SANADIN HIJIRA

Page 35/36

by @ummufadeela01

**SANADIN HIJIRA**


*By Ummu Fadeela 

(C... 35/36)*


Karkacewa kadan Hajja Titi ta yi, dariya na son kwace mata ta wayance da goge saman hancinta.
"Ai tabbas zaki iya Hajiya, nima zan yi farin ciki a ce kin je din, sai dai ba a nan matsalar take ba. Wato su can suna mutunta babban mutum, ba za su yarda ki yi musu aiki ba, amma idan kin amince iya yarinyar kawai zata samar maki duk abun da kike bukatar. Idan aikin ma ya karbeta ina fada maki sai dai ta gina maku tamfatsetsen gida na bugawa a jarida shafin farko ta zo ta dauke ki, kinga alheri goma da ashirin ke nan..."
Da hanzari Uwa ta katseta ta hanyar fadin, "Wa! Kin taba ganin yar kishiya da aikin alheri? Wannan sai naka ai, dan haka bari kiga yadda za a yi. Yaganah, Yaganah!!" Yaganah dake tsaye cirko-cirko gaban motar kayan ta shigo da sauri jin uwar tata tana kwala mata kira.
"Yauwa yar albarka, maza yi juyi gaban wannan matar, gabas da yamma, kudu da arewa, ta kare maki kallo lungu da sako."
Kamar yadda ta fada haka Yaganah ta yi. Muskutawa Titi ta yi tana kallon yanayin kirar Yaganah mai kama da an daurawa tabarya zani, ta ce, "Ehh, ba shakka, je ki abunki 'yanmata." Dubanta ta dawo kan Uwa ta ce, "Wannan din ma ta yi, amma sai dauka na biyu zan zo in dauke ta, yanzu dai ki bani waccan din ta fi."
Fir Uwa ta ki yarda a dauki Fanne zuwa Saudiyya; a ganinta ai wannan ma ci gaba ne ta samu, ita kuma bata kaunar duk wani ci gaba da tsatson Aminatu zai samu.
Mikewa Titi ta yi tana tabe baki ta ce, "Ni fa daman taimakonki ne zan yi ba wani abu ba, amma naga kina bata mini lokaci dan haka kinga tafiya ta." Ta sanya hannu tana daukar bandir din kudin da ta ajiye wa Uwa.
Hannu biyu ta hada ta cafko kudin, da rawar baki ta ce, "A'ah ba za a yi haka ba Hajiya, ai mun zamo daya kuma. Kawai wai dama so na yi ko ni ko Yaganah a hada mu mu tafi tare, yanzu dai koma ki zauna mu yi maganar, ai wannan arziki ba ma so ya ketara kanmu ba."
"Ke dai barshi kawai, Allah ya hadamu da alkhairi."
Da kyar da sudin goshi Uwa ta lallaba Titi ta koma ta zauna tana faman shan kamshi.
"Yauwa, kince aikin a can Saudiyya ne ko, kuma albashi mai tsoka za a ke biyanta?"
"Ehh hakane, idan kina so ma albashin nata sai ake kasa shi gida biyu, a baki rabi a nan ita kuma a bata rabi a can."
"Yawwa Hajiya, haka za a yi. Yanzu yaushe ne ma kika ce tafiyar?"
"Nan da kwana biyar ne, amma daga yau zan tafi da ita dan a fara koya mata yadda ake tsafta, kinsan Larabawan nan tsafta garesu ba kama hannun yaro."
Ina ji ina gani Uwa ta tarkata min tsommokara na ta dura a Ghana-must-go, ta hannunta ni ga Hajiya Titi wacce ban santa ba, ita ma bata santa ba, da sunan zuwa aiki Saudiyya bayan ta damki dubu darin da Titi ta zube mata. Ko da su Amma suka yi magana, Uwa ta ce musu zan ke taya Hajiyar aikace-aikace ne a gidanta nan cikin gari kuma zan ke dawowa.
Cikin wani tamfatsetsen gida na alfarma Hajja Titi ta kaini. Na samu some 'yan mata uku a can, dukkansu sa'annina ne, sai daya da zata iya fina kadan; wannan ya saka na saki jikina kadan.
Muna zaune a dakin da aka tanada dominmu. 'Yan matan suna hira ina jinsu amma ko kanzil ban ce ba. Rabia't ta ce, "Wallahi Halima, ina fada maki zage damtse zan yi in yi aiki yadda ya kamata. So nake nan da shekara daya in fara goga kafada da Dangote a fagen arziki. Ke, an ce su kudi bai damesu ba fa, har a kwandon shara zubarwa suke; in takaice maki ma duk sanda kika yi shara sai kin tara kudi, kuma wata ya kare ki ji dumus, to Allah na tuba me ya fi raina?"
"Dan Allah Rabi'a kar ki fada min?" Cewar Halima.
"Tsaya nan, ai kawai aiki zamuyi tukuru mu wuce raini idan mun dawo." Shewa suka yi a tare suna tafawa.
Kallona na mayar daya gefen inda dayar yarinyar ke zaune, ta hada kai da gwiwa sai sheshsheka take. Da alama ita ma dole ne yasa take nan a yanzu kamar dai ni. Kyakkyawace fara sol da ita, na ji su Rabi'ah suna kiranta Nawwara. Yau kwannanmu uku a gidan, kuma tunda na zo haka na sameta, kullum kanta cikin kafa tana kuka.
Hada ido Halima da Rabi'ah suka yi sannan suka kwashe da dariya suna tabe baki. Ni dai ban ce komai ba, nauyin zuciyata kawai ta isheni; tabbas yanzu na kuma yarda kuka rahama ne.
Daga labulen dakin aka yi Titi ta shigo tana kare mana kallo, sannan ta yi murmushi ta ce, "Duk ku fito, ga mai aikinku ta zo." Haka muka bita daya bayan daya har cikin wani sitting room da mai aikin ta baje kayayyakinta na gyaran jiki ciki da waje. Kwana biyu kenan yau ake mana gyaran jiki kana ake bamu wasu nau'ikan abinci dangin su madara da 'ya'yan itatuwa da wasu magunguna kala-kala; a cewarta na karin kuzari ne dan mu yi aiki a can yadda ake so.
Koda muka iso bakin kofar, cogewa na yi na ki shiga.
"Haann FANNAH, karaso mana kin tsaya daga waje," cewar Titi tana kallona da fara'a saman fuskarta.
"Ni dai a mayar da ni gida, banison aikin kuma banison wannan abun da kuke bani." Tsakani da Allah na yi maganar dan ba karamar wahala nake ci ba cikin kwana biyun nan; da azababben ciwon ciki da na mara nake kwana nake tashi, ga wani irin al'amari da nake ji yana yawo da yamutsa jinin jikina a duk sanda na sha hade-haden da suke bamu.
Wani kalar daure fuska Titi ta yi kafin ta taso zuwa gareni ta ce, "Haba Fannah, ke da muke ganin zaki fi kowa samun abun da akaje nema kuma zaki botsare tun ba'aje ko Ina ba.

"Yar matsiyata kawai?" ta fada tana fincikoni zuwa cikin dakin. Turjewa na fara yi, ban yi aune ba na ji ta kwashe ni da wani wawan mari da ya haddasa min ganin taurari suna gilmawa ta saman idanuna. Ban dawo dai-dai ba ta kuma kifa min wani marin, sannan ta jani zuwa ciki.
Tana kallon mai gyaran ta ce, "Billy, ki fara da wannan sakaryar banzar." Da birkitattun idanunta take bin sauran da kallo; duk sun yi tsuru-tsuru kamar kace kyat su arce.
"Wallahi ina buga muku warning, duk wacce ta ce zata janyo min asara ba zata ga da kyau ba. Dan cikinku babu wacce ba hannun iyayenta a zuwanta nan, idan yarinya ta yi wani gigi kuma tsaff zata bace a wannan duniyar, ko duriyarta ba za a kuma ji ba na rantse." Ta yi kwafa ta fita.
Kamar yadda ta saba, haka ta dirje mana jiki kana ta dura mana abubuwan da ta saba kwabawa ta shayar da mu. Ina ji ina gani babu yadda na iya; Uwata ta sayar da ni dan wani abun duniya kalilan da zai kare ya barta.
Tsawon kwana biyar ana abu daya. Ni kaina na san na canja ba dan kadan ba. Fatata tana a baka wuluk dinta, amma yanzu wani irin walkiya take yi da saukar ido. Sannan an saya mana sutura na alfarma, kowa akwati guda a cike.
Daren ranar da zamu tafi, kamar yadda na ji suna fada, wata hamshakiyar Hajiya ta shigo tare da Titi. Kujera ta janyo ta zauna hadi da harde kafarta, tana kallon mu daya bayan daya sannan ta shaki iska ta fesar ta ce:
"Kamar yadda kuka sani baku bukatar karin bayani mai yawa, dukkaninku neman kudi zaku fita. Dan haka ku kasance masu ladabi da biyayya da kuma aiki tukuru dan ku kai ga ci. Duk abun da aka sanya ku ku aikata banda musu, domin abun da ya kai ku ke nan; ta hakan ne kawai zaku samu abun da kuka je nema. Banda taurin kai, ina kara jadadda muku banda taurin kai! Idan kunne ya ji, jiki ya tsira."
Daga haka ta mike tana yafa gyalenta ta fice, ta bar mu cike da wasi-wasi ba tare da ta bawa kowa cikinmu 'yancin fadin abun da ke ranshi ba. Daga wannan rana muka fada rayuwa irin ta kaskantattun bayi marasa galihu. Na yi kuka har hawayena suka kafe, na yi kewar Maahh har na ji tamkar in bita; idan ba don na san girman laifin dake tattare da kisan kai ba, tabbas da na kashe kaina.
A ranar da dare aka kwashe mu zuwa airport. Sai dai sabanin abun da aka sanar da iyayenmu cewa Saudiyya za a kai mu aikatau, fasfo da biza dinmu duka na Spain ne, kana jirgin da aka sanya mu ciki direct Spain ya wuce da mu. Tun da muka shiga wannan jirgi hankalina ya tashi, na tabbata tawa ta kare, rayuwa tana ta walagigi da ni.
"Shin rayuwa, me kika tanadar min a waccan kasar da ban san kowa ba, ban san komai ba?" Na aski kaina, lokaci guda wani irin amai yana taho min. Amai na dinga kwararawa tun daga farkon tafiyar har muka iso.
Kafin mu iso kuwa, tuni jikina ya dumame da zazzafan zazzabi, hakorana sai gamuwa suke da juna gab, gab, gab. Flight attendant din ce ta zo ta kwantar da ni da fara bani taimakon gaggawa kafin aka rufe ni da bargo. Gaba gaba daya sauran tafiyar ban san ya aka kare ba.
Time da muka sauka jikina ya kara rikicewa, sai rawar sanyi nake. Hakan bai rasa nasaba da sanyin da ake kwadawa a kasar mai tafe da dusar kankara. Still a nan ma wata hamshakiyar Hajiya ce tare da 'yan rakiyarta suka amshe mu; da ka ganta kaga magajiya Uwar masu zaman kansu. Sai sannu take min kamar zata mayar da ni cikin cikinta. Muna isa masauki ta kira wani baturen likita ya zo ya duba ni; dole aka min karin ruwa da allurar bacci sannan aka kunna room heater na samu bacci.


A Nigeria kuwa, shirye-shiryen auren Al'ameen da Badar ya mika. Ta ko ina shiri ake ba kama hannun yaro, kar ma Umma ta ji labari; Uwar Amarya kuma Uwar ango.
Kallonshi ta kuma yi a karo na barkatai, "Wai Sojana, mene ne manufar tsayuwar mu a bakin kasuwa ne muna kallon masu shiga da masu fita? Kai baka ce min komai ba kuma ba wani abu zaka siya ba, ka kafe gate na kasuwa da ido kamar an ce ka kirga masu shige da fice. Duba lokaci fa yanzu, kuma akwai abubuwa masu yawa a gaban mu."
"Zaki iya fita!" ya fada ba tare da ya kalli gefen da take ba, yana ci gaba da kallon mashigar kasuwar, hoping to see her again. Amma har shudewar tsawon minti hamsin bai ganta ba, bai ga alamarta ba. Tun ranar da ya fara ganinta a nan kusan kullum sai yazo wai ko zai kuma ganinta, amma babu ita, babu alamar mai kama da ita. Tsaki ya ja yana goge sumar kan shi da hannu, ya yi wa motar key suka harba titi.
"Sojana, wai me ke faruwa ne? You look so dull these days, uhyimm, kamar dai wanda za a yi wa auren dole ba, auren soyayya ba. Ni a zatona a lokacin da al'amarin bikin nan ya tashi sai ka fi kowa farin ciki, amma yi kake yanzu fa kamar baka son auren kumaaa..." ta karashe, hawaye yana surnanowa daga idanunta.
Ta gefen ido ya ganta, a take kuma yarinyar ta kuma fado mashi a rai; yadda komai nata kuka, kuka kamar 'yar ruwa. "Ko ina take yanzu? Wani hali take ciki?"
"Goge hawayen nan, banison ganinsu," ya fada in a caring way. Da sauri ta goge. Bai kara magana ba, ita ma bata ce ba har suka iso wani hadadden event hall wanda Badar ta naci sai a can za su yi booking saboda shagulgulan bikin nasu. Iya haduwa wajen ya hadu; suka biya komai aka yi signing sannan suka dawo gida.


**SPAIN**
Kwana biyu ina jinya komai yi min ake yi, ko tari na yi wannan magajiyar matar da na ji ake kira Mummy za ta taho da gudu tana min, "Sannu, me kike so?" Haka za ta yi ta tambayata. A rana ta uku ne na warke ragas.
Nan fa Mummy ta daura daga inda su Titi suka tsaya, har ma nata shirin ya fi na su. Wasu kalolin abubuwa ake bamu na ci da sha; ni dai idan na faki ido, wuff nake shigewa bayi in zubar sannan in yi flushing nashi.
Ranar da ba zan manta ba shi ne ranar da muka cika kwana goma sha biyu a kasar. Wani dare Mummy ta zaunar da mu ta fara kora mana bayani, "Yau za ku fara fita aiki. Duk wani shiri an riga da an gama maku, zam kuke yanzu. Duka kwastomominmu ma suna nan suna jira, dan haka kowacce ta je ta yi wanka, ina shigowa da kaya yanzu."
Dukkanmu wanka muka yi kamar yadda ta ce ba tare da mun fahimci inda zancenta ya dosa ba; a zatonmu gidajen da zamu fara aikatau din ne za a kaimu.
Su Halima da Rabi'ah sai kaudi suke yi. Nawwara dai tana nan yadda take kullum cikin kuka; wani lokacin sai in ga kamar na fita juriya. Ko mene ne nata labarin? Na aski kaina yayinda nake karewa kaina kallo jikin makeken madubin dake dakin namu.
Lotion na shafa wa fatata da ta kara kwanciya sakamakon yanayin weather din kasar da kuma gyaran da ya dinga samu, ga kuma abincin da nake dan tsakura ba irin wanda na baro a gida ba. Duk jikina ya yi weak, haka nake jina kamar in ta kurma ihu.
"Ko wanne irin gida za a kaimu yanzu? Wanne irin aiki zan ke musu; wanke-wanke ko shara ko kula da yayansu?" Tambayoyin da nake jero wa kaina ke nan, lokaci guda na kai zaune bakin gadon ina dafe goshina. Ina iya jiyo hayaniyar su Halima a palo, kana ina jiyo sheshshekar Nawwara dake aikin kuka ita ma.
Shigowar Mummy rike da kaya a hannunta ne ya sani dagowa. "Yauwa, tashi maza ku sanya kaya ana jiranku." Wasu irin tsinannun kaya ta ajiye bisa gadon tana fadin, "Fannah, hanzarta ki duba wanda zai miki dai-dai a nan."
Duk iya dube-dubena ban ga kayan da zan iya sanyawa jikina a matsayin Musulma mai ganin Gabas ta gaida Ubangijinta ba. Dago gajiyayyun idanuna na yi na sauke a kanta, da yanayin sanyina na ce. "Mummy, babu kayan da zan iya sanyawa jikina a nan," na fada ina sauke gajiyayyun idanuna a kanta.
"To sannu alarammiya, dama Titi ta sanar da ni kina da taurin kai. Ni kuma ba a min wargi, banison in fitar muku da the other side of me, dan haka ki hanzarta zabar guda ki sanya kafin kiji a jikinki. Ita waccan mai kama da soyayyen kosai din dake ta aikin kuka bata bani matsala wajen sanya kaya ba sai ke?" Ta karashe tana murtuke fuska kamar bata taba dariya ba.
Sosai muka sha artabu da ita, dan ni dai na san ina cikin hayyacina ba zan iya sanya wadannan kayan ba. Daga wanda zai iya tsaya min iya cibi da mini skirt, sai wando pencil da wata riga sharashara kamar abun tatar koko, sai wata doguwar riga ita zata kai har kasa amma hannun bireziya gareta sai wata tsaga a gefe-gefe da ta tashi daga kasa har kan cinya. Hawayen idona na share, ina ganin kayan a hankali na ce, "Ba sai sun sanya mini ba, zan saka da kaina!"
"Ahto, da dai kin kyautawa kanki," cewar ta tana kada kan wasu samudawan maza biyu da ta calling da sunan su sa min kaya tunda na ki.
Ina sharar hawaye da hannu bibbiyu na dauki wandon, wani crazy pencil ne na fara kokarin sanyawa dan shi din sai ya fi sauran mutunci. Sosai ya kamani da idan na yi kwakkwaran numfashi zai iya tsagewa. Top mahadin mini skirt din na dauka na sanya; kamar yadda na yi hasashe kuwa ko cibiyata bai rufe ba, da kadan ya wuce kirjina. Rigar wandon mai kama da net na daura a saman, still na yi gaban mirror din ina karewa kaina kallo. "Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen." Gaba daya halittar jikina ya bayyana kamar balan-balan aka hura aka dasa mini a gaba da baya duka. (Kar fa ku manta, Allah ya yi wa Fanne cikar halitta irin ta manyan mata da kananan shekarunta). Motsin da na ji alamar ana shigowa ya sanya ni saurin rarumar hijabin da nake sallah dashi na matse a kirjina kam-kam, kai ka ce rayuwata ce gaba daya a wajen.
Kamar wace aka janyo ta iso gabana tana kare min kallo daga sama har kasa. "Woww Fannah, kin ganki kuwa? Duk kin kerewa sa'anninki. Ni dama jikina yana ba ni kece arzikina. Ai tunda ake kawo min 'yan mata ban taba ganin yarinya full option power steering kamar ki ba. Masha Allah, komai ya ji sai godiya. Yauwa, hanzarta ki fito duk abokan tafiyarki sun kimtsa." Ta fada tana janyo hannuna kamar ba ita ta gama yi mani muzurai dazu ba har da barazanar kawo min kattin maza su shirya ni.
Turjewa na yi tana kokarin jana bayan ta wafce hijabin ta cilla shi saman gado.
"Ba zan iya fita babu lullubi ba. Duk da kasa ya rufe idanun Babana, Maahh kuma duniya ta boye min ita, amma tarbiyarsu gareni tamkar zanen kan dutse ne."
Cakk ta tsaya daga jana da take, tana kura min idanu kafin ta ce, "Jiran minti daya, ina zuwa."
Bayan kamar minti biyu ta dawo hannunta rike da wani nylon scarf fari mai touches na sky blue kalar rigar dake jikina. Kaina ta kama bayan ta kara kwantar min da gashina baya, ta daura scarf din cike da kwarewa tana murmushi ta ce, "Lallai wannan yarinya, da ace ke fara ce ba karamar fitina zaki haddasa ba. Saukin dai baki yana boye ababe masu yawa." Hannuna ta kama ta yi gaba ina binta a baya tamkar rakumi da akala. Duk takun da na yi haka jikina ke rangaji tamkar reshen bishiyar da iskar farkon damina ke kadawa. A hankali na sanya hannuna gami da janyo harshen scarf din duka biyu na juyosu gaba ina rufe saman kirjina dasu.


A dai-dai sanda muka iso palon, aka bude main door ya shigo sanye cikin riga da wando bakake wuluk. Ya daura wata jar rigar sanyi lafcece a jikinshi, wadda ya kasance kalar boot shoe dake kafarshi. Kunnenshi daya makale da dankunne na zinare, kana da chain daure ita ma ta zinare a wuyarshi. Gashin kanshi mai tsawon gaske an yi wa kitson chuku ya daure a tsakiyar kan. Rigar sanyin ya zare yana ratayewa jikin hangar dake bakin kofar, take zanen tattoo na lion dake kwance a hannunshi ya bayyana. Cike da takun kasaita yake shigowa palon. Dago kan da zan yi, caraf idanuna suka fada cikin ash colour idanunshi da ya kafeni dasu, ko kiftawa bai yi. A tare kirjin FANNAH da JACK ya bada sautin dum-dum. A hanzari na janye idanuna daga nashi dan ba karamar tsoro suka bani ba; tunda nake ban taba ganin idanun dan Adam mai kama da na mage ba sai yau.
Sake ni Mummy ta yi tana nufar shi. 


"Barka da zuwa our Capt, ka kuwa zo a kan gaba dan yanzu nake tunaninka a daina."
Sai da ya zauna ya daura kafa daya kan daya, still idanunshi a kaina, cikin accent nashi na turawa da ni dai ban ji ba ya ce, "Wucewa na zo yi ta layin na ga bari in shigo mu gaisa, shekaranjiya ma na dawo kasar."
"Ka ko kyauta gaskiya, kuma ka zo a kan gaba dan akwai kaya kala-kala sai wanda ka zaba." Ta fada tana baza idanu a kanmu.


Sai a lokacin Jack ya dauke idanunshi daga kaina, ya fara bin su Halima da suka kafe shi da idanu tamkar sababbin mayu da kallo. Cikinsu babu wanda Jack bai burgeta ba sabanin ni, dan tsoro ya bani tabbas.
Dan tabe baki ya yi sannan ya yafito ni da hannu. Wata irin faduwar gaba na ji lokacin da Mummy ta ce, "Maza matso mana FANNAH, kin wani tsaya sandandan kamar dogarin shugaban kasa. Maza matso ga Capt din Spain gaba daya yana kiranki yarinya." Ta karashe, murna da farin ciki ya ki barin fuskarta.
Kasancewar da Hausa ta yi maganar, bai jin abun da take fada, amma ganin na fara takowa toward him ya sa shi gyara zama yana kallon yadda jikina ke rangaji. Wani deep breath ya sauke lokacin da na kai duka a gabanshi amma na ba da distance sosai. Yafitoni ya kuma yi yana nuna min kusa da kafarshi, yana motsa baki cike da aji ya yi magana, amma ban ji me ya ce ba dan turancin nashi ya min tsauri da yawa.
"Ya ce ki matso. Taho kusa mana FANNAH, ke komai sai an koya maki? Iyeee, haka ake rayuwa? 

Yauwa, dan matso," Mummy ta fada duk jikinta yana rawa kamar wace ke gaban alkali. Still ban motsa daga inda nake ba, ina nan duke kaina a kasa amma ina jin yadda idanunshi ke yawo cikin kowanne lungu na jikina.
Magana Mummy ta kuma yi, wannan karon da dan zafi-zafi ganin ban motsa ba. Da kyar na iya jan jikina zuwa kusa dashi na rakube can jikin kujera. Su Halima da Rabi'ah dai na gefe, kowacce a ranta tana ayyana da ita ce wannan hadadden gayen ya kira, "Manna, wayyo inama a kaisu aikin gidanshi."
Yunkurawa kadan ya yi, ya zari tissue paper dake zaune saman centre table dake kusa dashi. Hannunshi ya mika ya shafo fuskata, da fari kal din tissue din ya daga. Cike da mamaki yake ganin abun ganin bai lakato bakin fenti ba, dan duk zatonshi bakin fenti ta shafa a fuskartata; wannan dalilin ya sa shi kasa daina kallonta. Yunkurawa ya kuma yi zai shafo wuyata, dan tabbatarwa na yi hanzarin matsawa baya wani irin takaici yana mamaye zuciyata. Tabe baki Jack ya yi, ya koma yana gyara zamanshi mai kyau. Dariya Mummy ta yi ta ce, "Real Africans kenan. Haka wasu daga cikinmu suke, wannan true skin nata ne kuma she's very proud kasancewarta a haka."
"I see!" Ya fada yana mikewa tsaye, ya sanya hannu cikin aljihun wandonshi ya zaro dallar Amurka masu yawan gaske, ya zubesu bisa table dake gabanshi ya ce, "A bani ita ta tayani kwana!"


Wani irin wawan guda Mummy ta tsanyara, wanda ya yi dai-dai da kadawar hantar cikina; haka kawai, ba wai dan na ji me ya fada bane.
Ban gama tunani ba na ji muryar Mummy na fadin, "Fannah tashi ku wuce, lallai yarinya kakarki ta yanke saka, kin shigo turai da kafar dama." Ta kuma kallon Jack dake aikin kallona har lokacin ta ce, "Capt, ka jira a mota tana fitowa yanzu, kasan sabuwar zuwace tana bukatar lallashi." Ta fada da kalar turancinsa. Bai ce komai ba ya fita yana taku cike da izza da takama, kai da ganinshi ka san ya gama samun duniya.
Juyowa gareni ta yi ta ce cikin harshen Hausa, "Wannan ne zai tafi dake zaki fara aikinki, kuma bana son gardama. Idan kin mishi abun da ya dace, ko a gobe ma zai iya dawar dake; idan kin yi taurin kai kuwa jikinkine zai fada maki, ahto ni dai ba ruwana kuma na sanar dake."


"Amma Mummy, wannan namiji ne ai, kuma kamar ma ba musulmi ba. Aikin me zan yi wa namiji, ai addininmu ya haramta hakan!"
"Ke dai tashi yar albarka, idan kun iso kya fahimta. Ana kai ki gabas kina nufar yamma. Tashi tun kafin raina ya baci in kira maki su John su mika ki, kina ganin dai uban kudin da ya jibga a kanki kwana daya kawai." Da kyar Mummy ta iya lallabani na mike amma ji nake kamar ba ni ba, ina tafiya tamkar iska zai kadani kasa. Daga karshe da kanta ta rike hannuna bayan ta kwashe kudin da Jack ya ajiye ta dura su cikin rigar mamanta muka fito.
Tunda muka doso motar tashi ya kafe ni da idanu yana cije lebenshi na kasa, a ranshi yana ayyana anya ba surgery aka yi wa yarinyar ba; koma dai mene ne idan sun je gida zai laluba ya gano. Sai da Mummy ta bubbuga motar ya dawo hayyacinsa ya bude, ta sanya ni ciki ta ce cikin harshen turanci, "A dai bi komai a sannu dan sabuwa ce!" Bai ce mata komai ba ya rufe motar yana mata key muka bar yankin gaba daya.
Tun ranar da muka shigo kasar yau ce farko da zan fara fita, dan haka na zage ina kallon kayatuwar birnin tamkar ba a cikin duniya ba; tabbas na zaune bai ga gari ba. Na fada a raina lokaci guda ina juyowa. Karaf na kamashi yana aikin kallona, musamman kirjina ya mai da hankalinshi kacokam a kansu kamar ba driving yake ba. Kara janyo dankwalina na yi ina rufewa amma bai min ba. Daga karshe dankwalin gaba daya na kwance na lulluba kana na daura hannuna bisa kirjina na takure. Take kalle-kallen garin da nake ya fita a raina, na takure waje daya kamar mai jin sanyi; duk da dai ana kwada sanyin kam, amma cikin motar akwai na'urar dumama waje.
Kallon gefen ido ya mata ya dauke kai, har ya shigo street da zai sadaka da gidansu...