Page 30
*SANADIN HIJIRA*
BY
Ummu Fadeela
Chapter 30....
***
Sosai suka dukufa wajen ganin sun ceto rayuwata amma abun ya ci tura, bayan shudewar awa daya da mintuna ashirin da biyar suna kokarin su ko wanne daga cikin likitocin ya gwada baje kolin basirarsa amma babu numfashi babu alamun shi a tare da fanne, gabadaya sun fitar da rai da rayuwata dan haka duk suka fara ja da baya suna cire facemask dake rufe a fuskarsu.
A hankali Al'ameen ya zare nashi facemask din, idanunsa tarwai a kan fuskarta, duk na cin mutum bai isa gane expression dake fuskarsa ba, bedsheet da ke gadon ya janyo ya rufe mata har saman fuskarta da shi bai kara yadda ya ga inda take ba walking slowly ya nufi kofar fita.
Da kallo sauran dr 's din suka bishi. Cak ya tsaya kafarshi daya a waje daya a ciki sakamakon karar machines da aka jonawa Fanne da suka ji ya fara reading din din din din din. Kusan a guje dukkansu suka koma kanta, harda Al'amin din ya ya ye bedsheet din da hanzari aka mayar da oxygen tube da aka zare suka fara aikinsu gadan-gadan cike da farin ciki dan tuni sun fitar da rai da ita dama.
Sai da suka kara shafe wasu mintocin masu yawa sannan akayi nasarar zakulo numfashinta sai dai she's still unconscious. Ruwa suka daura mata again kana aka barta under control na support machines.
Har zuwa dare Fanne bata a hayyacinta numfashine kawai ya bambantata da matacciya, a darenne kuma Al'ameen zai wuce Abuja da sojojin su da suka samu manyan raunuka da wadanda suka mutu, luckily Musty bai mutu ba amma ya samu raunuka sosai dan har lokacin baya gane wadda ke kanshi.
Dakin da aka kwantar da Fanne ya shiga, ya dan dade tsaye kanta hannayensa harde saman kirjinsa. Karamin takarda ya yanka ya rubuta
"Accept your faith, and Be a good Muslimah".
Nannade pepan ya yi ya daga filon da take kwance a kai ya sanya da sassarfa ya fita daga dakin ya nufi inda jirgin da zai tashi dasu yake.
"How about your patient Capt? Ban ji ka ce komai a kanta ba"
"Tana karkashin kulawarka" iya abun da ya fada ke nan ya haye jirgin ya bar dr wunti da sakakken baki, girgiza kai ya yi a ranshi ya ce, 'mai hali dai bai fasawa.'
Yana tsaye wajen har jirginnasu ya lula sararin samaniya sannan suka koma cikin barikin.
*Abuja*
Kai tsaye a harabar babban barikin sojin jirgin ya tsaya a ka fara fito da jama'ar dake ciki ana wucewa da su cikin asibiti direct. Kusan shi ne karshen fitowa, yana sauka MG ya matso sosai ya kama hannayensa "we are proud of you Capt". Ya fada da dan murmushi, duk da an yiwa sojojinsu rauni sosai amma gabadaya social media da sauran kafafen labarai sun dauka labarin nasarar da sojoji sukayi na murkushe yan ta'addan.
"No sir, Musty, Musty ne ya cancanci duk wata ya ba wa da karramawa, ba dan shi ba da har yanzu muna can. Thou yanzunma bawai an kai kololuwar nasara ba ne, dan yaran nan suna nan kamar kasa I wonder ina ake samosu haka, and ina suke samun muggan makamai irin haka?".
Haka ne Capt," cewar Mg, ya ci gaba da cewa, "lamarin nan fa akwai lauje cikin nadi just stay quite, mun shirya tafiyar wasu runduna su karbeku before"
A barikin Al'amin ya yi spending night din suna ta kai kawo tsakanin dakunan majinyatan shi mancewa yake da yana da rauni a kafadarsa sai idan ya dan fama ciwon.
Washegari karfe bakwai na safe a bakin tangamemen get na shiga gidansu ya sameshi, horn kofur din dake driving na shi ya danna mai gadi ya fito da hanzari ya bude mashi hadi da rusunawa yana kwasar gaisuwa. Hannu kawai Al'ameen dake kishingide bayan motar ya iya daga mi shi.
Cikin jerin motocin dake zube parking space ya tsaya kana ya fito da sauri ya bude bayan motar yana komawa gefe ya saluting mishi. Shudewar minti daya sannan ya zuro kafafunsa kasa slowly yake takawa zuwa entrance na gidan.
A gigice ta mike sakamakon daka mata dundu da ta yi a gadon baya. duk ta fige ta fita a hayyacinta sai idanu kwala-kwala kawai ya rage a fuskar, ta yi wani irin baki na masifa har ma fiye da yadda yake a baya kafin ta fara bilichin, ga wasu kuraje buka-buka da suka kara yiwa fuskar tata mamaya. Tana mutsuke idanu dan baccine ya dauketa wadda rabon da ta samu baccin tun ranar da Sojanta ya sa kafa ya tafi Borno.
"Me haka Saudat?" Ta yi tambayar kasa-kasa kamar ba Badariya ba duk ta yi sanyi..."Kya tambayeni me haka mana Small Mom, tun da yaron can ya sa kafa ya bar garin nan shikenan kika firgice kika rude, kika hanawa kan ki da ni nutsuwar zuciya da ta gangar jiki eyeee, bakya kula dani da sauran damuwowina" cewar Saudat tana kaiwa zaune kusa da Badar ganin gabadaya ta bata attention dinta tana jin abin da take cewa, "Yanzu kina kyauta min kenan Sweetheart? Kinsan bana jin dadin rayuwa bake a kusa dani, ta kuma fada tana shafo fuskar Badar da jikinta ya fara yin sanyi. Har Saudat ta fara sakin jiki, zarafff Badar ta mike tana nuna kofa har wani kakkarwa take, da rawar baki ta ce, "Sojana! Sojana kamshinsa nake ji, ta so kiji Saudat wallahi kamshinsa nake ji."
Wani irin takaici ne ya mamaye zuciyar Saudat a lokaci daya cikin harzuka ta ce, "Sai ki tafi can Borno ki gano sojannaki ai a na nuna miki Annabi kina rumtse idanu..." Ba ta jira karshen maganar ba ta ruga a guje ta kama handle na kofar tana budewa.
A tare zuciyar Badar da Ummah da kuma Abeey wadda suke saukowa daga saman Abeey din ya bada sautin dam damm hango Al'amin a tsakiyar palon kasa yana tsaye ki kam da karewa palon kallo. Har wani karkacewa Ummah ta yi hadi da take kasan babbar rigar Abeey da ya shirya tsaff dan halartar wani taro saura kadan ya fadi kasa ya yi nasarar kama rails dake wajen.
"Sojannaaaaa!!!" Ta fada ta deba da wani irin gudu kamar ba Mace ba ta nufi Al'ameen a tamanin tana iso inda yake ta durkushe bisa kafafunta kamar zatayi sujjada ta kama kafar Al'ameen ta kifa kanta bisa tana sakin wani irin kuka.
Bai ce komai ba kallonta kawai yake kamar sabon mutum, isowar Umma da Abeey wajen ne ya sashi motsawa Ummah ta kamo kafadunta, "Ta shi Badariya yau dai zamu samu salama a gidan nan ga Soja ga Badar!" Ta fada with so much excited. "Dan albarka yanzu kake tafe, kai mun godewa Allah da ya dawar mana da kai lafiya, kafin yau ai gidan nan yadda kasan mutuwa akayi".
Barka dai ya fada yana kallon Abeey da ya tunkaroshi fuskarshi kamar gonar auduga yana isowa bai yi wata-wata ba ya rungumeshi kam-kam kamar zai maidashi cikin cikinsa. "Alhamdulillah Aminullahi, Alhamdulillah Aminullahi," shi ne kawai Abeey ke maimaitawa har abun na shi ya fara zama out-of-control.
*Maiduguri*
A hankali na bude idanuna, kamar wacce aka cikara na mike ,amma sai naji wani abu kamar igiya yana bina ga kuma bakina da naji a daure, hannu nasa na janye injine dake taimako wajen fita da shakar numfashi hannuna na ji a daure shima duba na nakai wajen ban ga komai ba dan haka nasa daya hannun na finciki inda nake jin yana daure, take canula dake jikin ya fita wajen ya fara digar jini dis dis dis. Na mike bana gani sosai amma wani gefe na kwakwalwata na bani cewa yanzu din darene, kofa na laluba na fita ina tafiya kafata babu takalma, gashina a waje rigata tun waccan ta yi butu-butu a kallon farko zaka tabbatarwa kan ka hankali ya yi bankwana da kwakwalwata.
Ban san ina nake jefa kafata ba ina dai tafiya ne kawai amma empty brain nake, babu abu guda daya da nake iya tunawa, komai ya goge a kaina, har na yi nasarar fita daga barikin amma babu wadda ya yi min magana kamar wadanda aka shafe ganinsu daga gareni.
Tafiya kawai nake a gefen babban titin ba tare da nasan in da nake jefa kafata ba, ga motoci tsilli-tsilli suna wucewa kasancewar dare ya fara nisa, ina tafiya ina rangaji kamar wacce ta shawu ta yi mankas, na yi tafiya ta akallah sa'a guda da rabi, zuwa lokacin dare ya tsala kafafu sun dauke, ababen hawa sun daina zirga-zirga.... Bakin wani tangamemen ginin makarantar gwamnati na tsaya ina maida numfashi ba tare da nasan ina ne ba, na dai samu kaina da tsayuwa a wajen ina shaka da mayar da numfashi sama sama, tun ina kallon waje guda har bacci ya yi galaba a kaina na bingire nan wajen...
Hayaniyar da nake ji sama-sama a kaina ya sanya ni bude idanu, hannu na sanya ina kare idanuna da hasken rana ya dallareni dal.
"Mahaukaciya yar machukule!, mahaukaciya machukule!, mahaukaciya yar machukule!."sautin yaran dake zagaye dani basu da iyaka ya dinga ratsa dodon kunnuwata. Da kyar na iya mikewa zaune ina bin wajen da idanu, tamkar kasuwa haka wajen yake cike makil da jama'a sai hada hada ake yi. Wasu na suyar kosai, wasu suna saida koko gefe kuma babban teburin mai shayi ne, ga masu suyar waina. Na dawar da dubana gareni, kwance nake a kasa jikina yayi futu-futu kai na babu dankwali kafata babu takalmi bani da bambanci da mahaukaciya.
"Mahaukaciya yar machukule" Muryar dandazon yaran ya kuma dakar dodon kunnuwata, hakan ya haddasa mini dagowa ina binsu da kallo daya bayan daya kamar mai son fahimtar abun da suke cewa.
"Shegun yara yan kwal uba masu neman tada zaune tsaye,duk ku bar wajen nan kafin tayo kan ku a rasa mai kwatar ku yan bantan uba kai". Cewar Uwa wacce masifa da bala'inta ya dawo sabo fil tun bayan da 'aka bata matsayin shugabar mata yan gudun hijira na sansanin da suka samu mafaka tun isowarsu Maiduguri, tana ratso dandazon yaran tana korasu, sake baki tayi tana kallon Fanne dake zaune wanwar a kasa sai binsu da idanu take yi.
Duk da yadda gaban Uwa ya yanke ya fadi hakan bai hana ta matsowa kusa dani ba tana kare min kallo kafin ta daddage iya karfinta ta kwala kiran " Yaganah".
Yaganah dake tsaye wajen mai suyar waina ta tako kamar bulugari ta ratso dandazon jama'ar zuwa gaban Uwa...zaro ido tayi ta ce, "Fanne?"
"Yauwa yar albarka kema kin ga abun da na gani ke nan?" Fadin Uwa tana kara kusantoni da kyau. kallon su kawai na ke yi har Yaganah ta kamo hannuna Uwa tana ta jaraba da zagin yaran dake wajen ta uwa ta uba. Cikin babban makarantar muka shiga dake cike makil da yan gudun hijira inda suka samu mafaka cikin azuzuwan dalibai. Har cikin daya daga ajin Yaganah ta kaini Uwa na biye da mu a baya a ranta tana kissima dalilin da ya sa ta daukeni.
Yawancin yan gidanmu duka a cikin wannan ajin suke gwamutse manya da yara, babu komai sai tabarma da sauran tarkacen bargo da botikai wadanda red cross suka raba musu. Dukkansu kaina sukayo suna kallona kowa yana min magana, nidai idanu kawai na ke binsu da shi, ba dan banajin abun da suke fadi ba amma bakina ya kasa furta komai.
Mun shiga uku, Uwani ko gamo yarinyar nan ta yi ne cikin dajin,?" Cewar iya. Alokacin Amma ta shigo kamar warce a ka hankado.
"Fanne? ina Fanner take? Fanne Aminatu faa, ina Aminatu?". Cewar Ammah tana zama kusa dani ta kama hannayena duka biyu, duk idanu suka zuba min kowa yana jiran jin me zance..."
Aminatu?" Na tambaya a zahiri karon farko. Ehh, ina Maahh din ki? ina kika barta?" Ammah ta kuma fada.
"Maahh,! ina maahh ina kika barta?". Na maimata tambayar da ta mini ina kallonta, gabadaya yan dakin suka zaro idanu suna rufe baki a tare, "shikenan ta tabbata" cewar Uwa tana watsa hannu gefe...
*****
Abeey ya dau lokaci yana rike da Al'ameen sai godiyar Allah ya ke yi a zahiri jikinsa yana kakkarwa, sai da Ummah ta janye shi tana nuna mishi kafadar Al'ameen din dake daure da bandeji tukunna. Hannunsa ya kamo ya ce, "Aminullahi abubuwa sun yi mana yawa a dan tsukin nan, labaran da suke zuwar mana ba masu dadi bane, ga jikin Ummienka ya kuma rikicewa lallai lokaci yayi da zaka bar wannan aikin ka dawo gare mu Aminullahi muna tsananin bukatar ka, shi kaninka banda shiririta babu abun da ya sanya a gaba, ga Yar uwarka itama zaman auren ma ya gagareta" ya karishe fada idanunsa kamar zasu fado yana kallon Al'ameen da jiran jin abun da zai fadi.
Kasa ya yi da kai yace, "Amini afuwa Abeey!"
Wani irin boyayyen ajiyar zuciya Abeey ya sauke har saida suka dago dukkansu suka kalleshi, daburcewa ya yi yana janyo shi da fadin, " muje kaga yadda jikin Safeenatu ya zama sannan mu san what next".
Kamar rakumi da akala ya janyo shi shi kuma yabi bayanshi har dakin Ummie, zubewa Badar ta yi wajen takai goshinta kasa hadi da yin sujudul shukr hawaye na sakko mata, kada kai Umma tayi ta wuce kitchen dan lamarin Badar ya daina bata mamaki yanzu sai tsoro....Finciko ta taji anyi ta baya Saudat da ke rike da ita bata direta ko ina ba sai upstair a dakinsu hadi da murza makulli, idanunta jawur dasu kamar garwashin wuta ta ce, "Ina gaf da kasawa Badar, idan na kai makura kuma komai na iya faruwa kin sani baki bukatar karin bayani, plsss do something,!" Ta fada tana rungumarta.