SANADIN HIJIRA

Page 31/32

by @ummufadeela01

*SANADIN HIJIRA**
Ummu Fadeela


31/32

*Eid Mubarak, Allah ya maimaita mana wasu shekaru masu albarka.*
Wani irin rawa jikin Al'ameen ya dauka lokacin da ya yi arba da Ummie kwance sambal kamar gawa, ga wasu kuraje da suka feso a ko wacce hudar gashi na jikinta, abun ba kyan gani. Da sassarfa ya karisa gareta ya kamota, luuuu ta yi baya.
"Ka ganta ko Aminullahi, babu irin kokarin da Dr. Shettima ba ya yi amma jikin Safeenatu sai kara gaba yake tamkar wutar daji."
Ciccibarta kawai Al'ameen ya yi ya rataya a kafada ya nufi hanyar waje yana magana, "Why Abeey, me yasa za a barta a gida da wannan yanayin?"
Zabura Abeey ya yi shi ma ya rufa mishi baya, "Aminullahi ina zaka kaita? Da ka bari mun kira Shettima ai, yana mata kokar..."
Hango shi da yayi har ya iso parking space ya sanya shi yin shiru da kara saurin takunsa. A bayan mota ya shimfideta yana kwala kiran driver da ya taso a guje, daman a shirye yake za su fita da Abeey dake da meeting karfe takwas. Bayan motar ya shiga, Abeey ya shiga gefen mai zaman banza, driver ya ja suka rankaya.
A kidime Abeey yake matuka, ya zaro wayarsa a aljihun gaban babbar rigarshi ya yi dialing lambar Dr. Shettima. "Yauwa Shettima, a gyara waje na musamman muna nan tafe da Hajiya, jikinta ya kuma rikicewa, ehh, gamu a hanyan a kimtsa komai yadda ya kamata." Kittt ya yanke wayar yana juyowa da kallon Ummie.
"Da na yi tunanin ko zamu canja mata asibiti ne daga can su bamu referral mu wuce India," Al'ameen ya fada, tashin hankalinsa ya gaza boyuwa. Da sauri Abeey ya ce, "Ba bukatar hakan don gudun komawar komai baya." A dai-dai lokacin suka iso bakin tangamemen asibitin COMFORT SPECIAL HOSPITAL. Suna shiga dama an shirya komai, gadon daukar marasa lafiya aka daura Ummie bisa hadi da tura shi emergency. A guje Al'ameen ya rufa musu baya shi ma ganin yadda ake gudu da ita, Abeey ma ya fara bin su da sassarfa.
Garamm ya yi karo da mutum har wayar dake hannunsa ta fadi kasa ta tarwatse, shi kuma ya yi baya-baya zai fadi sakamakon babbar rigarsa da ya take. Da zafin nama wanda suka yi karon ya taro shi yana tsaida shi kan kafafunsa, a lokaci guda ya tsuguna ya dauki wayar Abeey, hannunshi ya kamo ya sanya wayar a ciki yana murmushi ya ce, "Yi a hankali!"
Suman tsaye Abeey ya yi baki a sake, illahirin organs system dake jikinsa suka tsaya cak daga aikinsu na tsawon minti daya. Lokacin da ya fara dawowa hayyacinsa, a can ya hango shi wani matashi ya bude mishi bayan mota ya shige.
"Alburhan?" Ya ambata a zahiri. A tamanin Abeey da ya manta abun da ya kawo shi asibitin, ya garzaya tashi motar yana baiwa driver umarni, "Yi sauri ka bi waccan motar, kada ka kuskura ta bace maka." Ganin yadda ubangidan nashi ya rikice ne ya sanya Bala taka motar da kyau yana bin motar da Abeey ke nuna mishi, don wannan shi ne karo na biyu cikin tsukin sati daya da hakan ke faruwa; zai so ganin wani al'amari ne ya rikita Abeey haka.
Sai kai da kawowa Al'ameen yake a bakin ICU din. Tunda Dr. Shettima ya karbi Ummie aka shiga da ita bai cikin nutsuwarsa, gaba daya kwakwalwarshi ta toshe.
A ciki kuwa wayar Abeey Dr. ke ta faman kira, amma abu daya ake ta maimaita mishi, layin a kashe. Ya kira ya fi sau ashirin amma still a kashe wayar take, dan haka ya maida hankali kan Ummie da sauran Dr.s dake wajen suka fara bata taimakon gaggawa!
Abeey kuwa tun karon da suka yi da Alburhan wayar ta tashi daga aiki shi bai ma kula ba. Sosai Bala ke sharara gudu yana bin motar duk inda ta bi, har wajajen Gwagwalada ya ga motar ta shiga wani street. Bai yi kasa a gwiwa ba ya bita har jikin wani madaidacin gida aka yi parking. Da hanzari Bala ma ya taka burki ya gangara gefen hanya ya gyara tsayuwar motar.
Wani matashin saurayi ne ya fito da sauri ya bude bayan motar, dattijuwar mata da yarinyar yar shekara shida suka fito suna magana suna dariya.
Sakato Abeey da ya fito a hanzarce ya yi yana kallonsu, dai-dai kuma suna kallonshi ganin ya nufo su. Hannu saurayin ya mika mishi suka yi musabaha ya ce, "Ranka ya dade lafiya dai, ko akwai wanda kake nema ne?"
Da rawar baki Abeey ya ce, "Eh, wanda kuka fito da shi daga Comfort Hospital yanzun nan, ina yake?" Ya tambaya yana leka bayan motar to confirm. For his surprise kuwa wayam, bayan motar babu Alburhan babu dalilinshi... "Yallabai ba daga Comfort muka taso ba gaskiya, ina ga ka yi batan kai ne." Daga haka saurayin ya sa kai ya bi bayan matar da tuni ta shige gida!
Kamar mara laka a jiki haka ya juyo yana kallon Bala da idanu ya mishi tambayar "ya aka haihu a ragaya?".
"Yallabai ina ga inda hold up ya rike mu dinnan ne muka yi batan kai ganin motar iri daya ce."
Bai ce komai ba ya shiga mota kanshi na juyawa ya ce, "Mu wuce office." Shi shaff ya ma manta da sun kai Ummie asibiti, sai da ya shiga ofishinsa ya duba agogo. Saura minti biyar kacal su shiga meeting da wasu manyan excos daga America, hannu ya dunkule yana kaiwa iska naushi. "Alburhan! Alburhan!! Alburhan!!! Bayan ka mutu ma ba zaka bar zuciya da gangar jikina su huta ba neeee?" Ya fada da karfi idanunshi suna canza kala, fuskarshi tana sauyawa daga asalin farin Balaraben dattijo mai cike da kamala zuwa wani abu na daban.
(To fa! Abeey, me ke faruwa ne? Ni dai na yi nan.)
Sai bayan shudewar kusan mintuna talatin Dr. Shettima ya fito, sauran likitocin suna bin shi a baya. Da hanzari ya mike ya nufi Dr., kafin ya ce komai Shettima yana bubbuga kafadarshi, "You don't worry Soja, jikin Hajiya ya fara dawowa dai-dai, mun bata duk wata kulawa da ta dace, zaka iya shiga ka ganta." Wani irin ajiyar zuciya ya sauke kana ya nufi dakin da take.
Har yana hadawa da dan gudu-gudu Dr. Shettima ya isa ofishinsa, lambar Abeey yake ta ci gaba da gwadawa amma babu wani ci gaba dan har lokacin switch off ake sanar mishi. Hannu kawai ya goya a baya da fara zagaye a tsakiyar ofishin.
Tana kwance har lokacin sambal, numfashinta na sauka da sauri-sauri, daga inda yake yana iya jiyo zafin hucin jikinta. Kujera ya janyo ya zauna ya harde hannu yana kallonta tunaninshi yana komawa baya; lokacin da take da lafiya, irin soyayya da kaunar da take nuna mishi, bata taba hada kaunar shi da kowa ba a cikin duniyar nan, bata iya cin komai sai ya ci, bata iya bacci har sai ya dawo, wannan watarana a kan kafarta yake bacci. Yana tuna yadda ta ke kaunar aikin soja da yadda ta dage har sai da ya zama cikakken Soja, amma rana tsaka kaddara ta shigo hadi da yin kutse cikin wannan soyayyar!
Karar da wayarshi ta yi ne ya dawar da shi duniyar gaskiya. Cike da kasala da damuwa da suka yi wa rayuwarshi rubdugu ya zaro wayar da ya dauko a part nashi dake barrack, ya ma manta da ita. Isowarshi gida ga abun da ya tarar; kurawa wayar idanu ya yi ganin sunan Dr. Wunti yana yawo bisa screen din. Kamar ba zai dauka ba, tana gaf da tsinkewa ya daga gami da karawa a kunne, ya maida idanunshi ya lumshe, haka kawai yake jinsa a gajiye likis kamar ya yi tseren gudu!
Da madaukakin mamaki yake saurarenshi kafin ya samu kwarin gwiwar fadin, "Me kake son cewa Wunti?"
"Wallahi Capt., mun nemi yarinyar nan mun rasa sama ko kasa kamar wacce ta yi batan dabo tun jiya da dare. Abun mamakin kuma babu wanda ya ga ko da gilmawarta."
Shafa goshinsa ya yi sanda ya hadiyi wani kakkauran yawu sannan ya ce, "Ya batun gawar mahaifiyarta?"
"An hadata da wasu mutane hudu da aka gane danginsu yanzu aka gama janaza din su." "Nan ma Ohk," kawai Al'ameen ya fada ya kashe wayarshi yana jin wani daci a ranshi... Mutsu-mutsu Ummie ta fara saman gadon kafin ta fara wani irin gurnani mai ba da tsoro ga duk wani mahaluki dake kusa idan ya ji shi. Tana yi tana buga kanta jikin gadon hadi da kafafunta tana fizge-fizge.
A zabure Al'ameen ya yo kanta, ba karamin mamaki da tsoro abun da ta ke yi din ya ba shi ba. "Ummie, Ummie, Ummie," kawai yake ambata cikin rashin sanin abun yi. Tarwai ta bude idanunta da ta ji su tamkar bishiyar gamji da ta kafa rassa, a kan shi ta sauke su tana kallonshi dishi-dishi.
"Ummie!"
Ya kuma ambata cikin wani irin yanayi. Kamar wacce aka kwadawa guduma a tsakar kanta haka Ummie ta ji kiran da Al'ameen ya yi mata. A gefe daya kuma ta ji wani abu kamar kullin zare yana warwarewa cikin kwanyarta, zirrrr take ji daga tsakiyar kanta har cikin kanta. Hakan yasa ta hada hannu biyu ta daura bisa kanta ta matse da karfin gaske gami da tamke idanu ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un." A take abubuwan da suka faru suka dinga rububin dawowa cikin kwakwalwarta tamkar yanzu al'amarin yake gudana!
Kara birkicewa ya yi, ya kamo hannunta da ci gaba da ambatar sunanta. Wannan karon ihu ta zabga da karfin gaske ta mike da hanzari, amma rashin karfin da jikinta ke tattare da shi ya rinjayeta ta koma baya zata fadi. Da hanzari ya riketa yana ajiyeta bisa gadon, "Ummieee!"
Ya kuma fada, wannan karon jikinshi har rawa ya ke yi. "Na'am Aminullahi," ta fada can kasan makoshi tana kallonshi da jigatattun idanunta. A lokaci guda wasu irin hawaye suka fara ambaliya a fuskarta. Rufe idanu ya yi, ya mari kan shi ko zai farka daga wannan mafarkin da yake ya bude idanu; still ita din ce kwance tana kallonshi da idanun marasa lafiya.
Waige-waige ya fara yi cikin dakin yana neman Abeey ya ga abun da yake gani. Wayam babu shi babu alamarshi, sai a lokacin ya fara tuno tun shigowarsu asibitin fa bai kara ganin Abeey ba. Cike da mamaki ya kuma juyowa ya kama hannun Ummie yana tattabawa wai ko zata dake shi kamar yadda ta saba, amma sabanin tunanin shi idanunta ta mayar ta lumshe su kamar mai bacci...
Safa da marwa kawai Abeey yake cikin makeken office nashi. Dammm gabanshi ya yanke ya fadi da masifar karfi tuna cewa sun kai Safeenatu asibiti. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un," ya ambata lokacin da ya daga wayarshi ya ganta a rufe. A rude ya bude kofa ya fice da sauri, bai saurari sakatariyarshi da take sanar da shi lokacin meeting ya yi ba. Tsabar bai a hayyacinsa ma, mancewa ya yi da akwai elevator ya dinga taka bene har ya sauko kasa. Bala driver ya koma gida, dama idan ya kawo shi komawa yake sai lokacin tashi ya taho ya daukeshi, but luckily bai tafi da motar ba. Da sassarfa ya leka cikin motar ya ga akwai keys a jiki, without thinking twice ya fada motar gami da murza key ya bar cikin kamfanin a guje, karon farko bayan shekaru masu yawa zai yi driving da kanshi!
Gudu kawai yake shararawa a kan titi tamkar shi kadai ne a kai. Kamar wanda aka bawa umarni ya ga center mirror, karaff suka hada idanu da Alburhan hakimce a bayan motar yana daga mishi hannu da wannan mugun murmushin nashi. A firgice Abeey ya juyo back seat, amma wayam babu kowa. Yana kara juyowa idanunshi ya kuma fadawa cikin na Alburhan ta center mirror, wannan karon har sunanshi ya ji yana kira, "Akhi Fadlallah".
Wani wawan birki ya ja a tsakiyar titin, ji kake gwarammmm! Ya bugi motar dake gabanshi yayinda wacce take bayanshi kuma ta bugi bayan tashi motar. Take wajen ya rikice gami da hada kwarya-kwaryan dandazo; abun ya faru ne suddenly.
Tsawon minti daya, wannan Abeey ya dago daga buguwar da kanshi ya yi kan sitiyari yana kallon jama'ar dake wajen bibbiyu. A haukace ya ja motar ya bata wuta, sai matsawa wadanda suka taru don kawo agaji suka yi suna ta zaginshi, wasu na fadin, "Irin tsaffin mashayan nan ne, yanzu haka ma watakila a buge yake."
Direct ward da ya san ake kwantar da iyalinsa ya wuce bayan ya shigo asibiti. A hankali ya tura dakin ya shigo da sallama a bakinshi yana kokarin dai-dai ta nutsuwarshi. Karaff idanunshi suka fada cikin na Ummie dake kwance lamo tana jin yadda Al'ameen ke rike da hannunta ya kasa cewa ko uffan. Wani irin zillo zuciyar shi ta yi yana kuma kallonta, bai yi aune ba Al'ameen ya zo da wani irin sauri ya rungumeshi yana wani irin farin ciki, "Abeey Ummie, Ummiena, Ummiena ta warke!"
Galala Abeey ya saki baki yana kallonshi, kanshi ya ji yana juyawa. Kafin ya samu karfin gwiwar cewa wani abu, kawai ya ga Ummie a gabansu tana zare idanu tana tangadi saboda rashin kuzari. "FADLALLAH!" Ta kira sunanshi ciki-ciki dan muryarta bata fita sosai. "Fadlallah ina yake, ina yake na ce, me..." Sai kuma jikinta ya fara rawa. Al'ameen bai ji me take fada ba, amma tsaff Abeey ya ji ta kuma ya fahimci abun da tace daga motsin bakinta.
"Aminullahi yi hanzari kirawo likita, kira likita da sauri jikinta na rawa."
Ficewa Al'ameen ya yi, Ummie ta kuma nufo Abeey, "Me kuka aikata mishi na ce?" Ta kuma fada, wannan karon da dan karfi. Dummm gaban Abeey ya yanke ya fadi. "Ta warke, wallahi ta warke! Hosni zo ka gani ta samu lafiya, shikenan ta samu lafiya," haka kawai yake fada. Lokaci daya idanunshi suka sauka kan karfen da ake daura drip da shi, bai tsaya wani tunani ba ya nufi karfen da gudu ya dauka. Kafin Ummie ta yi wani yunkuri, ya rotsa mata karfen a tsakiyar kanta, ya kuma rotsawa a keyarta. Take duniyar ta fara juyamata, ta fara ganin sama yana komawa kasa, kasa na komawa sama, diffff ganinta ya dauke, ta fadi a kasa wanwar...