Page 29
*SANADIN HIJIRA*
BY
Ummu Fadeela
Chapter 29.....
***
Iskar bakinsa yake hurawa cikin bakina wadda ya ke wucewa direct zuwa cikin huhuna. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke ina bude idanuna. Zaraff ya mike yana komawa gefe yana tabe baki da kwabe fuska kamar bai yi komai ba.
Dan siririn kuka na sanya dan ji na ke kamar ana yankar naman jikina ne tsabar ciwo, bai ce min komai ba na ga ya kama hanya yana tafiya, da dishi-dishin idanuna na bishi da kallo har ya bacewa ganina kana na maida idanuna na lumshe ina fatan Allah ya dauki raina a wajen dan tabbas a inda nake din ko dan yatsata bazan iya dagawa ba balle in mike har in bishi.
Kusan minti talatin ina kwance lamo a cikin tarin ciyayin dake wajen, taku na faraji a raina ina godiya ga Allah da ya amshi addu'ata duk zatona mala'ikan mutuwane (Hooo Fannetun Maahh,mutuwa ta nan zuwa ba sai kin mata gaggawa ba).
Jibgegen kifin dake hannunsa ya aje a gefe ya kara tafiya, bayan shudewar wasu mintuna goma ya dawo da karare da kananan itatuwa busassu ya tattarasu waje guda ya debi ciyayi ya daura a kai.
A hankali na bude idanuna jin shiru har lokacin ban ji komai ba ga sautin tafiya da itatuwa da nake ji. Yana durkushe gaban kiraren da ya hada lighter ne a hannunsa da ban san ina ya samo ba yake ta kokarin kunna wuta dashi, jikinsa gabadaya ya jike sai digar ruwa yake alamun dake nuna ya shiga cikin kogi.!
Zaro ido na yi lokacin da ya dago lafcecen kifin yana tsireshi a jikin wata doguwar sanda ya daura saman wasu itatuwa hudu da yayiwa wutar da ya kunna rumfa dasu ya koma gefe yana ta ciccije lebe alamar akwai abun da ke damunsa. Kimanin minti biyar kifin na gasuwa sannan ya matso ya juya daya bangaren yana kara tura itatuwan da kara ciyawa akai hayaki yana turnuke mishi fuska. Sai da ya ga ya gasu yadda yake so sannan ya yanko reshen mangoron ya figi ganye ya hadasu waje daya ya daura katon gasashshen kifin a kai, tun da ya fara bai ga bangaren da nake ba sai yanzu da na ji yana tunkaro ni. "Ke," ya fada dai-dai ya ajiye kifin a gefena, duk da uban yunwar da na ke ji hakan bai hanani jin zuciyata tana tashi ba sakamakon warin da kifin ke yi.
"Ke," ya kuma fada da dan karfi. kumburarrun idanuna na bude na saukesu a kanshi. Alamar tashi ki zauna ya min da idanunshi, jiri na ke gani sosai amma yadda ya tsareni ya sa ni yin kundumbalar mikewa zaune ina kawar da kai gefe.
"Ci abinci" ya fada a gajarce yana nuna min kifin dake gabana.
"Ni banacin kifin" cikin zaro idanu ya ce, "What?ke kinsan hatsarin da na shiga kafun in samo maki wannan, who do you think you're da zaki dinga gwara ni haka? na cirar maki mangoro kince baki sha,, na wahala na shiga kogi da raunin dake hannuna na samo maki this thing ya fada yana nuna kifin da hannu irin abun kyamar nan, and i cooked just because of you, sannan ki ce ba ki ci?who are you?" Ya karishe yana haki alamar ya yi magana dayawa kuma ranshi ya baci.
Jikina rawa yake sosai kamar ana kada mini ganga bakina na rawa na ce, "ka yi hakuri, da gaske banacin kifi, ban taba cin kifi ba koda a miyace".
Durkusowa ya yi dai-dai fuskata ya sanya idanunsa cikin nawa duk yadda na so janye nawa idanun hakan ya faskara, yana kallona strictly ya ce, " Are you a muslimah?" Mamaki tambayar tashi ta bani da kyar na iya gyada mishi kai.
"Good, kin san me ake nufi da rantsuwa ko? to wallahi, billahi, idan baki ci abincin nan ba zan tafiyata ne in barki a dajin nan komai ma ya sameki dan dama ban san ki ba, ban hada komai dake ba, ko na sanki ne?" Ya tambaya yana zaro min idanunsa.
Girgiza kai na yi. Idanuna na tsiyayar hawaye jikina na rawa. "Good kin ga ke nan idan na barki a nan duk abun da ya sameki bani da asara."
Zaraf ya mike ya fara kai kawo a wajen, ranshi a bace, shi zata rainawa hankali, ita wace da zai dinga mata hidimar da ko Ummie da Badar bai jin ya taba dafawa ko ruwan zafi amma zata karkace taga tsabar idanunsa tace bata ci, ( mtsssw stupidity) ya fada a bayyane yana tattara fatar goshinsa.
Na dade ina kallon kifin zuciyata na tashi sannan na kai hannuna kai na yanko kadan, ba domin barazanar zai tafi ya barni na ci ba,a'a haka kawai na ji ya kamata in ci. Sau uku na ci ina yamutsa fuska ana hudun ne na ji cikina ya wani irin yamutsawa ya fara rugugi kamar sabon hadari, bakina na toshe da zara-zaran hannuna idanu muka hada ya min alamar kar ki yadda ki amayar da shi.!
Kai na hau girgiza mishi ina mishi alamar ka ji tausayina bazan iyaba, da sauri na saki hannun na fara kakarin amai, ina yi ina jijjiga kai na, kasancewar babu komai a cikinnawa dama iya kifin ne ya fito ya barni da kakarin azaba, sosai na wahala kafin daga karshe na zube a wajen ina maida numfashi dakyar-dakyar.
Al'ameen tsayawa kawai yayi da baki a bude yana kallona kamar wadda aka dannawa pause, ya dade yana kallona sannan ya kalli jikinsa dake jike har lokacin yana mishi kaikayi, ya tuna wani kazamin kogin da ya shiga duk don ya samar mata abun da zata ci, take tsikar jikinsa ta tashi yarrr. Adaidai lokacinne kuma jirgin sojin sama ya fara shawagi a inda suke, daga kai ya yi yana kallon igiyar da aka zuraro masa har kasa da wani green light da kasan jirgin ke fitarwa, igiyar ya gani sannan ya juyo ya ganni tsawon minti daya, sai na ga ya juya ya nufi igiyar, da sauri na rumtse idanuna.
"Shi ke nan ya tafi ya barni" zuciyata ta fada wasu hawaye masu zafi suka surnano daga kwarmin idanuna...!
Kamar a mafarki na ji an yi sama dani, a firgice na bude idanuna na sauke su a kansa hannunsa dake dauke da rauni rike da saman doguwar igiyar sai digar jini yake, daya hannun kuma yana rike dani gam-gam kamar wadda ya rike yar tsana waist na shi daure cikin dan circle din da a kaiwa igiyar. A hankali na daura kaina saman faffadan kirjinsa na kwantar ina lumshe idanu dan bani da wani zabin da ya fi hakan sakamakon juyawa da kaina ke yi. Taune lebe Al'ameen ya yi lokaci guda yana jin zugin da shoulder dinshi ke mishi. A haka muka shilla sama muka samu nasarar shiga cikin jirgin.
Da hanzari wani ya matso da niyyar karbata a hannunsa Al'amin ya yi mishi alamar ya bari, hakan ya sa shi matsawa shi kuma ya shimfideni saman wata kujera.
"Gosh! Capt kana zubar da jini fa, wani cikin jirgin ya fada hadi da surar wata akwati ya matso inda Al'amin ya zauna ya jingina kanshi jikin head na kujerar, shoulder na shi ya kama, "Kasa kasa Al'amin ya ce, "Na fitar da harsashin dake ciki" a dai-dai time da sojan ya zare daurin da yayi wa wajen.
"But Capt why ba kayi dressing na wajen ba? duba kaga yadda ya yi zurfi? Ya fada yana kokarin gyara wajen sannan ya fara dinkewa, lips nashi na kasa ya kama da hakora yana cizawa kamar zai hudasu tsabar zafin da yake ji yana ratsashi, ta gefen ido yake hangota kwance inda ya ijjiyeta tamkar gawa, shi da yake soja ma yanajin wannan zafin ya itakuma.?
Tsabar radadi bayajin labarin yadda jirgin ya dawo jiya ya yi ta neman su da daya sojan yake bashi," Sai yau mukayi amfani da agogon dake hannun ka muka gano inda kuke capt." Ya fada yana ci gaba da aikinsa. Jin Al'ameen bai ce komai ba ya sa shi jan bakinshi ya bame a zatonshi miskilancin nashi ne ya motsa.
Ko da a ka gama tashi yayi ya nufi yarinyar Al'ameen ya bude jajayen idanunshi da suka kada sosai ya ce, " Wunti inject her before, bazata iya jurewa ba" gyada kai wanda aka kira da Wunti ya yi ya fara hada allura, sai da a kayi allurar sannan Al'ameen ya maida kanshi ya kwanta yana rufe idanu.
Na ga lokacin da yake hada allura, duk tsoron na da Allura amma bani da karfin tashi inaji ina gani ya soka allurar a jikina, yana zarewa kuwa ban dauki lokaci ba bacci yayi awon gaba dani. Nan ya samu dama ya fara dinke hannuna bai dauki lokaci ba dan nawa bai kai girman na Al'ameen ba. duk wannan bidirin da ake yi jirgin yana ta falfala gudu a sararin samaniya har muka iso babban barikin sojojin dake birnin Maiduguri. Direct asibitin cikin barikin a ka wuce damu, duk yadda aka so rike Al'ameen yaki yadda dole suka barshi ya koma cikin barrack din bayan ya damka ni dake baccin wahala a hannun Dr wunti a na min karin ruwa.
Throughout ranar a gadon asibiti na yi shi kwance, ruwa leda biyar aka kara min sannan na dawo hayyacina na fara tantance baki da fari!.
A hankali na bude idanuna da nake jin su tamkar itaciyar da ta kafa rassa, na sauke bisa ceiling dake ward din, abubuwan da suka faru ne suka fara dawowa cikin kwakwalwata bit by bit, na zabura na mike da karfi wanda ya haddasawa canula dake makale hannuna fita kana karfen da aka makala drip din a kai ya gangara gami da kifuwa a gefe, "Subhanallah, meke faruwa nan?" Cewar dr wunti dai-dai shigowarsa kenan tare da Aminullahi da ya yi wanka yana sanye da armless riga saboda raunin dake jikinsa da wando three quarter kalar na sojoji, ya yi wani fayau dashi sai karan hanci da matsakaitan idanunshi da suka kara fitowa".
A haukace na dirko na iso gabanshi, "Maahh, ina mamata ta ke, ina ka kai mini ita," duk na birkice. shafa fuska Al'ameen ya yi yana kallon dr ya ce, "A kan matar da kake sanar min yanzu ta ke magana" Da sauri dr Wunti ya dago ya kalleni duba na tausayawa da ya sanya na ji kafafuna suna rawa da kokarin gaza daukata. " ehh,e,,ehhhh matar, ita mamatace ina take ku kaini wajen ta".
Na fada da kyar dan fat fat fat kirjina ke bugawa.
"Ohk zamu kai ki wajenta blacky, amma yanzu kam you need rest, akwai bukatar ki huta sannan ki yi wanka kici abinc..."
"A'a, banaso duka, ni dai Maaahh ita na ke son gani, ku kai ni wajenta, zan huta a can". Na fada ina kuka sosai.
Juyowa ya yi ya kalli Al'ameen kallon ka bani mafita,. da kai Al'amin ya mishi magana hakan yasa shi fadin ohk muje to sukayi gaba ina binsu a baya, yayin da kafafuna ke hardewa kirjina kamar zai fado kasa.
Bakin wata faffadar kofa naga mun dosa kafun Dr wunti ya ja ya tsaya sakamakon karar da wayarshi tayi, ya daga gami da karawa a kunne," Yes Sir." Ya fada yana kamewa a wajen. Sai ya juyo ya kalle mu yace, "Capt ku karasa kawai oga yana kirana right now, ka duba no 15". Ya juya da sassarfa ya bar wajen ba tare da ya bari Al'ameen ya ce komai ba.
Gaba yayi ina bin shi a baya har cikin wani daki da na gaza fahimtar menene a wajen bayan masu tsaron filin sun bude mana kofa. Na dai ji gudun zuciyata yana karuwa naga filine fetal a wajen sai wasu lokoki dake manne jikin gini da suka cika dakin, 'Mutuary' na ga an rubuta jikin wani allo ban gama tantance abun da hakan ke nufi ba naga ya janyo loka mai dauke da no 15 a jiki, sai ga wani abu mai kama da gado ya fito Maahh tana kwance a ciki kamar ka kirata ta amsa fuskarta sai walkiya yake, sai naga kamar tana yimin murmushi.
Murmushin na yi nima idanuna suna cika da hawaye na nufeta, "Maahh ina ta kewan ki,ko bacci bana iyawa, ashe ke kina nan kina baccinki kin manta dani". Na fada ina turo baki da nufar inda take. "Maahh, ki tashi ina yaronmu, ki tashi ki bani yaronmu, na san kin mishi wanka shima yana bacci ko?"
Al'ameen na tsaye gefe ya harde hannu a kirji yana kallonta with mixed expression, seriously yana son hanata da yimata bayanin Maahh is gone, gone forever, but he actually don't know where to start, and haka kawai ya ji gabansa yana bugawa dan haka ya tsaya kawai bakinshi kamar an sanya sufagulu.
"Bata min magana"! Na fada ina kallonshi jikina na rawa. na kuma mai da kaina inda take ina ambatar sunanta wannan karon da karfi-karfi.
" Ya haka Capt? Ya zaka barta a kan gawa kamar haka?" Cewar Dr wunti yana karasowa wajen su. Sake hannu Al'ameen ya yi yana watsasu gefe da dage kafada, "I don't know what to do Wunti, that's why".
"Mtssww you have to be change Capt, wannan behaviour din naka yana bukatar canji" ya fada yana nufo ni da na yi mutuwar tsaye ba tare da sun an kare ba, tun da Dr wunti ya furta Kalmar gawa na ji kamar jijiyar da ta sada ganina zuwa kwakwalwata ta tsinke, take na fara ganin komai na dakin yana wal wal wal kamar spark na wutar nefa, kalmar gawar da suka ambata na ke ta kokarin tuna mecece, shin wacce yarece ma tukunna.
"Gawa"
zuciyata ta kara tunamin. Wani irin ihu na zabga da na yi imanin cewa ya karade illahirin asibitin da kewayenshi, kamar wacce a ka ja da magnet na ganni a gabansa, hannunshi na kamo cikin fitar hayyaci.
"Maahh, ka taimake ni ka tayar da ita ka min rai ka ce ta tashi koma ina ne mu tafi tare, help me I have only her in this dunya, ita kadai na ke dashi babu kowa kuma! Maahh kar ki tafi, ya zan yi idan kika barni!? Da waye zaki barni? mutuwa me yasa baki daukeni ki ka bar min Maahh ba?"!!! Na fada a hankali muryata na shigewa ciki na kai durkushe kan kafafuna, na daura tafin hannuna duka biyu a bude a kasa kana na daura kaina bisa hannun kamar wacce ta yi sujjada.
Dage kai Al'ameen ya yi sama, a duniya babu abun da yake mugun bashi tausayi kamar kukan mace, har rige rigen matsowa suke tsakaninshi da Dr ganin na durkushe ban dago ba, " Ke" ya fada yana kai hannunsa saman kafadata. Da hanzari suka matsa dukkansu ganin na zube a wajen warwas babu alamun numfashi a tattare dani.
Da azama ya dagoni ya rataya a kafada, "No Capt kawota kanada ciwo a jikinka," Ba lokacin wannan bane wunti mu wuce emergency da wuri kar ta samu paralysis. duk yadda Dr ya so karbarta Al'amin ya ki haka suka wuce emergency da hanzari wani karamin soja ya turo gadon daukar marasa lafiya ya kwantar da ita aka wuce dakin taimakon gaggawa, likitoci uku ciki harda Al'ameen ne suka rufu akan Fanne da numfashi ya kaura daga gangar jikinta.......