SANADIN HIJIRA

Page 33/34

by @ummufadeela01

*SANADIN HIJIRA*

*By Ummu Fadeela*

 (C... 33/34)



*REPOST*


#2023
#REDLIPS
#PINKLIPS
#BLACKLIPS

***


Baya-baya ta yi kafin ta fadi kasa, komai ya dauke mata diffff!
Saurin mayar da karfen Abeey ya yi yana huci kamar zakin da ya yi sati bai hadu da abincinshi ba. Jin takun kafa ya sa shi matsowa kusa da ita cikin hanzari yana kinkimarta hadi da rungumeta, a dai-dai lokacin Dr. Shettima da Al'ameen suka iso.
"Subhanallah, Ummie!" Ya fada yana nufarta da hanzari. Tare suka mayar da ita saman gadon. Abeey yana share zufar dake tsatstsafo mishi a goshi ya yi wa Dr. Shettima magana da idanu; gyada kai Dr. ya yi yana basarwa, ya nufi gadon da hanzari.
Da kyar Abeey ya yi kundunbalar fadin, "Shettima yi hanzari ka dubata, faduwa ta yi yanzun nan, yi hanzari na ce!"

Aune-aune da dube-dube likitan ya fara. Daga karshe ya tabbatar musu Ummie fa bata warke ba, sai ma rikicewa da abun ya yi sakamakon faduwar da ta yi. Duk yadda Al'ameen ya so daurewa kasawa ya yi, dan hakan ya tsugunna jikin gadon ya kwantar da kanshi saman cikinta yana dauke hawayen da suka taru mishi a idanu da yatsarshi.

Misalin karfe sha daya na safiya, Umma da Badar suka shigo asibitin da abun breakfast hankali a tashe, don ba su san abun da ya faru ba sai da Abeey ya kira Umma da wayar Dr. ya sanar mata. Sosai ta nuna tashin hankalinta a kan halin da Ummie ke ciki. Badar kuma yi take kamar zata mayar da Al'ameen cikin ta ganin halin da yake a ciki; da ya ki cin abinci ma kuka ta sanya mishi, dole ya taba kadan amma sam babu appetite a bakinshi.

Tsawon sati biyu Ummie ta kwashe a asibitin karkashin kulawar Dr. Shettima da Al'ameen. Hakan ya sa jikinta ya fara samun lafiya, don Aminullahi yana sanya ido sosai kan lamarinta, Shettima baya samun damar yin abun da bai dace ba. Amma hauka tana yin shi tuburan, kamar ma karuwa ya yi fiye da farko. Bayan sati biyun aka sallame su suka wuce gida. Duk yadda ya so convincing Abeey a fitar da Ummie waje ya ki, ya dage lallai sai a nan gida za a dubata.

"Banda abunka Aminullahi, ai Shettima yana kokari, mu kara bashi dama," Abeey ya fada yana kallonshi.
Bayan wata daya... Abubuwa da dama sun faru, ciki har da sanya ranar auren Al'ameen da Badariya nan da wata daya mai zuwa, dan haka ake ta shirye-shirye babu kakkautawa ta kowanne bangare, yayinda Saudat ita ma take nata shirin ganin da gaske aure Badar zata yi.
"Small Mom, yanzu da gaske aure zaki yi ki barni, bayan kinsan akwai aurena a kanki? (A'uzubillah)!" Cewar Saudat tana tsare ta da idanunsa da suka yi laushi.

"Haba sweetheart, ki daina daga hankalinki mana. Kinsan babu yadda za a yi in barki fa, dan Sojana ya ce a nan zamu zauna kafin, dan yana son ya ga yanayin jikin Ummie. Kinga kenan muna tare."
Narai-narai Saudat ta yi da idanu tana kwabe fuska, "Na san kina tarewa zaki manta da ni Badar, kawai ki hakura da auren nan mu ci gaba da zama. Babu wani bukata taki da ba zan iya biya maki ba."
"No sweetheart, ba zaki iya min ciki in haihu ba, kuma ina bukatar ganin kwai na a duniya kamar yadda kika ajiye Humaira. Lallai nima ina bukatar haihuwa, but na miki alkawari babu abun da zai sauya na daga kulawar da nake baki. Shi Sojana ma ba mazauni bane, kullum fa yana yawo tsakanin bariki da jeji fa," ta fada tana murza hannun Saudat din.
"Promise!"
"Yes, promise!" Ta fada tana dage mata gira daya.

"That's my wife," cewar Saudat tana matsota jikinta. *(Ya Allah, ka kare mu, ka kare mana zuriyar mu daga fadawa munanan ayyuka irin na mutanen Annabi Lud'u AS. Masu aikatawa kuma Ubangiji ka shiryar da su tafarki madaidaiciya domin kyawawan sunayenka tsarkaka, ka kawo mana saukin wannan al'amari da ya zamto kamar wutar daji mai ci ta kowanne bangare na duniya).*


**Maiduguri**



Rayuwa muke yi a sansanin 'yan hijirar kamar awaki, kowa ta kansa yake. Har lokacin kuma ba na uhm, ba na umm-umm, gani nan dai a zahiri kamar mutum amma babu tunani. Uwa kuwa ta kara samun lasisin mayar da ni baiwa; duk wasu ayyuka ni nake yi amma ba na magana. Sau tari na kan ji kamar an cire komai na jikina ne, sai kwarangwal kawai. Idan an bani abinci zan ci, idan an ce in yi sallah zan yi, duk abun da aka sani ina yi amma ba baki.
Muna cikin wannan halin ne wata a cikin 'yan gudun hijirar ta kwadaitawa su Uwa mu gudu zuwa Abuja; a can za a fi kula da mu matsayin 'yan gudun hijira, duk abun da gwamnati ta bayar zamu fi saurin samu. Haka ko aka yi muka tarkata muka wuce Abuja mu da yawa; wannan shi ne zaren da ya janyo ni har zuwa ga kaddarata.
Ba shakka kamar yadda suka fada, a can birnin tarayya an fi girmama mu a matsayin 'yan hijira, an fi kula da mu. Muna samun masu kawo mana ziyara daga 'yan siyasa zuwa manyan masu kudi, ba ma rasa abun da zamu ci da wajen kwana. A hankali kwanci-tashi na fara dawowa hankalina, tunanina ya fara daidaita. Ina iya bambance fari da baki. Na kan boye kaina a daki ko a wani lungu in ta kuka idan na tuna da Maahh, har sai na ji kamar zuciyata zata fashe nake hakura. Sai dai har zuwa lokacin zuciyar tawa bata yarda cewa Maahh ta tafi, ta tafi tafiya mai nisan zango irin na har abada ba; wannan ya sa ba na mata addu'ar mamata, sai dai in roki Allah ya dawo min da ita duk inda take!
"Fanne! Wai ba zaki fito bane ana jiran ki, ko sai na zo na fitar da ke ne yar banzar yarinya? Wato rufa miki asiri da na yi ina kula da ke albarkacin mijina Modu da kasa ya rufe masa idanu, shi ne kika ga gadon bacci na har zan aikeki kina min iyayi ko? Kin fito ne ko ko sai na shigo?" Uwa ta fada tana banko labulen tantinmu, ni da Yagana da Fandou da sauran 'yanmata sa'anninmu kusan goma ne a tanti daya!
Hawayen dake shatata a kumatuna na goge da bayan hannu sannan na dauki hijabina na fito.
"Kin mula kin fito kenan?" Yaganah ta tambaya tana hararata. Duk da mutuwar Ya Muhajir amma har yanzu Yaganah tana adawa da ni, hakan ya tabbatar mini da cewa kiyayyar ta gareni a jininta take kamar dai Uwa!
Ban ce mata komai ba, ita ma ta san ba zan ce din ba dama. Haka muka rankaya kasuwa don yi wa Uwa sayayya abun da ta aike mu. A cewarta na fi kama da 'yan gudun hijira idan mun je tare, an fi yi mana arhar abun da zamu saya dan na yi kalar tausayi, shi yasa take nacewa a fita da ni.
Yana zaune karkashin bishiyar shakatawa da aka kawata da kujerun zama a farfajiyar gidan, fararen kafafunshi sol daure a kan kujera daya, ya harde hannaye yana ta faman karkada 'yan makullai, idanunshi a lumshe kamar mai bacci. Amma ba bacci yake ba; ya rasa dalili these days yarinyar take yawan fado mishi a rai, yana yawan tuna incident nasu tare. "Ko tana ina yanzu?" Ya yi wa kanshi tambayar, sai kuma ya tabe baki, *as in* ina ruwana na!
Badar ce ta fito cikin wata irin shiga ta alfarma na Egyptian Abaya, sai walwali take yi, fuskar ta shar cike da farin ciki. Bayanta Hajja Titi ce, aminiyar Hajja Fanta, Umma cikin shirin fita... "Sojana! Mun fito fa!"
Idanunshi ya bude yana watsa su kanta, lokaci guda ya mike yana zuba hannunshi a aljihun trouser dinshi, ya yi gaba suka bi shi a baya. Kusan kwana biyar kenan yau, kullum sai sun fita suna hada lefen auren Badar da Sojanta, inda Umma ta wakilta aminiyarta Titi suke yawon soyayyar a tare. Tare da Badar suka shiga gaban motar, Titi kuma ta shige back seat.

A hankali muke takawa, musamman ni dan gaba daya illahirin jikina babu karfi a kafa muka tafi kasuwar.
Wajen ya samu da aka tanada musamman dan parking a cikin kasuwar. Duk suka fito Badar ta leko kanta ta gilashin motar, "Sojana zamu dan jima a ciki fa, ko dai zaka tafi ne idan mun gama in kiraka?".
"Ba bukatar hakan, kuje zan jiraku," ya fada yana kallonshi. "Ohk, thank you Sojana, I love you!" Gyada mata kai ya yi yana rufe idanu da kwantar da kanshi jikin headrest.
Sai kuma ya bude idanun da sauri tamkar wanda aka bawa umarni. Karaff ya sauke su a kanta; tana tafiya tana faman jan hijabin jikinta, she's so uncomfortable. Ta kara yin duhu, ta rame matuka, sai manyan idanu kawai suka rage a fuskarta. Ga wata da alama 'yar'uwarta ce sai magana take mata sama-sama amma bata amsa ta. Wani irin faduwa gaban Al'ameen ya yi, kamar magnet aka sanya aka janyo shi. Haka ya fito daga motar, shi kan shi bai san dalilin hakan ba. Kafin ya rufe motar ya juyo, ya nemeta sama ko kasa ya rasa. Mutanen dake cike makil wajen ana ta hada-hada ya dinga ratsawa, amma wayam babu Fanne babu labarinta. Gajiya ya yi ya dawo cikin motar ya zauna shi kadai yana ta tsaki kamar dangin tsaka. "Me ya dameka da ita Aminu?" Zuciyarshi ta yi tambayar. Wani bangare na zuciyar na ba shi amsa, "To check if she's fine."
Hajja Titi da Badar suna zaune cikin wani makeken kantin sayar da gold, an cika su da kayan refreshment. Badar sai ruwan ido take yi, dadi kamar ya kashe ta; set na gold uku Al'ameen ya ce ta zaba a cikin lefe. Da kyar ta iya zaba, ta mika debit card suka cire kudinsu sannan aka musu packaging suka fito.
Fitowarsu ya yi dai-dai da isowarmu bakin shop din. Hannuna rike da leda mai layi-layi yellow cike da kayan miya, sai faman jan hijabina nake saboda yanayin cikar halittar da nake da shi; ba na iya tafiya normal, duk sai in jini a takure. Glass na fuskarta Hajja Titi ta zare tana kare min kallo hadi da yabawa da halittata, tana kiyasta makudan kudin da zasu samu idan sun yi safarar wannan yarinyar.
"Ohh ya Salam, kinga na yi wani babban mantuwa Badariya. Kawai ki karasa ku koma gida da shi kar ya gaji da jiranmu, kinsan babu dadi. Ala bashshi idan na kammala abun da zan yi na biyo dan sahu," cewar Titi tana mikawa Badar abun da ke hannunta.
"Amma Umma..."
"Shhhht," Titi ta fada tana daura yatsarta bisa lebe, still idanunta zube fes kan su Fanne dan kar su bace wa ganin ta. "Maza jeki, yanzu ina tahowa." Sai da ta tabbatar ta tafi sannan ta fara biyo mu da sassarfa tana zaro wayarta daga cikin jaka. A dai-dai lokacin muka tare abun hawa, ta karaso da hanzari ita ma ta shige sahun muka fara tafiya.
"Hajiya ina kika nufa?" Mai adaidaita sahun ya tambaya.
"Yaro ka fara sauke 'yan matan tukunna."
Haka muka dinga sharara gudu har bakin kofar shiga sansaninmu. Wani irin dadi ne ya mamaye zuciyar Titi ganin 'yan gudun hijira ne, komai zai musu a saukake.
Sauka ta yi tana mikawa yaron sabon dubu daya. Da murmushi take kallon Yaganah dake mika kudin, ta ce, "Bashshi yarinya, kwa sai alawa da shi, na biya muku."
Duk juyowa muka yi jin abun da ta fada. Yaganah ta zube a kasa, "Mun gode Hajiya, mun gode Allah ya kara arziki."
"Tashi abunki babu komai, hala ku 'yan gudun hijira ne?"
"Ehh, daga Borno muka fito, an kashe mana iyaye..." Nan Yaganah ta dinga bawa Titi labari, ita kuma ta nutsu sai sauraronta take. Kafin ta ce, "Ita 'yar'uwar taki bata magana ne?"
"Wa? Wai Fanne? Tana yi mana, ta dan samu..." Shiru ta yi ta hango ni can bakin gate ina kokarin shigewa ciki. Wani irin dogon tsaki Yaganah ta ja, har sai da Titi ta yi dariya. "Da alama ta gaji da tsayuwar ce, maza bita kar a nemeki idan ta shiga ita kadai." Sabuwar dubu daya kuma ta zaro a jakarta ta mikawa Yaganah. Hannu na rawa ta amsa tana ci gaba da kwarara mata godiya ta tafi.
Ajiyar zuciya Titi ta sauke, ta zaro wayarta tana karawa a kunne. "Hello Hajiya babban, a kan sakon da na tura miki yanzun nan, na bi bayansu kuma abun farin cikin shi ne yaran a sansanin 'yan gudun hijira suke rayuwa."
"Ohk babu matsala Titi, a bude store a kai musu ziyara, a tabbatar an dawo da yarinyar dan akwai tafiyar da za a yi nan da kwanaki biyar."
Haka kuwa aka yi washegari, sai ga babbar mota cike da kayayyaki dangin shinkafa, garin tuwo, garin danwake, mai, manja, maggi da dai sauran kayan bukata na abinci ya shigo tsakiyar farfajiyar wajen. Yuuuu illahirin jama'ar dake wajen suka fara diddikowa zuwa jikin motar. Hajja Titi ta fito sanye da facemask, bayanta wasu 'yan sanda biyar ne da suka yi hiring dan aikin!
"Kada ki damu Hajiya, duk mutanen da ke wannan waje a karkashina suke. Ni ce shugabar mata, za mu raba kayan nan cikin aminci da yardar Allah."
Hajiya Titi dai sai gyada wa Uwa kai take yi, amma a zahiri hankalinta kacokam yana kan wadda ke kwance bisa wani dan yololuwar katifa dake a cikin tantin; kallon ta kawai take kamar idanunta za su yi magana.
Wani wawan dundu Uwa ta zubawa Fanne dake bacci a gadon bayanta wanda ya sa ta mikewa babu shiri. Ta rigada ta saba da ire-iren wadannan cin zarafin daga Uwa, dan haka ko digon hawaye babu a idanunta.
"Tashi ki ba mu waje za mu yi maganar arziki, kin yi mana shame-shame a waje kamar gawar jaraba."
"Ashsha Hajiya, ki bita a hankali mana, yarinya ce ai," cewar Titi da ta kuma bina da idanunta kamar zasu fado kasa, ta daura da fadin, "Yarki ce? Na ga babu kama a tare da ku."
Yake Uwa ta yi tana sosa keya, ta ce, "Yar wajen abokiyar zamana ce da Allah ya yi wa rasuwa, rikonta ya dawo hannuna!"
"Haba ko da na ji! Yanzu sana'ar me take yi? Ai zama a irin wajajen nan babu abun yi akwai wahala, gata 'yanmata da ita."
"Ke dai Hajiya bari kawai, haka nan muke fama sai idan Allah ya taba mana zuciyarku ku masu kudin kun kawo mana taimako da shi muke dogara. Duk ba ma wannan ba, maganar rabon kayan abincin za mu yi shi ya fi muhimmanci," cewar Uwa tana dariya.
"Duk yadda kuka saba rabonku ku yi kawai, komai yana hannunki, kuma ma an zama daya ai. Kawai duk sanda na tashi kawo tallafin ke zan nema, amma maganar aikin ko sana'ar ma yana da muhimmanci duba da yadda rayuwa ta zama yanzu. Idan babu damuwa, ni zan yi wa ita diyar taki hanyar samun aiki mai gwabi. Ina sanar miki idan ta fara karbar albashi daga yanzu har kan jikokinki na biyar ba zasu san wani abu shi talauci ba, kun yi bankwana da talauci har abada."
Zaro ido Uwa ta yi tana dafe kirji, "Hajiya wani irin aiki ne haka?"
Murmushin nasara Titi ta yi ta ce, "Aiki ne irin su wanke-wanke da goge-goge a gidajen Larabawa can Saudiyya!"
"Saudiyya, Hajiya? Kina nufin dai can Makkah, Madinah garin Manzo?"
"Can fa Hajiya! Idan kin amince kawai mu tafi da ita, dan nan da kwanaki biyar za a yi tafiyar dama," ta karishe tana zaro bandir din dubu-dubu ta ajiye gaban Uwa. Wani irin zillo kirjin Uwa ya yi da ta ga damin kudin, a gefe daya kuma kunnuwanta na mata amsa kuwwa da kalmar "Saudiyya". Ina! Babu yadda za a yi Fanne ta tafi Saudi ta barta a nan cikin wahala ita da Yaganah, babu wannan maganar.
Titi ta katse mata tunaninta da fadin, "Ga wannan so-min-tabi ne. Idan ayyukan nata suka mika yadda ake so, ba kananan kudi zata ke turo maki ba!"
Jiki na rawa Uwa ta mike ta fara juyi a gaban Titi, "Dube ni da kyau Hajiya, wallahi ban wani tsufa ba, in banda ma wahalar rayuwar yau ai sharrr nake da ni wallahi dan ban taba haihuwa ba. Dube ni da kyau Hajiya, me zai hana ni ki dauke ni kawai zuwa Saudiyyar? Ina fada maki babu wani aiki da ba zan iya ba, kai in takaice maki ko su matan Larabawan sai in wanke su tsaff in tsane in goya su, to Allah na tuba me zai gagareni!"