka gansu sai ka tausaya musu...Duk yadda Uwa taso daga kafa da niyyar yin tsallen kwado ta kasa, tsugunne take rike da kunne ta kasa gaba ta kasa baya sai numfashi take sama-sama.(Kar Ku manta Uwa irin mutanen nan ne masu jiki sosai da albarkar nonuwa tulai-tulai ga tumbi Ma sha Allah)... Bata ankare ba taji saukar dorina a gadon bayanta, ji kake shauuuu."Wayyo Allah Ina ganin azaba yau ni Uwani "ta fada lokacin da ta zube a kasa.
"Bakiga azaba ba yanzu ne zaki fara gani, ki dinga yin birgima daga nan har ki iso gida inda kika fito". Yaron ya fada yana kuma shauda mata dorinar. Birgima Uwa take yi a kasa tana juyawa kamar mai shure-shuren mutuwa har ta fara kukkuje fuskarta abun gwanin tausayi.
Karar da suka jiyo na ababen fashewa da Musty ya shiga cikin yaran suka tarwatse tare shiya ja hankalinsu suka ranta a na kare dama suna cikin wadanda aka bari gadi a bayan gari ne. Da hanzari su Iya da sauran tawagarsu suka mike suna dawowa baya," Innalillahi, Ke dai Uwanin kina ganin talatar rayuwarki, me zan gani haka?" cewar Iya lokacin da suka yi arba da Uwa a yanayin birgima, da gudu Yaganah ta zo tana makale Uwa dake kwance ta kasa tashi ta saki Kuka. "Uwa me kike yi haka, dan Allah ki tashi." "Yawwa, Yaganah wannan ba lokacin kuka ba ne yan nan yi maza ki daga ni muyi ta kammu na kasa tashi."
Da kyar Yaganah ta iya rike hannun Uwa ta mike amma ta gagara tafiya sai rawar da jikinta ke yi. Allah ya taimakesu wata mota irin tirelar dakon kayar nan ta taho cike makil da mutane kamar wasu zasu fado kasa, dukkan su yan gudun HIJIRA ne, amma haka motar ta tsaya suka dinga duruwa a ciki, Uwa dai sai da karo-karo wasu maza majiya karfi hudu suka dagata aka sanyata cikin motar, da kyar ta samu waje ta rakube a hakama jama'ar dake kusa da ita sai bala'i suke yi wai ta shanye fili, ita dai bakinta alekum dan zuwa yanzu ta fahimci cewa ita din karamar yar tasha ce, motar ta cika ta batse babu ta inda mutane basu makale ba daga sama har kasa, da kyar direban ke iya jan motar suka nausa.
Sai muce Hajiya Uwa Allah ya kiyaye hanya.!
Al'ameen
Wasu daga cikin sojojin dake gaba gaba, sun ga yadda Musty ya fita a guje da yadda ya afka cikin yaran da kuma yadda abubuwan suka fashe wuta ya tashi a wajen, hakan na nufin shi ya yadda ya saida ko ya bada rayuwarsa domin saura, hakan ne ya sa suka kara kaimi Amma hango Al'ameen da sukayi a kasa a take sai jikkunansu suka yi sanyi, ba karamar Nasara kunan bakin waken da Musty yayi ya kawo musu ba, dan cikin dandazon su ya shiga dayawansu sun mutu, ciki hadda Musty dake kwance shame shame jikinsa duk jini.
Bayan lafawar komai ne jirgin taimakon gaggawa da ma'aikatan agaji suka iso sakamakon kiran da suka samu, gawawwakin sojojin aka dinga diba ana daurewa da igiya daga sama kuma jirgin yana shawagi wasu suna janyo igiyar daga cikin jirgin, koda aka iso kan Al'ameen sai suka fahimci bai mutu ba, amma akwai harbin bindiga a kafadarsa, a gefe daya kuma suna ta mamaki ganin mata har biyu da kuma jariri yashe a wajen..!
Bude jajayen idanunsa ya yi bayan ruwa mai sanyi ya ratsashi..."Musty don't do it plsss"! Shi ne abun da yake ta maimatawa da karfi har ya gama farfadowa, a zabure ya mike a dai-dai lokacin kuma ake daure Musty dake kwance shame-shame za'a tura shi cikin jirgin.
"Yanzu tafiya zamu yi? zamu tafi cikin taraddadin ta yiwu a dawo ko a mutu, kada ka manta halin da Zeenat ke ciki, shekaru biyar muka yi muna jiran wannan ranar sai gashi ya iso amma zan shiga jeji in barta"! Muryar Musty ya shiga mashi amsa kuwwa a kunne lokacin tahowar su tamkar yanzu yake maganar, umtse idanu ya yi da karfi ya bude yana saukewa akan yarinyar, sai a lokacin kwakwalwarsa ta fara aiki mai kyau.
An gama kwashe gaba daya sojojin da suka mutu da wadanda suka ji muggan rauni, sai ya rage sojojin dake kasa basu fi su goma ba, dan haka suka yi deciding tafiya gaba dayansu. Duk kama igiyar suka yi suna zurarawa cikin jirgin, ya rage sauran Al'ameen da Fanne sai maaahh da jaririnta da dukkansu ke halin suma. Lokacin da igiyar ta kuma saukowa sai Al'amin ya kamo Maaahhh ya fara daure mata a waist nata, a dai-dai lokacin ne kuma Fanne ta farfado,
"Maaaahhhhhhhh!"
Ta fada cikin wata irin gigitacciyar murya tana nufo wajen da wani irin gudu, "Maaaahhhh. Ina zaka kai min ita, ka sauko min da ita, I have only her in this Dunya" ka sauko min da ita!.ta karishe cikin karaji tana kamo Maahh.
Duk da ihun ta yana amsa kuwwa cikin kunnuwanshi da yake jin tamkar zata fasasu amma bai saurareta ba sai ma tura Maahh da yayi bayan ya gama daure mata igiyar. Kamar sokuwa haka take bin igiyar dake tafiya sama da Maahh, daga can kuma wasu biyu dake tsaye bakin jirgin suka yi azamar amsar ta kana aka sako igiyar again.
Da sauri ya kama yana kokarin daurewa Fanne kawai jirgin ya fara bada wata JAR danja (Full loaded, only one person). Haka yake ta ambata, tashin hankali da ba'a saka mata rana Al'ameen yaga Gabas yaga Yamma yaga Kudu yaga Arewa, amma bai samu mafita ba, ga jirgin daga sama yana kara turo mishi warning na rashin tsaron dake wajen, idan ya shiga ya wannan yarinya da jaririn dake kwance a kasa za su yi, idan ita ta shiga shi ya ya iya da jariri. Kansa ne ya sara mishi da karfi ya tattare naman goshinsa sannan ya tsugunna gami da daukar jinjirin Maahhh ya daure zuuuuuu, haka igiyar ta haura sama lokaci daya kofar jirgin ta rufu kafin ya fara juya falfelarsa ya na niyyar barin wajen,.
Sai a lokacin Fanne ta dawo daga sakin bakin da tayi tana kallon yadda igiya ke tafiya da Maahh da abun da ta haifa. "Ina zaka kai min su, Maahh ce fa, ina zaku kai ta?"
Al'amin bai samu damar bata amsa ba suka fara jiyo karar mashina da motoci ana ta kabbara, zaro ido ya yi hango yawansu kamar ma ba'a taba su ba, bai yi wata-wata ba ya janyo hannun Fanne da niyyar su bar wajen dan tabbas wadannan suka riskesu ko burbushin kashin su baza'a samu ba, amma sai Fanne ta turje tana cigaba da kuka da fadin, Maahh ina ka kaisu ka barni nima su kashe ni, su kashe ni in huta da wannan duniyar mai cike da tashin hankali, ka sake ni na ce, su kashe ni nima, Maaahh , baba, ya muhajir. Su kashe ni nima in je wajen su.
"Baki da hankali?" Ya mata tambayar a tsawace duk kokarinsa na son ganin ya yi controlling temper dinsa amma ya kasa yarinyar sai turje mishi take. Bai yi wata-wata ba ya sharara mata wani wawan mari da ya sanya Fanne ganin wasu taurari sun wuce ta idanunta, tun bata farfado ba ya damki hannunta suka fara gudu a cikin dajin, yadda yake gudu yana janta kai kace karfinsu daya ne da ita ga raunin da bul*let ya ji mata sai tsiyayar jini yake haka shima a bangaransa karo Fanne ta yi da wani kututturen icce tayi taga-taga zata kifa, Al'ameen ya yi azamar kamota ta fado a jikinsa, without thinking twice ya dagata cidak kamar baby ya goyata a bayanshi ga ciwo akan shoulder dinsa amma haka ya daure suka cigaba da gudu ba tare da ya san inda suka nufa ba.!
Sun yi tafiya mai nisan da ya daina jiyo karar ababen hawan yaran kafin ya samu kasar wata bishiyar giginya ya sauke Fanne dake ta sauke numfashin wahala da azaba, bin sa ta yi da kallo bayan idanunsa da hanci da kuma karamin bakinsa babu abun da take gani, kana bata da nutsuwar yin wani tunani dan gaba daya kwakwalwarta toshewa tayi, babu abin da zata dorar akan yanayin dake faruwa.
Bata sauka kan tunaninta ba taji ya kamo hannunta lokaci guda ya sanya wani dan almakaci da ya fitar a cikin wata bakar jaka dake daure akan cikinsa, dai-dai saitin damtsen ta ya sanya ya tsaga inda jini ke fita, zaro idanu ta yi tana kokarin kwace hannunta, Al'amin ji yake kamar ya bar yarinyar ya yi ta kan sa dan ba karamin ciwon kai take sanya mishi ba, amma zuciyar musulunci ya kasa barinsa ya aiwatar da hakan. Naman goshinsa ya tattara waje daya yana shakar numfashi da fesarwa a lokaci guda.
Dogayen hannayensa ya sa kana ya janyota jikinsa ya mata wani irin riko da hannu daya, duk cikar sura irinta Fanne amma sai ta zama wata yar tsurut a jikinsa gabadaya ya mata rumfa, bata iya samun damar kwacewa ba ya fara aikinsa da sauri sauri, duk yadda ihu da zambarmar da take yi yake sashi ciwon kai sai da ya zaro bul*let din, kasancewar babu sauran kayan aiki a wajen kawai ya zare rigar kakinsa ya keta gida uku daya ya daure mata damtsen nata dashi, daya kuma ya rufa mata saman kan ta da gashinta ke baje ba kyan gani.
Sakinta ya yi tayi taga taga zata fadi ya kuma azamar kamota yana fadin, "Yi a hankali" ciki ciki kai kace bashi yayi maganar ba, jikin bishiyar ya jinginata shima ya rumtse idanu ya janyo nashi harsashin, fittt ya fito gami da buduwar nama jajawur dashi. Ihu Fanne ta saki da karfin gaske tana rumtse idanu. ko inda take bai gani ba ya janyo sauran kyallen rigar tashi, amma duk kokarinsa na son daure kafadar kasawa ya yi. dube dube ya fara a wajen ganin ba mafita ya tunkaro Inda take zaune sai sharar hawaye take yi idanunta sun yi jawur kai kace garwshin wuta ne tsabar azabar da take karba a damtsenta, ga tinanin Maahh dake neman haukatata amma ko kadan bata ga fuskar tambayar wannan mutumin da ya sha murrr ba...
Dammm gaban Fanne ya yanke ya fadi lokacin da ya mika mata kyallen hannunsa yana mata nuni da ta daure mishi kafada, kara rumtse idanu ta yi lokacinda ya kuma mata nuni da yatsarshi a zatonsa ko bata fahimta bane.
A bangarena ni kuma zuciyata ce ke harbawa da karfi karfi dan ganin shi da na yi babu Riga, damatsanshi a cike dam, kirjinsa a bude fari sol kamar ka taba jini ya fito sai gargasa da ke kwance yarayara kai kace yaryadasu akayi, daga kasan cikinsa kadan wasu Zane ne kwance guda shida sunyi layi layi, kai da ka ganinsa ka san wannan gym product ne, baya wasa da workout. Duk a cikin second goma na kare mishi wannan kallo na maida idanuna na rufe.....