Page 28
*SANADIN HIJIRA*
BY
*Ummu Fadeela*
Chapter. 28....
Babu yadda na iya ganin yadda yake ta taunar lebenshi kamar zai huda su ya kuma tsare ni da idanunshi da kwayar cikinsu kawai nake iya hangowa...
Durkuson da ya yi a kusa da ni gaf har ina iya jiyo fita da shakar numfashinsa a zafafe ya taimaka matuka wajen zaburata na karbi kyallen da yake nuna min, da karfi na rumtse idanuna yayin da na yi arba da zurfi da kuma fadin ramin da harsashin ya samar a kafadarsa.
"Oucchhh"
Na fada lokacin da na daga hannu na kai da niyyar daure mishi wata irin azaba ta ziyarci damtsena dake daure nima.
Wara idanu yayi da sauri yana bina da kallo, kasa kasa tamkar mai ciwon baki ya ce, "Yi a hankali". Ban ce komai ba na cigaba da kokarin daure mashi amma hakan ya ci tura, ganin na kasa ne ya sa shi kama gefen kyallen da hannunshi guda mai lafiya, da ido ya nunan in kama gefen da nawa hannu mai lafiyar nima, da wannan dabarar muka yi nasarar daure mishi kafadar sai aikin taunar lips yake kamar zai cire su daga ma'ajiyarsu.
Mun yi tafiya a cikin dajin ta akalla mintuna arba'in, a lokacin rana ta fara faduwa, duhun magariba ya soma shigowa, yunwa, wahala, ciwo duk sun yiwa Rayuwa ta dabaibayi. Na tambayeshi Maahh kuwa har bakina ya kusa karkacewa amma gogan ko gefen da nake bai kalla ba, bare in sa ka ran zai amsa ni.
A wannan yanayin na kasa, na kai du'ke k'asa, "Wayyo Allah na!" na ambata cikin gigicewa.
Al'ameen da har ya yi nisa ya juyo jin muryata ina ambaton Allah, daure fuska ya kuma yi a ranshi yana ayyana yarinyar nan ta zamar mishi LIABILITY kamar bazai dawo ba tsawon minti biyu yana tsaye ki kam a zatonsa zata tashi, ga mamakinsa kuka ta sanya mai tana rerawa kamar tsuntsuwa. Yarfe hannu ya yi ya tako gabana."Me aka miki?" Ya tambaya a miskile kamar zai kai mini Mari. "Me aka miki?" Ya kuma tambayata har lokacin ina durkushe ban ce komai ba sai kukan da nake rerawa ina damke cikina...
"Cikina wayyo Maahh mutuwa xan yi, yunwa nakeji wayyo cikina". Na fada da dan ragowar kuzarin da ya yi mini saura.
Tabe baki ya yi yana lumshe idanu kamar mai jin bacci a ranshi yana ayyana, "kamar ba ita ke fadin a barta su kasheta ba dazu, gashi just yunwa kawai ya sanyata raki. Gefe da gefe ya kai kallonshi amma babu wani abu mai kama da wanda dan Adam zai iya ci dan haka ya juyo gareni.
"Tashi mu karasa fita a dajin nan idan mun samu gari a kusa sai ki sami abinda zaki ci" Da kyar yake maganar da ka ganshi kasan shima dauriya yake.
" Ni bazan iya tashi ba wayyo Maahh wayyo baba hannuna, kafata, bayana, cikina." Iya gaskiyata nake fada dan har ga Allah ji nake tamkar zan mutu.
"Okay, idan kin gama kukan ki karaso" daga haka ya juya ya ci gaba da tafiyarsa ba tare da ya Kara juyowa inda nake ba. Zaro idanu na yi yayin da na hango ya yi tafiya ta akalla taku goma a tsakaninmu. Ban san sadda wani karfi ya zomin ba na tashi a rikice na bi bayanshi har da dan gudu na hada kafun na cimmashi ina layi kamar wacce ta shawu.
Murmushin gefen baki Al'ameen ya yi bai ce komai ba.
Da kyar nake iya daga kafata ga magriba ta fara shiga har lokacin kuma babu alamun karshen wannan dajin. Mun yi tafiya sosai naga ya ja ya tsaya hakan yasa ni tsayawa nima ina sauke numfashi sama-sama ga damtsena dake zugi yana barazanar ballewa. Jikin wata bishiyar mangoro naga ya tsaya, yana karewa bishiyar kallo, akwai yaya nunannu a bisa sai dai sun yi nisa.
Bismillah yayi ya kama reshen dake kusa da hannu daya yana rumtse idanu saboda ciwon dake kafadarsa haka ya hau saman bishiyar ya dinga tsinko kyawawa nunannun mangoro yana jefosu kasa, ya cire kusan guda goma sannan yayi wani irin tsalle ya dirko kasa, tabbas SOJA soja ne, idan ba haka ba waya isa aikata haka da irin raunin dake hannunsa kuma ya zauna lafiya.
"Zo kici"!
Ya fada yana katsemin tunani gami da nunan mangoron da idanu. Bana cin mangoro kwata-kwata a rayuwata, bana cin kifi, hakama kankana bana Shanta lokacin da nake halin al'ada. " Bana cin mangoro!" Na fada idanuna suna kawo ruwa a take. Kallon second biyar ya min ya ce, "Ohk" sannan ya tsugunna ya tattare mangoes din duka ya koma karkashin bishiyar ya zauna gami da tankwashe kafafu. Ba tare da ya kuma kallon in da nike ba ya dauki mangoro guda da ganin fuskarsa shima kyankyamin su yake yadda yake kwabe fuska, amma yana kaiwa bakinsa sai labari ya canza domin wani irin dadine ya ziyarci harshensa, Al'ameen zai iya rantsuwa bai taba cin mango mai dadin wannan ba. (Shegiya yunwa). Wasa wasa sai da ya ci kusan guda biyar sannan ya tsaya, har lokacin ina durkushe a wajen tsakaninmu akwai distance kadan bai ce min ba, nima ban ce mishi ba.
Ina ganin shi ya kammala cin iya wadda zai iya ya mike tafiya ya fara yi still bai ce min komai ba, da kyar na iya mikewa ina ganin hajijiya na kokarin kayar dani na bi bayansa jikina rawa dan da gaske duhu ya fara shigowa..."Koma ki zauna ruwa zan nema" ya fada dai-dai lokacin da ya juyo muka hada idanu.
Wani irin tsalle kirjina ya yi lokaci daya gabana ya fadi sadda kwayar idanunshi ta shiga cikin nawa. Da sauri na sadda kaina kasa, Cikin in ina na ce, "baz..bazan iya baza..n iya zama ni kadai ba kuma tsoro nake ji Allah." Ci gaba da tafiya ya yi, na bishi ina kara saurin takuna; luckily ba muyi tafiya mai tsawo ba muka samu wani dan kududdufi mai gudana, bazan iya tantance yanayin ruwan dake ciki ba da akwai duhu kadan, ina ganin shi ya tsugunna gaban rafin,hannunshi ya fara wankewa sannan a hankali a kuma karon farko ya fara kiciniyar cire hularshi ta Sojoji dake rufe ruff da fuskarshi, damm,dammm kirjina ya bada sauti lokacin da na yi arba da kyakkyawar fuskarshi ta cikin duhun magriba, daga yanayin hannunsa da kuma rigarshi da ya cire dazu na san cewa farine, amma ban tsammaci ba Indiye ne ko balarabe ba sai da na ga fuskarshi.
Juyowar da ya yi fuskarshi da alamar ruwa zuwa hannu yasa ni dauke kaina daga kallonshi kirjina na ci gaba da bugawa fat,fat,fat. Fahimtar da na yi cewa alwala ya yi kuma yana shirin barin wajen bai min magana ba na ce, cikin marairaicewar da ya kasance yanayina." Dan Allah ka jirani, tsoro nake ji".
Da hanzari na dauro alwala muka koma jikin wannan bishiyar ta mongoro, a yadda yanayin ya koma na tabbata a cikin gari an yi sallar magrib, babu abun da ke tashi a dajin sai kukan halittu daban-daban masu bada tsoro. Wani irin rawa jikina ke yi, ina ganinshi ya saiti gabas ya fara jero sallolin da ya rasa cike da nutsuwa, yadda yake karatu a sallar kuwa bazaka taba tsammanin ko kalmar (zo) ya sa ni da hausa ba.
Rigar da ya daure min a kaina shi na kwance na yafa ya sauko har saman kirjina, duk yadda naso ganin na yi Sallah a tsaye hakan gagarata ya yi dole na yi ta a zaune.
Muna zaune wajen har duhu ya mamaye ko ina, wani irin tsoro ne ya ke zagaye duk wata kafar sadarwa ta jikina kuma akwai rata a tsakaninmu dashi, yana jingine jikin bishiyar ya harde hannayenshi duka biyu a kirji ya kifa hularshi saman fuska. Wani irin sanyi yake jin yana shigarshi, ga duhu ga rashin riga, a gefe daya kuma tunanin gida ne ya addabeshi mussaman Ummie.
Dan muskutawa yayi yana dan kara kishingida hakan ya bawa busassun ciyayi dake wajen damar motsawa da bada sauti kadan.!
A firgice na tashi dama a tsorace nake, jin wannan sound din ya sani zabura ina zare idanu, sai kuma na fara jin kamar ana tafiya kuma ana magana a bayana, a guje na kwasa na nufi inda na ganshi, taga taga na yi lokacin da na yi karo da shi kafin in fada samanshi ribbb. "Damn it!" Ya fada yana dafe gefen kanshi dake sarawa.
Jina a jikin mutum ya tabbatar min a kan shi na fadi, amma tsabar tsoratar da nayi maimakon in tashi sai na kuma cukuikuyeshi ina sakin kuka. Ina kiran sunan Allah. Da kyar ya iya rabani da jikinsa ya matsa, duk da bana ganin shi amma daga jin muryarshi cikin fushi yake magana.
"Ke baki da hankaline? ba kisan a dole nake zaune waje guda dake b..." "Maahhh, ni dai ka kaini wajenta, tsoro nake ji wani abu yana tafiya a bayana, kaji ai gashi nan ma suna magana, wallahi magana suke zasu kamani ka taimakeni tsoro nakeji."
Na fada ina kara komawa jikinsa dan gabadaya na gama fita a hayyacina, jikina sai rawa yake duk na firgice. Mamaki hana Al'ameen ko motsi ya yi, yana jin yadda jikin yarinyar ke rawa kamar an jona mata shocking
Jin baice komai ba ni kuma na kasa matsawa sai sheshshekar kukan gararin da rayuwata ke ciki nake, tabbas ina sha'awar mutuwa, ashe wannan tashin hankali ke sa rayayye yaga kabari ya dinga sha'awar da shi ne a ciki mana...tun ina sheshsheka a hankali dan tsoron fitar da sauti nake har ya zama sai ajiyar zuciya nake saukewa, a hankali kuma wani irin baccin da na kwashe akalla sati ban yi ba ya fara fizgata, a hankali baccin ya fara nisa kaina ya gangaro zuwa saman shoulder dinsa dake dauke da rauni.
Duk motsin da Al'ameen zai yi da niyyar zameta daga jikin shi sai ta kara kwakumeshi ba tare da tasan tana aikata hakan ba.!
A hankali yanayinsa ya fara sauyawa, numfashin datake fitarwa mai dumi yana sauka akan bare skin nashi, wani al'amarine mai matukar girma yake ji yana tasowa daga tsakiyar kansa har cikin yatsar kafarsa. Sabanin sanyin da yake shigarshi dazu, yanzu wani irin zafi yake ji yana ratsa duk wata hudar gashi dake jikinsa, a take kuma shima nashi jikin ya fara rawa, "I can't," ya fada da dan karfi yana tureni daga jikinsa, idan ya barni tabbas komai yana iya faruwa.
Cikin bacci na fara lalube zan koma, karaff ya damki hannuna ya rike kamar zai ballasu, cikin sanyin murya kasa-kasa ya ce, "Ke wacce iriyar malalaciyace haka? Ba'amiki tarbiya a gida bane? bakisan haramcin dake cikin hada jiki da wanda ba muharraminkiba?."ya karashe fada yana dan sauke numfashi ga zufa sai karyo mishi yake kamar ya hadiye kunama.
Tun rikon da yaiwa hannuna na farka, wani irin bugu kalamanshi suka min a zuciya ban aune ba wasu zafafan hawaye suka fara wanke min fuska. Baya baya na fara matsawa ina girgiza kai da kallon saitin inda nake jiyo muryarshi, ba yau aka saba jifata da munanan kalamai ba, Uwa tana zagina dubun wannan, amma ban san meyasa na yau din yafi min zafi ba. Ina kuka ina share hawaye da bayan hannuna.
"Wallahi Allah tsoro nake ji, kuma ban san na Tabaka ba, Maahh Baba sun min tarb...."kasa karasawa nayi wani kuka mai cin rai yana kuma taho min babu shiri.
"Rufe min baki ko in tafiyata in barki a nan, ruwa ruwa da an miki magana sai ki wage baki kina ihu kamar dangin Yan-ruwa."
Ai tun bai gama magana ba na hada hannayena duka biyu na danne bakina dasu. Tsaki Al'ameen ya ja yafi cikin carbi yana tattara naman goshinsa da yaki da yanayinsa.!
Haka muka kasance a wajen har lokacinda sanyin asuba ya fara fesowa, cikinmu babu wadda ya samu zarafin komawa bacci tun bayan abun da ya faru.
Kamar jiya, koda gari ya fara wayewa yau ma wannan rafin Al'ameen ya nufa ya daura alwala, nan jikin bishiyar ya yi sallah, sai wani ciccijewa yake ko gefen da nake bai gani ba, nikuma duk yadda naso tashi hakan gagara ya yi dan zuwa lokacin hannuna yayi tsami ko motsashi bana iyawa. Ya dade zaune a wajen yana lazimi da hannunshi kafin ya shafa addu'a ya tashi..."Ke,bakya sallah ne?". Ya watso min tambayar, yana tsareni da mayun idanunshi.
"Ba,baz...bazan iya tashi ba, hannu..na, cikina.haji.ji.iya nake gani kuma." Na fada ko wacce kalma tana katsewa daga jumlarta.!
Tsaki yayi yana taune lebenshi at the same time yana tattare naman goshinsa ya ce, "Get up my frnd". Yunkurawa na yi da karfi jin tsawar da ya min fuskar nan babu Rahama, sai dai kafin in gama mikewa na yi baya luuuuuu na zube a k'asa.
Curewa nayi waje guda ina maida numfashi dan bani da karfin yin kuka duk da azabar radadin da naji. Mai karatu yayi Imagining how weak zan zama, kwanaki dayawa ban ci komai ba ga kuma tashin hankalin da na fuskanta kuma nake kan fuskanta.!
Cike da madaukakin mamaki Al'ameen ya bita da kallo.'ita wannan wace iriyar malalaciya ce haka, ba karfi ko kadan'? ya yiwa kanshi tambayar. .
(Yo Aminu an fada maka kowa ma soja ne, Mace kuma Yar raki ce ai ahto.)
Kamar zai shareta sai kuma ya nufo inda nake kwance, " Ke" ya fada yana kallo na, ina jin shi sama-sama amma ban motsa ba dan a lokacin kamar raina ne ke bankwana da gangar jikina nakeji.!
Durkusowa ya yi dai-dai inda nake ya kuma cewa "ke"! Da kyar na iya dago shanyayyun idanuna na sauke akan fuskarshi, bibbiyu nake gani dan haka bana iya bambance komai, " Ka kaini Maahh " shi ne abun na fada idanuna suka koma hadi da rufuwa rufff kaina ya fadi gefe. Dam damm gabanshi ya fadi, hannuna ya kamo da sauri, "Ke, bude idanunki, tashi,wace ke,daga ina kika fito?" Duk ya rude bai san ma me yake fada ba. Hannuna dake rike a nashi ya daga yana duba dai-dai pulse vein dina. Wani wawan ajiyar zuciya ya sauke ganin yana harbawa, mikewa yayi ya nufi rafin dake kusa da su, ruwa ya cika a hannunsa, sai dai kafin ya karaso inda nake duk ruwan ya zube kusan sau uku yana zuwa amma kafin ya karaso ruwan yake zubewa sai hannunshi kawai yake shafamin a fuska, a na biyar dinne Al'amin ya rasa mafita, wani dabara ne ya fado mishi, dan haka ya matso kusa gareni, yana bata fuska kamar wanda yaga kashi, hannu biyu ya sanya ya bude bakina, a hankali ya daura bakinshi a kan nawa idanu ya lumshe kafin ya fara hura iskar bakinsa a hankali cikin nawa.....